TAURIN KAI

PAGE 5

by @zahraroyal

*TAURIN KAI*

*Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.......*

PAGE 5

*MIMI POV*

Hawaye ne masu zafi ke mata zuba a gefen fuskarta. A hankali take sauke lumfashi kamar bata so, motsi kaɗan take yi, saboda ƙarin ruwan dake aka saka mata.

Kwata-kwata jikinta bata jin daɗinsa, ga rayuwar ma gaba ɗaya jinta take kamar ta mutu ma kota huta da yanyin da take ciki.

Shigowar Mama ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Mama harta zauna kusa da ita.

"Kukan dai Mimi?"

"Mama dan Allah ki taimaka kiyi ma Abba magana mana wallahi Allah ni bazan iya auren Mubarak ba"

Sosai Mama ta zuba ma Mimi ido kawai tana karantar yanayinta sosai kamin ta ce.

"Kiyi hakuri fa Mimi, suman nan da kikai hakan bai hana Abbanki janye ƙudurinsa ba, dan yanzu haka kamin ki farka sai da Mubarak ya zo duba ki, kuma da alamar yasan da maganar auren da aka maida naki akansa"

Girgiza kai Mimi ta fara yi hawaye na sake wanke mata fuska, cikin muryar kuka muryarta na kyarma take cewa.

"Mimi mutuwa zanyi wallahi zuciyata zafi tak....

Tashi tsaye Mama tayi tana duban Mimi da kyau, danta fara kaita bango kuma ta nunata da yatsa tana cewa.

"Bari na fito miki a mutum Mimi, banga wadda zaka ce wai dan babu shi bazaka iya rayuwa ba, idan kinga ana hakan sai dai idan abun bai zo kanka bane. Ke yanzu akan wani kike son kassara rayuwarki?, wadda duka-duka ma yaushe kuka huɗun?, baki ce zaki mutu danmu ba sai dan wani?, to ai bismillah Mimi kinga idan kika kashe kan naki ai bashi keda asara ba, koda baki duniyar zaije ya auri wata ne nama gaya miki"

Mama na faɗar haka ta juya ta barta tana hawaye, tun tana hawaye har kukan nata ya fara fitowa fili. Su Mama basu san yadda take jin Jafar a ranta bane, ta tabbatar shima bazai iya rayuwa ba ita ba, bazai taɓ barin ta ba.

Ƙarar kiran wayarta ne ya katse mata tunanin data faɗa.

Saida ta kusa tsinkewa kamin tasa ɗayan hannunta wadda ba'asa ƙarin ruwan ba ta ɗakko, dama tana kusa da ita.

Ganin mai kiran yasa ta saki murmurshin daya taho da wasu guntun hawayen da suka bi mata ta gefen fuskarta.

Tana ɗaukar wayar ko gaisa basu yi ba Jafar ya fara jefo mata tabbayar ya jikinta, duk hankalinsa a tashe.

"Love, Abba na zo amma ya hanani shigowa inda kike, wai zan ƙara tayar miki da hankali ne. Haba Mimi mi yasa Abba zaiyi saurin yanke hukunci?. Nima yanzu haka gani nan kwance bana jin daɗin komai nawa. Yanzu shikenan ina gani za'a rabamu?"

Kuka mai ƙarfi ne ya ci ƙarfin Mimi ta kuwa sakar masa shi. Bawan Allah duk sai ya ruɗe ya shiga rarrashinta.

Mimi bata san Mama ta shigo ɗakin ba sai dai kawai taji tasa hannunta ta amshe wayar dake kange a kunnanta.

Sai lokacin Mimi ta ɗan zubara kaɗan har tana shirin guje ƙarin ruwan da aka sa mata wadda ya kusa ƙarewa saura kaɗan.

"Wato Abbanki daya hanaki waya da Jafar shine kike yi ko?, ance kiyi nesa dashi hakan zaisa ki samu ƙarfin zuciyar da zaki iya rabuwa dashi cikin sauƙi, amma da yake ko duka shaiɗan na maku kuwwa a kunne kuna zama kuna sake zuge junan baza ku iya rayuwa babu ɗaya ba ko?. Ya za'ai ku iya rabuwa kuwa kuna haka?. Wallahi Mimi kifa fita daga ido na rufe. Tunda har yau an maida ma Jafar kayan aurensa an amshi na Mubarak ya kamata ki tsaida hankalinki ga Mubarak kawai, ki manta da Jafar"

Kuka sosai Mimi ta saki tana sake girgiza kai ta ce.

"Mama bazan iya auren wani idan ba Jafar ba, dan Allah ku gane mana"

"Mtsww, gobe ki shirya zaku je awon jini dashi Mubarak ɗin"

Ai sai Mimi ta fara addu'ar Ubangiji yasa shima jinin nasu yazo ɗaya taga yadda za'ai ayi auren, ita da auren wani ba Jafar ba gara ta mutu ba aure haka take ji.

Zuwa can kamar a maganar ta zo mata a cikin kanta taji Mama na faɗin.

"Duk da dama ya ce shi yasan nau'in jininsa A'A ne, amma zuwa a ƙara tabbatarwa yafi"

Wani tashin hankali ne ya rufe Mimi tana haɗe wani abu a maƙoshinta, tana sake jin fargaba da tashin hankalin rasa Jafar. Wata zufa ce ke yanko mata sai zare ido take tana jin yadda ƙirjinta ke daka, addu'a take Ubangiji yasa nau'in jinin nasa ya sauya zuwa A'S.........

*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*

A hankali ta sauke botikin tallar tana sauke lumfashi ta dube Iya dake ƙirga kuɗin data miƙa mata na cikin tallar.

"Ya naga babu naira ɗari biyar kuma, ina ta shige?"

Na'ima ta yi ƙasa da kanta tana cewa.

"Iya yinwa naji shi yasa na ci"

Baki buɗe Iya ke duban Naima tana nunata da yatsa ta ce.

"Ban gane kinci abinci ba?, yanzu ke Naima har abincin ɗari biyar ɗin kika cinye?"

"Iya yinwa fa naji shi yasa, kuma ai banci komai ba shi yasa na ci ɗin"

"Ai kuwa yau zaki gane kin ci abincin ɗari biyar yarinya"

Inna na daga zaune ƙofar ɗakinta tana girgiza kai, tausayin yaran na kamata.

Ɗaukar waya Iya tayi tana danna ma Kawu Isa ya zo dole ne a matso da aurenki da Musa nan kusa-kusa tunda kin fara nuna kin gagari mutane"

Fashewa da kuka Naima tayi tana nufar inda Inna take tana cewa.

"Wallahi bana son Musa"

"Marar kunyar banza, ɗan uwan naki kike ikirarin baki so?, to idan anyi auren naku kisa kansa gabas ki yanka dan tsohuwarki"

Mita kawai Iya keyi har Khadija ta shigo gidan itama ɗauke da kayan talla.

Bata tsaya wani abu ta miƙa ma Iya kuɗin tallar itama tana nufar inda Naima take zaune sai kuka take.

"Ke ina kuma zaki je?, ai kin tsaya dai na ƙirga kuɗin ko?"

Shiru Khadija tayi tana yin gaba ta rabu da Iya, danta lura yau dama Iya da rigima ta tashi.

"Ya Naima miya faru kike kuka?"

Naima na hawaye ta ɗago zatai magana Mubeena ta shigo gidan.

Bata idasa saida abun tallar nata ba ta shigo gidan, tana dungurar ma da Iya kayanta ta wani damƙa mata kuɗin tana yin gaba wajan ƴan uwanta tun daga can take cewa.

"Miya faru kuma?"

"Ke wai Mubeena mi yasa baki da kunya data ido ne?, ni zaki dungure ma abinci?, tsabar rainin wayo ma ko baki saido min abincin ba"

"Iya bana da lokacin ki a yanzu"

"Lahhh haula walaƙuwata. Mubeena rainin naki har ya kai haka?"

"Mi ya faru ne Ya Khadija?"

"Ba komai"

Cewar Naima.

"Ya Khadija miya faru ki gaya min?"

"Nima wallahi Mubeena ban sani ba, tabbayar da nake mata kenan nima, sai gaki kuma"

"Dan Allah ki gaya min Ya Naima"

Tashi Naima tayi tana nufar ɗakinsu tana cewa.

"Ba komai"

"Wai mi yasa zurfin cikin Ya Naima yayi yawa ne?, ita da Inna halinsu ɗaya, yaushe zaku zauna ana danne maku haƙƙi amma kuyi shiru?, idan bazaku iya ba ku gaya min mana ni na ɗauki mataki"

"Ki ɗauki mataki ke a su wa iyee, ƴar nema?"

Juyawa tayi tana duban Iya kanta tsaye ba shakka ko tsoro ta ce.

"Ni a ƴar uwarsu kuma jininsu man. Duk da nasan abunda ke faruwa bai wuce kece musababinsa"

"Mubeena karna sake jin bakin ki a nan wajan, wuce kiyi abunda ke gabanki"

"Amma Inna dan Allah mu shikenan bamu da ƴancin yin komai sai Iya?, ita zata rinƙa yankewa duk wani abu na rayuwarmu ne? dan kawai....

"Bakin ki bazai iya shiru ba kenan?. To kiyi yadda kikaga dama Mubeena"

Inna ta faɗa tana tashi ta shige ɗaki.

"Eh da anyi magana ƴarki tana yi ma mutane rashin kunya iyaka abunda zaki ce mata kenan ai, tsabar dama kece ki zuge ta tana min rashin kunyar, wallahi duk na kusa maganinku daga ke har ƴaƴan naki"

Wani tsaki Mubeena ta saki tana kallon Iya da wani bala'in haushi, danji take kamar taje ta make Iya, dan tasan ba mai hassasa duk wannan abun sai ita.........