SAKATA COMPLETE

Page 10

by @legendspen

*SAKATA*❤️⚓️

🌻Stroy and written🌻
             By
Sayyid writer (Legend)✍️
  

   *FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)🖋️📚*

    SHAFI NA GOMA
          (P.10).

بسم الله الرحمن الرحيم


"Har mu mutanen nan zasu mayar ƙananan mutane, har mu za'ayi wanan cin fuskar." Abbanah yake faɗa, shi dai Babban ciki yayi shiri ya zauna kan kujera, Alhaji ƙarami da kawu Madu ne suka shigo sai Yaya ilyasu, babu Abinda nake ta maimaita wa a raina sai. "Innullahi wa inna illahir rajiun, yau kashi na ya bushe. Duka wanan taron a kai na." 

"Lafiyan ku wai?." Hajja ta tamabaya, bayan su gama zama. "Iyayen yarinyar da Mus'ab zai aura ne suka aiko, wai sun gano yana da wata cuta dan haka sun fasa bashi aurenta."

Wani irin dum! Naji a ƙirjina, a fili na furta"Na shiga uku." dan tsorona kar naji an faɗi sunana, ance ni na faɗa. 

"Shikenan sai sun kashe mun jikan, sai sun raba shi da duniyar, Mus'ab idan ka mutu ina zan sa kai na, ina zan sa rayuwata." Hajja ta faɗa tana matse ƙwalla, Abbanah ne ya ce."Hajja ki yi haƙuri dan Allah, iyayen yarinyar nan ba su kyauta ma na ba, kuma sun nuna su ƙananan mutane ne, amma zamu ɗau mataki a kan hakan." Abbanah ya ƙarashe maganar da alaman karaya, zuciya ta ce ta tsinke lokaci guda, ganin fuskar Abbanah da ta Hajja a haka, ga Abbanciki da Alhaji ƙarami sun zuba ta gumi, kawu Madu da Yaya ilyasu tsaye carko-carko,"Duk ni naja wanan abun." na faɗa a rai na. "Yanzu ya za'ayi kenan?." Hajja ta faɗa ta na ci gaba da kukan, Ummanah da Maman ciki sai Anty mamansu Walida ne suka shigo su ma, idanun Ummanah sunyi jawur, kamar ni a kace ba za'a ba wa Masrur ba, ina ga ma tayi kuka.

Zama su ka yi su ma, Hajja ta sake maimaita abinda ta faɗa, cikin sharɓar hawaye. "Hajja zamu sake bashi zaɓi idan yana da wata, sai muje mu nema mai, idan babu sai aduba cikin 'yan Uwa." Abbanah ya faɗa, ni da ke cikin ɗaki na ce. "Sai dai ko can waje, ko ku bashi Walida da ke ƙanwarsa, tunda dai Sadiya an ba da ita, ni kuma ga Masrur abu na, daman ita ce soyayyarsu ke ƙasa na dabo." 

"Nikam Abba ba ni da wani zaɓi a yanzu." Mus'ab ya faɗa, wani kukan Hajja ta ƙara saki, sanan ta ce. "Shikenan, ya cire rai da auren. Ubangiji ka wadaran yarinyar nan da iyayenta." 

"Hajja kiyi haƙuri,amma ni ina da shawara." Ummanah ta faɗa."Kai Umma kin fiya shiga abinda ba ruwanki." na faɗa daga can inda nake a cikin rai na. "Wace shawara ce haka?." Hajja ta tambaya, zama Ummanah ta gyara sanan ta fara magana. 

"Mus'ab dai ɗan mune na gida, kuma tun da wanan maganar ta fara fita ta na zaga gidajejen wa'yanda a kaje nema masa aure, to haka za tai ta zagayawa, ƙarshe ko ina su hana bayan an gama tozarta shi." 

"Hakane wallahi, abinda yake ta faman sani kuka kenan." Hajja ta tare Ummanah, Abbanah kuma kallon ummanah ya yi sanan ya ce. "To mai kike gani?." Shiru ta yi na 'yan mintina, sanan ta sauke wata ajiyar zuciya. "Mai zai hana mu haɗa aurensa da Salma, tun da muna da ita a cikin gida, kun ga dai Sadiya har anyi mata bai ko, ita kam ina ga ko saurayi ma ba ta dashi." Ai ban san lokacin da nayi wani tsalle ta tagar Hajja na dirgo falon, sai gani kamar wacca aka jefo. 

"Wallahi Ummanah ina da saurayi, ina da wanda na ke so, ko Hajja za'a tambaya yanzun nan na gama waya dashi, a gaban ma shi Mus'ab ɗinne, dan Allah kar ku auran Mus'ab." Gaba ɗaya na rikice, na manta a gabansu wa nake, haka shima Mus'ab, ji yake ana magana kamar ihu, amma kwakwalarsa kam dai ta ɗauke, babu abinda yake nanatawa a ransa sai. "Ummah karki yi mun haka, bana son yarinyar nan, natsane ta, bana ko son ganinta." Abbanah ne ya da ka mun wata tsawa, wacca ta sani haɗiye maganar da nake shirin yi, amma jikina sai karkarwa yake, hawaye na bin kuncina, zuciyata na wanu irin tsalle kamar zata fito waje. 

"Amma Allah yayi miki albarka da wanan shwarar." Hajja ta faɗa ta na murmushi."Har mu za'ayi wa hulaƙanci, jikoki 27 Allah yabani, ba a isa a hulaƙantani kan ɗaya ba." Hajja ta sake faɗa, Abban ciki kam cewa ya yi. "Tabbas wanan shwarar tayi, sai dai yakama ta a duba ita yarinyar."

"Har wani haƙƙi take dashi, da ya huce ta yi mana biyayya." Abbanah ya faɗa cike da ɓacin rai, dan shi maganar da Abban ciki yayi ma ta ɓata masa rai."A'a Yaya, a duba yarinyar nan." Alhaji ƙarami ya faɗa. "Yanzu idan ace yarinyar wajenka na nemi ayi wa haka, cewa zakayi a'a ko me?." Hajja ta faɗa kamar zata yi kuka."Ni Hajja ba haka nake nufi ba, kuma kin sani da Mus'ab da Salma da kowane yaro dake cikin gidanan, ɗaya nake ɗaukansu, bantaɓa banbanci su a kan komai ba, Sabida haka na taso naga yayuna sunayi, duk cikin mu wanda bai godewa Abban ciki da Abbah ba sai Allah ya saka musu, tun tasowar mu suke tsaye a kan mu, har zuwa kan yaranmu dan haka bana banbance tsakanin 'ya'yansu da nawa yaran, amma Hajja ki kalli yanda Salma ke yi, a bata damar idan wanda take dashi ɗin ya dace, sai a bawa Sadiya Mus'ab ɗin." 

"Ai har gwanda sadiyan." Mus'ab ya faɗa, bayan ya dawo daga suman da yake."Ni kam Alhaji ƙarami sai nake ganin kaman Salman ce ta fi cancanta, domin ita nata saurayin da take iƙirarin tana da shi, bai ko taɓa zuwa ya gaida ku, bare kuma mu Mata, sanan idan har Salma ba ta taimaki ɗan uwanta ba, wa zata taimaka?." Ummanah ta faɗa, shiru Alhaji ƙarami yayi, sai kuma a lokacin Kawu Madu ya ce."Tabbas hakan yayi, kuma wanan shine amfani da ranar zumunci da zaman lafiya, mu ɗin  ahali ne guda, a kullum burin mahaifinmu mu zama tsintsiya ɗaya, gashi Allah ya amsar addu'arsa ta hanyar bamu mataye na gari, nima ina goyan bayan wanan abun." Maman ciki dai ba ta iya cewa komai ba, tabbas tana farin ciki da hakan, kuma ta ƙara yadda Ummanah macece ta gari, sai dai kuma tana tausayina, domin ta san ba na son Mus'ab kuma shima bai so na. 

"Yanzu zuwa yaushe za'asa ɗaurin auren?." Abban ciki yayi magana, wani irin ihu na saki tare da zubewa ƙasa, domin nasan tun da Abban ciki yayi na'am da maganar to fa sai dai wani hukunci na ubangiji fasa wanan auren. Shi kan shi Mus'ab ji yake kamar ya ƙwalla ihun, dan yana buƙatarsa sosai."A haɗe shi da na Sadiya wata biyu." Abbanah ya bashi amsa. "A'ah wallahi, tun da ita ta gida ce sati uku ko biyu ya isa, domin kusan ba lafiya ba ce dashi." Hajja ta faɗa."Hakane kam Hajja, ni a ganina kwana goma sha huɗun zaifi." Ummanah ta bawa Hajja amsa. "Shikenan, Allah ya nuna mana." Abban ciki ya faɗa, tare da tashi, haka kowa ya tashi sai a lokacin Maman ciki ta kula da cewar bana numfashi, da sauri tayo kaina tana faɗin. "Yarinyar nan fa ta suma." Dawowa su kayi kaina, banda iyayen mu maza da suka fice, Anty ce ta samu ruwa ta bawa Maman ciki ta shafa mun, can bayan 'yan mintuna na sauke ajiyar zuciya tare da buɗe ido, suka sauka a kan Ummanah, ai kuwa na tsala ihu tare da tashi zan fice, da sauri suka riƙeni har da ita Ummanah ɗin, turza ƙafa kawai nake bana iya magana. "Innullahi wa'ina illahir rajiun." kawai Hajja ke maimaitawa, kowa yayi shiru sai karatu da ake mun, tunaninsu Aljannu na tayar, nikam kawai zafin ƙiyayya ce, ta samun harda haushin Ummanah, domin zuciyata babu abinda take nuna mun sai, zallan tsanar da Ummanah tayi mun, gwada kawai na bar musu gidan, son da nake su daina karatun yasa na tsaya da abinda nakeyi, hakan yasa suma su ka tsaya. 

"Dan Allah kar ku auran Mus'ab, bana son shi, Ummanah mai yasa ko da yaushe kika zaɓi ki ba ƙanta mun." Saukar marin da naji a fuskata ya sa nasaki wani fitsari mai mugun zafi, da gudu na ƙara kwasa zan fice, Mamman ciki ta roƙoni. "Nutsu Salma, idan aka barki ina zakije da gudun." Shiru nayi ina kallon tare da zazzaro idanu, kamar wata karya. 

"Ku kyaleta da gidansu, yanzu zan saka a ɓaɓɓalamun ita wallahi." Hajja ta faɗa tana hararata. "Kuma wallahi Mus'ab ne, insha Allahu sai kin aure shi, kinyi biyayyar aure, kin haifa masa 'ya'ya, wanan rashin zama ƙarƙashin inuwa ɗayan naku, bi'izinillahi sai ya zama Alheri a rayuwar ahalin gidan Galadima." Wani mugun Haushin Hajja yazo ya dirja a ƙirjina, gaba ɗaya na rasa menene yake mun daɗi, kukan ko shirun?."Tashi muje." Umanah ta faɗa a tsawa ce, tashi nayi kamar mara laka a jikina, ji nai iska na ƙoƙarin dauka na tayi wurgi dani, dan gaba daya na koma 'yar tsurut. A waje muka ci karo da su Walida sun tawo da gudu, ban ko kallesu ba nayi ɓangarenmu, suka rufamun baya har zuwa cikin ɗaki. "Salma mai ya faru?, ance kin ta da Aljanu a ɗakin Hajja." ji nayi a zuciyata, daman Aljannun nayi ko na ƙarya ne, nayiwa Hajja mugun duka, amma mu tara lokaci na gaba."Wai muna tambayarki, kinyi shiru." 

"Ku tashi ku kyaleta, mugun hali take ji." Ummanah da ta shigo ta basu amsa, tashin su kayi suka fice, na haɗa kai da gwiwa tare da fashwewa da kuka mai ƙara ina faɗin. "Wallahi bazan auri Mus'ab ba, wallahi ko za'a kasheni da duka." ba ta ko kalleni ba ta ci gaba da abinda take, ni kuma na ƙara cewa. " Wallahi ko tsinemun ne sai dai ayi."


A ɓangaren Mus'ab kam, Mama ce ta kalleshi, sanan ta ce. "Ka tashi mu huce ko kaima kukan zakayi?." bai ce uffan ba ya tashi yayi gaba, ai kuwa suna shiga ɓangaren su ya zube a ƙasa tare da faɗin. "Mama Wallahi ba zan auri yarinyar nan ba." Bai kai ga rufe baki ba, Mama ta ce. "Wallahi Mus'ab ko bayan babu raina, ka ƙi auren yarinyar nan, ko ka musguna mata bayan aure, ban ya fe maka ba."


To jama'a, mun iso iyakar free pages, kuma daga nan zamu faɗa cikin labarin, cikin rigima da zallar ƙiyayya.

Gashi dai ance za'ayi musu aure, shin Mus'ab zai bari ya auri yarinyar da bai so, ko Salma za ta auri namijin da tafi tsana?.

Idan har anyi auren, yaya zaman zai kasance, ya Salma zatayi da soyayyar Masrur?


sakata ce zallan kiyayya da dumin ƙaddara!
  
Paid pages suna ɗauke da abubuwa masu matuƙar yawa, da ɗaure kai.

N500 kacal. Masu buƙatar complt kuma 1k ne.

8129553971
Opay
Sani Muhammad lawan.

Shaidar biya ta nan
***.

Paid pages zai fara zuwa ranar Monday, masu buƙatar complt 1k. 

***