2.
*JANJANI!*
*HADIZA D. AUTA.*
***
Ina kuke ma'abota son ado da ƙwalisa? Kuma masu ra'ayin gayu da ƙyalƙyali. To ku shiga group ɗin mu domin burge kanku da makusantanku.
Masu zuwa taro irin na alfarma, masu ra'ayin fita da fitarta don kwarkwasar burge Habibi, ku matso kusa ga bikin zuwa har da zanin ɗaurawa.
Muna da kayan kece raini da shiga wurin biki a cikin taƙama. Kayanmu zai sa a fita daban a cikin matan gidan bikin suna ko shagalin aure. Ni kaina, na haɗu da wata customer a wurin biki na kasa gane ta ba. Sai kallon ta nake yi cikin burgewa ina ƙara kallon kyakkyawar shigar da ke jikinta da yaranta, na bi ayarin masu tambayar mene ne sirrin, kuma ina ta saye kayan matso kyawu da kwarjini? Buɗar bakinta ta ce mana,
"Tun da kuna son ku ji sirrin, ku zo ku saye kaya a inda nake sayen nawa a koyaushe. Saboda can ne nake fitar da kaina kunya har na fitar da yarana, su ma suna fita fesfes kamar yaran masu kuɗi. Kuma wannan dalilin ya sa yarana suke acan-acan tamkar sabon wata daren goma sha uku. Dukan ku ku garzayo mu je wurin *DEEJAH ROYAL COLLECTION* ku ga abin mamaki."
Idona na mutsuttsuke saboda sunana da na ji Lantana tana bayyana wa matan gidan. A take na shiga zayyana musu komai daki-daki, saboda ina kawo leshi na alfarma a cikin farashi mai sauƙi, atamfa ta zuwa ganin Shugaban Ƙasa har da ta daidai ƙarfinki, takalmin shiga dangin miji, jakunkunan kere sa'a, kayan kitchen na isa, uwa uba kayan gwanjon yara masu kyau da ƙarko sai an darje.
Ku yi joining group ɗin mu ku kwashi garaɓasa.
*BIYU.*
Daram-da-dam! Shi ne kalar sautin da na ji zuciyata tana yi babu ƙaƙƙautawa. Jikina ya hau kyarma, nan take gumi ya shiga tsattsafowa a jikina. Hannuna yana rawa bakina yana kakkarwa na shiga nuna ta ina ƙoƙarin haɗiye wani dunƙulallen yawun da ya tsaya mini a maƙogwaro, wanda ya ƙi wucewa ta daɗi kuma ya ƙi bari numfashina ya fito daidai kamar yadda ya saba. A haka na yi ƙarfin halin furta maganar da na ji tana fita daga bakina ba tare da na shirya ba.
"Aur...aure fa?"
Yanayin fuskarta ya sa na ji wata jarumta ta lulluɓe ina ina cewa, "Yo ai Bangis ya gama aurensa a duniya tun daga kaina. Sai dai idan ya je lahira ya auri matan hurul'aini, amma ba dai matan da duniya ta gama ƙyanƙyashewa ta yaye ba."
Na ƙare maganar cikin tafasar zuciya numfashina yana ƙoƙarin sarƙewa. Wani kalar murmushi na gani kwance a kan fuskarta kafin ta tako a hankali ta tsaya gabana, tamkar ba ta fahimci kalar tashin hankalin da ta jefa ni a ciki ba. Kafaɗata na ji ta dafa, hakan ya sa na sandare tamkar mutum-mutumi ina kallon ta, bayan ta sauke mini hannun da nake nuna ta da shi, ba tare da na samu kuzarin motsawa daga suman firgicin da ta jefa ni cikin komarsa, ta ce.
"Don Allah ki kwantar da hankalinki kin san ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba. Saboda ban zo gidanku don na ɗaga miki hankali a banza ba. Na zo ne a bisa umarnin Bangis saboda ba ya son yin gaban kansa, a cewarsa ba zai taɓa aurena ba idan ba tare da yardarki ba. Hakan ya ba ni ƙarfin gwiwar tunkarar ki ido da ido ba tare da na tsaya a kiran waya ba kamar yadda ya so na yi, saboda zuwa da kai ya fi saƙo."
Tsahirtawa ta yi da maganar tana sakin kafaɗata ta koma haɗa hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo, bayan ta yi wani kalar durƙuso a gabana tamkar mai roƙon gafara tana cewa,
"Don Allah ba don ni ba, ki amince na auri mijinki mu raya sunnar Ma'aik...."
Wani kalar kukan kurar da na yi mata mai haɗe da ihu da kururuwa, wanda ni kaina ban san na aikata abin da na aikata ba, sai da na gan ni saman ruwan cikinta kuma maƙure da wuyanta tana shure-shure, yayin da Bangis da sauran 'yan aikina suke kokawar ɓanɓare hannuna da ke riƙe da ɗan maƙwallatonta, ina ƙoƙarin fisge shi daga cikin maƙoshinta. Kafin na ji saukar wani kalar mari a gefen fuskata, wanda ya saka ni sakin ta na koma kallon Bangis zuciyata tana tafasa, kafin na haɗiye ɗacin zuciyar na yi magana cikin wata raunanniyar murya ina nishi.
"Ni ka mara a sanadiyyar karuwa?"
Yana ƙoƙarin ɗaga ta fuskarsa a haɗe ya mayar mini amsa da cewa, "Kisa kike ƙoƙarin yi mana a cikin gida, kuma ni ba zan zuba ido na bar ki ki jawo mana musiba ba. Dubi yadda kika farfasa mata fuska da duka, amma hakan bai isa ba har sai kin kashe ta hankalinki zai kwanta?"
Ya ƙare maganar a fusace cikin ɗaga murya, kafin ya koma korar 'yan aikina cikin tsawa yana faɗin kowa ya bar wurin, har da haɗa musu da shuri tare da jefa musu filallan kujeru yana nanacin ba ya buƙatar ganin kowa su tafi su ba shi filin falon, tamkar wani zararre.
Ni kam tsabar mamakin da ya ba ni ya hana ni ɗauke kallona daga kansa, ina ta jan numfashina da ƙarfi saboda ya kasa daidaituwa a cikin ƙirjina. Hannuna a kan gefen da ya mare ni na shiga maimaita faɗin,
"Ni ka mara a kan karuwa?"
Sai a lokacin ya ba ni amsa da cewa, "Saudat, ba karuwa ba ce, kuma idan har ba kya ra'ayin abin da ta zo da shi ai lafazin baki kaɗai ya isa ki nuna mata rashin gamsuwarki, ba sai kin saka mata hannu kin dake ta ba har kina neman kashe ta ki jawo mana fitina."
"A tunaninka abin da ta zo mini da shi ba fitina ba ne? Shi kansa zuwan nata cikin gidan nan ai wata babbar fitina ce, mai haɗe da baranzana ga rayuwarmu duka, bayan tashin hankalin da take ƙoƙarin jefa mu daga ni har kai, amma kana ƙoƙarin goya mata baya. Don haka ta yi gaggawar ficewa daga gidan nan ko na yi biji-biji da rayuwarta a yanzu nan! Sai ka ga asalin musibar da kake faɗa a aikace ba a baki ba!"
Na ƙare maganar tare da zabura na yi kanta, ina ƙoƙarin kai mata wawar cafka ta zame cikin zafin nama ta nufi hanyar fita waje da sassarfa. Bayanta na bi da gudu ina ihu da aikata mata kalolin zagin da ni kaina ban san na iya su ba sai a ranar. Riƙe ni ya yi har ta fice ban daina kokawar ƙwace kaina daga ƙaƙƙarfan riƙon nasa ba. Takaici ya sa na saka hannu biyu na tura shi baya da ƙarfi bayan na daki ƙirjinsa. Hannu na shiga nuna masa ina magana hawaye yana bin fusakata, don sai a lokacin na ji ruwan hawayena ya dawo bakin aiki.
"Ba ka isa ba Bangis! Na ce da kai ba ka isa ka yi abin da kake ƙoƙarin aikatawa ba Bangis! Saboda a kan wannan abin zan iya kashe kaina, na kashe ta, kai ma na kashe ka. Idan kuka je lahira sai ku yi auren a gaban Allah bayan wutar jahannama ta gama ƙona jikinmu gabaɗay....!"
"Lubna!"
Ya kira sunana cikin ɗaga murya, ni ma na ɗaga tawa muryar ina faɗin, "Ba na son jin komai daga bakinka Bangis! Don Wallahi-wallahi zan jawo abin da sai kowa ya yi danasani daga kai har ita! Matuƙar ba ka yi watsi da wannan baƙin ƙudurin naka mai muni ba! Yadda ka aure ni ni kaɗai tun ina da cikakkiyar lafiyata; haka za ka ci gaba da rayuwa da ni ni kaɗai a yanzu, ko kana so ko ba ka so! Saboda ba a halacci wata macen da za a kira da sunan matarka ba idan ba ni b...."
"Kin fi son na je na yi ta zina ina bin matan banza da na auro wata mu rufa wa juna asiri?"
"Ai asirina da naka duka suna tafin hannuna, kuma aurenta ba zai sa asirin ya rufu ba matuƙar na ga damar buɗewa kowa ya sani."
Wani kallo ya yi mini cikin sanyin jiki kafin ya bar wurin da zafin nama ya nufi hanyar ficewa. Ni kam sai a lokacin ƙafafuwana suka kasa ci gaba da ɗaukar gangar jikina. Ƙasa na sulale ina wani irin marayan kukan da ban san ina zan sa kaina na ji sanyi ba.
Ban san ya aka yi 'yan aikina suka ƙaraso wurin ba, saboda wani kalar numfarfashi nake yi ƙirjina ya danƙare da ƙuncin rai da tsananin ɓacin rai. Ganin halin da nake ciki suka rirriƙa ni zuwa harabar gidan, a take ɗaya daga cikin direbonina ya ja mota bayan sun saka ni suna jera mini sannu. Bai zame ko'ina da ni ba sai wata asibitin da ke Abuja, wadda nake yawan kai ziyara lokaci bayan lokaci ana duba mini lafiyata.
Cikin ɗan lokaci aka ba ni gado, nan take likitoci suka rufu kaina suna ta gwada bajintarsu. Idanuwana a rufe ina jin komai da ake yi mini, amma sun yi mini nauyin da ba zan iya buɗe su ba, kafin nannauyan barci ya yi awon gaba da ni, wanda ban tashi farkawa ba sai misalin ƙarfe shida na yammacin ranar. Abin takaici, babu abin da ya fara zuwa kaina da idona sai fuskar Saudat, tana yi mini murmushinta mai cike da barazana ga ɗan sauran farincikin da ya rage a cikin rayuwata.
"Bangis."
Na ambaci sunan a bakina ina yamutsa fuska bayan na yi wata zabura daga kwance.
"Ga ni, me kike so?"
Cikin sauri na buɗe ido, sannan na koma dafe kaina da ke mugun sarawa tamkar zai rabe gida biyu. "Don Allah ki yi haƙuri, kuma ki kwantar da hankalinki kin san ba isasshiyar lafiya ce da ke ba."
"Na kwantar da hankali fa ka ce?"
Na yi maganar ina kafe shi da ido ko ƙiftawa ba na yi. Saboda mamakin maganarsa tamkar bai san komai ba, tamkar bai san ƙuncin da ya yi silar jefa ni ba. Kamar ya manta baƙin sirrin da nake dako a raina mai hana ni sukuni a duka lokacin da takaicinsa ya dawo mini sabo.
"E, ki rage damuwar da kike yi don Allah. In dai a kan batun da Saudat ta zo da shi ne wallahi makamancin hakan ba zai sake faruwa ba har abada. Wanda ya faru ma kuskure ne da tsautsayi, irin wanda ni kaina ban so ya faru ba tun a farko, nacin da take yi a kan na aure ta ne ya sa na ce ta yi miki magana, don waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi, amma daga wannan karon za a kiyaye in sha Allahu."
Duk da maganganunsa sun rage mini nauyin da nake jin a cikin ƙirjina; amma sunan Saudat da ya ambata daga bakinsa ya ƙara mini zafin da nake ji a cikin zuciyata. Saboda babu sunan da na ji na tsana a lokacin kamar sunan, don a raina ina jin ko a cikin dangina aka samu mai irin sunan sai na tsane ta ko da ba ta yi mini komai ba.
"Karɓi ki sha."
Zancensa kenan da ya saka ni ƙare wa fuskarsa kallo kafin na dawo kan abin da ke hannunsa. Ruwan tea na gani a kofi yana miƙo mini fuskarsa a raunane cikin ladabi har yana ranƙwafa mini, tamkar bawa da uwagijiyarsa. Murmushin takaici kawai na yi, ina ƙoƙarin yunƙurawa da niyyar na tashi zaune amma na kasa, daidai lokacin wata ɗaya daga cikin 'yan aikina mai suna Laure ta buɗe ɗakin ta shigo. Da hanzari ta ƙaraso, ganin Bangis yana ƙoƙarin taimaka mini na jingina bayana, filo ta yi hanzarin kaiwa jikin ƙarfen gadon Bangis ya daidaita mini zaman, saboda ban da kuzari ko kaɗan, sannan jikin nawa ta ko'ina ciwo yake yi mini.
Da ido na yi masa nuni da kofin alamun ya ba ni na sha, abin mamaki sai ya koma wayancewa yana faɗin,
"Bari na zubar da wannan a sake haɗa miki wani saboda ya yi zafi sosai."
Cikin sauri ya nufi toilet ɗin da ke cikin ɗakin jinyar, jim kaɗan ya fito da kofin a wanke alamun ya zubar da tea ɗin kamar yadda ya faɗa. Ajiye kofin ya yi gefe bayan ya yarfe shi sannan ya ɗauki wani ya miƙa wa Laure ya ce ta haɗa mini wani tea a ciki.
Idona a kanta har ta gama ta rage masa zafi ta iso bakin gadon tana faɗin, zan iya sha da kaina ko ta ba ni na sha da kaina. Hannu kawai na miƙa mata cikin ƙarfin hali da niyyar karɓa, wataƙila fahimtar zan iya zubar da shi ya sa ta fara ba ni a baki da ƙaramin cokali ina sha, tamkar wata ƙaramar yarinya. Bangis ya shiga duba agogo da ke hannunsa yana cewa,
"Zan tafi akwai wanda zan gani yanzun nan. Idan na gama abin da ya kai ni da wuri zan dawo ta nan mu yi sai da safe. Idan kuma kika ji shiru harƙallar ce ta riƙe ni, in sha Allahu tun da sassafe za ki gan ni."
Kiss ya yi mini a goshi da kumatu sannan ya fice cikin sauri yana ɗaga mini hannu alamun bye-bye. Fitarsa ta sa na dakatar da Laure daga ba ni tea, nannauyar ajiyar zuciyar na shiga saukewa wata bayan wata. Saboda wani lokaci ina rasa gane kan Bangis da ma'aunin da zan auna shi. Yau zallar kulawa da tsagwaron soyayya mai saka ni mantawa da kowa sai shi kaɗai a cikin duniyata, gobe kuma miskilancinsa da ke hana ni rawar gaban hantsi har na ji na tsani kaina da duk wanda ya raɓe ni.
"Ina wayata?"
Zancena kenan a lokacin da na gama nazarin sarƙaƙƙun halayen Bangis masu wuyar fassara. Kai-tsaye ta sanar da ni tana hannunsa kafin na sake yin wata magana; sai ga dattijuwar mai aikina Inna uwa da wayar a cikin ladabi ta sanar da ni 'yar laɓai ne ya ce a kawo mini, a cewarta har ya ja motarsa ya tafi kuma ya sake dawowa ya ce ta kawo mini.
"Hummmm!" Na furta, ina karɓar wayar na shiga nazarin wa ya dace na fara kira. Saboda na kasa tantance me zan yi da abin da zan aikata, don rabin fushina ya faɗa a lokacin, duba da yadda Bangis ya ba ni haƙuri kuma ya tabbatar mini an rufe babin zancen. Amma haka kawai na ji ina ra'ayin neman Zee, sai dai na yi mata kira ya fi huɗu ba ta ɗaga ba, a ƙarshe ma sai jin wayar na yi busy idan na kira. Hakan ya tabbatar mini da ta yi blocking ɗin lambar alamun ba ta son yin wata magana da ni. Dole wayar Laure na karɓa na tura mata saƙo, ina sanar da ita ina asibiti kuma ina buƙatar ganin ta cikin gaggawa, ko babu komai zan ji daɗin hakan idan ta kawar da laifukan da na yi mata ta zo.
Bayan nan na kira Anti Mami muka gaisa, ita kam ban sanar da ita rashin lafiyar ba, amma yanayin muryata ya sa ta gano da kanta ba na yanayi mai daɗi.
"Lubna, na ji muryarki sai a hankali, ko jikin ne har yanzu?"
Ta faɗa cikin kulawa, "Da sauƙi sosai Anti." Na yi maganar a taƙaice saboda ba na son ta san ina cikin wata damuwa, duba da yadda take hana kanta zama lafiya har sai ta samu tabbacin na samu kaina, a duk lokacin da ta samu labarin ina ciwo. Duk da ba ta ƙasar amma tsabar kulawa koyaushe ba ta gajiya da jera mini sannu.
Shigowar likitan da ke duba ni ya sa na ajiye wayar bayan mun yi sallama da ita. Aka ɗura mini wasu allurai nan take na koma barci, barcin da ban tashi farkawa ba sai da aka yi kwana biyu. A lokacin ne na buɗe ido na ga Zee a gefena kamar almara. Hannu na saka na murtsuke idona bakina yana rawa na ce da ita,
"Yaushe kika zo?"
Cike da kulawa ta yi mini bayanin kwananta biyu a cikin asibitin tare da ni. Cike da mamaki na maimaita kalmar kwana biyun da na ji ta ta ambata. A nan take yi mini bayanin likita ya ce ina buƙatar hutu sosai, shi ya sa aka yi mini allurar da zan yi kwanaki ban farka ba. Raina babu daɗi na ce,
"Har na yi kwana biyu ban san na yi ba? To ai irin haka sai na mutu ba tare da na sani ba."
Na yi maganar cikin zubowar wata ƙwalla mai zafi daga cikin idona zuwa gefen fuskata. A nan take sanar da ni ta ce da likitan kada a sake yi mini irin allurar, ganin yadda nake komawa tamkar babu rai ko hannuna ba na iya motsawa, idan aka ɗauke numfashina da ke fita a hankali babu wanda zai yarda ina da rai. Inda ta ƙara da cewa,
"Sai dai bayanin da likitan ya ƙara yi mini ya sa na shiga kokwanto a kan lamarin allurar. Saboda an ce Bangis ne ya ce a yi miki allurar, kuma a hana kowa shiga inda kike gudun a sake tayar miki da hankali, a jawo miki wata sabuwar matsala."
"Bangis kuma Zee? Shi ne zai ce a yi mini allurar da zan yi kwanaki ban farka ba?"
"E, haka dai likitan ya faɗa mini, wataƙila duba da yadda aka ce mutane suna ta zuwa duba ki ne, don a cikin su har da abokansa da wasu daga cikin danginku da ke nan cikin Abuja. Su ma sun ce Anti Mami ce ta sanar da su rashin lafiyar, sannan kuma ta roƙi alfarmar a zo a duba mata ke."
"Allah Sarki Anti. Ai na ce mata jikin da sauƙi, kuma ban faɗa mata ina asibiti ba." Na ƙare maganar cikin wani sabon kukan da ya zo mini babu shiri. Kafin Zee ta shiga rarrashi na tana sanar da ni ai sun je gidan aka ce musu ba na nan, shi ne suka garzayo asibitin don su ga yanayin jikin nawa. Amma duk suka zo barci nake yi sai dai su bar abin da suka kawo su juya. Sannan ta ƙara yi mini bayanin cewa,
"Ni fa na gargaɗi Likitan da ke kula da ke a kan kada a sake yi miki irin wannan allurar, saboda masu zuwa duba ki suna buƙatar sanin halin da kike ciki."
"Hakan ya yi Zee, ni ma ba na buƙatar allurar. Amma Bangis fa?"
Wani kallo Zee ta yi mini a ƙufule kafin ta haɗe rai tana cewa, "Shi ma an ce yana leƙowa ya gan ki ya juya. Duk da ni har yanzu ba mu haɗu ba, don lokacin da yake zuwa ni na tafi gida yin wani abu."
Daga haka ta ja bakinta ta yi shiru ba ta sake cewa da ni komai ba. Na so a ce na yi mata tambayoyin da ke raina a kansa, amma sanin ba zan samu amsa yadda nake buƙata ba na kawar da kai ina goge hawayena da ya kasa tsayawa, sai gogewa nake yi wani yana ƙara saukowa a kan fuskata.
"Da ma kin daina kukan nan, kada ki ƙara wa kanki lalur...."
Banko ƙofar ɗakin da muka ji an yi ya sa muka kai kallonmu wurin babu shiri. Bangis ne ya ƙaraso gaban Zee yana nuna ta da hannu cikin faɗa yana cewa,
"Sau nawa zan raba ki da matata?"
Wani kalar murmushi na ga Zee ta yi masa tana yi masa kallon sama da ƙasa, sanin ba za su kwashe ta daɗi ba na yi hanzarin faɗa masa ni ce na kira ta ba zuwan kanta ba ne. Kaina ya juyo fuskarsa cure ya shiga nuna ni da key ɗin mota yana faɗin,
"Ok, ke kika kira ta ko? To ta zauna ta ci gaba da jinyar taki. Ni ko ban zo ba za ta zamo madadin...."
"Ka yi haƙuri don Allah."
Na faɗa cikin raunanniyar murya hawaye yana mini zarya a kan fuska. A fusace ya yi gaba da niyyar ficewa daga ɗakin, ban san me ya tuna ba ya sake juyowa yana cewa,
"Wallahi ba zai taɓa yiyuwa wannan munafukar ta hana likitan yin abin da zai taimaki rayuwarki ba. Kuma a wannan karon ma na ba ki zaɓi ni ko ita kamar yadda muka yi a baya. Saboda na gaji da ikon da take nunawa a kanki ke kuma kina biye ta tamkar ita ce ta kawo ki duniya. Sau nawa zan sanar da ke ba ta son tarayyata da ke?"
"Bangis, wallahi Zee ba ta da matsala, kawai dai ka kasa fahimtar ta n...."
"Yi mini shiru malama! Babu wani ƙudurin alheri a ranta dangane da mu face na shiga tsakanina da ke. Kuma na rantse da Allah a wannan karon ba zan ɗaga mata ƙafa ba, matuƙar ba ta fita daga cikin rayuwarki b...."
"Dakata Malam! Kada ka ɗauki cewa zan zuba maka ido ka ci zarafina a banza! Sannan kada ka yi tsammanin wai wannan barazanar taka za ta saka ni rabuwa da Lubna, saboda Allah ne Ya haɗa mu tun kafin ka san za ku haɗu har ka aure ta. A kan me zan ji tsoron ka? Me kake iya yi mini? Ko an faɗa maka ni ita ce da zan ƙyale ka ka ci kashi a kaina, a kan banzar allurar da kake sa ana yi mata, don kawai a sabauta mata rayuwa?"
Ido ya zaro a cikin kaɗuwa ya ce, "Yanzu Zee ni kike yi wa sharri? Ta ya zan sa a yi mata allurar da na san mai cutarwa ce?"
D. Auta ✍️