TAURIN KAI

PAGE 7

by @zahraroyal

*TAURIN KAI*

*Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSO....*

PAGE 7

*HANNAH POV*

A hankali ta waiga tana jin kiran da Aunty Maryam ke mata yasa ta aje kayan da take linkewa nata tana fitowa daga ɗakinsu tana amsawa.

"So nake kiyi sauri zaki raka ni wata unguwa ne"

Turo baki tayi tana faɗin.

"Anjima fa zan tafi Islamiya"

Wani kallo ta watsa mata tana ci gaba da abunda take yi ta ce.

"To bazaki je ba"

"Haba Aunty Maryam Islamiyar?"

"Kware na ce bazaki je ba, koda magana?"

"Ni wallahi Allah.."

"Ke wallahi Allah mi?"

"Kinga Maryam ki barta taje Islamiyar ta dan Allah"

Cewar Aunty Sa'a dage zaune kusa da Maryam ɗin tana shiri itama zata fita, Aunty Haja dama bata wuni gidan ba tun safe ta fice.

"Aunty Maryam kawai ki jani mu tafi, dama wake aron Hannah zuwa wani waje ta rakasa?"

Fannah ta faɗa tana kallon Hannah dake kwaɓe fuska kamar zata saki kuka.

"Jeki ki shirya keda Fannah ɗin zaku raka ni"

"Uhum uhum ni..n..ni..ni wallahi gaskiya"

Hannah ta faɗa tana bubbuga ƙafarta ƙasa cike da shagwaɓar data zame mata jiki kamar zata sakar ma Aunty Maryam kuka.

Maryam ta ɗago tana dubanta cike da taƙaici ta ce.

"Dalla gafara can wallahi ko kukan jini zakiyi yau dai baki zuwa Islamiyar nan, ga inda zaki raka ni na gama magana, kima wuce ki bani waje, kije ki fara shiri, saura kuma ki sanyo min ƴar iskar Hijab ɗin nan taki, gayu zakiyi kisa gyale nama gaya miki"

"Ni gaskiya Hijab zan saka"

"Ina faɗa kina faɗa?"

"Wai mi nake ji ne tun ɗazu ne ina bacci?, amma hayaniyarku ta tayar dani"

Cewar Ammi na fitowa daga ɗaki.

Fannah ce ta ce mata.

"Waifa Ammi daga Aunty Maryam ta ce ta shirya zamu raka ta wani waje muyi gayu sosai, shine Hannah ke cewa wai Islamiya zata je ita dai ba inda zata bimu"

Wata uwar hararara Ammi ta zafga ma Hannah tana cewa.

"Zaki wuce kije ki shirya ne ko kuwa?"

"Amma Ammi hadda fa muke yi kuma kin sani"

"Koma miye kuke yi, yau dai ba inda zaki je, dama ina so naga Ustaz ɗin nan naki so kawai nake ya kama kansa akanki, dan wallahi tarayyar ku bana sonta nama gaya miki"

Kamar zatai kuka ta juya ta koma ɗaki tana jin wani bala'in haushin Aunty Maryam da Aunty Fannah kamar ta rufe su da duka haka take ji. Duk gidan wake zuwa Islamiyar idan ba ita ba?, duk dai su duka sun sauke al'qurni mai girma tun mahaifinsu na raye, baya wasa da zuwa Islamiyarsu, sai daya rasu ne suka watsar da ita, sai ita ɗaya dage zuwa hadda dan itama tuni ta sauke, tana ƙara sanin wasu littatafan addini ne sosai, shi yasa ma ta fisu sanin ya kamata, su kam yawanci basu san wasu littatafan ba saukar kawai akai.

Tsaye Fannah take da Aunty Maryam sun shirya sunyi wani irin kyau sai ɗaukar ido suke, idan kayi masu kallo ɗaya zaka iya rantsewa cewar bada ga gidan nan nasu suka fito ba, kai tsaye zaka ce daga gidan wani hamshaƙin suka fito, gashi Allah yayi masu farar fata mai ɗaukar hankali irin ta fulanin asali.

"Wai bazaki fito bane Hannah?, kin bar mutane a tsaye, sa'anninki ne mu wai?"

Cewar Aunty Maryam kamar zata ari baki, dan ta fara bata haushi, tun ɗazu sunfi minti biyar a tsaye.

"Gani nan fa Aunty Maryam"

Ta faɗa tana fitowa sai faman gyara gyalen da akasa ta dole tasa take, kwata-kawata bata ma iya yafinsa ba, sai zamewa yake, duk jinta take kamar a tsirara take.

"Mtsww ke gyalen ma wannan na ƴan gayu baki iya yafawa ba?, Mtsww wallahi kin bada mu"

Faɗin Fannah tana hararar Hannah dake turo baki ta ce.

"Dan Allah Aunty Maryam ki barni nasa Hijab ɗita, wallahi duk jina nake a takure, kamar zan fita tsirara fa haka nake ji Allah"

Ammi ce dage bayanta ta fito daga ɗaki tana cewa.

"Kisa Hijab ai kin ɓata wannan gayun kuwa, kinga yadda kikai kyau kinma fisu haɗuwa Auta ta"

Ammi ta faɗa cike da jin daɗi, dan yau tayi kyau sosai gashi tasa siket da riga, sunyi mata kyau sosai, duk da basu matse taba amma uban hips ɗinta da suka cika mata siket ɗin data sa shaf ɗinta yayi mugun bayyana, gata da dukiyar fulani suma sun tasu, dan duk tafi su cikar komai na ƴa mace, sai ka ce ita tayi ma kanta su.

"Dalla can kinyi kyau, ba wata Hijab ɗin da zaki saka ki ɓata min tafiya"

Aunty Maryam ta faɗa ta kamo hannun Hannah ta shiga gyara mata gyalen, lafiya lau ta yafa mata shi kamar nasu, ai sai ta koma kamar ka sace ta ka gudu, Fannah tsabar kyan da tayi mata harda faɗin Woow.

Ita kam wacce ake dominta sai faman ɓata fuska take dan Allah ya sani a mugun takure take ita kam, dan ji take kamar ta ɗora hannu sama ta fasa kuka.

"Ina Aunty Sa'a ne? ta ce mu jira ta fa mu wuce tare"

"Tab ai wannan tuni kuna cikin ɗaki kuna shiri aka kira ta a waya naga ta miƙe da hannu nima tayi min sallama ta fice da sauri, kawai kun haɗe idan kuka dawo. Su Aysha dama da Aunty Haja a tare suka fice, su tun safe ma"

"Ammi sai ke kaɗai za'a bari?, ki zo mu tafi tare man"

"Kefa Autancin nan nasakawa kina abu kamar sakarai, ya za'ai ku wani tafi dani idan banda abunki?, kuje dai yanzu Allah ya tsare, saura kuma kiyi masu ba dai-dai ba"

Ammi ta faɗa tana murmushi tana kallon Hannah dake ta ɓata fuska, kamar zata saki kuka.

Fannah ce taja hannun Hannah suke fice Aunty Maryam na gaba suna take mata baya.

Tunda suka fito unguwar ta su suna ratsawa suna wucewa, duk inda suka wuce sai an kalle su, wani wajan ma suji ana faɗin wow wa'incan fa akwai kyau wallahi, kaga bare ƙaramar cikinsun can.

Da yawa haka ake faɗa wani wajan kuma suna wucewa za'a fara zaginsu ana cewa a haka zasu ƙare da yawon iskanci kwararo-kwararo, uwarsu ta ɗaure masu gindi.

Maganganu kowa da abunda zai faɗa.

Basu wani damu ba garama Hannah dake ta ɓata fuska tana jin kamar ta fasa kuka.

Suna tafiya sun zo bakin titi Hannah ta sauke ajiyar zuciya ganin sun tsaida mai napep ya tsaya taji Aunty Maryam na cewa za'a kaisu Arabian arena.

Sun dai-daita da mai napep suka shiga gaba ɗaya.

Suna shiga Hannah ta kasa hakuri ta ce.

"Tunda muka fito wasu sai zagin gidanmu suke, wallahi bana jin daɗin abunda ke faruwa"

"Yo ai Hajiya mutane dama ana biye masu ne?, ai kayi da kyau ma yaka kare bare kuma baka yi ba, ai su mutane Hajiya da kike ji da gani komai kayi sai sun tanka maka, idan mai kyau ne walau marar kyau, ai su basa raina abun magana"

Cewar mai napep ya sako masu baki.

Wani murmurshi kaɗan Aunty Maryam ta saki tana sake duban Hannah ta sakar mata wani kallon gargaɗin ta rufe ma mutane baki, sai ta juya wajan da mai napep ke tukinsa ta ce.

"Ai su mutane haka suke bawan Allah, komi kayi baka iya ba, komiye kake sai an zage ka anyi zunɗanka, ni shi yasa ka ganni nan maganar mutane bata damuna, kowanne idan ka baccinka a cikin rayuwarsa akwai taɓo shima, yaji da tashi rayuwar da abunda ke damunsa, amma bazai ji dashi ba, sai ya rinƙa hango na wani yana zaginsa, wata ƙilama shi yafi ka tsula tsiyar, amma yanzu yana ɓoye laifinsa ya rinƙa hangen na wani yana zaginsa"

"Hakane wallahi Hajiya haka halin ɗan adam yake, sai dai kawai Ubangiji ya shiryar damu baki ɗaya amma kam ana kuskure a rayuwar nan"

Haka sukai ta fira da mai napep har suka isa unguwar ya sauke su dai-dai wani madai-daicin gida mai kyan gaske, suka fito gaba ɗaya Aunty Maryam ta miƙa mai napep kuɗinsa ya juya ya tafi.

Kallon gidan kawai Hannah keyi ita da Fannah.

Fannah ta kasa hakuri ta ce.

"Wow gidan nan ya birgeni wallahi, inama ace namu ne"

"Ki dai rinƙa gode ma Allah a duk yadda yayi ki"

Faɗin Hannah, dan ita kwata-kawata kyan gidan da kyale-kyalensa basu wani ɗauki hankalinta ba, itafa shigar dake jikinta ce yafi damunta, dan wallahi sosai take jinta kamar ta tafi babu kaya.

"Mtsww ke kuma waye yasa dake dalla can?, ke babu damar mutum ya nuna sha'awar abu sai kinyi ma mutane wa'azi?, to waye bai san dai-dai ba wai nufinki?. Ke shikenan ba damar ka nuna kana son abu kaza sai ki ce wai ka gode Allah, to an gaya miki shi Ubangiji idan ka roƙeshi abu baya baka ne?, ai ƙara maka yake ma akan wadda ya roƙa ɗin, ina laifi na dan kawai naga wannan uban gidan daya fi namu nesa ba kusa ba nayi sha'awar ya zama namu?"

"Ke dalla Fannah rabu da ita, kamar baki san halinta ba?, kuma gida irin wannan ai kamar mun mallakesa ne, muddun dai Ammi nada mu. Ku biyo ni bana son kuma wasu ƴan maganganu na gaya maku, duk wani shirme ko wasu maganganu a barsu daga nan"

Bin bayanta sukai har zuwa ƙofar get ɗin gidan ta ƙaramar ƙofar get ɗin.

Mai gadi ya leƙo bayan Aunty Maryam ta kwankwasa.

Yana ganinta ya shiga washe baki, dan da alama yasanta ma.

Mamaki ne ya kusa kashe Hannah dan yadda mai gadi kema Aunty Maryam kirari kai sai ka ɗauka ai matar gidan ce, ko wata daga cikin gidan.

Aunty Maryam na murmurshi ta fiddo kusan dubu uku ta damƙama mai gadi yana murmurshi ya amsa sai zafga godiya yake yana ƙara mata kirari kamar zai ari baki.

A zuciyar Hannah cewa take.

Ita kuma Aunty Maryam yaushe aka santa a wannan gidan?. Koda yake fa akwai yawon tsiya ba inda basu shiga.

Ta ƙare maganar zucin tana faman taɓe baki tana ɗan satar kallon gidan, ba laifi yafa tsaru iya tsaruwa kam.

Su Hajiya Fannah kam ba wani mamakin yadda ake ma Aunty Maryam daga shigowarsu, hankalinta na can wajan kalle-kallan gidan daya gaba tafiya da imaninta, ji take inama-inama.

Ai bata ƙara tsinkewa da lamarin ba saida taga sun shigo wani ƙaton parlo na gidan.

Wata hamshiƙiyar budurwa ce zaune tana latsa waya.

Amma ɗagowar da zatai ganin Aunty Maryam yasa ta tashi tana buga wani uban tsalle ta rungume Aunty Maryam suna dariya a tare.

"Ke banza karki karya ni fa"

Cewar Maryam tana dariya.

Dariya ta saki tana ɗan sakinta ta ce.

"Ohhh Maryam kwana da yawa, koma kiran mutane baki yi, kun ɓoye abunki"

Murmurshi kawai Aunty Maryam ta saki tana cewa.

"Hmm bari ke dai Nihal muna nan gefe, da yake ban cika zama a ƙasar bane kawai"

Jin abunda Aunty Maryam ta faɗa yasa Hannah fiddo ido waje, Fannah ko ko a jikinta dan ita tasan dama suna irin wannan ƙaryar ta su ɗin wasu ne.

"Hhh ai ko manya ne. Ku zauna mana, yau ki ce harda ƙannanmu aka taho min dasu ma"

Zama sukai Maryam na sake cewa.

"Wallahi kuwa gasu nan da yake kin san na ce miki basu daɗe da dawowa daga Abuja ba, kin san acan suke school amma sun kusa gamawa, shi yasa ma yanzu da yake hutu suke ne yasa na ce bari dai na taho miki dasu"

Nihal na jinjina kai tana murmushi ta kalli su Fannah da sosai sai taga jikinsu da shigarsu irin na ƴaƴan manya ne. Da yake dama su Aunty Haja idan suka samo kuɗinsu suna yin ɗinkunansu masu azabar kyau da tsada, ta fannin sutura basa da matsalarta, dan basa zuwa aro wajan wasu, da kuɗin da suke samu wajan samari a nan da yawa suke kashe kuɗin nasu, dan Fannah ma akwai sayo kayan sakawa da kayan kwalliya da kyale-kyale. Kuma duk abunsu basa yarda ayi zina dasu, da wasu mutunen ke masu kallon ai yawon iskanci suke zuwa shi yasa suke samo kuɗin da suke iya riƙe kansu. Sai dai sam ba hakan bane, dan dama can akwaisu da wayo, da sun harkar girma, bare ma Maryam duk wayon saurayi saita ci kuɗinsa, ga shigema ƴaƴan manya, da haka take samun kuɗin kashewa, da wasu suturun, dan wani lokacin idan suka tafi shopping da ƙawayenta masu kuɗi a nan itama take kwaso rabonta, dan da ita ake sayen komai.

Duk a ciki Hannah tafi ɗaukar hankalinta dan gani tayi kamar wata ƴar shugaban ƙasa, yadda fatar jikinta fara tas ga kyan da Allah ya zuba mata.

"Ai ko gasu nan masha Allah, sunma so su fiki kyau ai"

Tana murmushi Aunty Maryam ta ce.

"Ai dama haka mutane ke faɗa. Ni kam wai ina mutanen naki wai"

"Ohhh wai Ya Fu'at kike magana?"

"Shifa babban Yayanku"

"Hmm wallahi in gaya miki baya ma ƙasar ya tafi India ƙaro karatunsa na doctors, amma ya kusa dawowa"

Har cikin ran Aunty Maryam bata ji daɗin hakan ba amma sai ta zame tana murmushi kawai ta ce.

"Ohh masha Allah, na su mu gaisa kam, sai labarinsa kawai nake ji kullum a bakinki amma bamu taɓa haɗuwa ba"

"Hm ai Ya Fu'at kar kiyi fatan ma ku haɗe, ɗan rainin wayo ne na ƙarshe in gaya miki fa, mai iya masa sai Allah kawai sai su Mami kuma da Abbey. Kinga na cika ku da surutu ma bari naje nasa a kawo maku abun motsa baki"

Tashi tayi na ficewa.

Tana fita Fannah ta kamo hannun Aunty Maryam ta ce.

"Aunty Maryam ita kuma wannan a ina kuka haɗu da ita, waye kuma Ya Fu'at?"

"Wai Nihal?, a wani biki muka haɗu da ita, shikenan kam ta amshi number ta, da yake a halayenta tana bala'in sun ƴan gayu masu kuɗi, tana harka dasu, bata san harkar ƙaranta, tunda ta ganni na birgeta, dan ita da kanta ta zo ta same ni na bata number ta, daga nan fa muka jone, koda gigin wasa bata taɓa sanin wacece ni ba, duk ɗaukarta nima ƴar wani ce a Nigeria, dan a yadda nake nuna mata ma mun fisu kuɗi"

Jinjina kai kawai Fannah keyi ita kam daɗi ne ma ya rufe ta.

Hannah kam cike da al'ajabi da mamaki ta tsura ma Aunty Maryam ido kawai.

"Ya Fu'at kuma saboda shi ne yasa na taho da wannan ƴar Hannah, dan so nake kawai ya ganta yaji yana sonta, dan akwai alaƙar da nake son haɗawa a ciki gidan nan"

"Niiii kuma Aunty Maryam?"

"Kware kuwa kuma burina saiya cika, kika min hauka kuma naci ub*anki"

Turo baki Hannah tayi tana ƙunƙuni. Tana jin haushi, duk salon tusa kai ne, ita kam wallahi bada ita ba wannan abun.........