AGOLA (Behind the palace walls)

Chapter 34

by @hauwajaywrites

*I'm touched by Ur concern and all the get well wishes. Thank you for being so amazing! I love and cherish every single one of you, and I'm grateful for your kindness. You're all truly special, and I appreciate each and every one of you Dudes. Oh, and I'm now doing fine, Alhamdulillah.*

34.........

Tunda Sadeeq ya dawo Leena taki kula shi, da farko shima ya so share ta sai yaga ba zai iya ba, ya bita dakin ta, tana zaune akan darduma daga gani bata jima da idar da Sallah ba, har inda take zaune ya karasa ya zauna yana facing dinta ya kama fuskan ta da hannu biyu yana kallon ta yace "Toh me kuma nayi ma wife ɗina?" Nan da nan Leena ta fashe masa da kuka, ya ɗan ja baya yana kallon ta sai kuma ya rike fuskan ta yana kallon ta a ɗan ruɗe yace "What is it, Baby?" ta sakaita kukan ta tace "kai ka mayar da Niswa gida ko?" ya yamutsa fuska yace "who is she?" tace "Kanwar Rayyan da ɗazu ta zo mana" be san sanda ya fara dariya ba, shi gaba daya abun da ya gani a fuskar Leena kishi ne, ita kuma ganin ya fara dariya ya sa taji haushi ta mike zata bar wajan yayi saurin riko ta yayi hugging ɗin ta yadda ba zata iya kwace kanta ba yace "Haba dear, I thought kin san hali na, ni ba ma zance miki Nasan fuskar ta ba ma yanzu haka, and I don't want to know, to Meyasa zan mata lift? Ko kin manta Sadeeq ne?" Sai yanzu Leena taji hankalin ta ya kwanta, kuma Sadeeq din da ta sani ta san ba zai kula ta ba, tayi shiru tana shakan kamshin sa me daɗi. Washe gari tun da wuri Leena ta shirya, tun kafin Sadeeq ya karasa parking Leena take kokarin buɗe kofa, ya juya yana kallonta yace "ki gaida min da Ammi na, anjima in shaa Allah zan shigo na gaishe ta" ta gyada masa kai tana murmushi tace "Nima ka gaishe min da Mami" be amsa mata ba sai kallon ta da yake yi, tace "what?" yayi frown face dinsa yadda take yi a baya tayi dariya ta sauka daga motar tana kallon sa, yayi kasa da murya yace "i'll miss you so much, boo" waving dinsa tayi ta wuce gidan da ɗan saurin ta, ta gashi da masu gadi sannan ta wuce ciki ta buɗe kofar parlorn na su, su anty Binta dake breakfast a parlorn suka daga kai suna kallon ta, Leena ta hango Ammi dake dinning area ita da Ayaan da gudu ta tsallake su Anty Binta ta suka bita da ido taje ta rungume Ammi, Ammi dan shock ta kasa magana ma, Leena tace "I miss you soooo much, Ammi na" Ayaan yace "Addah, i miss you, too" ta sake Ammi tayi hugging ɗin sa, Ammi sai kallon ta take tace "Leena, ina lafiya dai? Leena ta gyada ma Ammi kai tace "Eh, Lafiya kalau" Leena da take rike da hannun Ayaan zata koma wajan su Anty Mairamah ta gaishe su Ammi tace "Toh me kuma na zuwa?" Leena ta tsaya tana kallon Ammi tace "Ammi baki son gani na ne? Ashe ma ba kiyi missing dina ba" Ammi tace "Toh bamu waya ne?" Leena tayi ƴar dariya tace "kai Ammi, an fa kirasa ne a wajan aiki shine zamu koma Abujan tare shine yace na zo na Miki sallama" Ammi tace "Okay! Ayyah, toh Allah ya taimaka" su Anty Binta suka fara dariya Leena ta koma cikin parlorn tana gaishe su, sai kuma ta tsaya kallon su tace "Toh anty me nayi kike dariya?" Anty Binta tace "A'a baki yi komai ba Leena" Ayaan ya hau jikin ta yace "Addah tare zamu tafi?" Leena ta masa magana a kunne, Ammi sai bin Leena take da idanu, haka su Anty Binta ma, Leena zata shige dakin ta tace "I'm finally back in my own space, it feels so good to be home" daga haka ta shige dakin na ta, Anty Mairamah tayi ƴar dariya tana kallon Ammi da ta dawo cikin parlorn da kallon tace "Toh Yaya sai ki kwantar da hankalin ki yanzu, Kinga dai Leena alamar ma tana cikin farin ciki ne" Ammi kawai tayi murmushi ta mike ta wuce dakin Leena, Leena da har ta kwanta kan gadon ta tana tuna memories ɗin baya ta daga kai tana kallon Ammi, Ammi tace "Leena is good ki shiga wajan Hajiya yanzu ko?" Leena tace "Ammi da sassafen nan?" Ammi ta Harare ta tace "yanzu ne sassafe? Za ki tashi ne ko sai taji labarin kin shigo sai ita da kanta ta zo gaishe ki?" Leena tayi dariya tace "zuwa 11am zan shiga wallahi, amma yanzu Ammi barin ɗanyi bacci" Ammi tace "wato har yanzu kina nan da wannan baccin na ki ko?" daga haka ta bar kofar dakin. Sadeeq yace "ke kaɗai ne a gidan kenan?" Jiddah ta gyada kai tace "duk sun tafi aiki" daga haka ya fara haurawa stairs tayi gyaran murya tace "Ya Sadeeq" ya juyo alamar yana jin ta tace "shekaran jiya fah naga wata me kama dakai da kuma me kama da Leena a Couples Date Spot" kallon daya ya mata ya cigaba da haura stairs ɗin sa, Jiddah ta fara dariya, ya dauki abinda zai dauka ya sauko, ganin ba kowa yasa kawai ya koma gidan sa. Around 11am Leena ta fito zata part din Hajiya anan compound ta haɗu da Niswa, Niswa ta buɗe ido da ta ganta tace "Yaushe kika zo?" Leena tace "Ɗazu" daga haka ta cigaba da tafiya Niswa tace "Ikon Allah! Kamar baki son magana" Leena ta tsaya tana kallon ta tace "Thought ai shikenan" tana maganar ne babu yabo ba fallasa Niswa ta girgiza kai tace "Amma zaki wuni mana ko? Sai dare zaki tafi ina? Kin san gida da daɗi" Leena ta gyada mata kai kawai ta cigaba da tafiyan ta Niswa ta bita da harara daga haka ta koma bangaren su da sauri. Leena tayi sallama a kofar parlorn Hajiya ta shiga da gudu tayi hugging ɗin ta dake zaune a parlorn ta tace "Hajiya I really miss you" Hajiya tace "Dan Allah cika Ni, kwana biyu Allah yasa kin daina wannan karyan turanci daga aure kuma zaki fara" Leena na dariya, ɗaga kai da zata yi ta haɗa ido da Rayyan dake zaune, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa itama ta ɗauke kanta tace "Yaya ina wuni" be kalle ta ba yace "Lafiya" daga haka ya mike yace "toh Hajiya barin tafi" daga haka ya fita, Hajiya tana kallon Leena tayi kasa da murya tace "ki gode Allah ƴarnan, samun mahaifiya irin uwar ki kam sai an tona, yanzu kaf duniyan nan ba wanda nake tausayi kamar Riyan wallahi, yaro ya dade be yi aure ba ace a bari ya zabi zaɓin sa amma inaa uwar ta kawo masa wata, yanzu haka dazu Daddyn ku yace wai bikin saura sati biyu" Leena tayi shiru tana sauraran Hajiya a hankali tace "Allah basu zaman lafiya" Hajiya tace "Toh Amin, amma shi kam yace min baya son ta, uwar ne ke son aure, kuma kwatakwata bana kaunar ita mahaifiyar yarinyar amma ya zamu yi?" Leena tayi shiru tana kallon Hajiya. Sadeeq da har bacci ya fara ɗaukan sa yaji knocking ɗin da akeyi yayi yawa hakan yasa ya mike ya saka zallabiyan sa ya nufi compound dan zuwa ya buɗe gate ɗin, bayan ya buɗe daga sama har kasa yake kallon ta yace "Lafiya?" ta kashe murya tace "Toh kabari na shiga mana amma ka wani tare hanya" strictly yace "Who are you?" ta sake baki tana kallon sa tace "Leena's elder sister mana" wani irin kallon ya mata and he slammed the door in her face ta ja baya da sauri tana mamakin abinda ya mata. Leena dake ta game da Ayaan Ammi tace mata "Leena Daddyn ku ya dawo kije ki gaishe shi" Leena ta mike tace "Toh" tana kallon Ayaan tace "tashi ka raka Ni" ya mike ta kama hannun sa suka wuce har part ɗin Daddy tana sallama Ayaan ya shige da gudu ya fada kan  Daddy da ke cin abincin, Leena na biye da shi a baya Daddy na masa wasa yace "Oh yau Addah ta zo shiyasa ban ganka ba ko?" Yana dariya yace "Eh Daddy" Leena tsintan kanta tayi tana jin kunyan sa, ta sauke kai ta gaishe shi, ya amsa yace "Ya me gidan na ki?" Leena tayi shiru kuma taki ta daga kai, Daddy yayi dariya yace "ina ba wata matsala ko?" tace "Eh Daddy" yace "Ma Shaa Allah" ta ɗan zauna sai kuma ta mike ta masa sallama ta fi, tana fita taga Niswa ta shigo gidan Fuu kamar zata tashi sama, ta bi ta da kallo tana shiga parlorn su tagan su suna hira Leena ta zauna tace "Yauwa Anty Binta kin san ranan kawai sai ga Niswa ta zo min wai, ita da fah da can ko magana bata min" Basu Anty Binta ba hatta Ammi dake can zaune sai data ɗago tana kallon Leena da mamaki, har haɗa baki aunts dinta suka yi wajen cewa "Uwar me taje yi kuma?" Leena ta buɗe hannu alamar bata sani ba Anty Binta tace "Daga yau duk sanda ta sake zuwa Miki karki kuskura ki sake mata fuska? Anty Mairamah tace "wani sake fuska kar ma ki buɗe mata kofa, ki faɗawa mijin naki idan ita ce karma ta shiga, dan mutanan nan basu da imaani" wayan ta ne ya fara ringing da sauri ta kwace wayan a hannun Ayaan ganin Sadeeq ne ta mike sai kuma tayi realizing reaction dinta ta ɗan kalle su sai ta koma ta zauna Anty Binta tace "Ni wai yaushe Leena kika zama mara kunya ne?" Anty Mairamah tace "tashi ki shiga ki amsa wayan mijin ki" Leena tace "Ba fah shi bane" daga haka ta wuce cikin dakin ta. Sadeeq dake kwance a parlorn gidan su duk tsokanar da Sultan ke masa be tanka sa ba, ya kuma kiran Leena a karo na biyu tana dauka ya mike ya haura sama wayan kare a kunnan sa after few minutes sai kuma ya sake sauka ya wuce kofa. Bayan ya isa kofar gidan su Leena ya shiga har cikin gidan ya gaida Daddy, sannan ya wuce bayan yayi sallama da Ammi ya wuce ɗakin Hajiya, Leena ta rike Ammi sai kuma ta fara kuka Ammi tace "bana son iskanci, sake Ni kar mijin ki yayi ta jiran ki" sai kuma ta turo baki Anty Binta tace "Toh Leena Allah bada zaman lafiya mu ma jibi zamu koma" Leena tayi hugging ɗinsu tana jin kamar su cigaba da zama da Ammi, Anty Mairamah tace "zamu yi waya, Allah yasa ma kina yin abubuwan da nake faɗa Miki" ta saci kallon Ammi daga haka ta wuce ta fita ba tare da ta sake kallon Anty Mairamah ba, dakin Hajiya ta wuce, ta mata sallama sai kuma ta tsaya Hajiya tace "Lafiya kuma?" tace"Hajiya baki da abun daɗi ne?" Hajiya tace "A'a nikam babu komai" Leena tace "toh barin sha ruwa" Hajiya tace "ke da zaki gida yanzu" Leena ta karasa jikin fridge ɗin Hajiya ta buɗe tana ganin Nono da fita ta ɗauke ta karasa cikin parlorn tana dariya tace "Ni dai na dauke wannan" Hajiya ta sake baki tana kallon ta tace "ai kwana biyu da baki nan na huta, amma daga zuwan ki dan abun da ya rage min kin ɗauke, bayan mijjn ki ya loda miki" Leena tayi dariya daga haka ta wuce, tana buɗe gate taga yana tsaye yana jiran ta fito, tun da ta fito har ta karasa jikin motar idon sa na kanta, har ta karasa sai sannan yace "Baby, do you know how much I miss you?" da sauri ta juya tana kallon layin na su ganin babu kowa tace "dan Allah ka bari kar wani ya zo" yayi kissing forehead ɗinta sannan ya buɗe mata kofar front seat ta shiga, a kofar gidan Mami yayi parking, duk suka sauka bayan sun shiga yaune rana ta farko da taji tana jin nawin mutanan gidan Jiddah tayi hugging ɗin ta tace "Aunt Leena" Leena ta gaishe ta, Sultan ma na dariya yace "Aunt amarya" duk ta gashe su, ta karasa ta zauna gefen Mami amma a kasa, sannan ta gaishe ta Mami tace "tashi ki zauna, bana son wani surkuntaka, I'm still the same Mami from years back, please still see me as that Mami, Okay?" Leena ta gyada mata kai. Har dare suka kai a gidan Mami, duk babu wanda ya nuna wa Leena yanzu da baya ba ɗaya take ba, kamar ma yanzu sun fi son ta than a bayan ma, duk suna dinning suna dinner, Leena na kusa da Jidda, Opposite ɗinta kuma Sadeeq ne, bini bini sai ya daga kai ya kalle ta, ganin kamar she's not comfortable kuma kamar ta fi sipping drink din ya dauki nasa ya juye a cup din ta Mami tayi kamar bata gan sa ba, Jiddah ta daga kai sai suka haɗa ido da Sultan, ya Ciro Wayan sa yana kallo sai kuma yace "Ohh, who is she?" Zun zurutun dariya sai da Jiddah ta kware Mami tace "bana son shiririta fah Jiddah" daga haka ta mike ta wuce dakin ta Leena ta ɗan rikice ganin ta kware ta mike zata buɗe mata bottle water Sadeeq yayi saurin rike hannun ta yace "zauna" tace "Zan bata ruwa ne" kallon da yake mata yasa ta koma ta zauna, Jiddah ta sakaita dariyan ta tana kallon Sultan ta yayi kamar be san meke faruwa a wajan ba kamar ba shi yasa ta dariyan ba ya ɗan ware idon sa yana kallon ta yace "what?" ta Harare sa tace "Ban sani ba" yace "Ohh, Toh wacece ita?" Jiddah ta sake fashewa da wani dariyan ta mike tace "Wallahi Ya Sultan baka da kirki" daga haka ta wuce ciki, Sultan ya mike shima yana avoiding eye contact da Sadeeq, Sadeeq ya dawo kusa da Kujeran ta yace "ko ki ci ko nayi feeding din ki" gudun karya bata yasa ta fara ci dan ta ga kamar shi ba kunya gare sa ba. Bayan sun ma Mami sallama, ta haɗa ma Leena su turarurruka ta bata Leena tayi ta godiya, Jiddah ta raka su har compound tana kallon Sadeeq tace "Ya Sadeeq ka bari next tomorrow sai mu hada hanya" ko kallon ta be yi ba yana rike da hannun Leena suka fita. Fu'ad yana kallon abokin na sa da tausayi yace "Toh kai yanzu Rayyan ba yadda za kayi ka yi convincing Mummy akan maganar yarinyar" Rayyan ya sauke ajiyan zuciya yace "Fu'ad ba zaka taba gane wa bane, Mummy bata dauki maganar da sauki ba fa" Fu'ad yace "Wallahi dama kanwata Husna ka aura, kasan tana mugun son ka, kuma nasan zaka iya controlling dinta yadda kake so dan zata bika saboda tana son ka" Rayyan ya daga kansa yana kallon sama shi gaba daya yama rasa wani tunanin zai fara yi a wannan moment ɗin" ya sauke ajiyar zuciya, Fu'ad yace "sai hakuri fah Rayyan, wannan jarabawar ka ne, kayi addu'a Allah baka sa'an ci, kawai kayi biyayya wa mahaifiyar ka" Rayyan ya kalle sa yace "Ni yanzu tashin hankali na idan na tuna bikin wai in 2 weeks time ne" Fu'ad ya dinga kallon sa cike da tausaya masa. Ayrah dake kwance tana waya har pass 11pm sai ga Layla ta shigo, Ayrah tace da wanda take wayan "Excuse me, I'll call back" ta dinga kallon yayar ta ta da ta shigo tace "Amma anty Layla ya kamata kima kanki fada, idan mune muke wannan yawace yawacen ya kamata ki tsawatar mana amma ace ke ne kike yi" Laylan ta sake baki tana kallon ta har ta gama magana ta wanke ta da mari tace "How dare you talk to me like that! Do you think I'm your mate or something? This is the first and last time you'll speak to me like that. Make sure you know what you're saying before you approach me, I'm not your mate Ayrah, Okay?" Ayrah ta rike kuncin ta tana kallon ta ta bangaje ta ta wuce dakin ta.