Kuncin zuci
by @bintuuu
Basu wani dau lokaci ba suka Isa London, suka dau hanyar gidan Anty Amnah dake arean Kensington.
Anty Amnah ta kasance likita ce kuma tana auren babban likita mazaunin London da yaransu twins maza 'yan kimanin shekaru bakwai. Sunyi murnan ganinsu sosai, twins sai tsallen murna suke suna maqalqalesu Na'ima na dariyansu, bayan sun huta Anty Amnah tayi serving dinsu abincin da ta girka musu sunaci ana hira har suka gama.
Daren ranan suna bisa kan gado cikin dakinsu wanda suke sauka idan sunzo gidan, Na'ima na zaune ta miqe kafanta hannunta riqe da ipad dinta twins suna kwance jikinta suna game tare while Nafisa kuma na kwance gefensu tana chat a wayanta, Kiran Abba ne yashigo wayan Na'ima ta dauka da sallama tana gaisheshi, amsawa Abba yayi ta dayan bangaren tareda tambayanta ya karatu, tace "Alhamdulillah Abba" yace "Hope babu wani matsala" ta amsa da "Eh" yace "Ma Sha Allah, ku dage da karatu Na'ima, banason wasa" tace "in Sha Allah, nagode Abba" da haka yace "Ina Nafisan?" ta amsa da "Gatanan" tareda miqawa Nafisa wayan, bayan sun gama gaisawa da Abban taji Nafisan na tambayan ina Mami,
Suna cikin maganan dinki da Mamin sai Nafisa ta sake miqo mata wayan bayan ta saka a handsfree, bayan sun gaisa Mami tace "Na'ima ga kayanku nan ansiyo wanda zaku saka a bikin, inason aika muku wajen me dinkin Nafisan amma bansan wani kalan dinki kike so ba kuma" cikin sanyin murya Na'ima tace "kowanne kalla yayi" Mami tace "A'a badai kowanne kala ba, saka wayan a handsfree" Nafisa dake gefe tace "a handsfree yake fa Mami" sai Mamin tace "Yauwa kinaji Nafisa, ta fada miki kalan wanda takeso din sai ki turawa Meerahn, nidai zan aika kayan gobe sai ku gama maganan a tsakaninku" Nafisa tace "toh Mami zanyi magana da ita a WhatsApp" da haka sukayi sallama Nafisa na kallonta tace "Meerah never disappoint, zansa ta turomin latest one's sai mu zaba"
Na'ima bata amsa mata ba ta karbi wayan nata ta miqawa jabeer dake kusa da ita ya cigaba da game dinda sukeyi.
Suna nan zaune anty Amnah ta shigo dakin tace "sun hanaku bacci ko" Na'ima tayi murmushi tace "A'a game ai mukeyi" Nafisa tace "Anty, Ya faruk bai dawo ba?" tace "A'a" don tunda yakawo su nafisa aka taba hira dashi ya sake ficewa akan akwai gurin da zaije daga nan ya wuce masauqinsa kuma.
Anty Amnah na tsaye tayi clapping hannunta kadan tace "Boys, it's time for bed" jabeer yafara kukan shagwaba akan shifa a wajensu na'ima sai kwana, hararansa tayi tace "My friend get down from that bed" Na'ima tace "Anty kibarsu mu kwana anan din" tace "A'a zasu takuraku, oya muje" Haka ta tusa kansu suka bar dakin tana musu saida safe.
Washegari suna breakfast gaba dayansu, Nafisa ta saka Faruk a gaba da roqon sai yayi rescheduling flight dinsa Anty Amnah ma na tayata , mijinta da yake gurin yace "What if he has something to do back home?" Anty Amnah tace " babu ma...beside, it's weekend. work can wait till Monday, right son?" faruk ya danyi dariya yace "Zan duba available flight for Monday then" Nafisa tayi saurin cewa "zaka samu in Sha Allah" mijin Anty dasuke kira Uncle Yasir yayi murmushi yace "Su nafisa qorafi ya fara karbuwa" dariya tayi tace "zai samu Uncle"
Itadai Na'ima tayi shiru tanacin abincin dake gabanta sannan tana sauraronsu, Faruk ya amsawa Nafisa da "I'm not sure yet" sai ya dauki wayanshi dake kan table din zai duba.
Nafisa ta juya ta kalli Na'ima tareda kai mata qaramin bugu a kafada tace "kinaji inata faman roqo ko ki tayani" Na'ima tayi murmurshi batace komai ba tacigaba da shafawa jafar nutella a jikin bread, sai Faruk ya dago kansa yace "Habibtin Mami ko in tafi?" dariya tayi kadan tace "A'a Yah Faruk" Anty Amnah tace "Itama batason ka tafin ai, kawai nafisa tafita baki ne"
Faruk ya gama rescheduling flight din ya ajiye wayan yace "There... it's done, saiku shirya anjima mu tafi park" Nafisa ta ajiye tea din hannunta tayi masa thumb up tace "You're the best" twins ma sai sannan suka fara ihun murna jin an ambato zuwa park.
Zuwa 11 o'clock suka tattara aka tafi park Anty Amnah ta hada musu lunches dinsu suka saka a booth dan ita da Abban twins sunce baza suje ba zasu huta a gida kasancewan weekend ne.
Wunin ranan a park sukayi, acan sukayi sallolinsu suka ci abinci, Faruk yasasu sun hau different wheels yana musu video sannan sunyi games kala kala shima har Nafisa ta ciyo kyautan teddies ma twins, sunci banza sunci wofi dai sannan suka koma gida da yamma duk a gajiye.
Washegari wayewar sunday yakamata su na'ima su koma Oxford don school, amma tunda suka tashi Nafisa take mitan itafa ta gaji, bayan sun idar da sallah ta cigaba da mitan, Na'ima na jinta batace komai ba ta miqe tana linke sallaya.
Ganin Na'ima bata kulata ba sai tace "Sis ko mubari sai gobe mu koma?" Na'ima tayi murmushi tace "Allah ya kaimu toh" dan tasan qarshenta hakan ce zata faru daman, Nafisa tace "Kinga dama bawani lectures muke ba dama, it's not a big deal" Na'ima ta koma kan gadon ta kwanta tace "hakane Anty Nafisa" itama tana dariya ta hau gadon dan sake komawa wani baccin.
A gurin breakfast Nafisa ta fadawa su Anty Amnah bazasu koma school ba acewarta basuda wani active school activity ranan Monday din" Faruk ya juya yana kallon Na'ima yace "Dagasken take?" ta gyada kai tace "Eh" baice komai ba Anty Amnah tasake tambayanta "Na'ima are you sure?" ta sake amsawa da "Eh dagaske ne Anty" Nafisa na murmushi tace "Bafa karya muke ba" Faruk yace "Ai nasanki ne Nafisa" Anty Amnah tace "Toh shikenan sai ku huta sosai, nima zanje hospital anjima kadan akwai patient dina dazan duba she's under my care" Faruk yace "Ina uncle fa?" tace "Yana bacci tukunna, yayi night surgery jiya".
Yammacin ranan sai ga Faruk da tickets na football match da za'ayi da dare cikin Chelsea stadium, one of the most known stadiums in London, tsalle Nafisa ta rinqa yi kamar ba ita tayita mitan gajiya ba, itadai Na'ima nata fara'a dan batasan komai gameda ball ba amma tanason zuwa taron itama dan she's curious to see the match in person.
Dawuri Faruk ya kaisu stadium din dan 8:00 pm za'a fara match din, bayan yayi parking a gurin da yayi booking suka fito zasu taka zuwa cikin stadium din babu Anty amnah, dan tace batason shiga hayaniya kanta yana ciwo kuma ta gaji twins ma sun barosu a gida, shigansu cikin stadium din Faruk yayi gaba suna binsa a baya yana neman seat numbernsu, sai Nafisa ta juyo tana kallon Na'ima tace "Nice huh?" Na'ima na murmushi sai bin ko'ina da kallo take, tace "It's beautiful..so beautiful" bayan sun samu gurin zamansu basu jima ba aka fara match din Faruk ya miqe yace "I'm coming" sai ya fara kutsawa cikin mutane zai fita daga stadium din, bai jimaba yadawo hannayensa riqe da popcorn da drinks ya rungumosu a qirjinsa, zama yayi tareda miqawa kowaccensu yace da Nafisa "What did i missed?" Idonta na kan field din ta amsa da "Not much" tana kai popcorn bakinta.
At first Na'ima bata gane yanda wasan yake tafiya ba sai Nafisa ke kwatanta mata kasancewar ita ta taso cikin maza a gidansu suna yawan kallon football match sosai.
Cheering din mutane da ihun Nafisa dake gefenta ne yafara sa mata interest sosai akan wasan, aqarshe dai da ita aka miqe ana ihu a stadium din, ba qaramin nishadi match dinnan ya sanya wa Na'ima ba, bakinta har kunne dan fara'a, Faruk ya sunkuyo kusa da ita yana dan daga murya yace "Do you like it?" Ta gyada kai cikin yar dariya tace "Sosai" shima yayi murmushi kawai.
Ranan taga football celebrities dinda ko a mafarki bata taba tsammanin ganinsu face to face ba, it's one of the nights that Na'ima bazata manta ba.
Bayan an tashi daga match din suna hanyan komawa gida ta tambayi Faruk "Kuma yanzu shikenan an kori dayan team din kenan?" yana dariya ya amsa da "Eh" ganin she's new to it, Nafisa ta juyo daga front seat tace "BoBo zan siya mana tickets muje next match tunda kinaso" Na'ima tace "Ai da dadi ne, bansan haka ball din yake da dadi ba" sai Nafisa ta juya tana kallon Faruk sukayi dariya tare sannan ta sake juyowa gurin Na'ima tace "Welcome to the team girl" .