FreeArewaPen original
UMARNIN ZUCIYA.
- 1views
- 73chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1.
*JANJANI!**HADIZA D. AUTA**FARKO.* Zaune nake a cikin katafaren falona, wanda ya sha kayan alatu kuma ya ƙawatu da ado irin na zamani. Babu motsin komai a cikin falon sai na agogon da ke bugawa, tare da ƙarar Ac. Zuzzurfan tunanin da na afka ya hana ni jiyo ƙarar wayata da ke gefena tana neman agaji. Sai da na kai kallona a kanta sannan na cire tagumin da na yi, ina sauke nannauyar ajiyar zuciya na ɗauki wayar. Ganin sunan mai gadinmu ya fito ɓaroro a cikin fuskar wayar; na ɗauka cikin rashin kuzari ba tare da na ce komai ba ina jiran cewarsa. "Hajiya kin yi baƙuwa, ta ce sunanta Zee Musa, a bar ta ta shigo ko a ce da ita ba kya ƙasar?" Ƙirjina ne ya hau bugawa kafin na ba shi amsa da cewa, "Bar ta kawai ta shigo." Ina gama faɗar hakan na ja guntun tsaki babu shiri, saboda sunan Zee da na ji a kunnena, ya saka ni jin wani kalar ɓacin rai ya ziyarci zuciyata. Duk da in...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.