TAURIN KAIFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

TAURIN KAI

  • 1views
  • 29chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · PAGE 1

*TAURIN KAI* *ZAHRA ROYAL STAR**ROYAL STAR WRITER'S ASSO......**Tsokaci*Littafin *Taurin Kai* na ɗauke da wani babban darasi na rayuwa, musamman ga iyaye mata da ‘ya’ya mata. Yana bayani ne kan yadda rashin tarbiyya da son duniya ke iya lalata rayuwar yara, musamman idan uwa ta gaza fahimtar nauyin da ke kanta.A cikin labarin, an nuna irin yadda wata uwa ke amfani da ‘ya’yanta mata wajen cimma burinta na duniya, ba tare da la'akari da tasirin hakan ga rayuwarsu ba. Wasu daga cikin su har matan aure ne, amma hakan bai hana ta raba su da mazajensu ba, domin kawai su dawo gidan iyaye su rika zama abin amfani gareta.A daya hannun, akwai ɗaya daga cikin ‘ya’yan da ta ƙi bin wannan tafarki, duk da ƙoƙarin da aka yi na lalata ta. Wannan kuwa shine babban sako na littafin — cewa duk da yadda yanayi zai kasance, mutum na iya tsayawa da gaskiya da akida idan har yana da imani da kai da kuma goyon bayan Allah.*Taurin Kai* ba wai kawai labari bane, darasi ne mai zurfi da ke haskaka illar rashin tarbiyya, kwaɗayi da sakacin uwa, da kuma ƙarfafa gwiwar waɗanda ke ƙoƙarin tseratar da rayuwarsu daga mummunan tasiri.PAGE 1*Ƙofar Marusa, Katsina state Nigeria*Sanye dake take da kayan Islamiyya a jikinta, Hijab ɗin har ƙasa dan har tana jan ƙasa idan tana tafiya. Tana tafiya a hankali kamar mai tunanin wani abu daban, sai dai gabanta take kallo inda ta hango Aunty Haja tsaye da wani jifgegen mutum a ƙofar gidansu. Lumfashi kaɗan ta sauke tana bin wata Mota dake parke a ƙofar gidan. Jingine suke jikin motar suna fira da hara kamar wa'inda suka daɗe da sanin juna.Tana zuwa ƙofar gidan taja ta tsaya tana girgiza kai zatai magana Aunty Haja ta wani ɓalla mata wani mugun kallo haɗe da hararara tana nunata da yatsa ta ce."Ahir ɗinki bakin nan naki ya furta wani lafazi wallahi, dan kin san Allah yau mai raba ni dake a gidan nan sai Allah kawai""Amma Aunty Haja abunda kike ya dace kenan ace da au..."A'a wai kune dama a tsaye a ƙofar gidan ne?. Ai kamata yayi ke Haja ki shigo daga ciki, kin san unguwar ne akwai fa ƴan sa ido"Ammi ta faɗa tana yin wuff ta katse lafazin da Hannah ke son furzarwa."Ammi kiyi ma Hannah magana bana son tana shigar min hanci, zan fyato ta ne wallahi""Dalla rabu da ita. Ke zo ki wuce ciki shashasha marar zuciya kawai, wacce ta gado ƙashin tsiya wajan ubanta"Wani malolan baƙin ciki ne ya tokare maƙoshin Hannah tana duban yadda Ammin ta fito daga ita sai wani yalolan mayafi wadda da kyar ya iya rufe mata jiki, kuma daga ita sai ɗaurin ƙirji.Shi ko ƙaton mutunen dake tsaye tare da Aunty Haja sai satar kallon Hannah yake, dan ba ƙaramin tafiya tayi da imaninsa ba, saboda duk cikin ƴaƴan Ammi Hannah ɗin tafi su kyau nesa bama kusa ba, kusan za'a ce ita ce ta kwaso kyan Mahaifinsu wadda ya kasance Fulanin asali ne irin na daji, duk da itama Ammi ɗin bafu...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters29
premium19
11

PAGE 11

Premium
Updated a year agoAvailable now
12

PAGE 12

Premium
Updated a year agoAvailable now
13

PAGE 13

Premium
Updated a year agoAvailable now
14

PAGE 14

Premium
Updated a year agoAvailable now
15

PAGE 15

Premium
Updated a year agoAvailable now
16

PAGE 16

Premium
Updated a year agoAvailable now
17

PAGE 17

Premium
Updated a year agoAvailable now
18

PAGE 18

Premium
Updated a year agoAvailable now
19

PAGE 19

Premium
Updated a year agoAvailable now
20

PAGE 20

Premium
Updated a year agoAvailable now
21

Episode 21

Premium
Updated a year agoAvailable now
22

PAGE 22

Premium
Updated a year agoAvailable now
23

PAGE 23

Premium
Updated a year agoAvailable now
24

PAGE 24

Premium
Updated a year agoAvailable now
25

PAGE 25

Premium
Updated a year agoAvailable now
26

PAGE 26

Premium
Updated a year agoAvailable now
27

PAGE 27

Premium
Updated a year agoAvailable now
28

PAGE 28

Premium
Updated a year agoAvailable now
29

PAGE 29

Premium
Updated 10 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play