KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Sunga gata gurin Mami don tun kafin suyi wanka su huta ta fara sallamansu da home made juices datayi musu na musamman. Al'ameen ya shigo musu da kayan Mami tasa shi yakai musu dakunansu. 
Bayan sun huta kadan anan falon suka nufi stairs gurin dakunansu dake jere gefen na Mamin, dakin Na'ima ne daf da Falon Mami while Nafisa tana opposite din su a corridor'n.
Na'ima na shiga dakin tasamu sai tashin qamshin turare yake, ko ina neat ta miqa hannu kan gadon ta dauko teddy bear din da Abubakar ya taba kawo mata farkon zamanta a gidan, sai ta rugume teddyn tana bin dakin da kallo kamar yau ta barshi, qarasawa tayi ta bude babban wardrobe dinta, nan ma ta ga kayanta jera cikin tsanaki sai qamshi suke ga sabbin kaya a gefe masu yawa an jera matasu wasu a hanger, wasu kuma a linke neatly,
tana nan tsaye gaban wardrobe din a sannu farin ciki yake samun waje cikin zuciyarta aranta tace "I missed this" lallai tayi missing pampering din da Mami take mata, and she made the right choice coming back.
Mami ce ta shigo hannunta riqe da sabbin towels wankakku a linke tana fadin "Kinga dazu fa nace Lantana ta jera muku su a bandakunan ku, ashe ta manta" sai Na'ima ta qarasa da fara'a zata karbesu daga hannun Mamin amma bata miqa mata duka ba ta dauki uku ta bata tace "Sauran na Nafisa ne" Na'ima tace "Bari nakai mata Mami" tace "A'a kiyi wankan tukunna sai ku sauqa qasa ga abinci can"  Na'ima ta gyada kai tareda amsawa da "Toh" sai Mami tayi murmushi tana kallonta tace "Welcome home daughter" itama murmushin tayi kawai batace komai ba Mami ta juya ta fita daga dakin tajiyo shiganta dakin Nafisa. 
Bayan tayi wankan ta shirya cikin simple black abaya mara nauyi tayi daurin dankwali da mayafin ta fice, tasamu Nafisa a falon har ta fito itama suna magana da Al'ameen da Abubakar wanda yadawo daga school babu jimawa.
ganinta yasa Abubakar tasowa da fara'a yace "Anty nah oyoyo" tana murmushi ta shafa kansa tace "Kaima oyoyo" da haka suka zaunaa falon cikin walwala aka fara hiran yaushe gamo.
Mami ta fito daga kitchen dinda ke babban falon  hannunta riqe da food flask tayi gurin dinning area tana jerashi jikin sauran 'yan'uwansa akan table, sai ta juyo garesu tace "Abar surutun haka, kuzo kuci abinci tukunna" sai suka miqe dukansu suka qarasa dining din, bayan sunyi settling Nafisa tace "Mami, Abba fa??" tace "Yana gurin aiki ai kinsani, bakuyi waya bane" Nafisa ta janyo coolern dataga favorite dish dinta ta fara zubawa a plate tace "Yacemin he'll be at home when we arrive" sai Mami tace "Bai baro gurin aikin ba tukunna" ta juya tana maida hankalinta kan Na'ima data fara cin abincin da ta zuba, tace "Habibti ki dudduba coolers din ko akwai favorite dinki" Nafisa tace "Tuwon da ta zuba shine favorite dinta Mami" Abubakar juya yana kallon Na'ima yace "tuwo kuma Anty" Na'ima ta gyada kai sannan tace "Ina yah faruk fa" Al'ameen yace "Wannan ya fice aiki tun safe ai" Mami ta qara da "Sai dare ma zai dawo halan, yace they have a lot of works" Na'ima ta gyada kai tacigaba da cin abincinta.

Daren ranan bayan Abba yadawo yaci abinci ya huta suka je gaishesa cikin babban falonsa, bayan sun shiga da sallama Nafisa ta qarasa kusa dashi ta zauna tana fara'a tace "Abbaa" shima cikin fara'a ya amsa da "Yaran Abba, kun dawo lafiya?" Na'ima ta qaraso zata zauna nan qasa yace "Tashi ki zauna a kujera daughter"  tana dan murmushi tace "Nan yayi" ya sake insisting ta tashi din sannan ta tashin ta zauna a wani kujera dan nesa dasu, Mami ce ta shigo falon hannunta riqe da tray na tea flask da cups akai Na'ima ta miqe ta karba ta qarasa  ta ajiye nan table din dake gaban Abban sannan ta koma ta zauna, sai Mamin ta wuce dakin Abban dake nan falon yin wani uzurin.
Gaishe da Abban sukayi ya amsa yana tambayansu karatun nasu
Nafisa na tsiyaya masa tea din a cup tace "Abba abokinka dinnan has been very helpful a lot, watanni biyu ma da suka wuce shi yakaimu London gidan anty Amnah" Mami ta fito daga dakin ta qaraso ta zauna nan gefensa itama, Abban yace "Haka yakamata ai, kuma yana bani report ai yace kuna qoqarin karatun ba laifi" ya juya yana kallon Na'ima yace "Haka ko Na'ima"  ta amsa da "Eh Abba" Mami tace "Nafisa zaka tambaya dan Na'ima bani da haufin tana karatu" murmushi Na'ima tayi tace "Nafisa tana karatu fa sosai Mami" sai Nafisan tayi saurin amsawa da "Sosai sosai ma" Atare Abba da Mami suka juya suna kallonta, sai Abba yayi murmushi yana kai cup din shayin bakinsa while Mami ta girgiza kai ita da Na'ima suka dan yi dariya sanin halinta.
Sunanan falon suna hira Al'ameen yashigo falon da sallama yayi settling shima a kujera ya dan duqar da kanshi yace "Barka da dare Abba" sai Abba ya amsa then followed by Abubakar shima ya qaraso ya zauna kusada Al'ameen din shima ya gaishe da Abba. 
Har kusan karfe tara suka kai suna hira, zuwa sannan Na'ima ta sake anata hiran da ita jefi jefi take sa baki, Nafisa na bawa iyayen nasu labari game da rayuwarsu a England din Na'ima na tayata kadan kadan, by then sun sauqo qasa itada Nafisa da Abubakar kan babban carpet din dake shimfide a falon hannunsu riqe da kofin shayin da Nafisa ta zuba musu daga cikin na Abban.
Faruk ne yayi sallama ya shigo cikin sanyi alamun gajiya a tattare dashi, yan'uwan na amsa masa tareda sannu, Nafisa ta ajiye tea din ta miqe tana riqo hannunsa yana fara'a yace "Yan gatan Mami sun dawo kenan"  ya juya ya kalli Na'ima yace "Habibtin mami, kun iso lafiya" tana murmushi ta amsa da "Lafiya Yaya" suka gaisheshi gaba daya ya amsa tareda zama nan qasan carpet din shima yana me gaishe da iyayen nasa, suka amsa Mami na tambayanshi gajiyan aiki  Abba yace "Arinqa sararawa jiki da brain din dai babana" Faruk ya dan shafa kansa yace "Abba aikin ne these days suna buqatan lokaci sosai" sai Abba yace "Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin Mami ta tambayesa ko yaci abinci ya girgiza kai, nan falon Nafisa ta kawo masa abincin yanaci aka cigaba da hiran dashi cikin raha.   
Cikin walwala da fahimtar juna iyayen ke gudanar da hiran tsakaninsu da yaran nasu, wanda hakan yasa yaran suke bude cikinsu openly suna fadan abunda ke mind dinsu wajen iyayen, idan fannin gyara ne take iyayen suke gyara musu cikin lumana, idan kuma na raha ne suma ayi dariyan dasu.
And for that moment.
Na'ima knew..This is home.
These people right here.
Are like missing piece of her heart.
And she won't trade them for anything.