KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Washegari....
Na'ima ce zaune kan sallaya bayan ta idar da sallahn asuba hannunta riqe da qaramin carbi tana azkhar, bayan ta gama ta dauki Quran din gabanta ta miqe ta kaishi ma'ajiyansa sannan ta nade sallayan, bata cire hijab dinta da ta dora kan dogon kayan baccin jikinta ba ta fice daga dakin ta shiga falon mami dake nan kusa da nata dakin, ta samu Mami zaune itama bisa sallaya tana azkhar
Mamin ta dago kai tace "Na'ima kin tashi" cikin sanyi tace "Eh" ta qaraso ta zauna tace "Ina kwana Mami" Mami ta amsa da "Lafiya Habibti,.how was your night?" tace "Alhamdulillah" suna nan zaune Nafisa ta shigo itama sanye da hijab ta zauna kusa da Mami ta gaishe ta sannan ta juya suka gaisa da Na'ima, Mami na kallon fuksan Nafisan tace "Baby, meya samu idonki haka?" dan wutan falon tar yake a kunne hakan yasa ta ga idon Nafisan wanda yadan kumbura, sai Nafisa tafara hamma tace "Bacci ne bai isheni ba Mami"  Mamin tace "Aikuwa kije kiyi dan ga idonki nan ya nuna" da haka Nafisa ta miqe ta shige dakin Mamin, sanin Mami zata dade zaune nan bata tashi ba yasa Na'ima miqewa ta shige dakin itama, ta qarasa kan gadon Mami da Nafisa ke kai ta kwanta tana jawo bargon, sai Nafisa ta juyo tace "Kinsan Allah, har wani banging kaina yake" Na'ima ta dan kalleta tace "Sannu sis, halan bakiyi bacci da wuri ba jiya" ta amsa da "Fada mukayi da mutumin, in na tashi zakisha labari" sai Na'ima tace "Kuma dai, yi baccin to" ta gyada kai ta juya tana gyara kwanciyanta, da haka suka koma wani baccin.
Sai wajen qarfe takwas Na'ima ta tashi ta fita daga dakin tabar Nafisa dake bacci, sanin Mami na bangaren Abba yasa ta wuce nata dakin ta shiga wanka, bayan ta fito ta nutsu tayi shafe shafenta ta shirya ta sauqa babban falon dake downstairs, hango faruk tayi zaune a dining yana breakfast shi kadai hannunsa riqe da waya yana dannawa, ta qarasa wajensa da murmushinta, ya dago kansa daga abunda yakeyi yace "Habibtin Mami harkin tashi" taja kujera daya ta zauna tace "Eh Yah Faruk ba dai har fita zakayi ba" ya gyada kai "Yeah, I'm swamp up with work at office these days wlh" tace "Ayya, Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin sannan yace "Kun sake zuwa kallon wani match din keda Nafisan kuwa?" Kafin ta amsa taji Nafisan dake bayansu tana tahowa tace "Me Nafisa tayi da sassafen nan Yah Faruk" ta qaraso taja kujera itama sai Faruk yace "Laifi kikayi babba" Na'ima na murmushi tace "He was asking ko mun sake zuwa kallon wani football match din" Nafisa ta kallesa tace "Can you believe the tickets were sold out within 24 hours" yace "May be baki siya da wuri bane, first hours akafi samun tickets daman"  zatayi magana aka kirashi video call a WhatsApp dinsa, sai ya dan daga mata hannu yace let me take this, ya dauka yana kallon fuskan wanda ke cikin wayan yace "Good morning Yaya" ta daya bangaren Ahmad ya amsa cikin deep voice dinsa "Morning Faruk, ya mutan gidan?" Faruk yace "Alhamdulillah" sai Ahmad yace "Good...I've send you some papers via email, I need your review on them" Faruk na kallonsa ya gyada kai, yace "Sure, ba matsala Yaya" sai Nafisa tazo bayan Faruk tasako kanta tace "Good morning Yaya" Ahmad ya amsa "Lafiya Nafisa, yaushe kika dawo?" tace "Jiya, yasu Mamma?" Na'ima dai na sauraronsu tana binsu da kallo, saita samu kanta da sauraron na cikin wayan jin yanayin accent dinsa that was so thick and it sounds British but not that deep British. 
Bayan sun gama gaisawa Ahmad ya maida hankalinsa kan Faruk yace "Please do take a good look on them I need your answers, karka dau lokaci" Faruk yayi murmushi yace "in sha Allah Yaya, I'll drop by tomorrow to give you the feedback" Ahmad yace "See you then,thanks Man" da haka sukayi sallama Nafisa na kallon Faruk tace "Wai yadawo gari daman" Faruk yace "Ya rigaku dawowa ma" tace "Ya Adam fa?" ya amsa da "Wannan yana gari da dadewa ma ai, what's with the questions?" tadan daga kafada tace "I just want to know ne" sai Na'ima ta miqe ta wuce kitchen tabarsu nan suna magana. 
Shiganta kitchen tasamu lantana tana aikin hada breakfast dinsu ta gaishe da Matar da kana ganinta kasan she's in her late 30's fuskanta cike da bille. Na'ima tace "Mama sannu da aiki, Ina kwana" Lantana ta amsa "Lafiya habibitin Mami, jiya kun dawo bananan ko" Na'ima tace "Eh mama, ya hakuri kuma Mami tace an muku rashi" tace "wlh dai, can suleja naje, yar wata qanwata ce ta rasu, yarinya qarama da ita, jiya kwanana hudu acan" Na'ima tace "Allah sarki, Allah yasa mai ceto ce" tace "Amin Habibitin Mami, bakiga yarinyar ba kuwa fara sol kamar ke dinnan, abun dai abun tausayi" sai Na'ima tayi murmushi ta fara tayata aikin, suna aikin Lantana na bata labarai gameda rasuwan wanda itadai ba fahimtan wasu take ba, Nafisa ta shigo itama suka gaisa Lantana na fada mata uzurin rasuwan, bayan Nafisa ta gama nuna nata alhinin  tace "Mama kince zaki soya mana gyada mai gishirin nan idan zamu dawo" ta qarasa maganan tana taya lantana bare maggin da zata saka a pepper soup dinda ke dahuwa akan gas cooker nan gabansu, lantana tace "aikuwa yau zan soya muku" 
Nan suka kammala sauran aikin tareda Lantana, Mami ta shigo kitchen din bayan sun gama tace "Sannu lantana, sannunku kuma" suka amsa.
Ta dauki breakfast dinsu ita da Abban ta tafi kaiwa can falonsa while su Nafisa suka kai nasu dinning Lantana na tayasu, basu jima da fara ci ba su Al'ameen da Abubakar sukayi joining.

Bayan sun gama suka kai kayayyakin kitchen suka dauraye, don ladabtarwan Mami ne akan bakomai mai aiki zatayi musu ba, abubuwa da dama dakansu sukeyi a gidan, bayan sun gama Nafisa ta fice, sai Na'ima ta dauko plate ta debi sauran cupcakes dinda Mami tayi musu jiyan ta wuce upstairs, dakin Nafisa ta shiga ta sameta gaban madubi zaune, sai ta tafi ta zauna kan gadon Nafisan dake gyare neatly ta ajiye snacks din hannun nata sannan tace "Oya..spill the beans, meya hadaki da Umar din jiya?" Nafisa ta miqe ta baro gaban madubin tadawo bakin gadon itama ta zauna tace "Sis I don't know what's wrong with Umar, bansani ba ko jealousy ne ko kuma insecurity ne yake damunsa, kai duka ma" Na'ima na kallonta tace "Amma ai so ne yasa hakan sis" sai Nafisa tace "Ina sonsa ai nima but this is too much and i hate it with all my heart, sometimes I wonder why i stayed with him for this long and why i can't let go" Na'ima tace "I know that loop, kinsani...I know what it means to be trapped In a loop going around without escape" sai Nafisan ta juyo tace "But...." sai kuma tayi shiru tana kallon Na'ima tarasa abunda zatace, ganin haka sai Na'ima tayi dan murmushi me ciwo tace "Shiyasa bazan taba judging dinki ba akan wannan conflict relationship din da kuke having, the guy loves you and you do too, try and resolve things tunda kowa yasani ba iya rabuwa zakuyi ba" ta qarasa maganan tana murmushi. Nafisa ta dan harareta tareda daukan cake daya takai baki tace "Tabdi, rabuwa kai, jiya ma nace masa I'm done yayi fushi kuma nakashe wayana" Na'ima ta jijjaga kai tana dan cin cake din itama tace "Nidai banason ku rabu, Ina laifin mai kishinka Nafisa?" sai Nafisa ta miqe ta koma gaban madubin tafara cleansing fuskan ta tace " I'm serious this time" Na'ima ta jijjaga kai tana dan dariya kawai, ta juya ta janyo laptop din Nafisa dake kan bedside drawer ta kunna zata fara kallo.