KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Lagos, Nigeria 

Mutane akalla sha biyar ne zaune cikin conference room din Oil & Gas company dake victoria island cikin garin Lagos, suna gudanar da meeting me muhimmanci tsakaninsu da turawan dake other side of the conference table.
Cikin nutsuwa suke tattaunawa da Ahmad dakeyin nashi bayanin  cikin harshen turancinsa mai dadin sauraro, kasancewarsa mutumin da yayi rayuwan qasan turawa na tsawon lokaci, he sure has his way of interacting with them.
Can dai yayi shiru kawai yana sauraronsu batare da yawan basu dogon amsa ba, Dan'uwanshi Adam dake gefenshi neh yayi saurin amshe conversation din knowing Ahmad bazai sake doguwar magana ba kuma tunda al'amarin yafara bashi haushi.
Haka Adam suka gama sauran tattaunawan , suka miqe gaba dayansu akayi musabaha har dashi Ahmad din telling them zasuji nasu final answer dinsu zuwa jibi.
Fitowa sukayi daga conference room din Ahmad yatafi wajen elevator zai koma nashi office din while Adam ya tsaya magana da wani employee dinsu.
Shigarshi office din nashi keda wuya Adam ya biyo bayanshi, ya qarasa kan executive chair dinshi ya zauna at the same time yana duba wasu folders da yasa secretaryn shi yakawo masa dazu, wucewa gurin fridge Adam yayi ya bude zai dauki ruwan sha , cikin husky voice dinsa  Ahmad yace "pass me one please" Adam ya dauko bottle water guda biyu ya qarasa ya ajiye masa saman table dinsa,
Ahmad ya jawo ruwan yana muttering "thanks". shiru sukayi da fari sai can Adam yace "so what do you think?" batareda Ahmad ya kallesa ba yace "I'm Out" cike da mamaki Adam ya ajiye nashi ruwan shima kan table din yace "what?..Dude are you serious?" 
sai Ahmad ya dago kanshi yana kallon Adam with seriousness, cikin idonshi Adam din yake kallo yace "You can't be serious" 
Ahmad ya juya yana duban foldern gabanshi yace "Well..too bad i am" Adam ya sake cewa "You can't cut out on this, ta ina aka samu matsala kuma?" 
Ahmad ya amsa da "The percentage...I don't like it" sai Adam ya juya tareda nufan gurin small lounge dake cikin office din a gefe yayi settling akan kujera ya juyo yana kallonshi yace "You know this deal is a fair one right?" 
Ahmad na kallonsa yace "we need to include some high risk, high return options" Adam yace "but we can't gamble with anything high risk" 
sai Ahmad ya sauqe numfashi yayi dan daga kafadarsa like he don't care, yace " No good thing comes without a little risk" Adam yace " then what are you going to do now?" 
Baya Ahmad yayi akan kujeran yayi relaxing bayansa yana kallon Adam yace "I'll sort everything out" sanin waye Ahmad yasa Adam din cewa "Okay..it's settled then" don yasan wasting din energy dinsa kawai zeyi wajen convincing din Ahmad saboda ya riga yayi making mind dinsa, sai yakuma cewa "I'll be flying back today, in few hours ma" Ahmad yace "Okay, take care" miqewa Adam yayi yana cewa "Dude, ka kwana biyu baka leqo ba fah"  sai Ahmad ya shafa kanshi kadan yace "akwai bikin yarinyar can wai ko, I'll be there next month in Sha Allah"  da haka Adam ya qaraso garesa ya miqa masa hannu sukayi shaking yace "see you then" Ahmad ya amsa da "thanks man,safe flight".
Bayan tafiyar abokin nashi kuma dan'uwa, Ahmad ya maida hankalinsa kan desktop din dake gabansa can kira yashigo wayanshi, Sunan ne Laila ya fito akan fuskan wayan ya juya yana kallo har ta tsinke bai dauka ba yakoma kan ayyukanshi.

Daren ranar na'ima ta fito daga wanka tana zaune gaban madubi  tana shafe shafenta da ya zame mata daily night routine yanzu, 
Kuma duk nafisa ce ta koya mata this kind of routine, ita ta siyo mata all skin care sets da suka dace da kalan farin fatarta sannan ta rinqa koya mata a sannu sannu har ya zamto bata iyayin bacci yanzu batareda tayi shafe shafennan ba, dago hannunta tayi tana ganin yanda yazama smooth and glowy, tasan kayan ba masu sauqin kudi bane domin fenty skin care sets nafisa ta siyo mata, And she's very grateful for all of it, when she says all of it tana hadawa da kyautatawan da nafee tayi mata a baya da kuma wanda take kan yi mata har zuwa yanzu.
Nafee ba qawarta bace kawai, ta zame mata yar'uwa or even more so, dan bazata taba mantawa da ita ba a duk inda taje a rayuwan nan.
Tana cikin wannan tunanin nafisa ta shigo dakin hannunta riqe da laptop a bude alamun tana kallon movie, qarasawa tayi kan gadon Na'iman tareda kwanciya tasa laptop din agaba itama kayan bacci neh jikinta, tace "BoBo, my crush is killing it in this new series" Na'ima ta juyo tana dan dariya tace "Au wai haryanzu dai Witcher din kike kallo?" Nafee tace "kinsan Allah..sabon nan yafi dadi ma, ki gama kizo ki gani" 
Na'ima ta juya ta cigaba da daure tumilin gashinta guri daya tace "A'a bazan gani ba"  
Nafee tace "dalla can ya hadu kizo mugani, Ina zuwa ma" sai ta miqe ta fice daga dakin bayan minute sai gata tadawo dakin riqe da packs na cheese balls ta wulla na na'ima kan gado sannan ta kwanta a gurbin da ta tashi ta cigaba da kallonta tanacin cheese din.
Bayan Na'ima ta gama itama ta hau gadon ta matso tareda daukan nata cheese din tana budewa tace "Gaskiya ni kin taquramin da series dinnan" Nafee tace "kiyi shiru ni mugani" 

Haka suka kai almost sha biyu suna kallon, na'ima da tace an taqurata sai ga ta itama ta zage tana kallon with full interest har Nafisa tayi bacci ta barta, saida ta gaji sannan ta tashi taje bandaki tayo uzurinta ta fito bayan tayi alwala tayi sallah sannan ta kwanta a gadon tana jawo duvet dinsu da Nafee ta kwashe a jikinta ta lulluba, bata qara wasu mintuna masu tsawo ba itama baccin ya dauketa.