KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

A Week Later...
Na'ima ce zaune cikin dakinta akan gado, hankalinta yana kan abunda take typing cikin laptop dinta, yau satinsu daya da dawowa gida and a lot has happened, sunje shopping, Nafisa ta jasu outing cikin gari and all other fun things, jiya ma part dinsu Faruk dake gefen main building din gidan suka wuni suna game din Ps wanda har da Al'ameen da Abubakar din sukayi.
Nafisa ce ta shigo dakin hannun ta riqe da leda ta miqa mata, karba Na'ima tayi tana duban cikin ledan taga sweets da chocolates masu yawa, Nafisa tace "karki fado sunana idan mami ta kamaki kinasha wlh" Na'ima tayi dariya sanin Mami ta hanasu yawan shan kayan zaqin, farkon dawowansu ta barsu suna sha amma ganin suna iya shanye chocolate kusan ashirin a zama daya tace bata so, kuma karsu sake siyo kayan zaqi masu yawa a gidan.
Nafisa na tsayen tace "Ki shirya muje gurin fitting dinnan Meerah tana ta kirana a waya" sai Na'ima tayi mata questioning look tace "Fitting kuma Nafee?"  ta amsa da "Eh na gown din da zamu saka wajen event din bikin Salma mana" Na'ima tace "Nifa bazanje event ba Nafisa" zama Nafisan tayi kusa da ita tace "Meyasa? Mami ta hanaki ne?" ta jijjaga kai tace "A'a kawai bazanje bane" shiru Nafisa tayi batace komai ba har Na'ima ta maida hankalin ta kan laptop din dake kan cinyanta ta cigaba da typing, can Nafisan ta miqe ta fita sai Na'ima ta dago kai ta bita da kallo jikinta na sanyi.
Fitan Nafisa ta shiga falon Mami ta sameta nan zaune da Faruk suna magana, turaren wutane a gaban ta tana mixing dinsu cikin kwalba, Nafisa ta qarasa kan kujeran gefen Faruk ta zauna.
Hankalin Mami na kan abunda take yin tace "Baby baku fara shirin fitan bane rana tana yi fa, kincemin zaku fita dazu" Faruk yace "Ina zasuje?" Nafisa tace "Dama fitting zamuje gurin Meerah na gown din event din bikin, Mami kinji wai Na'ima nacewan baza taje gurin dinnern ba" Mami ta dago kanta tana kallonta sannan tace "Ai daman ban aika kayan events da ita ba" kafin Nafisa tayi magana Faruk ya katse ta da "Ai tafiki hankali datace bazataje ba" Nafisa tace "Haba Yah Faruk it's just an event fa" yace "Yes but Nafee kinsan kalan mijin da Salma zata aura ai, you know who he is, yawanci guys masu ji da tashe acikin Abuja da wajenta zasu halarci event din, you can't be exposing Na'ima to that sort of places" Mami dai na sauraron fadan da Faruk yakewa Nafisan batace komai ba, sai Nafisa tace "but Yah Faruk i thought it's high time she starts living her life, doing the things she likes the way she wants to" Mami tace "Many things but not this nafisa, and you know things are not over yet" Nafisa na kallon Mami tayi shiru batace komai ba, sai Mami ta cigaba "Quite sure zata je gidan bikin ta gaisa da wasu 'yan'uwan because it'll be rude of her not to, tunda komai dadewa zasu iya haduwa da ita a cikin gidan nan, but not going to parties...and that's final" cikin sanyin jiki Nafisa tace "Yes Mami" sai ta miqe ta fice daga dakin suka bita da kallo.

Haka suka shirya akan Na'ima zata raka Nafisan gurin dinkin, ta saka black color Abaya da ta fito da haskenta da kyawunta while na Nafisan kuma maroon color, bayan sunyi sallama da Mami ta basu saqon toiletries da zasu biya super market su siya mata, suka fice daga gidan cikin motan Nafisan.

Bayan sun isa babban fashion store din wanda ya kasance gurin dinki, designing da kuma saida dinkakkun kaya sai suka tadda Meerahn tsaye a reception tana magana da receptionist din nata, ganinsu Na'iman yasa ta tako garesu tana murmushi tace "Look who we have in town" ta qaraso tayi hugging din Nafisa suna fara'a sannan ta juya tayi hugging din Na'ima ta sake cewa "I've been waiting for you guys like for'everr" Na'ima tayi murmushi dan tasan Meerah, ita tayi mata duk dinkunanta farkon zuwanta gidansu Nafisan, sai Nafisa tace "Sorry sis" Meerah na fara'a ta amsa da "Now you have to pay me double" sukayi dariya gaba daya, da haka ta jasu suka tafi fitting room din da ya kasance a upstairs na building din, bayan tayi serving dinsu refreshments Na'ima na zaune kan resting sofa wasu staff mata guda biyu suka shigo tare da Meerah suka hau gwada Nafisa dake tsaye kan gajeran stool, sai Nafisa tace "Husna tazo kuwa?" Meerah tace "Tazo almost a week now"

Bayan angama sukayi salla anan  room din sannan suka wuce gurin aiken da mami ta musu, basu suka koma gida ba sai yamma.

Shigowarsu gidan bayan sunyi parking Na'ima ta lura da wata baquwar mota, wata sleek ride dake fake nan parking space din, atare suka fito Nafisa ma da ta lura da motan tace "Su Yaya Ahmad sun zo kenan" Na'ima na kallon motan ta rufe cab din gefenta suka wuce cikin gidan hannun Nafisa riqe da ledan kayan da suka siyo.
Shigarsu falon sai Na'ima ta hango Mami zaune da wasu maza biyu zaune kan kujera sunyi backing dinsu, dayan yana having conversation da Mami while dayan yana riqe da waya a hannunsa yana kallonsu Mamin, qarasawa sukayi cikin falon Nafisa na gaba, mai maganan ya dan dago ya kallesu yace "Nafisa" ta amsa da "Yah Adam sannunku da zuwa" yace "Yauwa" Mami tace "Baby kundawo" Nafisa tace "Eh Mami" suka qarasa Nafisa ta ajiye kayan hannunta a gaban Mami sannan suka zauna kan kujera kan Na'ima na qasa, Nafisa ta sake cewa "Yaya sannunku da zuwa, Ina wuninku" Ahmad ya dago kansa, a nutse yace "Lafiya Nafisa" husky voice dinsa na shiga kunnen Na'ima, sai shima Adam ya amsa gaisuwan, cikin sanyin murya Na'ima tace "Ina wuni" tadai ji Adam ya amsa amma mai deep voice din da ake kira da Ahmad dinne bataji ya amsa ba, sai tadan dago kanta ta kalleshi, Caraf idanunta suka shiga cikin nasa yana nazarinta.
Kauda idonta tayi da sauri ta maida kallonta kan Tv dake falon tana jin bugun zuciyarta acikin kunnenta, Tunda take bata taba ganin idanun da suka mata kaifi ta kasa jure kallonsu kaman na bawan Allahn nan ba. Shima Ahmad dauke idonsa yayi ya cigaba da danna wayarsa, Mami tace "Ka dai ce bazaka dawo gida ba Ahmad, ka riqe Lagos dinnan har dawowa yana maka wahala" Ahmad ya juya ya kalli Mami a nutse yace "Akwai wasu abubuwan danake son nayi settling ne acan mami" sai Mami tace "Ai zamanka dai anan din yafi, tunda can din bawai iyali ka ajiye ba" ta cigaba da maganan tareda juya wa tana kallon Adam tace "Kaima Adam baka fada masa gaskiya ko" sai Adam yayi dariya yace "Nima gajiya nayi da fada masa gaskiya, may be yanzu zeji taku Mami" Mami ta maida hankalinta kan Ahmad din tace "Ai Mamma tace min kunyi maganan kuma har yanzu baka dawo ba" Ahmad yadan shafa kanshi yace "In Sha Allah za'ayi yanda kuka ce din Mami" 
Itadai Na'ima duk ta taqure acikin falon kaman ace cass ta arce, Adam ya juyo yana kallonsu yace "Nafeen Mami yaushe kika dawo?" Nafisa da tunda ta gaishesu ta maida hankalinta kan waya ta dago kanta tana murmushi tace "For a week now Yaya" yace "Ma Sha Allah, kin kusa gamawa amma" ta gyada kai tace "Eh saura 4 to 5 months haka" yace "Allah ya bada sa'a" yana kallon Na'ima da tun dazu idonta ke kan Tv bata juyo ba yace "Mami baquwa kukayi ne" ta amsa da "Eh 'yar dan'uwana ce dake can Nijar, tare suke karatun da Nafisan ma" Adam yace "Allah sarki" sai Mami tace "Zo ku miqamin kayan nan sama in na shigo zan waresu" Na'ima ce farkon miqewa kamar wanda falon ke mintsinta, sai Ahmad yadan dago ya sake kallonta ta qarasa ta karbi kayan, Nafisa ta miqe itama tace "To yaya sai anjimanku" suka amsa da Toh, tabi bayan Na'ima da har ta isa stairs, suna shiga falon Mamin Nafisa tace "Ke yanzu naga texts din mutumin bari kiga" Na'ima da taji duk kafafunta a sanyaye ta nemi kujera ta zauna anan falon tana tuna idanun wannan bawan Allah data baro a falo, Nafisa ta qaraso kusa da ita tana nuna mata wayan tace "Kiji wai yanzu ma yana hanya zaizo" cikin sanyin murya Na'ima tace "Kibarshi yazo sis, you have to settle fadan nan naku once and for all" sai Nafisa tace "Allah ko?" Na'ima ta gyada kai, shiru Nafisan tayi kamar me nazarin wani abu sannan ta miqe ta tafi dakinta, diban kayan Na'ima tayi ta dorasu kan table din dake nan falon sannan ta fice tana ture duk wani tunani daga ranta.