GANIN IDO

PAGE 43

by @oumameer2671

P43

Gidan part-part ne flat gasu nan iri ɗaya sun kai ƙwara biyar wanda an tsara su gwanin sha'awa, sannan wani abun burgewa shi ne;rufin gidajen ba kamar namu na Nigeria ba ne da muka saba gani, gini ne kamar na ƙasa zan ce wanda a saman rufin ɗin shafe yake da ƙasa ba kamar mu da ake rufi da zinc ba. Ga rumfuna nan suma an ƙawata domin zaman shaƙatawa, ga bishiyoyi nan suma sai kaɗa iska suke mai sanyi. Wani irin ƙamshi ne na musamman ke tashi a farfajiyar gidan wanda ya ƙara tabbatar mana da cewa mun zo wuri na musamman.

Kallona Hairi tayi murya a ƙasa sosai cike da nishaɗi tana jinjina kanta ta ce.

"Aunty Beena...wurin ya ƙayatar ko! Gaskiya I'm impressed!"

Gaba na yi na fara taka wa a hankali tare da riƙa hannunta na ja ta ganin su Baba Ustaz ɗin sun yi gaba.

Lokaci ɗaya ahlin suka fito gabaɗaya suka tsaya a balcony ɗin babban gidan. A matsayinmu na baƙi wanda wannan ɗin shi ne karonmu na farko a gidan;Maimakon muga sun yi mana tarba irin ta baƙi da ta 'ƴan gida kamar yanda aka saba yi idan mutum yaje sabon wuri,ba hakan ce ta faru ba, domin kuwa;gabaɗaya yanayin damuwa da baƙin ciki shi ne abin da ya yi wa fuskokinsu ƙawanya.

Kallon tuhuma muka shiga jefawa kanmu, musamman Ya Mohaa da ya ji wani irin faɗuwar gaba na jin tsoron kada ace korarsa za su yi. Sai yanzu yake jin nadama a ransa cewa;dama ace tun farko Baba Ustaz ɗin bai sanar musu ba. Ƙila sam ba su yi murna da zuwan Ahlin Alhaji Attahiru Araam ɗin ba. Ƙila zuwan na su ya tado musu wani miki da raɗaɗin da ya jima kwance a cikin ƙirazan su na tunawa da 'ƴar su da kuma jikan da suka ɗauka cewa za su rayu da shi a matsayin wanda za su riƙa gani ko bayan mutuwar 'ƴar su, amma haka shi ma ya mutu ya bar su. To don mi za su yi farin ciki? Tabbas dole su kasance a baƙin ciki da damuwa a duk lokacin da suka yi ido biyu da familyn Alhaji Attahiru Araam.

Muna kai gangar hawa ɗan matattakalar balcony ɗin muka ja muka tsaya.

Wata kamilalliyar dattijuwa ce wacce ke cikin shigar lafaya fara ta alfarma ta tako zuwa gaban Ya Mohaa ta tsaya a gabansa tare da fashewa da kuka. Hannayenta ta ɗora akan gefen kuncinsa na dama da hagu ta sumbaci goshin da kuma kumatunsa cike da bege sannan ta rungume shi cike da zallar nuna kewa ta ce.

"HAMMODI...Idonka kenan? Idon kenan Hammodi? Ashe daman kana raye tsawon shekarun nan muke ta baƙin ciki da kukan rashinka.."

Cike da mamaki ya janye tare da ƙura ido yana kallonta. A yanda take kukan ne ya yi matuƙar ƙona masa zuciya har bai san lokacin da hawaye shima suka wanke masa fuska ba.

Ganin irin kallon da yake mata yasa ta jinjina masa kanta yayin da take kuka da murmushi a lokacin ɗaya ta ce.

"Ni ce JADDA Hammodi...ni ce nan Kakar ka wacce ta haifi Mahaifiyarka.."

Wani irin abu ne ya ji ya daki ƙirjinsa lokaci ɗaya, jin furucin cewa wai itace Grand Ma ɗin shi. Without second thought ya sake rungumeta sosai yana mai jin wani irin sanyi a ransa duk da cewa ya kasa furta mata ko kalma ɗaya.

" Mun yi kewar ka Hammodi, mun yi kuka mun yi baƙin ciki da labarin mutuwar ka ya riskemu...babu watarana da za ta zo ta wuce ba tare da na saka Jaddin ka a gaba cewa ina so in je ko ƙabarinku kai da mahaifiyarka na sake gani Hammodi..."

Janyewa tayi ta kalle shi sannan ta waigo ga wani dattijo wanda babu abin da yake gani a fuskar sa face zallar zubin fuskar mahaifiyarsa ya ji ta ce.

"Je.. Je wurin Jaddin ka Hammodi..."

Cikin takun da bai gaza huɗu ba ya isa gabansa ya tsaya idanun nan tab da ruwan hawaye.

Sumbatar goshin sa yayi da kumatunsa kamar yanda ta yi wanda da alama ita ce mafi ƙololuwar tarbar da suke yiwa baƙon su.

Shi kam hawaye ne ya zubo masu cike da ɗaci da nuna tsananin kewa. Cikin wasu irin kalamai ya jinjina kansa tare da ɗora hannayen sa akan shoulders ɗin Ya Mohaan ya ce.

"Mutuwa kalma ce wacce duk musulmi na ƙwarai yarda da ita wajibi ce ga kowane ɗan Adam...tabbas mun yarda da kalma ta mutuwa a gareka Hammodi, amma kuma ta yi mana matuƙar wahala da nauyi a Ƙirji...labarin mutuwarka ya riskemu a lokacin da sam bamu tsammata ba. Mun Ƙirga cikakken lokacin da ya kamata ka dawo garemu bayan mun nemi alfarma a wurin mahaifinka ya amince, lokaci ne kaɗan ya rage ka dawo garemu, bayan mun gama duk wani shirye-shirye mun tsara maka komai yanda ya kamata...kwatsam sai mummunan labarin mutuwarka ya riskemu. Mutuwar ce kawai Hammodi...Amma mun rayu tsayin lokaci ba don kai da mahaifiyarka kun mutu a zukatanmu ba..."

Rungumeshi Ya Mohaa ya yi yana mai jin wasu irin hawaye yace.

" JADDI!!! Ban sani ba..ban taɓa sanin cewa ina da wata mahaifiyar ba...ban taɓa sani cewa ina da ku ba duk tsayin lokacin nan JADDI...ku yafe min, ku yafe min dan Allah..."

Ba su ba, hatta mu da muke 'ƴan rakiya sai da muka zubar musu da ruwan hawayen tausayinsu musamman Dayaa...wallahy komai rashin imaninka sai ka tausaya masa.

Bubbuga bayan sa Jaddin ya shiga yi, cikin wata irin wuta da ke ciciyar zuciyarsa ya ce.

" Tabbas! Duk wanda yake da hannu a cikin wannan mummunan aikin sai ya ɗanɗana kuɗarsa...ko duk abin da na mallaka zai ƙare sai na tabbar ya ji a jiki da zuciyarsa irin raɗaɗi da ƙuncin da ya wanzu a cikin zukatanmu tsawon lokaci..."

Hannun shi Jadda ta kamo ta tsaya da shi a gaban wasu mata ta kalle su sannan ta kalle sa ta ce.

" Wannan ita ce Fattoom, wannan kuma Razia, su ne ƙannen mahaifiyarka...sai Mu'aƙƙib ga shi nan.."

Ta faɗa tana mai juyawa wurin wani dattijon mutum amma bai kai Jaddi tsufa ba.

"Na rantse da Allah mai girma! Sai na tarwatsa rayuwar duk wanda ya shirya wannan makircin..."

Rungumar da Mohaa ya yi masa ne ta hana shi ƙarasa zaratan kalaman da yake fitarwa daga bakin sa masu nuna zallar ɗaukar fansa da rashin ɗaga ƙafa da duk wanda yake bayan wannan abun.

"Jadda...Miyasa za ku tsaya a nan? Ya kamata a shigo da su ciki."

Cewar wata matashiya.

Jinjina kai Jadda ta yi tare da faɗin.

"Haka ne, kin yi gaskiya Suwara."

A tare matan suka iso inda muke tsaye. Tabbas ba don girmamawa da karrama baƙo na daga cikin abu mafi muhimmanci da girma ba a wurin su, da tabbas ba zamu Iya gane kan su ba. Ganin yanda suka tsaya suna kallonmu yasa Aunty Labiba ta harɗe hannayenta alamar ban haƙuri  ta ce.

" Ku yi haƙuri.."

Janyota Jadda ta yi ta sumbaci goshinta sannan ta jinjina mata kanta da ɗan murmushi ba tare da ta yi magana ba. Haka tabi mu ɗaya bayan ɗaya ta yi mana sannan muka ɗunguma zuwa cikin katafaren parlourn wanda ya ji shimfiɗu da kayayyakin more rayuwa na alfarma.

Wani irin freezing muka yi ganin HAJIYA zaune a tsakiyar parlourn tana kuka.

Gabaɗaya yaran na ta ba ƙaramin kaɗuwa suka yi da ganinta ta ba a irin wannan lokacin.

Ya Mohaa kam dama tun a waje ƙwaƙwalwarsa a toshe take. Tunanin yan da su Jaddi suka san da labarin wai yana raye ne ya tsaya masa a zuciya, musamman da suke iƙirarin cewa wanda duk ya aikata musu haka sai ya ɗanɗana kuɗar sa. Ganin Hajiya da ya yi kenan shi ne amsar tambayar sa.

Cikin wani irin mamaki EMRAAN ya kalle ta ya ce.

"Hajiya!!! Mi kike a nan?"

Sautin kukan ta ya ƙaru jin kalar tambayar Emraan a gare ta.

Miƙewa ta yi ta tsaya tana kallon Muhammad ɗinta wanda zuciyar ta ta cika da kewarsa cikin wata iriyar karaya ta ce.

"Ni ce na ɓata komai Emraan...saboda haka, ya zama dole na gyara da kaina...shiyasa na iso kafin ku..na bayyana musu gaskiyar duk abin da ya faru domin na sauƙaƙ..."

"Babu wani sauƙi a kan ki Hajiya Batula, wallahy dole zamu gurfana dake a gaban kotu...Duk abin da kika Kawo mu a garemu ba dalili ba ne,domin bamu yi gadon talauci ba da har kike tunanin idan kika ce kina son mallakar dukiyar RANIA zamu tsaya jayayya dake..."

Cewar Fattoom tana mai bin ta da wani irin kallon tsana da wutar fansa mai babbaka a cikin ƙirjinta.

Murya cike da nuna zallar karaya da rashin mafita ta kalli Fattoom ɗin ta ce.

" Za ku iya yin duk abinda kuka ga dama, ƙofa a buɗe take... Ni miye ya rage min a duniya?? Dangina, 'ƴa'ƴana da ma sauran mutanen da ke kewaye dani duk sun guje ni akan wannan mummunan aikin da na yi. A yanzu rayuwata ba ta da wani amfani, saboda haka ku kai ni a zartar min da duk wani hukuncin da ya dace dani...Na riga na gama nawa, kuma na gode wa Allah sarki da ya tona asirin nawa na farga na sauke duk wani haƙƙin da na ɗaukarwa kaina na wannan yaron tun kafin na mutu ko kuma yayi min nisan da ba zan iya kamo shi ba...Haƙkin Mim....Mijina kuma da ya yarda da ni..."

Wani irin matsanancin kuka ne ya sarƙeta wanda ya hana ta ƙarasa fitar da sauran abin da yake ranta.

Cikin kaukkausar Murya Jadda ta bi ta da wani irin kallo ta ce.

" Wannan kuma duk ya rage na ki, duk wannan koke-koken da kike wallahy ba zai hanamu shari'a da ke ba...Jami'ai!!! Ku shigo ku wuce mana da ita!"

Ta ƙarasa maganar tana mai ɗaga murya.

Cikin ƙiftawar ido, sai ga jami'ai Mata da Maza sanye cikin kaki sun shigo cikin parlourn kai tsaye sun zagaye su.

Rarraba ido ya fara yana mai lissafin maganganun kakar tasa waɗanda suka nuna tsananin zafi da kaifin ɗaukar fansa.

Lokaci ɗaya ya yi wani taku, kafin su kai ga tsayawa gabanta shi har ya riga su isa. Hannun sa ya ɗora a saman kafaɗarta ya rungumota a ƙirjinsa cike da zafi a kalamansa ya ce.

"Ita ɗin fa Mahaifiyata ce!!! Ita ce wacce ta raineni tsawon shekaru....Baba!"

Ya kira sunan Baba Ustaz yana mai kallon inda yake tsaye ya ce.

"Idan za ka iya tuna kalaman mahaifina na ƙarshe a ranar da zai rasu akan gadon asibiti...A wannan ranar, Hairi tana kwance akan kafaɗata tana bacci, a lokacin tana shekaru uku, Nadeeyah tana tsaye a gefen haguna hannunta a cikin nawa, Labiba kuma tana zaune a gefensa hannunta cikin na Alhajin itama tana kuka, Emraan baya nan yana makaranta, Hajiya da kai, kuna tsaye kowa da damuwa baibaye akan fuskarsa. A wannan lokacin, Alhaji ya kira sunana ya ce; Muhammadu! Da ace ba'a fasa auren ka har karo biyu ba, da yanzu kai ɗin magidanci ne wanda yake ɗauke da nauyin iyalinsa....wata ƙila bani da rabon ganin iyalinka Muhammad, amma ga AMANAR ƙannenka nan da mahaifiyarka na ɗora akan kafaɗarka. Ka yi iya yinka wurin kulawa da su kada ka taɓa bari su yi kukan mahaifi..."

Jinjina kai Baba Ustaz ya yi cike da jin sabon tausayinsu ya ce.

" Wannan haka yake Muhammad. Tabbas an yi haka a ranar da marigayi zai bar duniya..."

Waigawa ya yi yana fuskantar dangin mahaifiyar tasa cike da ƙwarin gwiwa ya ce.

" Jaddi! Jadda....Uncle...Auntie...dama sauran dangina da ban sani ba. Haƙiƙa ina jin raɗaɗi sosai a raina kamar yanda kukeji...ban san ku ba tsayin shekaru, amma kuma na rayu, kuma kun ɗauka cewa na mutu tsayin shekaru amma kuma kun rayu..rana tsaka kuma, ba za to ba tsammani sai gashi ƙaddara ta sake haɗamu...wannan kaɗai ya Ishemu farin ciki yasa duk wanda yayi mana wani laifi mu yafe masa Jadda...Ita ɗin matar mahaifina ce, waɗannan kuma ƙannaina ne ubanmu ɗaya, su ɗin amana ce a gareni Jadda...shin idan kuka ce za ku ɗauki fansa, Amanar mahaifina kuke so na banzarar wacce ya bani yana gabanin mutuwa ko kuma tozarta mahaifiyar waɗannan yaran waɗanda bani da tamkar su a duniya. Ina son su...Ina son su sosai kamar yanda nake son kai na Jadda...idan suna cikin farin ciki na fi su kasancewa a farin cikin, idan ma suna baƙin ciki na fi su kasancewa a baƙin ciki....ko don waɗannan abubuwan guda biyu ina so ku dubi girman Allah ku yafe mata. Kuskurenta ɗaya da ta aikata ba shi zai sa mu kasa duba dimɓin alherinta ba....Kuyi haƙuri,Allah da kansa yace yana tare da masu haƙuri masu yafiya..."

Emraan na wani irin tururi ya ƙara so inda yake tsaye ya rungume shi yana mai fashewa da wani sabon kuka ba tare da yayi magana ba. Ganin hakan yasa Labiba matsawa tare da su Hairi suka rungume juna suna ta kuka.

Tabbas wannan Yaya na su shi ɗin mai zuciyar zinari ne. Duk da irin abin da Hajiya ta yi masa bai duba komai ba, ya yafe mata kuma ya hana dangin mahaifiyarsa su hukunta ta.

Gabaɗayan su babu wanda bai tarfar da ruwan hawaye ba wurin. Jinjina kai Jadda ta yi ta ce.

"Shi ke nan Hammodi, tun da kace haka, mun yafe mata,Allah ya yafe mana baki ɗaya..."

Gyaran Murya Jaddi ya yi ya ce.

"Alhamdulillah! Wannan sunna ce mai ƙarfi ta annabinmu annabin rahama da yazo a cikin hadisinsa ingataccen da ya ce, idan an yi maka mummuna ka saka da kyakkyawa. Allah ta'ala yasa mu dace duniya da lahira. Kai da rayuwa tazo maka a haka, ba don Allah baya sonka ba ne, yana daga cikin babin ƙaddarar ka cewa sai hakan ta faru da kai, ko da sanadin Hajiya Batula ko Babu sanadinta...In Sha Allah, wannan kyakkyawan halin da ka nuna na haƙuri Ubangiji zai saka maka da mafificin alherin da baka za ta ba... "

Ji na yi ya janyo hannuna ta baya na zagayo zuwa gabansa. Kallona ya yi, sai kuma ya kalli kakan nasa cike da alfahari ya ce.

" Ubangiji ya saka min Jaddi...domin ya bani wannan... A lokacin da nake cikin tsananin duhu da damuwa...wannan Ita ce matar da ya jeho a cikin rayuwata,... Mace ta gari wacce ta zaɓeni ba don wani abin da nake da shi ba..ita ɗin tana da wata irin baiwa, hikima da kuma hangen nesa. Sunanta Beenafah..."

Jinjina kai Ya yi yace.

" Masha Allah! Allah mai girma! Allah ya sanya wa wannan auren naku albarka ya bada zuriya ɗayyaba...wallahy kunga haƙuri da kuke gani...mu riƙe haƙuri da Addu'a, sannan mu dogara ga Allah. Wallahy duk wanda ya dogara ga Allah har abada ba zai taɓe ba....mu riƙa haƙuri da rayuwa da kuma mutanen da ke zagaye damu, wani zaune kawai kake da shi amma sam baya nufinka da alheri sai sharri a rayuwarka...sai dai kuma, komai zamuyi mu riƙa saka Allah sannan mu yi komai da zuciya ɗaya sannan kuma mu riƙe zumuncinmu da kyau... "

Ya ɗauki tsawon lokaci yana mana nasiha sannan daga ƙarshe ya sallami jami'an suka tafi.

Janyoni Jadda ta yi ta sumbaci goshina a karo na biyu sannan ta sumbaci gefe-gefen kumatuna guda biyu cike da nuna zallar ƙauna. Haka suka yi ta passing-passing suna ta yi min kirari suna saka min albarka.

" Jadda....Mu shiga da su ciki su huta su ci abinci, duk sai a yi wannan daga baya.."

Jinjina kai Jadda ta yi tana mai kallon wacce tayi maganar tana murmushi ta ce.

"Haka ne Taimiyyah, please ku shiga daga ciki."

Wani ƙayataccen parlourn muka tsallaka muka shiga inda aka bamu wurin zama muka zauna har da Hajiya wacce har yanxu ta kasa haɗa ido da kowa har su Labiba ma. Amma su kam sai wani janta suke da fira cike da kewa.

Wasu manyan faskata-faskatan silver tray ne aka shiga jera mana a kan wata kewayayyar shimfiɗa ta lallausar carpet lungun parlourn, wanda da alama shi ne dining area ɗinsu. Da alama dai al'adar su ce a haka, domin a irin matsayinsu da kuɗin da suke da su ba za ka ce wai rashi ne yasa ba'a saka table a wurin ba.

Wata matashiya ce ta zauna a gaban abincin tana Murmushinta mai kyau ta shiga yi mana bayani cikin raha da cewa.

"Ni sunana Suwara, ni er gidan Razia ce ta wannan gida. Yanzu zan muku bayanin wannan Kalolin abincinda aka jera muku domin kuji daɗin cinsa yanda ya kamata. To! Kamar dai yanda kuka ga an jere plate-plate sun fi goma sha biyar a tray ɗaya, Haka ne mu al'adar abincinmu yake. Wannan ɗin...."

Ta faɗa tana nuna mana wani plate a ciki Sannan ta ci gaba da cewa.

" Asida kenan, itace ginshikin abincinmu na Sudanese. Ana yin ta ne da gero ko fulawa sai a jujjuya ta kamar tuwo, sai a zuba mata wannan miyar wacce muke kira da mullah. Sannan wannan kuma, ita ce Mullah bamia, miyar kuɓewa kenan. Sai kuma wannan, Mullah sharmout, miya ce da akayi ta da naman da aka busar. Za ku ji ƙamshinta mai daɗi sosai, ga shi kuna gani har da Man shanu muka saka mata. Sai kuma Kisra da Mullah wanda kuna gani farin fanka ne (flatbread) da muka yi ta da gero, ga miyan Mullah Sharmout nan da ita za'a ci. Ko kuma aci da wannan Miyar Mullah tagalia, wacce miya ce ta nama da albasa, tumatir da ƙamshi. Mullah Rob Kuma, miya ce ta nono da gero,amma dai ita tana da ɗan ɗaci haka da santsi. Wannan kuma....Shi ne Ful medames wanda wake ne gashi kuna gani. Wanda aka tafasa sosai da mai, tafarnuwa da kuma lemon tsami...gashi kuna gani an ƙawata shi da ƙwai, salati da kuma burodi. Sannan ga Shawarma ga kuma grilled meat, Sannan ga Kuma Laham Mashwi wanda kuna gani gasasshen nama ne wanda aka shirya shi da kayan miya akai masa ado. Ga salata da sesame sauce. Ga cake, ga pizza ga Kuma doughnut. Ga kuma nama soyayye. Sai abin sha kuma, mu nan munfi amfani da lemukan da muka haɗa da hannunmu. So... Ga Karkade, zoɓo kenan. Sai Shai bi habahan, wanda shayi ne da aka haɗa da Clove, cinnamon, da kuma cardamom sai sugar. Ga kuma Gahwa, Coffee Kenan. Sannan abu na ƙarshe, ga Basbousa, ma'amoul, ga kuma dabino mai zuma."

Ya salam! Wai Allah ɗaya gari bam-bam inji Bahaushe. Na san dai kamar yan da na rasa bakin magana haka ma su Aunty Labiba, domin babu abin da muke sai murmushi, da mai bayanin da abincin da take mana bayani a kai duk abun burgewa ne.

Ganin yanda muke ta wani murmushi yasa ta jinjina kanta tana mai kallon sauran en uwanta ta ce mana.

"Bismillah.."

Kallon Dayaa na yi ina mai sakar masa murmushi,shima ɗin ganin yanda nake kallon sa yasa ya jinjina mini kansa ya yi min murmushi sannan ya janye daga kusa da Jaddi ya matso gangar tray ɗin.

"Mummy...yawuna tsinkewa yake yi.."

Cewar Hairi tana mai ƙara matsowa kusa dani. Murmushi na yi mata na ce.

"Mu ci."

Zaunawa muka yi muka ci abincin cike da nishaɗi da raha,kuma Alhamdulillah! har Dayaa da Emraan da nake ganin suna da tsantseni basu nuna komai ba.

Bayan mun kambala muka tashi suka wuce masallaci mu kuma muka shiga ciki muka yi salloli. Taimiyyah da Suwara da kuma wata wacce na ji sun kira da Laurat ne ke tare damu suna ta mana fira suna bamu labarai iri-iri.

Bayan sallar Isha ne muka dawo ainahin parlourn da muka fara shigowa muka zauna fira ta dawo ƙasa. Nan suka gabatar masa da dangin su gabaɗayan su da irin dangantar suke da ita. Haka suka yi ta bamu tarihi kala-kala da irin rayuwar da mahaifiyar Ya Mohaa ta yi har zuwa aurenta da kuma irin ziyarar ta ta ƙarshe kafin mutuwarta.

Daga nan kuma aka dawo firar rayuwar Ya Mohaa inda ya basu tarihinsa da irin aikace-aikacen sa.

Kallona Suwara ta yi tana murmushi ta ce.

"Aunty Beenafah! Mufa a nan, indai ke matar aure ce, to ya zama dole a riƙa ganin ki da lallen gargajiya...idan kuma baki da lalle a nan to ke budurwa ce...idan kuma ke ba'a ma'abociya son lalle ba ce, to haka za'a riƙa nuna ki ace baki ɗauki aure da daraja ba.."

Dariya muka yi dukkanmu sannan na jinjina kai na ce mata.

"Ci gaba da bamu labaran al'adunku please...abun akwai daɗi..."

Dariya Taimiyyah ta yi ta ce.

"To muma sai ku bamu labarin Nigeria kenan.."

Ɗaki muka koma muka ci gaba da fira. Muna nan sai ga Jadda ta shigo da farantin lalli a hannunta ta zauna a gefena cike da murmushi mai daɗi ta kama hannuna ta fara saka min.

Murmushi na yi jin yanda yake tashin ƙamshi na ce.

" Jadda Lallen nan sai ƙamshi yake.."

Jinjina kai ta yi tana murmushi ta ce.

"Lallen mu ba kamar sauran lalle yake ba, ana mishi haɗi na musamman."

Mu uku, haka ta bimu ɗaya bayan ɗaya ta yi mana ni da Aunty Labiba, da Aunty Nadeeyah Hairi ce kaɗai ba'a yi mata ba kasancewarta budurwa.

Gaskiya a yau, zance wannan ranar ta kasance ta musamman domin mun samu kanmu a wata duniya ta daban mai cike da nishaɗi da barin tarihi a zuciya.

Bayan an kammala kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare aka kawo wani turaren aka Ƙara turarawa sannan Jadda ta kalleni wanda kamar yanda babu wata alamar bacci a idonsu nima haka ne a wurina ta ce.

"Beenafah..tun da ke Allah yasa kin zo da Mijinki. Ki tashi ki tafi kada ki barshi shi ɗaya..."

Da sauri Aunty Labiba ta ce.

"Wallahy haka ne Jadda..dan Allah ki tashi ki tafi.."

Cuno baki na yi na ce.

"Ni dai wallahy ba inda zanje a nan zan kwana kamar kowa. Ai shima tun a jirgi ya ce min yasan cewa gidan mutane muke saboda haka wurin kwananmu ba ɗaya ba.."

Kallon-kallo suka shiga yi a tsakaninsu jin wata irin ɓarusa da na yi. Miƙewa Jadda tayi ta sulale yayin da su Aunty Labiba suka saukar da kansu a ƙasa babu wanda ya sake yi min magana wanda ni kam a tawa haukar a daidai nake.

Ya Mohaa kuwa, ya jima tare da su Jaddi da Uncle Mu'aƙƙib har kusan 2am sannan daga ƙarshe ya je har ɗakin Hajiya inda masaukinta yake ita ɗaya.

Bakin faskekiyar windown glass ya tarar da ita tana tsaye tana kallon hasken da ke ta walwali a waje.

Takowa ya yi ya zo har inda take tsaye ya tsaya a gefenta shiru ba tare da yace komai ba.

Ita kuma jin ƙamshinsa yasa ta waigo tare da ƙoƙarin tsayar da hawayenda suka samu gindin zama a kwarmin idanuwanta akan halin take ciki a yanzu ta kalle shi murya a ƙasa sosai ta ce.

"Ka yafe min Muhammad..."

"Momma! Abubuwa fa haka suke zuwa a cikin rayuwarmu kuma suna wucewa. Duk abin da zai zo mana, in ma na daɗi ko na baƙin ciki komai tsananinsa watarana mai gushewa ne. Alfarma ɗaya nake nema a wurin ki dan Allah..."

Hannayen shi ta kama tana mai silalo da wasu sabbin hawayen na damar cike da nuna karaya a kalamanta ta ce.

" wace Alfarma ce wannan Muhammad.?"

Shi ma hawaye cike da idonsa ya ce.

" Kin tsaurara abubuwa Momma...wannan abun bai kamata ace ya fita ko'ina ba. Sam hakan bai Kyautu ba. Dan Allah ki manta komai daga yau ki ɗauka tamkar komai bai faru ba...na yafe miki Momma..dangina ma sun yafe miki.."

Kanta ta ɗora akan kafaɗarshi tana mai ci gaba da raira kuka a hankali har sai da ya kambala maganarsa sannan daga ƙarshe ta ɗago ta kalle shi ta ce.

" Nima alfarma ɗaya nike so a wurin ka Muhammad. Dan Allah ku barni gobe na juya na koma gida. Duk da cewar komai ya wuce a wurin ku..ina jin kunya da nauyin kasancewata a nan..na gode sosai da karamci. Na gode sosai da kuma yafemin..amma dan Allah gobe kada ku hanani tafiya."

Jinjina mata kansa ya yi ya ce.

" Shi ke nan. In sha Allahu gobe za ki tafi, amma dan Allah ki yi min alƙawarin cewa ba za ki sake kuka ba Momma.. "

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana mai jinjina masa kanta alamar ta ɗauka amma kuma tasan cewa wannan alƙawari ne wanda ba zai taɓa ɗaukuwa ba a wurinta. Domin har abada hawayenta ba su daina kwaranya ba dangane da wannan abin da ta aikata, musamman yafe mata da yayi kai tsaye da shi da dangin nasa. Idan ta tuna sai taji Zuciyarta ta ƙara tsinkewa. Duk tsawon shekarun da ta ɗauka tana zaluntar sa ita bata taɓa jin cewa ba a daidai take ba, sai yanzu da asirinta ya tonu shi rana ɗaya yace ya yafe mata.

"Akwai rashin bacci a tare da ke, kuma ga shi kin gaji."

Hannunta ya janyo ya kawota bakin bed ya zaunar da ita sannan ya Juya ya fita jim kaɗan sai ga shi ya dawo hannun sa ɗauke da Tea mai zafi da kuma ruwa ya zauna a ƙasa ya bata yana faɗin.

"Ko abinci kin daina ci, ɗazu ma muka ɗai muka ci ke baki ci ba."

Karɓar Mug ɗin tayi tana sha tana hawaye wanda take jin yana wuce mata a Maƙoshinta tamkar saɓen dalbejiya.

Half Kawai ta iya sha,kuma shima bai matsa mata ba. Bayan ta ajiye cup ɗin ya bata ruwa ta sha. Sai da ya tabbatar ta kwanta sannan ya tashi ya kashe wuta ya fita.

Tana ganin ya fita ta sake fashewa da kuka tana wani irin girgiza kai tace.

"Astagfirullah Allah! Mi na aikatawa kai na ni Batula! Ga shi dai na ƙare da jin kunya...oh! Duniya kenan fa! Ya Allah ka karemu daga aikin danasani marar amfani."

Mohaa kuwa, koda ya koma ɗakin da akace an ware masa shi da Beenafah ya ɗauka zai tarar da Ita a ciki. Amma kuma wayam bata nan, agogon wayarsa ya sake dubawa ya ga dare ya tafi sosai amma kuma ace har yanxu ba ta zo neman wurin kwanciya ba. Numbern ta ya lallabo kai tsaye ya kira amma bata ɗaga ba, kira yafi biyar . Haka ya dawo jera mata text still ba respond, dole ba don ransa ya so ba ya cire kayan jikin sa ya shiga ya watso ruwa ya zo ya kwanta da tunaninta fal a ransa.

Ni kam ina ganin kiransa na tura ta a ƙarƙashin pillow na je na yi wanka na zo na kwanta abina.

Aslm, da fatan kuna lafiya Masoya...ina mai baku haƙuri ,kuma in sha Allah zamu riƙa tsallake kwana ɗaya na update.

✍️ OUM-AMEER ✍️