Page 9
by @legendspen
*SAKATA*❤️⚓️
🌻Stroy and written🌻
By
Sayyid writer (Legend)✍️
*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*
*(FUWA)🖋️📚*
SHAFI NA TARA
(P.09).
بسم الله الرحمن الرحيم
"Mitcheww." na ja wani dogon tsaki, tare da yin gaba. Sai dai ban kai ƙofa ba na ji an riƙo mun hannu, ina juyowa a ka ɗauke ni da mari, wanda nima banyi wani dogon tunani ba, na ɗauke shi da nawa marin. Sai ƙarar ya bada Tas! Tas.
Da mugun mamaki ya ɗago ya kalleni, ni kuwa sai haki nake kamar wata zakanya, banyi au ne ba kuwa naji ya kwarfeni da ƙafarsa na faɗi ƙasa Tim!, ai kuwa ya bini da duka. Ya fusa ta iya fusa ta, nima kuma na fusa ta iya fusa ta domin baki na bai mutu ba, faɗi na ke. "Shege, mugu, azzalumi, kuma wallahi zai ka ga gatana, wallahi sai munyi shari'a da kai." shi kuwa duka na ya ke amma da ƙafa, cikin sa'a na riƙe kafar ta sa, na gan tsara masa wani mugun cizo, kuma nak'i ci kawa har sai da na had'o da fata, da sauri ya janye k'afar tare da matsawa, nan take zuciyata ta ce mun. "Faɗan bai k'are ba." ai kuwa na tashi da mugum guda na ɗane bayan shi kamar wata biranya, na shiga gantsara masa cizo a wuya, shi kuwa faɗi ya ke. "Baki da hankali ne?, sauka a kai na." Salatin da Ummanah ta saki ne ya sa jiki na wani irin mutuwa, kirjina ya shiga bugawa da k'arfi-k'arfi. "Sannu 'yar biri." sai a lokacin na fara ƙoƙarin dirga ƙasa, idanunta suka kai kan ƙafarshi da ke fitar da jini, ga kuma shatun haƙorana a wuyansa. "Kashe shi zakiyi kenan." miri-miri nayi da idanu tare da fad'in. "Ina shigowa ya kifa mun mari." Ba ta ko kula ni ba ta shigo ɗakin tare da kama hannuna ta shiga jana a ƙasa, kamar kayan wanki.
"Nashiga uku na lalace." kawai nake iya fad'a a raina domin nasan yau na bushe har hanjina.
"Ummanah dan Allah kiyi haƙuri, wallahi shine ba shi da gaskiyya, wai sai na share masa d'aki daga na ce bazan share ba shine ya mare ni." Sai da na fad'a kuma, na tuna ɓaran-b'aramar da nayi, ni a rayuwata kwata-kwata ban iya ƙarya ba, komai gaskiyya nake fad'a kai na tsaye. "Shine kika fara gantsara masa cizo ko, ke ga mahaukaciya, karya ko?."
"Wallahi Ummanah ba haka ba ne, mari na yayi." ban ƙarasa rufe baki ba, naji saukar mari tare da bulala, ina ihu ina kororoto amma Umma ƙara zanbad'a mun ta ke. Daman Ummanah kwata-kwata ba ta iya duka ba, duk lokacin da ta dake ni sai tayi mun rauni, shi yasa Abbanah yayi mun fad'a kan na kiyaye abinda zai ɓa ta ma ta rai, to lokacin da ta da ke ni ma na ƙarshe a kan Mus'ab ne, kai Mus'ab ya zama masifa a rayuwata.
Tun ina kuka da bata haƙuri, har na yi shiru gaba ɗaya duk wani ƙarfina ya ƙare, sai da ta ga ji dan kan ta sanan ta kyale ni tare da fice wa, ta bar ni kwance ina kuka.
Nayi kusan minti goma a zau ne, zuciyata na ta saka mun abubuwa kala-kala, ta ce mun "in je ina bu ga masa dutse a kai, sai dai ko mene ayi mun.", ta ce mun."In je in ƙa re mai tana di, zagi ta uwa ta uba" ko hakan zai kawo karshen zumuncin nan." abubuwa kala-kala, ƙarshe na yanke mafita guda d'aya na tarka ta na bar gidan baki daya, na je gidansu Masrur ko a 'yar aiki ya kai ni, daga baya mu yi aurenmu.
A b'angaren Ummanah kam, ta na ga ma duka na ta nufi ɓagarensu Mus'ab, ya na zaune kan kujera ya rasa mai ke masa dadi, sallama tayi d'akin ya amsa. "Yanzu kai Mus'ab yarinya k'arama za ka tsaya har ta mare ka, ba ka b'abbalata."
"Ummah kiyi hak'uri, bana son na dake ta nayi mata rauni."
"Da ba ka ballataba, ai ko shi Abban na ku idan yazo ya ji abinda ta yi sai ya ɓallata, kuma ya na dawo zan faɗamai."
"Ummah dan Allah kiyi hakuri, laifina ne da nasa ta sharar."
"To wallahi daga yau, har zuwa ranar da zaka bar gidan nan ita zata ke maka sharar ɗakin, kuma ka ci abinci idan zaka ci." ta faɗa ta na ta shi, alamun shi ma ya ɓata ma ta rai,a tsakar gida su ka haɗu da Maman ciki, ganin yanda ran Ummanah ke haɗe Maman ciki ta ce."To mai kuma ya faru da 'ya'yan naki?."
"Bari ke dai, lamarin Salma ya fara isa ta, yarinyar nan kullum rashin arziƙinta ƙara gaba ya ke."
"Salma yarinya ce fa har yanzu, wai bakya tuna lokacin da aka haife ta ne?." wata harara Ummanah ta watsa Maman ciki, sanan ta ce."A'a ban haife ta ba, yawo nake da ita a ciki."
"Allah yabaki haƙuri, yanzu ta na ina?."
"Ta na can ta na jinyar jikinta." daga haka Ummanah ta huce, tabar Maman ciki da sakkaken baki, ɗaki ta nufa ta ajiye jakar ta tare da shiga bayi, sauri-sauri take ta fito tazo ɓangaren namu.
Ni kam tun da na yanke shawarar barin gidan, na shiga haɗa kayana, bayan na cika akwatina sanan na jawo wata katuwar jaka na shiga zuba wasu kayan ciki, har da jaka da takalmi na.
Bayan na gama na shiga d'akinta, inda take ajiye kudinta na nufa, naira dubu uku na dauka, sai kuma nayi tunanin dubu uku tayi mun yawa, nan da Gwari avenue baifi 2500, haka yasa na ajiye dari biyar na fito, ina kokarin janyo jaka da akwati na ta shigo, kallo na kawai tayi ba tare da ta ce."Ci kan ki ba." ta huce ciki, ni kam na ci gaba da jan kayana. Ina daf da bakin ƙofa naji an cafke ni, juyuwar da xanyi na ganta da wayar charger ta computer Abbanah, ba wata-wata ta hau zabga mun, ni kuma ina rusa ihu.
Mamam ciki ta shigo da sauri ta na fad'in."Innullahi wainna illahir rajiun, Menene haka dan Allah?."
"Barni na targad'a yarinyar nan, nayi mata rau ni."
"Kiyi ma ta rau ni, sabida me, haba dan Allah." Nikam narkewa na ƙarayi a jikin Maman ciki, ina faɗin."Wallahi sai na bar gidannan ba za'a kasheni ba."
"kiyi shiru ke kuma." Maman ciki ta faɗa, Ummanah kam ajiye bulal tayi tare da shigewa ɗakin, kallona Maman ciki tayi sanan ta ce. "Je ki mai da kayan, kuma kar ki sake irin wanan abun ko da wasa."
"Wallahi Mama bazan ko ma ba, duka na zata ci gaba, ni kawai a bar ni."
"Ki je ki mayar na faɗa mi ki." Maman ciki ta sake faɗa. "Wallahi ko kin mayar sai na dake ki, kuma har can ɓangaren zan zo." Kuka na fara, maman ciki ta ce. "To ai ba ɓangarena zan kai ki ba, muje." tunda ta ce haka, ɓangaren Hajja zata kai ni. Ai kuwa can ɗinne, Hajja na gani na haka ta fara sababi. "Amma wanan uwarta ki ba ta da hankali, to wallahi ahir ɗinta." Ni kam wata tsanar Mus'ab ce sabuwa ta sake fidda rashe a cikin zuciyata, a kan shi anyi mun dukan da ba'a taɓa kwatanta mun ba, an kira mahaifiyata sa mara hankali, duk a kan Mus'ab, kai Mus'ab ya zama tauraruwa mai wutsiya a inda nake." Maman ciki ce tai ta ba Hajja haƙuri, sai da ta ga tay shiru sanan ta ta shi ta tafi. "Tashi ki haɗa ruwan ɗumi." Hajja ta faɗa tana kallona, bayan fitar Maman ciki, ba musu na miƙe nayi Kitchen, a heater na ɗora ruwan ɗumin, sai da yayi sanan na sauke na shiga na watsa ruwa, naji daɗi sosai a jikina, na zo nabi lafiya kujera na kwanta, banko sassauta da tsinewa Mus'ab, har bacci ya ɗauke ni.
Sai wajen la'asar sanan na tashi, zaune na ganshi kan ɗaya kujera dake kallon tawa, amma hankalinshi na kan wayarsa yana dannawa, inaga ma baisan ni ce kwance kan ɗaya kujerar ba, miƙewa nayi ina turu baki, ina hararshi ƙasa-ƙasa, Allah ya gani na tsani Mus'ab, bana ko ƙaunar ganinshi domin a yanzu na fuskanci Mus'ab so yake ya rabani da Ummanah, domin a kwanciyar nan ta wa na ƙara tabbatar da hakan, indai nasamu saɓani da Ummanah tofa a kan lamarin Mus'ab ne, ko mene ribarsa oho, wani ɓari na zuciyata ya ce. "Mutumin da baya sonki, mene ribarsa idan bai rabaki da iyayenki ba?." a fili na furta. "Kurwata kur, mai ɗa ya ci ɗanshi mara ɗa ya ci ƙoƙon tsuliyarshi." Wani kallo ya watsamun, sanan ya ci gaba da danna wayarsa, nima na mayar mai da kallon da hausawa suke cewa. "Harara a duhu." tun da bai san inayi ba.
Bayi na shiga na ɗaura alwala, na fito na ta da sallah, har na kamalla yana zaune, yana danna waya."Mai bautar waya." na faɗa a raina, tare da shiga ɗakin da Hajja ke ciki. "Hajja abinci." Na faɗa daga tsaye. "Ke fa matsalata dake rashin kunya da rashin mutunci, haka ake yi a gidanku." na cuno baki gaba sanan na ce. "Ke kuma matsalal ki mita da sababi."
"Nayi mita nayi sababin, na rantse yanzu zaki ficemum a ɓangare." Shiru nayi nasan zata aika, kaddam ne daga aikin Hajja."To yanzu Hajja mai zan ci?."
"Shiga kitchen, ki dafa taliyar yara ina da ita lodi-lodi." Kicin ɗin na nufa, na shiga haɗa indomie na, ina mamakin yadda Hajja ke cin indomie, a yanzu haka akwai sama da katan biyar a cikin kicin ɗin, ina tsaye har ta kamalla, na juye a faranti na dawo falon, yana nan zaune kaman mutun-mutumi, yana faman bautar waya. Bayan na ajiye na shiga ɗaki, nayi narai-narai da fuska na ce. "Hajja tawa." Baki buɗe take bina da kallo, kamar ta ga sabuwat hallita. "Hajjana, dan Allah wayarki zaki bani, na kira malamin mu na sanarshi bani da lafiya ya sa banzo ba." ita Hajja ba ta wami damu da waya ba, kuma kullum wayarta cike da katin waya, haka su Sadiya za su zo da Walida suyi ta ɗauka suna kiran samarinsu, ni kam bantaɓa ba sai yau, ko da yake yanzu na fara soyayyar.
Dawo falon nayi, sabida naji ana cewa."Waya sa saurayi kana cin ainci tafi tsargawa." Nan da nan na danna masa kira kamar ko yaushe, sai dai yau kiran na shiga ya katse, kafin na gama tantance mai ya faru naga kiranshi ya shigo, murmushi nayi tare da kai lomar indomie baki na, bayan na ɗaga kiran."Fulani mai lambobi da yawa." Ya faɗa bayan na ɗaga."Mijin Fulani, mai gane Fulani a ko yaushe." Na faɗa cikin wani irin salon magana, dani ban ma san na iya ba, ko dan Mus'ab na nanne? Oho mun.
"Fulani, yau kuma wayar wa aka samu?." Ya tambaya cike da kulawa kamar ko yaushe."Wayar Hajja ta ce." Na bashi amsa cikin cool voice, wanda ni dai ban san lokacin da na iya ba."Uhm, Ummanki, Hajjanki, to ni wai wa za'abani?."
"Salma Galadima mana, ita za su baka, ni dai kabarmun Hajjana, da Ummanah."
"Ai kam na barsu, tun da zasu bani abinda nafi ƙauna." Dariya nayi na ce."Zasu baka mana, mussaman Ummanah."
"Yau mai Fulani ke ce?." Dariya na ƙarayi, sanan na ce. "Indomie ɗin Hajja na dafa."
"Yau kina ɓangaren Hajja ne?."
"Can zan kwana, ƙilama na dawo nan."
"Kai Fulani, ai Umma ba za taji daɗi ba."
"Uhm, zataji mana. Ai yanzu munafukai sun shiga tsakanina da ita." Dariya yayi, har ana jiyo sautin shi sosai ta waje, sanan ya ce."Fulani munafukai kuma."
"Uhm, munfukai masu bacci da ido ɗaya." Na faɗa ina ƙara kai indomie bakina, gaskiyya na yarda waya da saurayi ana cin abinci tafi tsargawa."Su waye haka to?." ya tambayeni. "Na ce maka masu bacci da ido ɗaya."
"Su ba su da suna?."
"Uhm..."
"La'ila ha ilallahu muhammadu rasulillahi, amma Salame baki da mutunci, Mus'ab ɗin na zaune kika saka taliyar yaran gaba kika cinye, shi dayake kawo wa baki zuba masa ba." Muryar Hajja ta tare ni daga niyar bawa Masrur amsa, dariya yayi ta cikin wayar tare da ce wa. "Fulani sai anjima." ban iya bashi amsa ba ya kashe wayarsa, sakamakon wani abu da yatsayamun a maƙoshi yaki tafiya, jin wai Mus'ab ke kawo wa Hajja indomie ɗin da nake ci yanzu, yau nice naci abinda Mus'ab ya kawo. Da wani mugun sauri na tashi na nufi banɗaki, domin kwararar da indomie din da naci, amma ina ciki na yariƙe ta katamau, duk yunƙuri na amai yaƙi fita, a dole na wanke bakina na koma ɗakin, ina ta faman cika da batsewa."Ke lafiyanki?." Hajja ta tambayeni. "Haba Hajja ai sai ki ce mun ga wanda ya kawo indomie ɗin, amma kika barni na ci haram."
"Uwariyanki Salame, abincin ne haram?."
"Habba Hajja, Haba Hajja ni dai baki kyauta mun ba." Sallama Babban ciki naji, sai kuma Abbanah ya na ta faman faɗa, ban ma iya ƙarasa tantance abinda yake faɗa ba, na tashi nayi ɗakin Hajja da nasan Ummanah ce ta faɗa masa abinda nayi ya zo ɓallani.
"Har mu mutanen nan zasu mayar ƙananan mutane, har mu za'ayi wanan cin fuskar." Abbanah yake faɗa, shi dai Babban ciki yayi shiri ya zauna kan kujera, Alhaji ƙarami da kawu Madu ne suka shigo sai Yaya ilyasu, babu Abinda nake tamaimaitawa a raina sai. "Innullahi wa inna illahir rajiun, yau kashi na ya boshe. Duka wanan taron a kai na."
"Lafiyanku wai?." Hajja ta tamabaya, bayan su gama zama. "Iyayen yarinyar da Mus'ab zai aura ne suka aiko, wai sun gano yana da wata cuta dan haka sun fasa bashi aurenta."
Legends pen.
(***/ ***).
Daga gobe zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000.
Payment via.
8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.