Page 8
by @legendspen
*SAKATA*❤️⚓️
🌻Stroy and written🌻
By
Sayyid writer (Legend)✍️
*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*
*(FUWA)🖋️📚*
*The Fearless Writers Team*
_Marubuta masu tsage gaskiyya_
SHAFI NA TAKWAS.
(P.08).
بسم الله الرحمن الرحيم
"Nasan kin san Mus'ab su na soyayya da Samira, to amma tun farko ba wata soyayya ba ce ta a zo a gani, dan bai taɓayi ma ta maganar aure ba. Kawai dai soyayyar tasu ta bazo ne, kowa ya sani to kwatsam su Abbanku su ka zo da maganar aure, bayan su Babban mu sunyi shawarar ba shi, sai ga wani zance ya fito. Wai Mus'ab yana dauke da wata cuta, kuma duk macen da ya aura za ta sha wahala a kan wanan cutar tashi, dan Allah ki faɗamun gaskiyya, nasan ba zaki ɓoye ba, sanan kin san Yayata ba wani kiɓa gare ta ba, kuma wallahi ba xan taɓa cewa daga bakinki na ji ba, ko a gidanmu."
Tsuru-Tsuru nayi da idano, tabbas nasan komai da ta faɗa gaskiyys ne, Amma idan na fad'a mene makoma ta, nayi munafunci, ko nayi taimako?.
"Wallahi, Salma ba zan ta ɓa cewa a bakin ki naji ba." Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke, sanan na ce."Kin san bani da alak'a kyakyawa da Mus'ab, abubuwan shi ba su shafe ni ba, kuma ba na saka kaina, domin nasaka SAKATA na kulle duk wata ƙofa da za ta had'a wani abu tsakani na da abinda ya shafi Mus'ab."
"Nasani, Amma ba zaki rasa sani wani abu a kai ba, bani zaki yiwa ba Salma, 'yar uwata da rayuwarta." Shiru nayi ina tunani a cikin zuciyata, mai zai sa na ɓoye gaskiyyar nan, mene ruwana da tonan asirinsa, idan ma na rufa mai aairi ban tsane shi ba, gwanda na to na masa asiri ko mutuwa ne ma yayi, karewa.
"Duk abinda na fad'a miki, idan har kika fad'awa wani ni ce na fad'a miki. Ubangiji ya gama ki da Masifa a rayuwa." da sauri ta gyad'a kai sanan ta ce. "Na yarda wallahi, babu wanda zaiji ke ce kika fad'amun."
"Eyh, tabbas Mus'ab na dauke da cutar da ni kaina ban ma san sunan ta ba. Amma ta danganci iyali, itace wacce ke sa mata su rame sosai. Yanzu shigowarki zaki ga ina dariya, ganin ki ne yasa na tuno yayarki shine nay dariya."
Shiru tayi, ni kam sai a lokacin na tu na ɓaranɓaramar da niya, daman ni a kwai mugun surutu, da fad'i ba a tambayeka ba."Shikenan na gode, kuma insha Allahu babu wanda zai ji maganar nan da ga bakin ki ta fito."
"Shikenan na gode." daga haka ta tashi ta fice, ni kuma na maida hankali kan abinda nake kafin ta shigo.
Haka na zauna a jin sukuku, idan wani ɓangarena zuciyata ya nuna mum abinda nayi ba dai-dai ba ne, sai wani b'arin ya ce. "Kinyi d'in, shi dai-dai yake miki."
Muna tashi daga makaranta mu ka yo gida, ni dai burinah naje nayi waya da Vida.mia nah, ya fi mun wanan zancen Mus'ab ɗin. Sai dai ina shiga ɗakin Ummanah ta aika ni ɓnagren sa, na kai mai Abinci. "Wai Ummah ke ce kike da haƙƙin ciyar da Mus'ab ne?." Wani banzan kallo ta watsa mun wanda ya sani ficewa, ni ban san me Mus'ab kewa Ummanah ba ta ke mugun son sa haka. Ɓangaren Hajja na fara zuwa, bakina ɗauke da Sallamah na shiga ɗakin na ta. Ciki-ciki ta amsa mun, ni kam bai dame ni ba. "Ya na nan?."
"Waye?." ta tambayeni, kamar ba ta san wanda nake nema ba. "Mus'ab." na faɗa a daƙile. "Allah magani maƙoci maye ni uwar su Yunusa matar Galadima, wanan yarinyar baki yi ba wallahi."
"Yana nan?." Na sake fada. "Yana ɓangaren uwarsa." Murgu ɗa baki nayi na huge, har na fita sai naji ban kyauta ba, Hajja fa ba ita ta kemun abinda Mus'ab ke mun ba, dawowa nayi na ajiye plast ɗin sanan na zo inda take na zauna."Hajja." na kira sunanta. "Na'am Uwatah." ta faɗa. "Hajja, kin ware mutum ɗaya cikin jikokin, kin nuna shi kaɗai kike so, kika damu da shi, kuma hakan kan haifar da tsana cikin zuri'ar ki." kallona tayi sanan ta ce. "Salame ai ni kin nuna mun ban isa da ke ba, kin nuna mun ke ware cikin jikokina, sabida kin dauki tsanar duniya kin ɗora a kan wanda kika kamar na damu da shi." ganin Hajja ba zata fahimci abinda na ke so ta fahimta ba, yasa na kwashe ƙafafuna nayi waje.
Ji nake kamar kar na shiga ɓangaren nasu, sabida nasan Maman ciki ba ta nan, walida kuma ba ta dawo ba, har na kai bakin ƙofa wani ɓangarena na zuciyata yace da ni."Yanzu fa yunwa yake ji, kuma yana jiran abincin nan, ke baki da hankali zaki kai masa yaci yayi maganin yunwar, kinga fa kin taimakeshi kenan."
Da sauri na ce."Allah kar kasa ko rana daya na zama mai taimako ga Mus'ab." ina fadin haka na canja hanya zuwa ɓangaren su Sadiya, a zauren su na ɓoye plast din kar a gani, nasan da zarar angani topa sai nai kai mai.
Sadiya na zaune tsakar gida na shiga, washe baki nayi ganin wayar Anty a hannunta, a fili na ce. "Antyn ba ta nan?."
"Yanzu ta je gidan Anty Nadra, wai ta kawo kayan kitchen."
"Su amarya, ni ɗan a ramun minti ɗaya nayi waya." Na faɗa, ban jira cewarta ba na dau wayar, a zuwa yanzu na haddace lambar Masrur tas a kaina, kira na danna bayan na loda lambar.
Kamar ko yashe bugu ɗaya ya ɗauka tare da faɗin."Fulani nah." Wani sanyi naji a raina, sanan na ƙara yardarwa raina Masrur soyayyar gaskiyya yake mun, domin dana kirashi yake gane nice.
"Na'am Vida mia."
"Fulani, yau nayi kewarki sosai."
"Nima haka, na si kiranka da safe amma ban sami lokaci ba har na tafi makaranta."
"Nima Fulani na tanadi morning messages ɗina, sai kuma na tuna wayar Ummanah ce." dariya nayi jin ya faɗi Ummanah kamar yadda nake faɗa."Me ya baki dariya haka?." ya tambayeni, murya cike da so da ƙauna, wanda ban san lokacin da na fara gane su ba. "Wai Ummanah, irin yadda nake faɗa." Dariyar yayi shima sanan ya ce. "To ba Ummnah ba ce." da sauri na ce. "Eyh, Ummanah ni kaɗai."
"Wallahi ban yadda ba." ya faɗa kamar zaiyi kuka, dariya yabani, ai kuwa na shiga yin abata babu ko ƙaƙautawa, sai da na gama sanan ya ce. "Dariya kike mun ko?." shima dai kamar zaiyi kukan. "Ni kai ne ka ban dariyan."
"To me nayi na baki dariya?."
"Kana magana kaman za kayi kuka."
"To ai kukan zan miki, tun da kina rabani da Ummanah."
"Ni dai ba zan baka Ummanah ba gsky." na fada, kuka har cikin raina da gaske."Shekrar ki nawa?." Naji ya tambaye ni. "Sha takwas da wata ɗaya." dariya yayi sanan ya ce. "Menen wata ɗaya?, sha takwas kawai hajiya."
"Hajiya kuma?." na tambayeshi."Eyh mana, Hajiyata, Fulanita."
"Wai nikam suna nawa ne da ni?."
"Dubu biyu." ya bani amsa, kamar yasan tambyar da zan masa kenan. "To faɗo su muji."
"Tom ki shirya."
"Na shirya ai." Na bashi amsa a matse. "Fulani."
"Ɗaya." yayi dariya sanan ya ce. "Gimbiya." na c e. "Biyu." ya k'arayin dariya, sanan ya ce. "Mai gadon zinare."
"Uku."
"ki daina lissafawa." na ce. "Thom."
"Habibiya, Hajiya, Uwar 'ya'yana, Matata, mai ɗaki na, abar ƙauna, wacce nake so." Dariyar da nayi ce ta tsayar dashi. "Mai ya baki dariya?."
Shiru nayi sanan na ce. "Duka kuma wa'yanan nawa ne?."
"Ai baki taaya na gama ba." bude baki nayi da niyar yin magana, naji sallamar Anty, sai a lokacin na tuna inda aka aiki ni, da sauri na ce."Kasan aike na akayi?."
"Ta ina zan sani baki fad'an ba, ina zaki."
"Wai Mus'ab a ka ce na kaiwa abinci, tun ɗazu."
"Maza-maza tashi ki kai ma sa." Tashi nayi ina fad'in. "idan na dawo zan kira ka, ko a wayar Ummanah ne."
Sanarwa!
Ranar litinin zamu fara posting paid pages, posting kullum, za'a fara siyar da complt ma ranar litinin, zaku iya fara payemnt tun yanzu
Payment via.
8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.
Shaidar biya.
***.
ci gaba
"Shikenan sai anjima, love you." A jiye wayar nayi tare da fitowa, kai tsaye nayi ɓangarensu.
Da sallama na shiga ɓangaren na su, sanin Walida ba ta dawo ba, kuma tun safe Maman ciki ta fita yasa na nufi ɗakin na shi, yana zaune kan kujera yana faman lallatsa da laptop ɗin shi, daman kowa yasan Mus'ab da aiki da na'ura, domin ko aikin da ya ke yi na na'ura ne. Suna da babban kamfani, wanda suke aiki da na'ura mai kwakwalwa sanan ma aika cin farin kaya ne, na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC. Ciki-ciki nayi sallama, yayi kamar bai ji ni ba, nima kuma ban sa ke maimaitawa ba.
Ajiye plast ɗin abincin nayi tare da juyawa, sai dai kiran suna na da yayi yasa ni tsayawa, ba tare da juyowa ba."Ke Salame." bantaɓa jin ya faɗi suna na ba, idan an tambayeni ma zance ba lallai yasan sunan, ashe shima salamen yake cewa, sunan da na tsana. Ƙin amsawa nayi jin Salame ya ce, na ci gaba da tafiya. "Ba da ke nake ba." ya faɗa a fusace amma cikin sanyin murya. "Ai ba suna na Salame ba." Na faɗa, zuciyata namun wani tuƙwiƙi domin ko kalma ɗaya bana ƙaunar ta haɗani dashi. "Ke ya dama wanan, ɗauki tsintsiya ki sharemun ɗaki." a wane sukwane na juyo nayi mai wani kallon. "Kana shaye-shaye ne?." Ganin ina ta kallonsa, idanu na kamar sa faɗo ƙasa tsabagen harara ne yasa shi cewa. "Ba da ke nake ba, ko baza kiyi ba ne?."
"Wallahil azeem ba zan ba." na faɗa a fili, kallo na yake cike da mamaki, rashin kunyar tawa har ta kai nan kenan?."A karo na ƙarshe, ki ɗau tsintsiya ki sharemun nan."
"Mitcheww." naja wani dogon tsaki, tare da yin gaba. Sai dai ban kai ƙofa ba naji an riƙomun hannu, ina juyowa a ka ɗauke ni da mari, wanda nima banyi wani dogon tunani ba, na ɗauke shi da nawa marin. Sai ƙarar ya bada Tas! Tas
Legends pen.
(***/ ***).
Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000.
Payment via.
8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.
Shaidar biya.
***.