TAURIN KAI

PAGE 8

by @zahraroyal

*TAURIN KAI*

*Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.....*

PAGE 8

*MIMI POV*

Kuka sosai take kamar ranta zai fita. Riƙe take da farar takarda a hannunta wacce akai masu awon jini da Mubarak.

Abban ne ya shigo yana mata wani irin kallon taƙaici, Mama kam tun ɗazu dama ta zuba mata ido kawai tana kallonta.

"Ke tsakaninki da Allah akan awon jinin nan kike ta kuka saboda kawai nau'in jinin ku ya zo ɗaya da Mubarak shine baƙin cikinki kawai ke a yanzu?"

Abba ya ƙare maganar yana sake zuba mata ido.

Zamowa tayi ƙasa daga akan kujera da take zaune tana sadda kanta ƙasa ta haɗe hannuwanta biyu ta shiga roƙon Abba cikin muryar kuka ta ce.

"Abba dan girman Allah...

Mama ce ta miƙe tsaye tana nuna Mimi da yatsa ta ce.

"Kika sake kika furta mana wani abu nan saina ɓata miki rai wallahi, tunda ke naga alamar yanzu kwata-kwata bama kijin kunyar mu, kunya ma kwata-kwata tayi wajanta kema kinyi naki wajan, akan namiji kizo ki tasa mu a gaba kina kuka, kin hana kanki kwanciyar hankali haka kawai ina dalili?"

"Kinga Zainab barta kawai. Ke Mimi tashi kije, amma ki sani bazan yi wata magana akai ba, idan har basu su Jafar ɗin ne suka zo da kansu suna neman a sake maida lokacin aurenku to shine zan amince, amma ki sani badan wai ina so ba, kuma duk abunda yaje ya dawo karki kuka dani, ki kuka da kanki kawai, na dai gaya miki. Zaki iya tashi kije"

Wata irin harbawa zuciyarta keyi tana sauke lumfashi mai ɗumi, tana jin wani irin sanyi dake sauka mata a ƙarƙashin zuciyarta.

Miƙewa tayi ba kunya ta shiga gode ma Abba dake binta da kallo kawai harta fice yana girgiza kansa, yana sake hango natsuwa sosai a tattare da ita daga mata wannan albishir ɗin.

Zama Mama tayi bayan Mimi ta fita tana duban Abba ta ce.

"Mlm yanzu kana nufin ka amince da aurenta da Jafar?"

Murmurshi mai ciwo ya saki irin nasu na manya kamin ya sake gyara zamansa ya ce.

"Abarta tayi abunda take so, wata rana da kanta zata zo ta ce a raba auren, bawai fata nake mata ba, amma idan yaro ya dage sai kawai ka barshi da zaɓin nasa, wata rana zai gane ashe gaskiya fa iyayen nan nasa ke faɗa masa, kuma abunda babba ya hango yaro ko ya hau tsauni bazai iya hangosa ba. Yanzu idan muka dage zata rinƙa ganin kamar ma mun danne mata haƙƙinta ne, muna son rabata da wadda take so ne. Kuma kinga shima kansa Jafar ɗin har yanzu basu zo suka ɗauki kayansu ba, duk da maganar da nayi masa, har yanzu banji daga garesu ba"

"Hmm hakane Mlm, shi yasa fa na ɗauke duk wani abu nashi na ɓoye, na gaya mata cewar sun aiko an masa dan kawai ta fitar dashi daga ranta, amma dai kagani kamar ma sake tusa mata son nashi ake. Ni na rasa gane wannan soyayyar zamani da yaran yanzu suke yi. Mu a lokacinmu ai sai dai kawai kaji ance anma wance miji, kuma baka isa ka ce a'a ba, amma banda yaran zamanin nan"

"Idan banda abunki Zainab ai mutanen da a tsaye suke akan ƴaƴansu, kuma yaran da na yanzu ai ba biyayyarsu ɗaya ba, yaran yanzu a haka ake haifosu da shegen wayonsu suke faɗuwa duniyar, baka isa ka ce ga abunda yaro zaiyi ba, sai yazo maka da wata maganar, Allah dai ya ƙara shiryar mana dasu kawai, amma yaran yanzu ba kunya ko kaɗan a tattare dasu"

"Ni Mlm abu ɗaya fa nake gudar masu daga Jafar ɗin har ita Mimin wallahi. Gashi dama ƴan uwa kamar jira ake har an fara yayato wai an fasa bikin har sun fara shirin ƙaƙuba masa wai Shamsiyya"

"Uhmm nima naji, dama ai can ita Shamsiyyar tana nuna tana son nashi, ƙananun maganganu ne daga cikin family nashi da namu mu kanmu duk ina jinsu suna dawowa ƙunne na, Allah dai ya tabbatar da alkhairi idan kuma babu Allah ya kauda abun shine kawai"

Sun daɗe suna tattaunawa akan al'amarin bikin Jafar dana Mimi daya zo masu da tangarɗa..

*Ƙanƙara LGA, Katsina state Nigeria*

Zama tayi tana yin shiru sosai, tun bayan abunda ya faru da Iya ta sanar dasu ta kasa gane kan Ya Naima.

Yanzu ma zaune take tayi shiru tayi tagumi. Daga Inna har Ya Naimar sun zama sai a hankali.

"Wai Inna bazaku iya sanar dani miye yake damunku ba?, nida Ya Khadija, nake ganin ai damuwarku damuwarmu ce ai ko?"

Inna dage shirin magana suka jiyo maganar Kawu Isa.

Kusan lokaci ɗaya da Inna da Naima suka ji wata irin harbawar zuciya, bare ma Naima data ji kamar an aiko mata da mutuwa.

Tashi Mubeena tayi tana yin waje tana iya juyo firarsu Iya da Kawu Isan.

Riƙe baki tayi tana jin abunda suke son ƙullawa.

"Ohhh wato abunda yasa su Inna cikin damuwa kenan ba?"

Can ta sake jinjina kai ta ce.

"Ai ko bazai yiwu ba, muddun dai ina raye"

Har Kawu Isa ya fito bata sani ba sai ji tayi Iya na faɗin.

"Ya rasulu Manzon Allah, ke yanzu dama laɓe kike mana Mubeena?, abun naki har ya akai kina min laɓe?"

Turo baki tayi tana ƙunƙuni.

"Ke dama abunda kike yi kenan a gidan nan?, to zaki ci ub*anki ne wallahi marar kunyar banza"

Kawu Isa ya faɗa yana nunata da yatsa.

Hararara ta zafga masa a fakaice tana turo baki.

"Ina ita uwar taki take ne"

Ya ƙara faɗa tana kallon ƙofar ɗakinsu.

Fitowa Inna tayi tana ɗan sakin murmurshi kaɗan ta shiga gaidasa, sai cewa yayi.

"Ohh ashe ana ciki?, to dama saƙo zan isar miki, sai ku fara Shirye-shiryen bikin Musa da kuma Naima, nanda sati biyu masu zuwa"

"Sati biyu kuma Yaya Isa?"

"Eh Sati biyu ku da akwai wani abu ne?"

"Ai nake ganin kamar yayi wuri da yaw.....

"Ke kinga Binta bana son rashin ta ido, wane irin yayi wuri kuma?, muna son kauda ƴaƴan nan dake gabanmu gasu nan sun kawo girma, kina neman kawo mana wata maganar banza"

Cewar Iya tana faɗa tana ma Inna wani irin kallo.

Lumfashi kawai Inna ta sauke tana girgiza kai bata ƙara magana ba ta juya ta koma ɗaki, tana iya juyo kukan Naima, da alama duk taji abunda su Iyar ke cewa.

Ita kam ya zatayi da rayuwarta, ita ba wasu ƴan uwa ba, sai ƴar uwarta ɗaya kuma tayi nesa da ita dan yanzu haka tana Logas tana sana'ar abinci, dan yanzu haka bata san inda zata same ta ba, da number tana shiga amma ta zo bama ta shiga kwata-kawata, damuwar tayi mata yawa gaskiya, ta rasa waye zata kira su raba damuwar nan a tare.

"Makira"

Iya ta faɗa tana bin Inna da kallo.

Ta juya wajan Kawu Isa suka ci gaba da magana akan bikin.

Ita kam Mubeena ta tsaye kamar ma sun manta tana tsaye a wajan, sai zagar mata uwa suke.

Kawu Isa na tafiya Mubeena tayi gyaran murya tana gyara tsayuwarta ta kalli tsabar idon Iya ta ce.

"Iya wai ko kunya ma baki ji ina tsaye wajan nan kuke zagar min uwa?. To indai ina nan wannan auren da kuke son haɗawa wallahi saina rusa shi"

Tana faɗar haka ta wuce tabar Iya sake da baki.

Riƙe baki Iya tayi a fili ta furta.

Wannan ƴar fa shaiɗaniya ce tsaf zata iya rusa abun nan fa. Anya bazanyi wani abu akanta ba itama?, bari dai Saude ta zo ita ce zan tunkara da yadda za'ai da Mubeena ta tabbatar bazata rasa shawara a wajanta ba.

Iya ke maganar a cikin ranta.

Ta sake yin kwafa kawai Iya tayi tana ƙara faɗa a zuci cewar zaki ci uwarki ne daga ke har munafukar uwar taki dake ɗaure miki gindi, duk sai nayi maganinku wallahi.......