Kuncin zuci
by @bintuuu
Tsaye Ahmad yake a parking space dake cikin compound din babban gidan nasu, Gida ne babba me cike da alatun rayuwa wanda kana gani kasan naira ta zaunu gurin mazauna cikinsa.
Yana tsayen ne jikin motansa da ya bude driver seat kuma bai shiga ba, wayarsa yake dannawa cikin nutsuwa yana nazarin saqon da aka turo masa.
Mai gadin gidan ne ya qaraso ganinsa tsaye nan tuntuni amma bai shiga motan ba, sai yace "Yallabai ko da abunda za ai maka?" Ahmad ya dago kansa yana kallon maigaidin yace "A'a yakasai jeka abunka" Yakasai ya dan risina yace "Toh yallabai afito lafiya" ya juya yana komawa bakin aikinsa.
Shiga driver's seat din yayi batareda ya kulle kofar motan ba ya miqo kafarsa daya waje ya cigaba da abunda yakeyi.
Yananan zaune for almost twenty minutes wata mota ta shigo compound din, bai dago kansa ba saida ta qaraso tayi parking dan nesa dashi sannan ya daga Ido yana nazarin motan, ganin wacce ta fito daga driver's seat yasa nan take yayi danasanin tsayuwarsa a wajen bai fita ba, aranshi yana cewa me yasa tun dazun bai tafi ba in yaso sai yadawo inya nutsu ya duba saqon nashi.
Laila ta juyo ta kalleshi, take ta fara murmushi tana gyara gyalenta da ta saqala a kafada, a daya side din ma qawartace ta fito suka taho tare Laila na gaba tana qarasowa garesa cikin zumudin ganinsa.
Duk wani mood din fitan yaji ya fita daga ranshi, sai ya fito daga motan ya rufeta yana maida wayansa aljihu idonsa na kallon wani gurin basu ba, qarasowan su wajen Laila tace "Yaya ashe kadawo?..Ina wuni" anutse Ahmad ya amsa da "Lafiya" batareda ya amsa tambayanta na farko ba, qawarta mai suna Luba ta gaisheshi ya amsa shortly, sai Laila tace "Nakira ba adadi baka dauka ba, i just want to know how you are" ta qarasa tana murmushi bakinta kamar gonar auduga, sai lokacin Ahmad ya dan kalleta, yace "Oh really? may be bana kusa"
Amasanshi ta qular da ita wanda har yanayin fuskanta yaso nunawa amma tayi saurin waskewa da wani murmushin tace "Kai yaya, I've been calling fa" bai bata amsa ba ya dago hannunsa yana duban wristwatch dinsa yace "I'm late Laila, and nayi mantuwa" ya juya tareda cewa "ki gaida su Mummy" da haka ya nufi babban part dinsa shida Adam wanda ke nan compound din gidan, yabarsu Laila nan tsaye a parking lot suna bin bayansa da kallo.
Laila ta cika kamar zata fashe, qawarta ta tabo kafadanta tace "Kawata waye wannan din? kinga yanda yake mana magana kuwa, ko shine Ahmad din naki?" Laila bata juyo ba balle ta bata amsa ta qurawa side din su Ahmad ido ta jijjaga kai tayi kwafa tace "Daman naji labarin yadawo nazo na ganewa idona" Luba tace "Uhm, guy dinnan is full of himself" Laila tace "Zanyi maganinshi ne, nikuma!!...yakusa zuwa hannu wlh" Luba na kallonta tace "A yanda kike rawan kafa a gabansa dinne zakiyi maganinsa, girl you must be fooling yourself" sai sannan Laila ta juyo tana murmushi kadan tace "Kedai ki zuba ido ki gani" ta nufi gurin motanta tace "Mutafi" Luba tace "Ha'aa bazamu qarasa ciki mu gaisa da mutanen gidan bane?" Laila ta wani hade fuska tace "Nagama abunda yakawoni nidai, in zaki zo mutafi to" sai Luba ta kyabe baki ta taho suka shiga motan.
Haka Laila ta tada motanta tayi reverse babu kunya megadi ya sake bude musu gate suka bar gidan batareda ta qarasa ta gaishe da iyayen Ahmad ba, wanda mahaifishi ya kasance yayan nata mahaifin.
Bayan Ahmad ya shiga part din nasu yawuce Adam dake zaune nan falo yana kallo ya nufi stairs zaije dakinsa dake sama dan canja kayan jiikinsa saboda dagaske kuma fitan ya fice masa arai, bayan yayi changing into qananan kaya masu kyau sannan ya dawo nan falon ya wuce qaramin dining area ya hado tea dinda Mamma, mahaifiyarsa ta aiko musu dazu.
Zama yayi akan sofan dake falon sai Adam ya juyo ya kallesa yace "Badai har kaje kadawo ba" calmly yace "Nafasa fitan" sai Adam ya gyada kai ya maida hankali kan kallon wrestling din da yake yi, shiru sukayi while Ahmad ya ciro wayansa yana dannawa as yana sipping tea dinsa a nutse.
Bayan wasu mintuna Ahmad ya ajiye cup din shayin yana kallon Adam yace "The investors have reached out, they want a meeting" Adam ya sake juyowa yace "Wait....about the app?" Ahmad ya amsa da "Yes" sai Adam yace "But for real though, you really want to sell it?" Ahmad ya gyada kansa, Adam ya cigaba "Dude, you have almost 6.5 million users, this is huge you know" a nutse Ahmad yace "I know, but they're offering big money on this. Beside, this year nakeson launching sabon ai" Adam na kallonsa yace "It's settled then, a Ina sukayi setting meeting din?" Ya amsa da "London, but bamuyi arranging date ba tukun" sai Adam yace "Okay, dama ka dade baka leqa branch nacan ba, this is your chance" Ahmad yayi murmushin gefen baki yace "Mundade dai" Adam yace "Dude I'm not the head, You are." ya daga kafada yace "It's part of your job too" murmushi kawai Adam yayi yace "Anyway, I'm happy for you...for real" Ahmad yace "Thanks man" sai ya miqa hannu ya dauko ipad dinsa dake kan center table ya budeta yana qara duba emails dinda investors din suka tura masa.
Wuraren qarfe sha biyu da rabi na rana jirginsu Na'ima ya sauqa Abuja, suka fito duk a gajiye
Bayan sun gama duk wasu formalities suka wuce bangaren arrivals, Nafisa sai juye juye take tana neman wanda yazo daukansu, can tayi tsuka tace "Yaron nan bai iso ba kenan" Na'ima tace "waye yaron, Umar?" Nafisa ta juyo tace "Wani Umar kuma, haka kurum yaga kamar nima ina zumudin ganinsa ne" Na'ima batasan lokacin da dariya tazo mata ba tace "Nafee babu mai iya miki sai Allah" sai Nafisa ta juya tana neman qanin nata da Mami tace zaizo daukansu tace "Sis mazan ne kamar zuma suke saida wuta" Na'ima jijjaga kai kawai tayi batace komai ba.
Can gefe suka hango Al'ameen riqe da name sign da sunayensu rubuce ajiki, shima hangosun da yayi sai ya ajiye sign din ya nufosu yana fara'a su Na'ima suka nufeshi suma, qarasowa yayi tareda yin side hug wa nafisa sannan ya juyo yana kallon Na'ima yace "Anty Na'ima ya zaman gajiya" tace "Alhamdulillah"
sai ya riqe wasu daga akwatin nasu suka qarasa wajen motansa Nafisa tace "Shine ko ka fada mana ka dawo sai gurin Mami muke jin labari" yana murmushi yace "Surprise naso muku fa Mami ta batamin shiri" Suma murmushin sukayi suka shiga motan, bayan ya gama sa kayansu a booth din ya shiga motan yaja suka bar airport din suka dau hanyan gida.
Cikin 40 minutes suka isa unguwar su Nafisan, Al'ameen yayi horn a kofar wani babban gida megadi ya taho da saurinsa ya bude musu, babban gida ne wanda kana gani kasan masu shi dasu ake murza nera a cikin qasar, suna shiga babban compound din suka hango Mami tsaye a entrance din building din ta fito jin qaran mota, dasauri Nafisa ta fice bayan sunyi parking tayi wajenta da gudu gudunta, sai Mami ta ware hannu tana dariya tace "Oyoyo yaranaa" Nafisa ta rungumeta tana murna, cikin nutsuwa Na'ima ta qaraso tana murmushi itama, sai Mami ta sake Nafisa ta rungumota itama tace "Welcome habibti" luf Na'ima tayi a jikin Mami tana jin kaso tamanin cikin damuwan da ta taho dashi yana washewa a hankali jin embrace din Mamin, cikin raha suka qarasa cikin main falon gidan suka bar Al'ameen yana debo musu kayan nasu megadi yana tayasa.