AGOLA (Behind the palace walls)

Chapter 54

by @hauwajaywrites

Chapter 54

_____Rayyan dake kwance a ɗakin sa har sannan ya kasa bacci, duk abubuwan da suka faru has been vividly flashing in his mind, ya runtse idon sa, he still can't believe, haushin Niswa da yake ji is growing stronger now, wayan sa dake ringing ne yasa ya mike ya ɗauka, ganin mai kiran yasa ba tare da ɓata lokaci ba yayi receiving, daga ɗayan ɓangaren yace "Sir, Everything is done, iyayen nasa ma anan kaduna suke, suna Millennium city! So, I left everything in the barrister's hands" Rayyan ya gyaɗa kai cike da fahimta sai kuma ya sauke ajiyan zuciya yace "Okay! It's a great job, thank you, but please kar ka kira Daddy da safe zan sanar masa da komai, cos yanzu yana bukatar hutu" yace "In Shaa Allah, sir" daga haka ya katse kiran ya jima zaune yana tunanin Layla daga karshe ya mike.

Nisreen yanzu har kukan da Niswa take yi ya fara bata haushi, gashi ta hana ta bacci, sai juye juye take akan gadon daga karshe ta mike zaune tana kallon Niswa data kifa kanta da resting chair ɗin ɗakin ta dinga kallon ta cike da takaicin a ranta tace toh dama ba tayi tunanin wannan ranan bane har ta fara aikata laifin or yanzu kukan me take yi, daga karshe taja tsaki ta dauki duvet ɗin ta da pillow ta wuce parlor dan ba karamin bacci take ji ba, rabon data samu bacci tun da bikin ya gabato. Niswa ta bita da kallo sai kuma ta mike ta wuce kan gadon, ɗaukan wayan ta tayi ta yi dialing numbern Farouq har ya yanke bai ɗauka ba ta kuma kiran sa kamar zai yanke sai kuma ya ɗaga yace "Baby" ta share hawayen fuskan ta tace "Uhm" yace "Are you still crying? Ko kuma wani abu ya sake faruwa ne?" ta girgiza kanta tana jin relief saboda yanzu shine kaɗai wanda yake mata magana in very calm way and she's ready to spend the rest of her life with him, a hankali tace "kai ma kasan dole zan samu pressure a gida, and still Daddy yaki min faɗa balle duka na, kuma wannan silent ɗin nasa ba kyau cos I knw him, yanzu ma cewa yayi dole aure zai mana nan da 2weeks, I'm so disturbed Farouq" Farouq yayi shiru meanwhile kuma yana tunanin me ta gama faɗa masa ta katse masa tunanin sa tace "Hello" yace "Yes, dear" tace "kayi shiru" yayi murmushi yace "No, ina realizing ne" tace "Toh baka ce komai ba?" yace "Sure, zance dear" a hankali kamar me raɗa tace "Farouq" yace "Na'am" tace "kana so na?" yace "Sure! I do love you" tace "zaka aure ni?" ta karasa maganar kamar me raɗa, yayi shiru for a while, tace "Why the mute, Farouq?" yace "Uhm, ina jin ki?" tace "Since you love me, kawai muyi aure! ka ji?" yayi wani irin murmushi mai wuyar fassara sannan yace "Niswa" tace "ina jin ka" yace "I'm sorry, that was then" Sabar shock Niswa tayi shiru ta ma gagara magana dakyar ta nemi strength tace "bangane that was then ba?" yace "Sure, a baya ne na so ki Niswa, not now da na gama sanin ki, I'm sorry ba zan taɓa auren mace irin ki ba, baki da qualities ɗin matan da nake so, ba zan iya auren ki ba" Niswa ta ji bugun zuciyan ta na bugawa da karfi sannan ta gagara ma sanin what exactly take ji at that moment, me zata ce masa dan she ne last hope ɗin ta ta fara furta 'innalillahi wa'inna ilahi raji'un' a zuciyar ta hawaye Masu zafi suna sauka kan kuncin ta tace "But amma kai ma kasan yadda ka same ni ko? Kasan kuma ba wanda nake kulawa sai kai, kasan bani da lokacin wani duk abin da nake yi kuma kana sane, shine yanzu zaka ki ni? har zaka iya guje min?" yaja dogon tsaki yace "Look bitch girl, don't even think about saying we know each other balle ma kiyi tunanin ko kin taɓa gani na, got it?" daga haka ya katse kiran, ta cire wayan daga kunnen ta ganin dagaske kashe wayan yayi maganganun daya gaya mata ne har sannan ta gagara believing wai Farouq ne zai faɗa mata? bata san sanda ta ɗaura hannun a ka ba ta fashe da sabon kuka.

Yana tsaye a bakin kofar dakin Ammi yana jiran ta, bata ɗau lokacin ba sai ga ta tana buɗe kofar parlorn, jin haka ya karasa jikin kofar bayan ta buɗe ya kalle ta from head to toe yace "sai kuma ki fito haka?" ta kalli sleeping dress ɗin jikin ta ta kalli compound ɗin gidan da babu kowa dan dare yayi sosai sai kuma ta tura baki tace "yanzu wa yake kallo na bayan kai" yace "Ya jikin?" ta langwabar tace "Alhamdulillah" mika mata maganin hannun sa yayi yace "make sure kin sha" ta gƴaɗa masa kai, yace "toh, good night kar Ammi tayi faɗa" ya kare maganar da wasa, itama ƴar dariyar tayi tace "waya ce ma Ammi na nan? Ai ta bar mana part ɗin ta" yace "Alright, sweet dreams" daga haka ya juya ita kuma ta koma ciki ta kulle musu kofar.

Niswa ta dinga kiran wani layin baya ɗaga wa ta sake kiran for the countless times, ta sake dialing har zai katse sai kuma taji an ɗauka ta sauke ajiyar zuciya tace "Sorry na hana ka bacci ko?" yace "Not at all, kin san bana bacci da wuri ai, just that bana kusa da wayar ne" tace "Okay, ina neman favor ne" yace "Ina jin ki, idan har bai fi karfi na ba" tace "Wannan yarinyar da ranan kace min kasan wata friend ɗin ta" yace "That stubborn girl?" tace "Eh ita" yace "Then, what is it?" tace "Ina son sanin duk rayuwar da tayi before, sannan kuma da duk wadda take mu'amala" yayi shiru for almost 30sec sai kuma yace "Hope all is well?" tace "Sure!" daga haka ta fara masa narrating duk abubuwan da suka faru.

Da safe, sai wajajen karfe 7am Rayyan ya shigo gidan, dakin Daddy ya wuce, bayan ya shiga Daddy ya daga kai yana kallon sa, ga kuma Ammi dake gefen sa, ya karasa ciki ya zauna ya gaishe su, bayan sun amsa Ammi ta miƙe, Daddy ya kalle ta yace "ina zaki?" tayi murmushi tace "barin je na ga ko sun ɗaura breakfast" ya gyaɗa mata kai, while ita kuma bata son tana shiga maganar su ne dan yadda taga Rayyan tasan maganar Niswan ne har sannan, kuma suna bukatar privacy, bayan fitan ta Rayyan yana kallon Daddy yace "Jiya da daddare mutumin da nasa ya min aiki akan sa ya gama komai, har ya mika ma wani lawyer da muka dauka case ɗin" Daddy yace "Good job, Allah maka Albarka" yace "Amin, ina ga kafin ya fita office zasu kai masa sammaci, amma kuma bai fiye zama a gidan iyayen sa ba dan su suna Millennium City ne shi kuma yana da gida a Malali ne which am sure nan yarinyar nan take zuwa" ya kare maganar cike da takaicin ta, Daddy yace "it's Okay ai, I'm ready to spend ko wani irin amount ne dan ba zan yarda ace ya lalata ta kuma yaki ta ba, idan ya so suje can duk rayuwar da za suyi dama su suka zaɓa hakan dan nasan ba lalle yace zai so ta yanzu ba" Rayyan yace "Ai bai isa bane Daddy, dan Nima I'm ready to spend" Daddy ya numfasa.

Bayan ya shiga parlorn su dan breakfast ya samu Mummy zaune a Parlorn ya gaishe ta a takaice ba tare da ya tsaya as usual ba itama ta amsa masa a dakile dan taji haushin sa ainun da har bai dauki mataki akan gaya mata magana da Layla tayi ba, Nisreen tace "Yaya ina kwana, jiya baka yi dinner ba" ya gyaɗa mata kai yace "Lafiya kalau" ya wuce dinning ɗin dan yin breakfast, Niswa ma ta fito da Niyyar shan tea dan ba dan yunwan da take ji ba ba zata fito ba saboda ko yadda taga rana haka taga dare jiyan, saboda spaced out da tayi har ta isa dinning area bata san Rayyan na zaune a wajan ba kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kan sa tana kallon sa ta sauke idon ta kasa a hankali tace "Ina kwana Yaya" sai da ya dauki some seconds kafin a takaice yace "Lafiya" haka nan taji ba daɗi tasan ba yadda za'a yi yaji Daddyn zubar ma Layla cikin da tayi ta ɗauki karamin flask ta juya zuwa dakin su, Mummy ta bita da kallo har ta shiga, bayan Rayyan ya gama serving kansa zai fara ci sai ga kiran Layla ya daga yakai kunne , bayan sun gaisa yace "Layla ko Ki sha magani ko na haɗa ki da Ammi" jin furucin sa yasa Mummy ɗaga kai da sauri tana kallon sa, in other side Layla tace "Toh gashi a nan mun gama breakfast zaka zo ka karɓa ne ko na kawo maka dan kasan bana son kana cin abincin can" ya kalli abincin gaban sa ya tuna da abinda Hajiya ta sanar da shi ya ture plate ɗin gefe yace "Thank God, kin kira da wuri wallahi har nayi serving kai na zan fara breakfast ɗin kika kira ni, barin zo na karɓa kawai" daga haka ya mike, shi har ga Allah yama manta da Mummy a parlorn yana katse kiran kuma text message ɗin barrister ya shigo masa so yana kan dubawa yana tafiya har ya fita a parlorn ba tare da yayi noticing ɗin Mummy dake zaune ba, ita kuwa tun sanda ya ambaci Layla da Ammi ta zura masa ido bayan last furucin sa ta sake baki ta bisa da kallo har ya fita, sai yanzu ta sake yarda da cewa Layla ta zama mata karfen wiya.

Mummy dake tsaye akan Niswa ta sake baki jin furucin ta, tace "Mummy ai ba karya bane, tun farko ke kayi mistake din bawa Yaya Layla, wallahi ko ƙaffara ba zan yi ba da kin hakura ya auri Leena da yanzu duk hankalin mu a kwance kika dake lalle sai Layla ai yanzu kina gani, kuma wallahi kar take kallon ku, kika sake kika sa Daddy ya ɗau mataki akan maganar nan sunan auren ki macacce" Mummy ta samu waje ta zauna sai yanzu ta hango abun da tun abaya bata hango ba, tace "wallahi kinyi magana with sence" Niswa ta share hawayen ta tace "Dan haka ki daina blaming ɗinta ke kika fara causing komai, da yanzu Leena ce zata tona min asiri ne?" Mummy ta sauke mata mari tace "Yanzu Ni zakiyi blaming? wato ma nice nayi causing komai? Idan har baki yi ba komai tsanar da ta miki ta isa ta sa a fasa auren ki ne? waya jefa ki cikin wannan halin? Ko dan Kinga har sannan ban ce miki komai ba" Niswa na shash-sheka tace "Mummy kin taɓa ce mana this and that are good? Kin taɓa ce mana wannan ba abu me kyau ba ne? Kin taɓa cewa kuje islamiyya dan dole idan muka ki? Amma Leena fah? haka Ammi tayi treating ɗin ta?, a cire son zuciya duk hassada da kyashi muke mata but she gets everything, nutsuwa, hankali da kuma addinin" Mummy tana mata wani kallo Niswa ta cigaba tace "Nima ban taɓa tunanin ganin kai na a wannan yanayin ba, ban taɓa ɗauka zan yi Wannan rayuwar ba, but I believe one thing, hakan ya zo ne a kaddara ta, kuma na san ba yadda zan kauce mata, da ace ina da sanin addini me yawa kila da nayi ma kai na addu'a, da Allah ya tsare ni daga haka" Mummy ta sake wanke ta da mari ta mike ta bar ɗakin zuciyar ta na kuna, Niswa ta kwanta kan tile tana kuka sosai bata taɓa expecting Farouq for once zai guje ta ba.

Bayan sun tabbatar da gidan ba kowa duba da gatekeeper ɗin sa yace yau ba a gidan ya kwana ba suka koma motar su, kiran Rayyan ne dake dakin Daddy ya shigo ɗaya daga cikin su, ya ɗauka, Rayyan yace "kun same sa?" Barristern yace "Yanzu haka muna gidan sa na Malali ne, baya nan so zamu wuce can gidan su ne, Ko da baya nan zamu bada message ɗin ma iyayen sa" Rayyan yace "Alright" daga haka sukayi sallama, dayan lawyern ya ja motar suka bar street ɗin.

Su huɗu suke zaune kan dinning ɗin suna breakfast gwanin ban sha'awa suna hirar su, Farouq da familyn sa kenan, shi da Kanwar sa sai kuma iyayensu, Baban na su ya ɗaga kai yace "Gaskiya Umar wallahi duk wacca na aura maka it's Okay, na gaji da maka magana" Kanwar sa Na'ila tace "Wallahi Daddy ka aurar da shi kawai kowa ma ya huta, dan bana jin Yaya na da budurwa ma" Farouq ya juya da sauri yana kallon ta ya tamke fuska yace "kee ina wasa da ke?" Mummy na kallon sa tace "daga ta faɗa gaskiya? to kabar min auta ta sarara dan Allah" Daddyn su yace "Toh ai autar na ki ma na kusan cewa tabar min gida, ina duk mate ɗin ta suna aure amma kullum sai kiyi ta saka mata cewa ita karama ce" Na'ila ta kalli Daddy tace "I'm just 23 fah, Daddy" sallamar gatekeeper suka jiyo daga parlorn Daddy kaɗai ya amsa yace "Alhaji wasu mutane biyu ne wai suna neman ka ko kuma Alhaji karami" Daddy yace "waye su?" yace "wallahi ban san su ba, amma suna dai sanye da kalar kayan da masu aiki a banki suke sakawa" yace "It's Okay, kace su shigo compound ɗin gani fitowa" daga haka ya juya zuwa isar da sakon sa, Daddyn Farouq ya mike yana goge bakin sa yace "barin duba ko su waye ne" daga haka ya wuce, da mamaki shimfiɗa a fuskar sa ya karasa wajan su, bayan sun gaisa suka ciro IDcard ɗin su suka nuna masa tare da kuma mishi bayanin meya kawo su, with shock yake kallon su sai kuma ya daure yace "Sure, ɗa nane hope ba matsala?" suka mika masu envelope ɗin hannun su suka ce idan ba damuwa ka isar mana da sakon nan zuwa gare sa, ya karɓa suka masa godiya daga haka suka juya suka fita, haka nan yaji hankalin shi ya tashi sai kuma ya juya ya koma parlorn na sa, briefly ya musu bayanin me ya kawo su, Farouq yaji hankalin shi ya tashi, yana mika ma Farouq envelope ɗin Mummy ta kwace da sauri ta buɗe tana karanta contents ɗin ciki, ta sauri ta ɗaga kai tana kallon Farouq, wanda Daddyn ma kallon nasa yake yi, Na'ila tace "Sammaci kuma daga court? amma ko sun fara hauka ne? Ko dai ba nan zasu kawo ba?" Farouq ya fara jin zufa na karyo masa strictly Daddy ke kallon sa yace "Umar karya kace min baka san akan menene ba, dan baka nuna wani shock da jin maganar ba, so what is it?" ya girgiza ma Daddy kai ba tare da yace komai ba, yana mamakin dama Niswa tasan gidan su ne ko kuma tracking ɗin sa akayi.

Bayan kwana biyu, Daddy ya fito yana tsaye a compound yana waya sai ga Rayyan da ya sako Niswa a gaba sun fito daga part din Mummy suna tahowa inda Daddy yake tsaye, bayan sun kara sa duk suka shiga motar bayan Rayyan ya data motar yana kallon Niswa dake bayan motar yace "Saura idan anje ki tsaya kina rufe baki kiki bayani ko yace ba haka bane kiyi shiru, dan wallahi tun a wajan zan fara dukan ki kamar jaka" bata ce komai ba haka Daddy ma.

Hauwa Jibrin Sulaiman

Hauwajay writes __ ***