AGOLA (Behind the palace walls)
Chapter 36
36......
Leena ta fara hada kayan ta, tunda Sadeeq ya kalle ta sau daya bai sake kallon direction dinta, ta gama parking kayan ta tayi zipping akwatin, ta ɗaga ta kai gefe, sai sannan ta zauna tana kallon sa tace "Toh kai naga baka hada kayan ka ba? Ko da safe zaka hada?" ya shafa kansa yana kallonta yace "Toh ai babu available flight to Kaduna" tace "Toh sai mu tafi da mota kawai" yace "A'a bana son ki wahala" tace "Toh ai na taɓa zuwa Abuja ma a mota banji na gaji ba" yace "Shiiiit, Stop stressing yourself out by taking on too much" ta ɗan bata rai tana kallon sa ya mata Murmushi kawai daga haka ya kwanta, Leena ta dinga kallon sa dama taga take taken sa kamar baya son komawan nasu, wayar ta ta ɗauka and checked if there were available flight to Kaduna for tomorrow, ganin Akwai kuma karfe 10:00am zai tashi ta ringa kallon Sadeeq, ta buɗe baki zata yi magana kawai sai kuka Sadeeq ya mike yace "Me kuma?" da sauri ya karasa wajan ta tace "Ni ka kyale Ni, bayan ga available flight kace babu?" ya fara sosa kanshi dan be yi expecting zata duba ba, yace "to be honest with you dear, bana son tafiyan ki Kaduna a wannan week din" tace "Why?" yace "Kawai haka nan, ki bari sai next week kawai In-Shaa-Allah sai mu tafi" daga haka ya mike ta bi sa da kallo harya fita, tayi tagumi dama ita har mamaki ta yi da yace zasu Kaduna dan ta lura kwatakwata baya kaunar wani ya raɓe ta, balle ma da yaji bikin Rayyan ake yi, ita kuma ba dan shi take son zuwa ba just that tayi missing Ammi ne. Yau ranan daura auren Layla da angon ta Rayyan, kuma da daddare za suyi dinner. Daddy da yake part ɗin Ammi yana breakfast, bayan ya gama yana kallon ta yace "Amma zaki wajan dinnern Rayyan ɗin ko?" ta girgiza masa kai tace ba fa najin dadi, zazzaɓi nake ji. So, bana tunanin zan iya zuwa" ya mike yace "Okay, Amma ya kamata ki je asibiti, ina ga ni daga nan idan nayi wanka zan wuce wajan daura auren ne sai kuma reception" tace "Toh Allah ba su zaman lafiya" yace "Amin" daga haka ya fita, ita kuma ta dauki kulan abinci da ta sawa Hajiya ta fita da shi, cikin compound ɗin a cike yake da jama'a ana ta hada hada, wasu kuwa suna bakin murhu suna girki, a haka Ammi ta wuce ba tare ta tabi ta kan kowa ba, a kofar dakin Hajiya tayi sallama duk parlon a cike yake da baki 'yan uwan Daddy, Ammi ta shiga ta gaishe da mutanen parlorn sannan ta wuce bedroom ɗin Hajiya ta same ta tana zaune da wata Kanwar ta ta gaishe su duk suka amsa mata ta ajiye mata kulan, Hajiya tace "Ai kuwa na gode, yanzu dama na gama shan tea gani nayi kamar sun ma manta da mu a gidan yau, shiyasa Sa'adatu kawai ta daura musu abin da za suyi ƙarin kumollo" Ammi tace "kila ta sha'afa ne, hidiman mutane da yawa sai a hankali" Hajiya tayi murmushi tace "baki san halin Khadija ba ne, dama ba son samin take ba, duk da cewa ba ita ke girkin ba, balle yau data ga jama'a, ai ko dan su sai ta zubo" Kanwar Hajiya ta mike tace "idan akayi shiru ma ai tayi nasara ne babban kula zan ɗauka na kai nace a zuba na sashin Hajiya, tunda dan ɗanta muka taru anan" daga haka Hajiya Rabi ta fita, Ammi dai bata ce komai ba, can kuma ta mike tace "Hajiya toh barin leka su" Hajiya tayi godiya, Ammi ta shiga har cikin parlorn Mummy, kannan Mummy sai wani kallon kaskanci suke mata amma bata damu ba ta zauna a dinning tunda taga jama'a ne a parlorn kuma wasu kamar breakfast su ke, Niswa ce ta fito daga dakin Rayyan Ammi tace "Yauwa Niswa ina Mummyn na ku" tace "Tana ciki" Ammi tace "Ko zaki mata magana" har ta fara tafiya kuma sai ta koma zata ma Mummy magana, bayan ta shiga da sallama da alama magana mai mahimmanci suke tattaunawa Niswan tace "Anty ne ke Miki magana" Mummy ta mata wani kallo tace waye kuma Anty?" Niswan tace "Maman Leena mana" autar su Mummy ce tace "Toh ke baki ganin magana muke ne da ba zaki ce mata tayi wucewar ta ba" Niswan tace "tsawan me kuma kike min? Ni nawa ba aika bane" daga haka ta fita ta banka kofar, autar su ta daga kai tana kallon Mummy tace "Anty Khadija ni Niswa zata ma haka?" Mummy tace "kiyi hakuri, Nima kaina lamarin Niswa tsoro ya fara bani, wallahi ko shakka ta bata yi yanzu, yadda nake controlling Rayyan idan ita ce wallahi ko rabin yadda nake masa ba zata ɗauka ba" tace "Hmm, kin zaune kuma? Kika san ko ita kishiyar taki ce ta mata wani abu dan ta zama fitsararriya?" Mummy tayi shiru sai kuma ta mike tace "Barin je Naji uban me ya kawo ta". Bayan an daura auren Layla da Rayyan. wata Kanwar mahaifiyarta ce ta shiga cikin compound ɗin tana rangaɗa buɗa tana cewa an daura, wata kawar Layla tace "dan Allah kuyi shiru kamar an daura ake cewa" duk suka yi shiru nan suka jiyo abinda take fada suka fara taya Layla murna, Layla sanin Rayyan ba kiranta zai yi ba ta dauki wayan ta ta kira sa har ya katse bai ɗauka ba ta ajiye wayan mai makeup ta cigaba da mata makeup sai kuma wayan ta ya fara ringing da sauri ta ɗauka ganin Rayyan ne tayi sallama hadi ta cewa "Ango na" Rayyan yace "Naga kin kira ni" tayi shiru sai kuma tace "Ai kamata yayi ace kai ka fara kira na" yace "It's Okay, tunda gashi ke kin kira, right? Layla taji haushin amsa da ya bata amma ba daman ta gaya masa bakar magana ko dan friends dinga da ke zaune a gefen ta tace "Okay angon Layla, sai an jima" tun kafin ta karasa magana ya katse kiran. Leena ta ɗauki kiran da Mami take mata, bayan sun gaisa Mami tace "Amma za ku zo ɗin kuwa daughter?" Leena tace "A'a Mami, yace wai sai next week ne" tace "Okay, ai dana ga har pass 5 nace barin tambaya, na ɗauka za kiyi attending bikin Yayan na ki ai" Leena tayi murmushi kawai Mami tace "Toh Allah kaimu next week din, sai ku dawo tare da Jiddah dan itama tace zata dawo gida next week" Leena tace "Toh in shaa Allah Mami" Mami tace "Allah kawo ku lafiya" Leena tace "Ameen Mami". da Daddare ko da Mummy ta masawa Niswan sai ta shirya taje wajan dinner, Niswa ta kira saurayin ta akan ya zo ya ɗauke ta, ba'a dade ba sai kuwa ya karasa har kofar gidan su lokacin har an fara zuwa dinner, ta fito cikin ankon ta ko ta kan autar su Mummy dake faman saka takalmin ta bata bi ba tayi ficewar ta, ta fita ta ga motar sa a parke a kofar neighbors ɗinsu ta karasa ta buɗe front seat ta shiga daga haka ya tada motar suka bar wajan. Duk yadda Layla ta so Rayyan ya zo gidan su da Rana ayi hotuna yaki toh haka a dinner din ma ba yadda bata yi ba amma ina yace shi ba zai yi attending ba ai dama tun farko yace ba zai yi attending ba daga karshe ma kashe wayan sa yayi da takurin ta. Rayyan da ke zaune amma idon sa a rufe amma yana jin hiran da few friends dinsa suke yi, Fu'ad ya kalle sa yace "Toh ai sai ka tashi a baccin ko ango? Yanzu za'a tashi a dinner sai mu kai maka amaryan ka" sai sannan Rayyan ya buɗe ido yana kallon su wani Friend dinsa yace "Dan Allah ku tashi mu samu mu kai su da wuri, ka ga Madam ta fara damuna da kira" duk suka mike suna tsokanar Rayyan da bayi da interest da tsokanar na su. Aka ɗauki amarya aka kaita gidan mijin ta Rayyan tare da few family and friends, bayan duk sun fito a cikin gidan still Rayyan yaki shiga daga karshe Fu'ad ya ja shi gefe yace "Haba mana ango to ka sake ranka mana" Rayyan yayi dariya yace "Toh ran nawa a kame ya ke?" Fu'ad yace "Toh ko kai fah, karka bari a fahimci halin da kake ciki" yace "Toh ai yanzu kam it's Over, tunda an daura aure kuma, sai dai Allah bani iko da juriya akan ta da kuma sauke nawin ta" Fu'ad yace "Toh Alhamdulillah tunda ka fahimci hakan, Amin Amin" Rayyan ya raka su har bakin gate sannan ya kulle gidan ya koma cikin gidan, dakin da yake tunanin nasa ne nan ya shiga dan shi tunda suka yi jere be taka gidan ba, bayan yayi wanka yasa kananan kaya yayi raka'a biyu sannan ya fita ya dauki laidan da Fu'ad ya tsiya musu kaza shi be ma duba me ke ciki ba kawai ya shiga dakin ta tana nan zaune bakin gado tayi tagumi tana tunani, jin shigowan sa ne yasa ta daga kai tana kallon sa, ba yabo ba fallasa ya karasa har cikin dakin sannan ya ajiye mata ledan hannun sa yace "Maybe zaki buka ci wani abu kisa a cikin ki" ta dinga kallon sa ya ajiye mata ya juya zai fita tayi sauri cewa "Sweetheart" Rayyan ya jiyo yana kallon ta" ta marairace masa tace "Toh kuma ina zaka?" yace "Zanje na kwanta mana, baki ga 12am saura bane?" bata kuma ce masa komai ba shi kuma daga haka ya fita ya ja mata kofa ta bisa da harara ta mike ta cire kayan jikin ta ta wuce toilet tayi wanka sannan ta shafa lotion ta feshe jikinta da different varieties of perfume, tasa sleeping wear, ta zuba kitson attached da ta sha a gadon bayan ta ko hula bata sa ba ta fito daga dakin ta a corridor ta tsaya tana tunani sai kuma ta karasa dakin da take tunanin na shi ne ta murɗa handle din a hankali luckily ta ji a bude ta karasa budewa, Rayyan da ke kwance ya lumshe ido da sauri ya buɗe ya juya yana kallonta ta da mamaki, ta karasa har jikin gadon sa ta zauna a kasan tiles har sannan Rayyan na kallonta da mamaki karara a fuskan sa tayi frowning face ɗinta kamar yar shekara uku tana wasa da fingers dinga tace "Ba zan iya kwana Ni kadai bane a can ɗin, ina tsoro shi yasa na shigo nan dan ban saba kwana Ni kadai ba" daga haka ta wuce ɗayan side ɗin gadon ta dauki pillow ta dawo nan kasan tiles ta kwanta Rayyan ya mike yace "Dawo kan gadon" ta tashi ta dauki pillow tace "Toh" yana kallon ta yace "Toh ina hulan ki?" tace "ban dauko ba" daga haka ya fita dakin ta ya shiga ya dauki wani veil sannan ya koma dakin sa ya mika mata tana murmushi tace "Thank you, Ya Rayyan" ba alamar wasa a fuskar sa yace "bana son na sake ganin ki da wannan abinda ke kanki gobe ki warware shi" tace "Toh" taga haka ta haura gadon shi ta kwanta yace "Hope kinyi sallah?" ta gyara kwanciyar ta tace "Zanyi gobe da safe" Rayyan tsabar shock sai da ya dauki seconds yana kallonta sannan yace "fita min a daki" ta kalle sa sai kuma ta mike tace "Toh ba Zanyi ba?" daga haka ta shige toilet dinsa ta fito ta gansa zaune a resting chair dake dakin, dakin ta ta wuce after some minutes sai ta kuma dawowa still yana zaune a rest chair tace "Na idar" ya kalle ta be ce komai ba ta koma ta kwanta akan gadon shi kuma ya kwanta a resting chair ya rufe idon sa can tace "Toh kai kuma acan zaka kwana?" yayi banza da ita, daga karshe ta hakura dan kanta har bacci ya ɗauke ta. Har bayan kwana uku haka Rayyan yake fama da Layla akan sallah, gashi kuma pure love take masa hakan yasa Rayyan ya ɗan sauko kaɗan, yana nuna mata baya son abu haka take hakura, kitson da ya ce baya so haka ta zauna ta sefa shi tas, gashi duk faɗan da zai mata takan hakura ta shanye, biyayya take masa kamar zata kwanta ya taka ta, a haka ta ɗauke hankalin sa da soyayyan ta, banda sallah bata barin sa ya fita ko ina, ko waya ne sai da ta san yadda tayi ta sa wasu contact dinsa a blacklist, da zaran yace zai tafi gida sai ta san yadda zata ce masa ya koya mata wani abu daga sallah hakan sai ya zauna ganin da gaske take son koyan sallah sai ya bata full attention din sa. Bayan sati ɗaya da bikin nasa, Mummy tayi tagumi ita kadai tasan damuwan da take ciki, Niswa ta kalle ta tace "Mummy lafiya dai?" Nisreen tace "ai tun ba yau ba Mummy ke cikin damuwa kuma bata son faɗa mana" Mummy ta gyara zama tace "kuna waya da Yayan ku kuwa?" Niswa ta tabe baki tace "Ranan na kira sa shegiyar matarsa ta ɗauka wai ce min tayi nasa shi bacci yana yi, so karki sake kira dan bayi da bukatar ki kuma" Mummy ta sake baki tana kallon ta, tace "Amma ai baki taɓa faɗa mana haka ba" tace "Sau nawa idan nayi magana sai ki ce kishi nake da shi? Shi yasa na ja baki na alaikum" Nisreen tace "Ni dai muna chatting dan shi ko jiya ma na tambaye sa kuɗi yace zai tura min" Mummy tace "Niswa gwada kiran shi da waya ta ki ji, kamar blocking dina yayi" Nisa ta karba yana fara shiga sai ya kashe kansa ta kira both lines din sa samething tace "Chap, ai kuwa wallahi blocking dinki yayi, tun ba'a kai ko ina ba?" Mummy tace "Dan Allah tashi ku shirya kuje gidan nasa" Niswa tace "Allah ni ba inda zani" Mummy ta sake baki tana kallon ta ita yanzu abun Niswa har tsoro ya fara bata tace "Wallahi Niswa idan baki daina mayar min da magana ba zaki sha mamaki na, nace ki tashi ku tafi, ku je kuga wani hali Yayan naku ya ke" ta mike tace "Ai sai da tun farko na fada amma kullum Ni ake gani kamar ina da bakin hali while Yayan ma ba son ta yake ba amma ai gashi tun yanzu sun shanye shi" Mummy tace "Toh akan ki, karki tsara wa ɗana baki" daga haka Niswa ta shige ciki baya dau lokaci ba ta fito Nisreen itama ta dauki nata veil ɗin, Niswa ta fita tana mita. Bayan sun isa gidan Niswa ta ja baya ta tsaya tace da Nisreen ai sai kiyi knocking, Nisreen ta fara knocking sun kai wajan 10 mins kafin suka ji muryan Layla tace "Wai su waye ne?" Nisreen tace "Mu ne, Anty" bayan ta buɗe kofar ta tsaya kallon su daga sama har kasa kuma bata ba su damar shiga ba tace "Yane?" Nisreen tana murmushi tace "Dama mun zo ne kawai" ta kalli Niswa take danna wayar ta ta Harare ta sannan tace "kun zo kuyi uban me?" tace "A'a anty muzo gaishe ki ne, sai kuma mu gaisa da Yaya" still tana rike da kofar tace "And so?" Sai sannan Niswa taja dogon tsaki tace "Naga dai gidan ba na uban wani bane, sannan wajan Yayan mu muka zo ko baki ji bane?" tace "Okay, Toh ai sai ku shigo mu gani, fitsararriya" ta mayar da duban ta kan Nisreen tace "Next time Karki sake zuwa min da wannan shegiyar in har kina son ganin Yayan na ki" Nisa tace "Wallahi sai dai kece Shegiya tunda ba wanda yasan da uban ku, ai kuwa ke kinyi kadan ki kirani shegiya dan kin san waye uba na" Layla ta sake baki tana kallon ta daga haka Niswa ta wuce fuu, ganin sauyin Layla lokaci ɗaya yasa Nisreen tsorata tabi bayan Niswa, Layla ta buga gate ɗin da karfi tace "Ai kuwa ganin Yayan naku sai ya gagare ku" daga haka ta shige cikin gidan zuciyan ta na ku'na saboda takaicin rashin yiwa Niswa wani abu dan kalmar ta ya dake ta sosai.