JIGO

BANKWANA

by @haseenadayyabu109

Bissimillahi rahmanirraheem

Wannan littafin kagaggen labari ne banyi Shi dan wani Ko wata ba,idan suna yazo daya to akasani,kada a juyamin labari plss.ina sanku masoyana.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Gudu yake kamar zai tashi sama gani yake sam motar bata sauri saboda yadda ya kosa ya karasa ga jigonsa,wani wawan burki ya taka saboda wata yarinyar bafulata data gitta da garken shanunta ji yake kamar ya janyo ta ya shake saboda takaici are you mad ya fada yana dukan stirring motan Ko kallonshi batayi ba saboda tasan halin kaɗo basu da kirki Ko kadan tsaki yaja ya figi motar yayi gaba yana ta kwashe mata Karama daidai yazo his destination.

Sam ji yayi bazai iya karasawa ba duk da yadda ya matsu da yazo din amma bai san a yadda JIGONSA yake ba,ajiyar zuciya kawai yake ji yake kamar zuciyarsa ta faso kirjinsa kirjinsa ta fito da abinda yake ji fitowa yayi ya nufi cikin gidan dan ko motar baya jin zai iya karasawa da ita cikin gate din yana tafiya kamar kwai ya fashe mishi a ciki fargaba fal cike a ranshi.Tura kanshi yayi cikin parlourn NANNE saboda yana da tabbacin anan zeyi tozali da jigonsa tsaye yayi bakin kofa ya kafe ta ido tausayi da nadama duk sun hanashi sukuni idan ya tuna saboda dashi take a wannan yanayin ji yake kamar ya kashe kanshi ya huta iska ya furzar mai zafi tunda ga zuciya.

A hankali ta bude kumburarrun idanun ta da sukayi ja saboda wahala ta sauke akanshi runtse idanunshi yayi saboda faduwar gaban data ziyarce Shi,EJAZZ ta furta a raunace hakan ya janyo hankalin sauran mutanen dakin juyawa su tsura mishi ido abinda ya tsana kenan gani yake kamar duk suna dora mishi alhakin faruwar komai,hannu take miƙo mishi saboda maganar wahala take bata a sanyaye ya karasa yana kallonta amma ya kasa rike hannun abinda yake gani a sauran shudaddun JIGONSA yake gani a idanun ANAYA girgiza kai kawai yake badai itama zata barshi bani kai inaa,inaa,inaa wannan karon zai iyayin hauka tabbas saboda hakurinsa ya kare lumfashin da yaji taja ya dawo dashi hayyacin sa a hankali take magana Ejazz ga amanar ƴata nan ka kulamin da ita ina kaunarka amma Allah baiyi zamu rayu tare ba ka yafe man,majina yaji sam babu digon hawaye a idanunshi sai jaa da suka kada sukayi na yafe miki Anaya plss karki barni kece jigona ya kifa kanshi a hannunta yana shasheƙa kamar karamin yaro salati yaji tana yi kafin a hankali komai ya fara saki dagowa yayi da sauri yana kallonta amma ina alqawarin Allah ya cika rai yayi halinsa juyawa yayi yana kallon mutanen dakin da duk suka sadda kai tabbas kunyar haɗa idanu suke dashi jijjigata ya farayi yana Ambaton Sunanta yana Kuka Sam baisan laifin da yayi ba ake hukunta sa har haka ba karo na biyar fa kenan sambatu kawai yake yana Kuka AMMA da AMMI suka matso suka janyeshi aka rufe mata fuska da mayafi kayi hakuri Ejazz haka kaddararka tazo addu'a take bukata ba Kuka ba juyowa yati