AGOLA (Behind the palace walls)
Chapter 33
33........
Har ta mike Sultan ya jawo ta tana kallon sa da alamar tambaya yace "Toh me amfanin zuwan? Ki kyale su kawai" Jiddah ta dinga kallon sa sai kuma ta zauna tace "Ni wallahi na so na gwada masa mun gan sa ai" yace "Toh ke ina ruwan ki? Ba matar sa bace yanzu" Jiddah tayi dariya. Bayan sun gama da dinner yayi clearing bill din sun, su na tafiya ba wanda ke ce da dan uwansa komai, Leena ta kwace hannun ta a cikin na shi ta koma bayan sa tana ɓoye kanta a jikin shi, da mamaki ya juya yana kallonta yace "What?" ta daura yatsan ta a bakin sa alamar yayi shiru, sai kuma ta nuna masa gaban su, Sultan ne da Jiddah suke fita a wajen sai labari suke suna dariya, ya kalle su sai kuma ya mayar da kallon sa kanta shi kam ma abun dariya ya bashi, kawai ya kama hannun ta da niyar su cigaba da tafiya ta kwace hannun ta tayi baya da sauri ganin Jiddah kamar zata jiyo, ya rungume hannu ya tsaya yana kallon ikon Allah, sai da Jiddah suka bar wajan sannan ta karasa inda ya ke yace "Why are you hiding?" tace "toh kawai sai su ganmu" ya gyara tsayuwar sa yace "Okay, toh kar su ganmu, ko?" ta gyada masa kai yayi murmushi yace "Ashe da na musu magana, sai su ganmu da hujja" har suka karasa jikin motar Leena taki masa magana shima be kuma ce mata komai ba. Bayan sun isa gida Leena ta riga sa shiga ciki, dakin ta ta wuce direct ta shiga toilet tayi alwala zata shimfiɗa sallaya sai gashi shima ya shigo da alama dai alwalan yayi , ya jasu sallar isha'i bayan sun idar Sadeeq ya bar ɗakin, Leena ta wuce toilet tayi wanka, bayan ta fito kamar jiya tana cikin shafa lotion sai ga Sadeeq ya shigo, da sauri ta sunkuya kasa tace "Excuse me, kaya nake sawa" Sadeeq yayi banza da ita ya zauna bakin gadon yana danna wayan sa, ta kuma maimaitawa ko alamar kallon ta be yi ba balle tasa ran zai amsa mata ta tura masa baki ta ja kayan ta dake kan stool da gudu ta shige toilet din tasa kayan ta, bayan ta fito daga toilet taga wannan kara yana kan gadon ne gaba daya ya kishin giɗa yana danna wayan sa ta saci kallon sa sai kuma ta wuce gaban mirror ta fesa turare, tana nan tsaye jikin mirror tana wasa da fingers dinta tana so tace masa zata kwanta amma ta gagara taga ya mike suna haɗa ido ya sakar mata murmushi, ta sauke wani ajiyan zuciya ita tunanin ta fita zai yi sai taga yayi hanyar toilet dinta haka nan taji hankalin ta ya tashi tace "En.. Uncle Sadeeq, nan kuma zaka shiga?" har ya sa kafan sa a toilet sai kuma ya juyo ya fita ya wuce ɗakin sa, ta karasa ta cire hijab ɗin jikin ta ta fara gyaran gadon, to her surprise sai ta gansa ya shigo rike da towel da shower gel ɗinsa a hannun sa dayan hannun nasa kuma rike da Pajamas ɗin sa ya zuba su nan bakin gado sabar yadda Leena ta ruɗe da ganin ya sake dawowa tama manta cewa Sleepwear ne a jikin ta, mara hannu da sauri tace "Uncle Sadeeq, toilet dinka ba ruwa ne zaka yi wanka anan?" daf zai shiga kenan sai ya juya yana kallon ta yace "Kar na shiga ne?" ta rasa me zata ce sai kuma tace "em.. wai dama nan ban kunna water heater din bane so ruwan da sanyi" kallon da yake mata ne yasa ta fahimci she's half naked da sauri ta sukuna nan da nan taji hawaye ya fara zuba mata, yace "It's Okay, dama na fi so nayi da na sanyin ne" daga haka ya shiga tashi tayi da sauri ta dau hijab dinta ta saka, tana gama gyaran gadon ta suguna a kasa tana jiran ya fita sai ta kwanta, bata tashi sanin Sadeeq ya wuce tunanin ta ba sai da ta gansa ya fito a toilet daga shi sai towel dake daure a kugunsa, Ga Muscles dinsa sun fito rada raɗa abinka da me gym, bata san sanda ta kwalla ihu ba ta rufe fuskan ta da Hijab ɗin jikin ta, sau daya ya kalle ta yayi murmushi ya ɗauke kansa tana ji yayi mata amfani da perfumes ɗinta still taki ɗagowa tsoron sa ma ta fara ji, bayan ya gama shirin sa cikin Pajamas dinsa ya kashe wutan dakin ya bar dim light ya rufe musu kofa sannan a hankali ya tako ya kwanta kan gadon, Leena ta ɗauka fita yayi tana tura baki ta mike kallon kan gadon ta fara yi kamar zata yi kuka ta dauki wayan ta ta haska be san sanda ya fara dariya ba Leena tayi kamar zata yi kuka tace "Toh kuma anan zaka kwana yau?" yace "A'a ba yau kadai ba, ai dama anan zanna kwana" ya karasa maganar yadda itama tayi cikin kwaikwayon murya ta, Leena ta ɗauki pillow ta koma kasa ta kwanta bayan some minutes Sadeeq ya shammace ta ji kawai tayi ya daga ta sama tana ta kokarin sauka amma ta kasa ya ajiye ta nan saman gadon. Bayan ya fito a wanka yasa Sleepwear dinsa ya kwanta yana duba numbern da yayi ta kiran sa gani yayi da 'Heart owner' Rayyan mamakin yaushe yayi saving wani number da wannan sunan? yana shiga message yaga wannan numbern still ta masa message ko karanta contents ɗin be yi ba nan da nan ya tuna cewa ashe Layla ce tsaki yaja ya kashe wayan sa sannan yayi addu'a ya kwanta. Washe gari har karfe 11 na safe Sadeeq na aikin rarrashin Leena, amma kamar kara tunzura ta yake yi, gashi yana son ya fita babu dama, ta masa magana ma taki ko breakfast yayi ta bata hakuri ta ɗanyi amma ko kulasa bata yi, daga karshe tagumi yayi yana kallon ta cike da tausaya mata. Ammi ta fito daga dakin ta jin su Binta sun dawo tana murmushi tayi hugging ɗinsu suma hugging ɗin nata suka yi, Ammi tace "sannu kun sha hanya" Anty Mairamah tace "danma Abban nasa yace sai dai mu biyo jirgi" Anty Binta ta daura "Wallahi Ammi mutanan nan suna da kirki, baki ga yadda suka karbe mu ba, da fah cewa suka yi ba zasu karbi lefen ba dan Daddy yayi magana ne" Ammi tace "Allah sarki" tace "Ummin sa tace yanzu motar da ya bata gift ai ya zama na ta tuntuni, toh me na kawowa sai kace kuna rike da mu har yanzu" Ammi tace "Self-conscious ne, gani za su yi tayi kamar muna rike da su" tace "wallahi, shiyasa da Daddy yace kar a dawo da lefen suka yi shiru, suka ce toh gold ɗin rabon Leena ne, mu kuma aka bamu 1Mil wai musha ruwa a hanya" Ammi tayi tagumi tana jin su. Tun da garin Allah ya waye Layla take ta kiran sa be daga ba kuma har sannan bata daina damun sa ba, wani colleague dinsa ya kalle me kiran sannan ya mayar da duban sa kan Rayyan yace "Anyi faɗa da Madam kenan" Rayyan ya kalle sa sai kuma ya jawo wayan sa ya kira ta back yana fara ringing ta daga ta kashe murya tace "Haba sweetie, bayan baka kira ni ba, ina kira kuma kaki daga wayan?" yace "Look Layla, ina wajan aiki ne, so duk lokacin da nake asibiti kuma duk wani lokaci ba nawa bane, ki gane wannan" ta sake kashe masa murya tace "Haba Habibi, sai kace wanda na masa laifi? Ji yadda kake min magana mana" yace "Ki bari idan na koma gida zan kira ki" daga haka ya katse kiran ya jinginar da kansa ya lumshe ido abokin aikin nasa ya tsaya kallon sa. Bayan ya cire Wayan a kunnan sa yana kallon ta yace "Baby, Kinga wajan aiki suna nema na akan nayi resuming" bata kalle sa ba kuma bata ce masa komai ba, yayi murmushi yana leka fuskan nata yace "wai har yanzu fushi ake da Ni Leena?" still bata ce masa komai ba ya mike yace "I think gobe zaki gida ki ma Ammi sallama next tomorrow in Shaa Allah sai mu tafi Abujan tare, Jiddah ma Nasan ta kusan resuming dan itama pass ta karɓa so ba zaki ji boring ba" sai sannan tace "gida ɗaya kake da Anty Jiddahn?" ya ware ido sai kuma yace "No, ita tana Quarters ɗin su ne, ni kuma ina gida na" daga haka bata sake ce masa komai ba. Da yamma Niswa dake kwance kan 3 seater taji ana sallama amma taki amsa wa, Layla da ta gaji da sallama ta gwada buɗe kofar kawai taga a buɗe yake ta shiga ciki da sallama ganin Niswa kwance kan kujera yasa ta sake baki tana kallon ta da mamaki sai kuma tace "Shegiya dama kina kwance nake doka sallama ba zaki amsa ba?" Sai sannan Niswa ta janye wayan daga fuskar ta ta mata kallo daya sai kuma ta mike ta zauna ta cigaba da danna wayan ta Layla tace "Banga laifin ki ba, ai ba tarbiyya kuka samu ba" sai sannan Niswa ta mike tace "Toh kuma sai kawai ki fara zagi na? Ni Naji Sallamar ki ne?" Layla ta mata tsawa tace "uban ki zanci idan kika ce zaki min ƙauɗin baki anan wajan, Shegiya mara tarbiyya har Ni zaki kalli sabar idon na ki ce zaki fadawa magana?" Mummy ta fito daga dakin ta, Niswa ta wuce dakin ta fuu kamar zata tashi sama, ita tun farko ta tsana wannan Laylan, Mummy tace "Layla ashe kece ke tafe?" ta zauna akan kujera tace "Eh mummy, ina wuni" tace "Lafiya kalau" sai kuma bata sake cewa komai ba Mummy na Murmushi tace "Naji kamar magana kike da Niswa?" ta gyara zaman ta tace "Allah Mummy bata da kunya 'ƴarnan, sallama fah nake yi amma ta share Ni" Mummy tayi murmushi tace "hakuri zakiyi Layla, kanan naki ne sai a hankali" daga haka ta kwalawa me aikin su kira tana zuwa tace "ki kawo mata ruwa" daga haka ta juya, Mummy tace "Rayyan ɗin ma baya nan amma ya kusan dawowa dan lokacin zuwan sa yayi" tana murmushi tace "Ai Ni ba wajan sa nazo ba, ke nazo gaisarwa" Mummy tace "Ayyah, Toh Allah yayi albarka" tace "Amin" tun kafin ta gama rufe baki sai ga Rayyan yayi sallama tun daga bakin kofar Layla take ta kallon sa ganin yadda yayi kyau a kananun kaya shi kuma kallo ɗaya ya mata ya karasa cikin parlorn ya gaida Mummy ta amsa tana tambayar sa ya aiki yace "Alhamdulillah" Layla ta ɗan sauka daga kan cushion ɗin ta gaishe shi, yana danna wayar sa ya amsa ko kallon ta be yi ba daga haka ya wuce ciki, Layla ta fara kuka tace "Mummy ina kingani da idon ki ko? Haka fa yake min ko kallona baya son yi" Mummy da ranta yayi mugun ɓaci tace "Layla kiyi hakuri, kuma bana son Maman ku taji wannan maganar dan Allah" daga haka ta mike tace "ina zuwa" Mummy ta buɗe dakin nasa ta shiga, kana ganin ta kasan ran ta ya ɓaci Rayyan ganin ta a haka da yayi ya mike da sauri kafin yayi magana ta dakatar da shi tace "Rayyan idan har kana son farin cikin na kuma kana son gamawa da duniya lafiya toh sai ka so abinda nake so, anan wallahi muddun kace zaka cigaba da wulakanta ta ban yafe maka ba" zata fita yayi saurin shan gaban ta ya duka ya rike kafafun ta yace "Mummy me yasa kullum kike son min baki akan wasu? Kin zaba ki cigaba da kallon na ina rayuwar da ba na farin cikin ba ne? toh kiyi hakuri" taji tausayin sa har ranta amma bata son nuna masa hakan, tace ka shirya kai zaka mayar da ita" yace mike tsaye yace "toh" ta fito lokacin Layla na waya ganin ta fito yasa ta yanke wayan, ta mike tace "zan tafi Mummy" Mummy tace "ki ɗan zauna Kinsan yanzu ya dawo a aiki bari ya wasa ruwa sai ya maida ki gidan" ta zauna tace "toh shikenan" bayan wajan 30 mins sai ga Rayyan ya fito fuskar sa ba yabo b fallasa yana kallon ta yace "Mu tafi" daga haka ya wuce abinsa tama Mummy sallama sannan ta bi bayan sa da sauri, ta buɗe front seat ta shiga, tun da suka fara tafiya ba wanda yace da wani kala sai can tace "Ya Rayyan, wai saboda ina son ka ne yasa kake wulakanta Ni?" Ya ɗan kalle ta sai ya mayar da kansa kan titin yace "Haka kike gani?" tace "gashi ina gani ƙarara rubuce a fuskan ka, kamar wadda za'awa auren dole? Haba mana try to be romantic mana" yace "Ko?" tace "i mean it" yace "Okay" daga haka ba wanda ya sake magana, bayan yayi dropping dinta yace "ki gaida Mama" tace "toh". Bayan Leena ta idar da sallar Asr tana evening zikr ɗinta sai ga Sadeeq ya shigo tana kallon sa ta tsunkuyar da kanta yace "wife kinyi bakuwa" tace "bakuwa kuma?" yace "Eh tana parlor" tace "babba ce?" Yace "No, mate ɗinki ce" tayi shiru tace "kila Zahra ce" ta mike yace "Zahra friend ɗinki ai na santa" da sauri ta juya tana kallon sa tace "kenan ba ita bace ?" yace "Sure" ta juya zata ajiye counter dinta akan mirror yayi hugging dinga ta baya da sauri ta janye kanta ta bata rai ita yanzu ma tsoro yake bata ma, murmushi ya mata, taki mayar masa, daga haka ta fita zuwa parlor, tunda ta shiga parlorn take kallon ta da mugun mamaki har ta isa cikin parlorn tana son gaskata abinda idon ta yake gaya mata, kallon ta take daga sama har kasa, taci wani uban masassan straight gown, gata da hips daya sa straight gown din ya mata kyau nan da nan Leena taji wani kishi wato Sadeeq ya ganta a haka kenan?, Niswa ta yanke mata tunanin ta tace "Kamar kina mamaki da zuwa na fah? Leena tace "Ya kike? Ya su Mummy" tace "kalau" Leena ta yi shiru tana mamakin zuwan ta Niswa tayi murmushi tace "Leena matar aure" Leena ta ɗan kalle ta, ta cigaba tace "Na ɗauka ai har zuwa sannan kina kuka sai naga akasin haka, ashe de kina son auren kike ta raina ma mutane hankali" Leena tace "Ba wanda nace masa bana so, kawai dai saboda na fi shakuwa da Muhammad ne than Sadeeq, beside na ta taso da son sa a raina" Niswa tayi ƴar dariya tace "Allah ko? naga alama kuwa, toh ko ruwa da abinci ba zaki bani bane ko haka ake wa baki?" Leena ta tashi ta dauko mana ruwa ta ajiye mata ita har sannan bata daina mamakin zuwan ta ba, Niswa ta ajiye veil ɗinta a gefe ta mike tace "Kinga yunwa nake ji barin dafa ko da indomie ne" Leena tace "Ai ban fara girki ba" tace "Toh ai dama bance ke ba, na'isa nasa Amarya aiki?" Leena tace "Toh ai saboda baya so nayi girki da kaina siyasa ko gas be yi refilling ba" ta rike haɓa tace "Toh fah" sai kuma ta koma ta zauna, Leena tana ta Allah, Allah ta tafi taga kamar bata da niyyar tafiya daga karshe ma ta mike a kan cushion ɗin ta fara chatting, Sadeeq ya fito daga dakin Leena yana kallon ta yace "Baby, zan ɗan fita na dawo" wuff Niswa ta mike, tana wani rangwaɗa, daga haka Sadeeq ya fita, Niswa ta dauki jakkan ta da veil ɗin ta tace "See yah" daga haka ta fita da saurin ta, Leena taji hawaye yana gangaro mata da sauri tayi bakin kofa ta tsaya tana kallon ta har ta fita. Sadeeq na kokari tafiya Niswa tayi saurin tsayar da shi ta kashe murya tace "Please kayi min lift mana, kasan unguwar ta ku ba'a samun taxi" Strictly yake kallon tace yace "Saboda Ni na kawo ki?" tace "Toh ai taimako zaka m.." tun kafin ta karasa magana ya ja motar sa a mugun speed, Nisa ta bi Motan nasa da mugun kallo tana jin wani bakin ciki....