KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Washegari da safe suka kai yayan nasu Airport da motan Anty Amnah, hatta Na'ima saida taji kaman tayi kuka balle Nafisa da ta fara hawaye.
Faruk na kallonsu yayi murmushi sannan yace "Come on girls, nan da 3 weeks or so zaku dawo fa kuma"
Nafisa ta qarasa kusa dashi ta riqo hannunsa bata bar hawayen ba, yana murmushi ya zare hannunsa daga nata, sai ya dagawa Na'ima hannu alamun Bye itama ta daga nata hannun cikin sanyin jiki, da haka ya juya na nufi cikin waiting lounge na Airport din.
Na'ima ta dan daga murya tace "Allah ya kaiku lafiya Yaya" sai da ya sake juyowa yayi musu murmushi sannan ya bacewa ganinsu. Haka suka koma gurin motan su cikin sanyin jiki suka bar Airport din. Bayan sun koma gidan Anty Amnah suka shirya kayansu tareda mata sallama suka tafi train station dan komawa Oxford saboda motan da Faruk din yaje daukansu na Anty Amnah ne.

After that memorable weekend in London, rayuwa ta cigaba yayin da suka maida hankali kan karatunsu wanda saura few months su gama.
The weeks that follows sunyi 
qoqari wajen hada wasu daga cikin thesis dinsu before the spring break, don dama auren Salma yazo within their break ne, hakan yasa lokacinsu yazamo swamped with schoolwork, duk da basa zuwa school din akai akai don sun shigo phase na research a fagen karatun nasu, wani lokacin raba dare suke zaune nan falo kowacce tana nata aikin bisa laptop babu bacci.

Duk da ayyukansu na makarantan da suka sako gabansu hakan bai hanasu zaman hira da cinye cinyen banza da hofi ba, dan nafisa ta koyawa Na'ima cinye cinyen itama basa zama shiru haka nan, aikace aikacen gidan nasu kuwa daman tun farko basu raba a junansu ba, duk wacce ta samu time yi take wanda dama Na'ima ce rinjayen aikin da dafa musu abinci most at times, kuma hakan bai taba damunta ba infact she love doing all the work tabar Nafisan ta huta because she'll ba glad to do more than that to Nafisa.
Ance kaso mai sonka, to hakan take wajen Na'ima, tanason kyautatawa Nafisan, most at times takan shiga dakin Nafisan ta gyara ko Ina ta wanke toilet sannan ta debo kayanta na wardrobe ta goge mata su tas ta jera. Wani irin bond ne mai tsafta a tsakaninsu wanda in ba wai sani kayi ba bazaka taba cewa qawance ne mafarin haduwarsu ba. Gashi dai ko daga yanayinsu mutum zai ga banbancin dabi'a sosai yayin da Na'ima ta zamo mara hayaniya, dan in kaga tana dogon surutu to da Nafisa ne, ga hakuri da shanye komai a ciki while Nafisa kuma mutum ce mai surutu da rashin hakuri a wasu lokutan, But friendship blends them together and they became sisters from different mothers.

As lokacin tafiyansu gida yana kusantowa sai Na'ima ta zamo so uneasy ta zamo wata sanyi sanyi har Nafisan ta fara ganewa amma batayi mata magana ba saboda wasu dalilai.
Ana gobe zasu tafi, Na'ima na dakinta tayi wanka tana zaune gaban mirror tana shafe shafen ta na al'ada, bayan ta gama ta cire hulan wankanta tana kallon kitson da sukaje saloon aka mata sai ta dauko wani hair oil tafara shafawa acikin lines na kitson tana tunani, bayan ta gama ta maida hulan ta saka kayan baccinta ta hau gadon ta kwanta, ji tayi ta kasa baccin kuma, sai ta miqe zaune ta jawo laptop dinta dake bedside drawer shima zata dan duba ko zai dauke mata hankali, shima tana dannawa ne amma absent mindly, daga karshe kawai ta miqe ta tafi kitchen,
bude cupboard tayi ta debo chocolates da cheese balls ta fito ta nufi dakin Nafisa, tana shiga ta sameta ta dora box dinta akan gado ta tsaya gaban wardrobe tana zaben kayan da zata koma gida dasu, Na'ima ta qarasa ta zauna kan gadon tana cewa "Wai dama baki gama hada kayan naki ba?" Nafisa ta kama qugu tana nazarin kayan wardrobe din tace "Sai na hada sai kuma inji ba dasu nakeson tafiya ba" Na'ima ta girgiza kai tace "Allah ya shiryeki Nafee, hada kayan ma saikinyi ruwan ido bayan tulin kayanki da kika baro can gida" sai Nafisa ta juyo tace "Hey...it's not my fault, I want nice and big collections" Na'ima tayi murmushi tace "Ruwan ido dai, bawani nice or big collections, kowanne so kike" sai Nafisa tayi murmushi tace "wlh kuwa, duk wanda na dauko sai inga inason bari, kawai zan barsu Inaga" Na'ima tace "kinjiki, sai munje ki damemu da mita akan da kin dauki wasu, matsa in nema miki" sai Nafisa ta amsa da toh tareda dawowa bakin gadon ta dauki chocolate daya zata bare. Miqewa Na'ima tayi ta tafi wajen kayan tana dubawa sukayi shiru na wasu mintuna sannan cikin kwantar da murya Nafisa tace "Na'ima in bakyason komawa babu me saki dole..you know that" juyowa na'ima tayi tace "Nafee we've talked about this over and over and i said Yes, why don't you believe me?" Nafisa tace "The eyes don't lie Na'ima, I saw it in you, how you became silent these days, shin in tambayeki...why do you choose to deprive yourself happiness ne wai Na'ima?" Ta miqe ta qaraso gaban Na'iman tace "That pathetic, stupid person!! Should be the one hiding, not you" ta sake dafa kafadan Na'iman tace "Those vicious and wicked people should be the one's living unhappy now, not you Na'ima"
Fashewa da kuka Na'ima tayi sai Nafisa ta riqe ta suka zauna kan gadon, itama Nafisan na hawaye.
Tayi kukan sosai da kanta tayi shiru tana goge idonta, cikin sanyin murya tace "Tsoro nake kada ayi forcing dina back to where i left, I don't know how to face what I've left Nafisa" sai Nafisa tayi saurin cewa "Abba da Mami bazasu taba barin hakan ya faru ba kinsani" 
Na'ima ta sunkuyar da kanta tace "Amma dole watarana hakan ya faru" Nafisa tace "Bance baza kije wajensu ba tunda bakida kamarsu a duniya, but forcing you back dinne ba wanda zai saki hakan, kuma kisani Allah yana tare dake a komai" shiru Na'ima tayi batace komai ba tana share hawayenta idonta na kallon kasan dakin.
ganin haka sai Nafisa ta cigaba "We will always be there, abubuwan da suka faru sun riga da sun faru, bance babu sauran gwagwarmaya agabanki ba amma what I want you to do is to Embrace life strongly as it comes, life is too short for you to be stuck up because of that stupid man, Embrace love when you find it, rayuwar nan bata jiran kowa  Na'ima, it's high time you actually start living your life to the fullest" tana gama fadin haka ta miqe ta koma wajen kayanta tafara diban na tafiyan, Na'ima na nan zaune tayi shiru tana maimaita maganganun Nafisan, encouraging words din suna shiga cikin kwakwalwanta da daddaya.
May be it's high time she start seeing all of it in a different direction, duk abubuwan da suka faru a baya zata ajiyesu for now idan lokacin komawanta yazo Allah zai mata jagora.
Anan dakin nafisan ta kwana sukayi ta hiransu kafin suyi bacci, Nafisa na bata labarin yanda Umar ya dameta da kira wai zaizo daukan su a Airport in sun sauqa, Na'ima tace "Blocking dai ya fasu" sai Nafisa ta dungureta da hannu tace "kin shiga uku da rashin mantuwa" Na'ima ta kama dariya tana dan girgiza kai.

Wayewar washegari tun asuba suka tattare gidan sukayi storing abunda sukasan zai baci kafin su dawo sannan suka kira Uber ta kaisu Airport dan jirgin safiya zasu bi.
Karfe shida da wasu 'yan mintuna jirginsu ya tashi zuwa Nigeria zuciyar Na'ima cike da wani irin yanayin da bazata iya fassarashi ba.