AGOLA (Behind the palace walls)
Chapter 43
Chapter 43
______Mami ta mike tsaye daga zaunan da take yi tace "Sultan barin tafi gidan na shi kawai" Sultan ya sake baki yana kallon ta sai kuma ya ga agogo da ke nuni da pass 12am tun ɗa zu yake son komawa gida amma ganin yanayin da Mami ta shiga yasa ya zauna har sannan, yace "Mami dare fa yayi, pass 12am ne fah yanzu" Mami ta dauki hijab ɗin ta ta saka tace "Gwamma kawai naje, baka ga yadda ya fita ba ne? gaba daya fa kamar baya cikin nutsuwa, kuma damuwa ta halin da yarinyar zata shiga ne, gashi sai bugun zuciya ta tana kara tsananta" Sultan ya mike ya ɗauki keyn motar sa yana kallon ta yace "Bari ni zan tafi, duk yadda ake ciki zan sanar miki, daga can kuma sai na wuce gida" Mami ta sauke ajiyan zuciya tace "toh sai ayi ta kiran sa ba zai daga ba? Kuma aina aka taba haka? Duk laifina ne da kawai kai na sa kaje ka dauki yarinyar ka kawo ta nan kawai, da kaga yanzu tana nan ai" Sultan yace "barin tafi Mami, amma Please ki samu ki kwanta yanzu, saboda kina bukatar hutu, dare na yi" tace "in shaa Allah, Nagode! Allah tsare ka" ya amsa da Amin. Tuki kawai yake yi amma gaba ɗaya tunanin sa ya cunkushe, toh ko gaskiyan Mami ne ko kuma ya samu tabin hankali ne, a bakin gate ɗin gidan yayi parking yana tunanin taya zai sanar da shi yana bakin gate bayan baya picking calls ɗin su, a hankali ya sauka a motar ya karasa jikin gate mamaki ya kama sa ganin gate ɗin a bude, kawai ya shiga gidan amma bai tashi jin mamakin gaskiya ba sai ganin parlorn ma a bude ya ke ya shiga da sallama at this point yama rasa wani tunani zai fara, kuma mai ya kamata yayi? A hankali ya karasa jikin kofar dakin sa ya kai hannu zai yi knocking yaga kofar a buɗe yake tsaya for some seconds yana bin kofar da kallo daga karshe kawai yayi karfin buɗe dakin, ya shiga da sallama yana bin ko ina da kallon sai kuma ya fita ganin alamun ba kowa a dakin, a haka ya fita ya koma mota bai kai ga tada motar ba sai ga kiran Mami, ya daga tun kafin yayi magana tace "me yace maka?" ajiyar zuciya ya sauke yace "yanzun nan na barsa agidan but everything is fine, ki samu kiyi bacci Mami" Mami tayi shiru for some seconds kamar tana son gano wani abu sai kuma tace "Toh Sultan" daga haka ta kashe. Bayan ya isa gidan sa yana bude kofar parlorn ya shiga ga mamakin sa Jiddah na zaune da alamar dawowan sa take jira, ta taso ta karasa inda yake tayi hugging ɗin sa, yayi kissing forehead ɗinta sannan ta sake sa yace "baki yi bacci bane?" tace "Taya zan iya? amma ka same sa agidan, I mean me yace maka?" yana rike da hannun ta suka kama hanyar bedroom yace "Everything is alright, babe". Tun a hanya take ta kuka gaba ɗaya ya rasa yadda zai yi da ita, dakyar ya daure yace "I'm sorry to say Leena, ko mijin ki shaye-shaye ya fara da zai barki cikin daren nan ki fito" dakyar ta iya buɗan baki tace masa "Ai saki na yayi" bai san sanda ya parka mashin ɗin sa ba ya juya yana kallon ta, ji yayi inama zai ga wannan Sadeeq din yanzu yana jin zai iya kashe shi dan tsanar sa da ya fara ji, ya gagara cewa ko kala sai kallon ta cike da tausayi da yake yi, itama bata ce masa komai ba daga haka ya tada machine dinsa har suka isa gidan su Leena bai ce mata komai ba, dakyar ta iya sauka a mashin ɗin shima da taimakon sa da sauri ta duka kasa ya karasa jikin gate ɗin su ya fara knocking mai gadi ya buɗe kofar yana kare masa kallo yace "daga ina?, kuma wa kake nema" kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kai yace "Leena na kawo" gatekeeper ya sake baki dan mamaki toh ai wannan ba mijin ta bane, toh me kuma alakar sa da Leena da har zai kawo ta gida, Malik ya bar mai gadi da tunanin da yake yi ganin yayi shiru ya karasa har inda Leena ke duke ya durkusa yace "zaki iya tashi kuwa?" Hawaye na sauka idon ta tace "A'a ba zan iya ba" ya karasa bakin gate ɗin yace ko zaka ma wata magana a 'yan uwan ta?" Mai gadi ya fara kare masa kallo sai kuma ya fito ya karasa jikin bicycle ɗin ganin Leena ya mike da sauri yace "toh..toh.. barin musu magana" daga haka ya karasa cikin gidan a kofar su Leena ya fara doka sallama, mai aikin Mummy data fito daga kitchen ɗin dake compound ɗin ta tsaya kallon mai gadin da mamaki, ko kallo bata ishe sa ba dan haka ko ta kanta bai sake bi ba, Anty Binta ce ta fito tace "kai malam lafiya zaka daga mutane a bacci?" yayi kasa da muryan sa yace "Kiyi hakuri, wani ne ya kawo Hajiya Leena kuma kamar ba zata iya tafiya bane yasa yace nazo na sanar da ku ko zaku shigo da .." ina Anty Binta ta katse shi "ban gane ba? Ina ita Leena take kuma" yace "Tana waje" muryan Ammi taji daga bayan ta tace "Leena kuma?" Ina har anty Binta ta fita tace "muje" tama manta cewa sleepwear ne a jikin ta har waje ta fita kallon Malik ta tsaya yi sai kuma da sauri ta duka tana kallon Leena ta kyar ta iya taimaka mata har ta tashi, Malik ya bi su da kallo har suka shiga cikin gidan anan parlorn anty Binta ta zaunar da ita, tashin hankali ƙarara rubuce a fuskan Ammi tana kallon ta tace "Leena lafiya?" tana sheshsheka tace "Ya sake ni ne?" Ba Ammi ba hatta anty Binta bata taɓa jin wani abu da lokaci guda ya buga zuciyar ta ba, ta durkusa hawaye har sun fara sintiri a fuskan ta zata yi magana Leena ta sa musu wani ihu saboda wani azabebben ciwon baya da bata taɓa jin irin saba, Anty Binta ta mike da sauri tace barin kira driver kawai yayi asibiti da mu, Ammi na rike da Leena tana tofa mata addu'a har anty Binta ta dawo dakyar suka iya daga ta suka kaita motar, har suka isa asibiti Ammi na mata addu'a. Da safe Ayaan ya farka bai ga Ammi ba ya duba dakin Leena inda Anty Binta ta sauka nan ma bai ganta ba, ya wuce kitchen still bai ganta ba, kawai ya fara sheshshekan kukan, ya wuce part ɗin Hajiya lokacin tana zaune tana lazimi ya shiga, ta daga kai tana kallon sa tace "me kuma?" ya karasa ya zauna a gaban ta yace "ina Ammi na?" Hajiya ta tsaya kallon sa tace "Ammi ka kuma?" yace "bata nan, ban ganta ba" simbil Hajiya ta mike tace "kamar ya baka ganta ba?" ya buɗe mata hannayen sa alamar bai sani ba Hajiya tace "Toh ita Kanwar Ammin naka fah?" yace "ai duk bangan su ba" Hajiya tayi shiru tana tunani, nan take taji gabanta ya fadi, toh ko dai kurciya da aka ce ana shirin ma Ammi ne har ya afku, kawai Ayaan ya bar sashin Hajiya ganin waje daya take kallo ya kama hanyar sashin su tun bai kai ga karasa part ɗin nasu ba yaga Ammi da gudu yaje ya rungume ta, saboda tashin hankalin da take ciki ko magana ta kasa masa sai ma rike hannun sa da tayi suna tafiya ciki, da sauri ta kunna water heater, ta wuce kitchen dan daura breakfast, ta fito da niyyar shiga ta haɗa masa ruwan wanka taji sallamar Hajiya ta amsa ta tsaya ta jira ta har ta karasa cikin parlorn, Hajiya tace "Ayaan dazu ya bar gidan na wai baki nan babu ita Binta ma" Ammi da damuwa ya cika ta ta zauna tana kallon Hajiya tace "Eh, ban dade da dawowa gida ba" Hajiya ta gwalo ido tace "Allah sa lafiya?" Ammi tace "Eh toh, Leena dai muka kai ta asibiti tun cikin dare amma har yanzu shiru" Hajiya tace "Ayyah toh Allah ya sauke ta lafiya" Ammi ta amsa da Amin Hajiya ta mike tace "barin je na shirya ai ta zama bai kama ni ba sai idan yaso mu koma asibitin táre" Amin tace "toh", kafin karfe 8 har sun koma asibitin, bayan sun shiga ward ɗin da suke Anty Binta ta nufo su da sauri tace "Ammi kina ji fah, wai ba zasu bari ta haihu da kanta ba saboda za'a iya rasa ta da kuma abinda zata haifa, so aiki za'a mata" Hajiya ta sake jakkan hannun ta Ammi ta ajiye basket in ba shiri tace "Toh suyi mana, su mata CD din mana" Anty Binta tace "Ai sai mijin ta yasa hannu" Hajiya tace "toh ana maganar rasa rai shi mijin nata ba zai sa hannu bane har sai mun rasa ta? Ko bashi da imaani ne?" a hankali Ammi tace "ai ya rabu da ita, jiya ya sake ta" Hajiya ta dinga maimaita Salati. Tun kafin Mami ta fita aiki sai ga Sultan da matar sa Jiddah, ga mamakin su Mami ko shirin aiki bata yi ba tana zaune, ko breakfast ɗin ta kasa yi, bayan sun gaisa tace "kun yi waya da Sadeeq din ne? Sultan yayi kasa da murya yace "Mami ai Sadeeq baya gidan sa, yanzu ma kafin mu taho nan sai da muka koma can gidan na su Jiddah har bedroom ɗinta ta duba ita ma Leenan bata nan?" Mami with shock take kallon sa sai kuma ta kalli Jiddah tace "ban gane me kuke nufi ba?" Sultan ya shafa kansa yace "Mami dan Allah ki kwantar da hankalin ki, nothing will happen in shaa Allah" Mami na kallon sa tace "kana nufin na kwantar da hankali na bayan bamu san whereabouts ɗin su ba? How Please?" Yayi shiru Jiddah tace "Mami koma ina suka je ai tunda matar sa ce it's okay, dole zasu dawo gida" Mami ta mata tsawa tace "Dama ke hankali gare ki? Me kika sani a rayuwa ma tukun? Duk kuna ganin yadda ya koma, damuwa ta yarinyar da tsohon ciki amma kice ai matar sa ce, naga da cikin ma bai daina harming dinta ba" taja dogon tsaki ta mike dakin ta ta wuce ta dauki hijab ɗinta ta fita ba tare da ta sake cewa wani acikin su kala ba, Jiddah ta sauke ajiyan zuciya tana kallon Sultan, ya shafa fuskar ta yace "Sorry, Mami dole ta damu, so ki daina kawo unnecessary things pls" Jiddah ta jinginar da kanta jikin cushion ɗin, ya mike yace "barin bi bayan ta". A mugun ruɗe Hajiya ta dawo gida ita bata ma san mai ya kawo ta gidan ba, suna gama magana da Binta ta kama hanyar gida bata kai ga shiga part ɗin Daddy ba ta hango Rayyan da shigowan sa gidan kenan da saurin ta ta fara zuwa inda yake shi kuma ya zuba mata ido har ta karasa ya buɗe baki zai yi magana ta riga sa "Rayyan ka taimake mu, yarinyar nan rai a hannun Allah ita da abinda zata haifa, yanzu sunce aiki CS yake ko me? Toh shi za'a mata, ga miji ya sake ta kuma ba wanda zai sa mata hannu" with totally speechless Rayyan ke kallon ta haka mamaki karara written all over his face Hajiya tace "Ji kuma wani wulakanci ina maka magana zaka zuba min idanu kana kallo na, ko kaima ka koma kamar ubanka da uwarka ta shanye ne?" Sai sannan yayi gathering courage dinsa yace "No Hajiya ban fahimci me kike nufi bane?" Hajiya ta kama hannu sa ta fara ja, yana shiga Mota ya jata a mugun speed bayan Hajiya ta fada masa asibitin da suke, Hajiya sai ihu take masa ya rage gudun da yake amma ina baya ko sauraran ta sabar yadda zuciyarsa ke bugawa. Mai aikin Mummy da gudu ta shiga parlorn tana "Hajiya!" Mummy da yaranta mata dake breakfast a dinning ta daga kai tana kallon ta tace "ke wata irin mara hankali ce" Niswa ta ja dogon tsaki tace "Ni wai Meyasa kike abu kamar dabbace" tayi kasa da murya tace "kiyi hakuri Hajiya dama labari ne na kawo muku" Mummy ta ajiye spoon ɗin hannun ta tace "Ina jinki" yarinyar tana murmushi tace "Dama jiya da Daddare dana je duba sauran abinci a kitchen ɗin waje naga mai gadi ya buɗe gate sai kuma ya koma bangaren Maman Ayaan can sai ga kanwar ta na Niger ɗin ta fito, ba'a dau lokaci ba sai ga itama da kanta ta fito sukayi gate naga sun Shigo da Leena kamar ta suma ne ma nake ga, dazu da safe kuma sai ga Hajiya ta shigo a ruɗe lokacin Ɗan ki ya shigo da motar sa da gudu tayi kansa tana cewa wai ya taimaka ita kuma Linan da abinda yake cikin ta zasu mutu, kuma wai mijin ya sake ta sannan.." Mummy ta katse ta da sauri ta fara dariya tace "Toh dama meya kaisa zama da gayyar tsiya? Je ki na gode, tabbas kina da dubu goma na wannan labarin mai daɗi" yarinyar ta fita tana Godiya Niswa tace "Oh'oh yanzu zamu ga yadda za suyi ai, kullum gadaran su wannan shegiyar kyaun nasu" har sannan Mummy na dariya Nisreen tace "amma nikam i feel bad for her, ba daɗi wallahi, Allah basu lafiya toh" Niswa wani kallo take mata Mummy kam buga mata baki tayi tace "Shegiya mai bakar aniya, da a baya niswa ce bata goyon baya na amma yanzu naga kece kike son ki daina" Nisreen ta mike tana rike da bakin ta tace "amma ai gaskiya na fada, sannan ba wanda zai so haka, atleast tunda bata auri Ya Rayyan ba ai shikenan sai ku hakura kuma haka nan" Mummy ta dauki mug ta wurge ta da gudu ta masa cup din ya faɗa kasa ya tarwase, Mummy ta dauki Wayan ta tashi kiran wani number. Ko gama parking mai kyau Rayyan me yi ba, da sauri ya sauka ya wuce ciki, sai sannan ya tuna ashe shi be san inda take ba dan ya bar Hajiya a baya ganin anty Binta yasa yayi wajan da sauri ya tambaye ta nan ta nuna masa inda suke, ko Ammi bai lura ba ya banka ɗa kofar dakin da take ciki ya karasa har inda take, ya fita ya farawa Nurses ɗin wajan ihuu kamar zai dake su, wani doctor ne ya karasa inda yake ya fara masa magana a hankali Rayyan yace "Ba za'a duba condition dinta ba lalle sai ansa hannu idan ta mutu kuma fah?" daga haka wasu daga cikin Nurses suka yi kansa sannin cewa shima likita ne kuma yakan zo asibitin, rigar aiki yasa ajikin sa da kansa ya kaita dakin da zasu mata aiki, tare da taimakon wasu likitoci suka mata aiki. Malik tunda ya koma gida ya kasa samun nutsuwa haka nan yaji damuwar Leena ya tsaya masa arai ya rasa yadda zai yi, har ya tafi makarantar da yake koyarwa amma hankalin sa na kan ta, daga karshe ya bar makarantar ya kama hanyar gidan su Leena, bayan yayi parking mashin ɗin sa ya sauka gatekeeper ya leko jin anyi parking machine nan da nan ya tuna Mutumin jiya ne a ransa ko yace ikon Allah, to ko dan uwan Leenan ne?