RUWA CIKIN COKALI

Chapter ,8

by @mamanafrah3028

***



*RUWA CIKIN COKALI* 
(Ya ishi mai hankali wanka)
 
                  
                NA


         MAMAN AFRAH

 
.        *Daga marubuciyar* 
  *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* 
      *****

           BOOK 1

         PAGE 7️⃣


               *MAMY*

  Da kallo ta bi bayan Mubin har ya ɓacewa ganinta tana jin babu daɗi a ranta, Zalika ce ta dawo da ita daga ƙaramin tunanin da ta tafi ta hanyar faɗin

"Mamy ki yi haƙuri kawai amma dai Baffa ba ya kyauta mana, tun muna yara bamu san daɗin hira ko zama inuwa ɗaya da mahaifinmu ba, gashi har mun girma abin yana mana ciwo amma hakan bata sauya zani ba" 
  Mamy ta ɗan nisa ta ce

"Zalika kin san na yi iya ƙoƙarina wajen ganar da mahaifinku kuskurensa amma ya ƙi fahimta ko ya gane bare har na saka ran cewa zai yi aiki da shawarata, kin san da yawa wasu mazan suna ganin mata basu da tunanin sannan kasancewar an ce mace tana ƙasan namiji haka ya sa wasu mazan suke ganin mace ba za ta basu shawara ba su ɗauka, bare shi da yake ganin kawai duk abin da zan faɗa ma labarin ƙanzon kurege ne don shi a tashi fatawar idan ya ba ƴaƴa abinci da biya musu dukkan buƙatunsu shikenan ya sauke haƙƙi!"
 
   Suna cikin tattaunawa suka ji mai gadi ya buɗe ƙofa, jim kaɗan sula ji shigowar mota wacce sun tabbata Baffa ne ya dawo domin lokacin dawowarsa ya yi.


   Zalika ce ta miƙe tsaye da sauri, Mamy ta riƙo hannunta ta ce

"Ina za ki je?"

  Zalika ta ce

"Ɗaki zan je"

 Mamy ta ce

"Mai ya sa?"

Zalika ta ce

"Kin san yanzu Baffa zai shigo ni kuma ba na son yake wannan ɗaure fuskar" Jin furucin ta sai Mamy ta sakar mata hannu abin da ya ba Mamy mamaki da sassarfa Zalika ta bar falon tamkar wanda take gudun kar wani abun tsoro ya afka mata.

  Karaf ƙaran buɗe ƙofar falon ya ziyarci kunnuwa Mamy wacce ta yi tsuru kamar mai jiran tsammani. Kamar yadda ta tsammata ɗin hakan ce ta kasance domin yadda ya turo ƙofar kamar wani kumurcin zaki haka ya shigo ran nan nasa a ɓace kamar an faɗa masa mutuwa, ko arziƙin sallama ba a samu ya yi ba, ƙofar ya mayar ya rufe sai da ya zo tsakiyar falon ya ja ya tsaya yana ƙarewa ko ina kallo. Har lokacin Mamy bata ɗago ta kalle shi ba.

  Takowa ya fara yi sai dai ya zo falon sannan ya nemi waje ya zauna bayan ya ajiye ledar da ya shigo da ita, kallonta ya yi ya ce

"Baki ganin mutum ya shigo kika watsa yina?" Sai da ta yi yaƙi fa zuciyarta ganin bata faɗa masa wata magana da za ta ƙona masa rai ba, a hankali ta buɗe dashashshiyar muryarta ta ce

"Sannu da zuwa"

  Kallo ɗaya ya juya ya mata ya ga ɓacin rai kwance a saman fuskarta sannan daga hakan ma ya fahimci tana cikin damuwa don yanayinta ya sauya kuma yana iya hango sawun hawayen da ya zuba a idanunta. 

   Sai dai kasancewarsa ba ya cikin mutanen da suka damu da damuwar iyalansu ba sai ya juya ya nufi hanyar da za ta sada shi da part ɗinsa, Mamy ɗago kai ta yj tana bin bayansa da kallo ji take kamar ta janyo shi ta buɗe kunnuwansa ta faɗa masa cewa ya gyara halayyarsa sai dai ta san wannan ba mai iyuwa ba ne.

   Bayan tafiyarsa da mintina kaɗan ta tashi ta goge fuskarta ta bi bayansa duk da ta san bin bayan nasa ba ƙaramin matsala ba ne amma dai tana ƙoƙarin sauke nauyin haƙƙinsa da ya rataya a wuyanta matsayinsa na miji a gare ta.


     Tana zuwa ta ɗan yi kamar minti uku a bakin ƙofar kafin ta tura ƙofar, taa shiga ta mayar ta rufe, Baffa da yake ɗaure da towel a ƙugunsa ya juyo ya ce

"Lafiya dai?" ,Duk da ba wannan ne karo na farko ba da ya jefa mata tambayar ba amma dai ta sosa ranta. Cikin sanyin murya ta ce

"Lafiya ƙalau, dama ruwan wanka zan haɗa maka"

  Baki sake yake kallonta kafin ya ce

"Ikon Allah na zaune ya faɗi, yanzu akwai ruwa a famfo a banɗaki da komai sai an biyoni" Jin furucinsa sai ta juya cike da takaici ta fita, ledar da ya ajiye ta ɗauka ta adana kayan bata san wane irin miji ne shi ba ko ta ce bata san wace irin zuciya gare shi ba da  babu ruwansa da iyalansa.

  Bayan an yi sallar magriba ya shigo gidan dawowarsa daga masallacin magriba kenan, sai da ya yi kamar minti uku da shigowa sai ga Mubin ma ya shigo don dama ta san ba zai bari ya bishi ba irin na ɗa da uba sai dai kowa ya yi tafiyarsa da ban.  A kujera ya yada zango ya ɗauki remote ya sauya channel ya ɗan ƙara volume.

   Ko da Mubin ya shigo bai tsaya a falon ba, tun da ya yi wa Baffa sannu da zuwa ya amsa dakyar a ciki-ciki sai ya wuce ya tafi ɗakinsa ya kwanta yana danna waya. Zalika ma da ta idar da sallah ta zo ta ce

"Baffa barka da dawowa, an dawo lafiya"

  Baffa ya amsa a taƙaice da

"Yawwa" Sum-sum ta koma ɗakinta a kan sawunta. Mai aiki ta shigo ta jera kayan abinci a dining kamar ba gobe, Mamy ta ɗaga waya ta kira Zalika da Mubin a kan su zo a ci abincin dare duk da cewa ana cin abincin ne kamar a gidan makoki amma babu wani raha ko nuna kulawa a tsakanin iyalan, don shi wanda shi ne ginshiƙin gidan bai bada damar hakan ba.

  Kusan a tare suka shigo falon, lokacin Baffa yana waya da wani abokinsa duk ya cika falon da karaɗin wayar da yake bakinsa a washe kamar an biya masa kujerar makka, yana magana yana dariya har da ƙyaƙyatawa. Daga Mamy har yaran sai suka mayar da shi TV domin su sai su manta ma da ganin fuskarsa a sake sai dai idan ya bar gida ko yana waya ko a kasuwa wajen shagunansa ki ga yana ta raha da jama'a, haka ake yabonsa cewa mutum ne mai fara'a da sanin darajar mutane amma su dai iyalansa basu san wannan ba.

    Yana gama wayar ya haɗe rai kamar bai taɓa wani abu dariya ba, lokacin da Mubin da Zalika sun koma kan dining sun zauna.

   Cike da izza ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya mayar da hankalinsa kan TV ransa a haɗe kamar ba shi ne yake dariya da ƙyaƙyatawa a waya ba.


  Sun jima zaune kan dining ɗin amma Baffa babu alamar zai taso, Mamy ma ta je ta ja kujera ta zauna, sai kallon kallo suke a tsakaninsu. Cike da takaicinsa ta ce

"Baffan yara kai muke jira fa" Ta faɗa tana kallonsa, kamar ba zai furta komai ba sai dai ya ƙara tamke fuska ya ce

"Zan zo ai" Ganin haka sai Mamy ta shiga zuba musu abincin, farfesun kifi ne, wani fulas ɗin soyayyan naman kaza, ɗayan farfesun kayan ciki, abinci ma kala biyar dambun kuskus, soyayyar taliya, sinasir, funkaso, ɓarjen alkama, drinks ma iya ganinka sai wanda kake so, kallon kwanukan da Mamy ta bubbuɗe tana zuba musu abincin Mubin ya yi ya ga, ga komai amma kuma babu farinciki!.

  An zubawa kowa har Baffa amma har lokacin babu alamun zai taso shi ko kaɗan bai san cewa iyalinsa suna buƙatar kulawarsa fiye da kayan more rayuwa da zai wadata su da su ba.


    Kowa sai juya cokali yake a ciki, tausayin yaran ya sa Mamy ta ce

"Baffan yara abincinka fa zai huce na zuba"

  Buɗar bakinsa sai ya ce

"Ki ɗakko nawa abincin ki kawo min nan ba na sha'awar cin abinci a kan dining yau" Kamar wanda ya zuba mata ruwan dalma a kunne haka ta ji yayin shigar maganarsa, idanu ta runtse don bata son ganin fuskokin yaran. Mubin da Zalika kamar wanda suka haɗa baki sai kowanne ya tashi riƙe da plate ɗin abincin sa a hannu, ƙaran buɗe ƙofa shi ne ya ankarar da Mamy ta buɗe idanunsa sai kuwa ta ga wayam gabanta babu yaran sun bar wajen, mayar da idanu ta yi kan dining ɗin sai kuwa ta ga duka babu plate ɗin kowanne a cikin su.

  Juyowa ta yi ta mayar da kallonta kan Baffa tana so ta ga ya zai yi tun da dai ta san ya san cewa yaran sun tashi daga wajen ne saboda ba zai ci abinci da su ba.


             *SADIYA*

   Sai da ta kama Kalifa ta ɗago shi sai ta shiga duba jikinsa a matuƙar kiɗime tana son ganin inda ya ji ciwo, kamar daga sama ta ji muryar mai mashin ɗin yana faɗin

"Tsorata ya yi ne da ya ji ƙaran horn, Allah ma ya kiyaye ban lura da shi ba ya taho" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har lokacin tana jin sanyin da ƙafafunta suka yi. Gefe kawai ta matsa tana jijjiga Kalifa don bata da ƙarfin halin furta masa komai, shi kuma ya ce

"Allah ƙara kiyayewa ake kula da yara" Yana gaɓa faɗar hakan ya ja mashin ɗin, jakarta ta koma ta ɗakko daga inda ta ajiye don ita dama wayar tata ma ko caji babu domin bata ma riƙe caji sosai shi ya sa bata tarki kiran Nasir ba, bare ma ta san ba ɗauka zai yi ba in ta kira sai in ya ba dama.

   Tana nan tsaye a ƙofar gidan lokacin an fara kiran magriba wani mashin da ya karyo kwanar ta gani kamar daga sama ta hangi Nasir a bayan mashin ɗin, sai da suka zo har ƙofar gidan ya sauka daga mashin ɗin ya ba mai mashin kuɗinsa mai mashin ya ja ya bar wajen, Kalifa ne ya hau faɗin

"Abba, Abba, Abba" ,Kallo ɗaya Nasir ya musu ya ɗauke kai mukulli ya fiddo daga aljihunsa ya buɗe ƙofar gidan ya shige har da ɗan turo ƙofar, wani abu ne ya tokarewa Sadiya a maƙoshi saboda abin da ya yi wa Kalifa sai ta ji duk abin da ya mata bai mata ciwo ba kamar wanda ya yi wa ɗansa , abin na matuƙar damunta ita a nata tunanin ko da a ce da Kalifa ta zo gidansa bai kamata yake yi wa yaron haka ba, bare kuma ɗansa na cikinsa. Haka ta daure ta taka matakalar ƙofar gidan ta saka hannu ta tura ƙofar ta shigo gidan ita tsabar bata da nutsuwa ma ta manta da wani abu wai sallama haka ta shigo gidan kamar wanda dama Nasir yake jira sai ji ta yi ya ce

"Ke! Babu manya a gidan ko? Na ce manya sun ƙare a gidanku, idan ma akwai manyan to basu bada tarbiya ba gskiya tun da kike shiga gida babu sallama" Maganar ta mata ciwo sai abin ya zame mata zafi biyu wato ga mari ga tsinka jaka, saboda bai san darajarta ba ya barta wuni guda a titi amma ya zo yana ƙara mata wasu maganganun mararsa tushe.

   Daurewa kawai take amma kuka neman ƙwace mata yake, sauke Kalifa ta yi don yanzu hankalinta ya fi karkata ga yin sallolin da suke kanta hakan ya sa da ta sauke Kalifan kawai ta yi gaba don yin alwala, shi ma Kalifan kamar ya san mai yake faruwa sai ya ja ya tsaya a ƙofar falon ya raɓe yake leƙen Nasir ɗin.

  Inda ta cika butoci ta je ta ɗauki ɗaya ta yi addu'a ta shige banɗaki ta turo ƙofar, ta tsugunna tana kama ruwa kawai sai ji ta yi an banko ƙofar har sai da ƙofar ta gwaru da jikin bangoda sauri ta tashi tsaye don dama ta gama kama ruwan.

 Juyowa ta yi tana kallonsa a tsorace ganinsa a fusace tamkar wani fusataccen zaki, kafin ta furta wani abu ya ce

"Wato ga ɗan iska ko saboda kin rainani ina faɗa shi ne kika yi tafiyarki kika barni in yi ta zuba ko?" ,Cikin sanyin murya da kuma ƙarfin da yunwa ta cinye mata ta ce

"Ka san dai a waje muka wuni ban yi sallar azahar ba bare la'asar kuma yanzu ana kiran magrib... Tun kafin ta ƙarasa ya katse ta da faɗin

"To ina ruwana da sallarki, in ban da rashin tarbiya ina magana ki tafi  wannan daga gani babu tantama gida kika ɗakko halayyar rashin tarbiya, dama ai an ce tarbiya daga gida take farawa, in ba don ni ba wa zai kwasa iyayenki ma da kin ishe su da Allah annabi Babanki ya sa na aure ki, don na ɗauke masa ɗawaniniya saboda yana so ya kawar da ke, ina faɗa a ko ina ban aure ki don ki zama abokiyar rayuwata ba na san aurena da ke ƙaddara ce baƙar ƙaddara ma kuwa, a yau idan na ga dama zan yanke igiyar aurena da ke kuma in auro wacce ta fiki komai don ke baki cika mace ba!."

  Kallonsa take yadda yake magana cikin ɗaga murya, idanunta suka fara tara hawayen da take ta ƙoƙarin maƙale suka fara ambaliya a dakalin fuskarta, a take maganganun da ƙawarta Noor ta faɗa mata suka fara dawo mata, wanda take faɗa mata cewa take kataɓus wajen rama abin da Nasir ɗin yake yi wa iyayenta na cin mutunci tun da iyaye ai sun fi ƙarfin wasa tun da shi bashi da mutunci bai san shi ba. Jin kalamnsa kuwa ai ta tabbatar iyayen nata yake faɗawa magana, ai kuwa ta fara takowa daga cikin banɗakin sai da ta zo gab da shi ta tsaya ta ce

"Nasir" Da mamaki yake kallon ta jin ta kira shi a wani gadaranci ko dai ya kira hakan da muryarta cike da fitsara.

  Baki ya saki yana kallon ta ta ci gaba da faɗin

 "Duk abin da za ka yi ka tsaya iya kaina amma iyayena ba sa,anninka ba ne da za kake faɗa musu abin da duk ya zo bakin ka ba zan ɗauki haka ba"

  Haɓa ya riƙw cike da mamaki ya ce

"To mai za ki iya idan an sako iyayen naki ko kina da matakin ɗauka ne? Iyayen naki da basu damu da farin ciki da baƙin cikin ki ba ni fa a wajena baki da maraba da wacce aka min tallar ta ko aka bani sadaka"

  Ita ma a harzuƙe ta ce 

"Ko ma ya suke iyayena ne kuma ko ma ya suka ɗaukeni wannan tsakaninmu da su ne, ni dai gargaɗina na ƙarshe da kai kar ka sake cin mutuncin iyayena"
 
  Idanu ya ƙanƙance ya ce

"Gargaɗi? Sadiya ni Nasir ne kike yi wa gargaɗi kamar wanda bakin uwa ya kamani har wata mace za take faɗa min magana"

Bata bi ta kan tambayarsa ba ta ce

"Ni da sakakkiya a gidan nan banbamcin mu kaɗan ne, ko kaɗan baka darajani, tsakani da Allah kana gani na amma ka tafi bayan ka san gidan a kulle na wuni a titi ni da ɗanka ko kishin iyalinka baka yi, duk namijin da ya san darajar kansa da ta iyalinsa ba zai wofintar da su su wuni a titi b...

  Wani gigitaccen mari ya ɗauke fuskarta da shi, da yake marin ya je mata ne a bazata sai ta ji tamkar ba da hannu aka mare ta ba, marin da Kalifa ya gani ne ya sa ya ruɗe ya fashe da wani kuka ya yi kanta ya je bayanta ya ƙanɗame ta har lokacin yana kuka, bata kula Kalifa ba duk da kukan nasa yana taɓa mata zuciya. Tana dafe da kumatun da ya mara ta kalle shi idanunta taf da hawaye ta ce

"Ni ka mara Nasir?" 

  Kamar zai kai mata wani marin ya ce

"An mare ki fitsararriya ko za ki rama ne? Har ni za ki ce ban san  darajar kaina ba, kuma wallahi sai na faɗawa wannan uban naki ya gargaɗe ki don zai iya zuwa ya ga gawarki matuƙar baki yi wa bakin ki linzami daga furta min kowace kalma ta zo bakinki ba" Yana gama faɗar hakan ya juya ya nufi falo, Kalifa ta ɗauka har lokacin yana kuka da alama tsorata ya yi da marin da aka mata tana ɗaukansa ya maƙalƙale wuyanta bata san lokacin da ta fashe da kuka mai sauti ba. Ta jima tana kuka mai cin rai kafin ta yi shiru ta goge hawayen, jin Kalifa ya yi shiru ya kwantar da kansa a kafaɗarta, sai ta duba sai ta ga ya yi bacci haka ta kawo shi falon ta kwantar da shi a kan kujera ta koma ta yi alwala ta zo ta kabbara sallah.

  Lokacin Nasir yana bedroom, sai da ta yi azzahar da la'asar tana yi tana hawaye duk sujadar da ta kai sai ta faɗawa ubangiji damuwarta a kan ya magance mata, tana shirin miƙewa ta yi mageriba sai ga Nasir daga bedroom ɗin kamar an jefo shi, gabanta ya zo ya tsaya yana riƙe da wayarsa da take ringing da alama wani yake kira don wayar a handsfree take ma.

   Kamar daga sama sai jin muryar Baba ta yi yana cewa

" Assalamu alaikum malam Nasiru mutumin kirki" Wani murmushin gefen baki Nasir ya yi kafin ya haɗe rai kamar Baban yana ganinsa ya ce

"Ni wallahi Baba ba na cikin yanayin da zan amsa sallama gabaɗaya raina a ɓace yake" 

  Buɗar bakin Baba sai ya ce

"Sadiya ce ko? Wannan yarinya mai ya sa bata jin magana wai, haka fa ta kwaso jiki wai wuni ta zo gidan nan na korata ɗakinta da tsakar rana shi ne kuma da ta dawo ta ɓata maka rai" Sosai Sadiya ta ji duk ta muzanta dole Nasir yake mata abin da ya ga dama saboda mahaifinta shi yake bashi kowace dama, shi yake zubar da kima da darajarsa, shi ya sa ba ya siya mata mutunci bata san wane irin uba ne ta samu ba.

  Nasir ba yabo ba fallasa ya ce

"Ai Sadiya bata san darajar miji ba ko kaɗan, ban da zagi da baƙaƙen maganganu babu abin da take a gidan auren ta, yanzun nan ta gama cewa ban san darajar kaina ba da ta iyayena" Ya faɗa cike da ɓacin rai, Sadiya jin har da ƙarya ya shirga bata yi mamaki ba da ya yi haƙuri ma in dai Baba ne a kan a samu matsalar da za ta koma masa gida ba sai da ƙarya zai mata faɗa ba.

Baba ya ce

"Bata wayar" Wani kallo Nasir ya mata yana wani ƙanƙance ido irin na fitsararru ya miƙa mata wayar tana ƙoƙarin danna wayar Nasir ya katse ta da faɗin


"Kar ki kuskura ki cire min waya a handsfree ki bari in ji, idan ma shi yake ɗaure miki tsantsa ki rainani" Yana gama faɗar haka ya koma kan kujera ya zauna tare da harɗe ƙafafu.

  Baba ya ce

"Sadiya wallahi ki fita idona in rufe, mijin da ya rufa miki asirin kike zagi, shin wuta balbal kike son shiga Sadiya?" Kallonta ta mayar kan Nasir da ya kaɗa kai alamar ta dai ji rufa mata asiri ya yi.

  Kafin ta samu zarafin furta komai Baba ya ci gaba da cewa

"Wallahi idan ba so kike in zo har gidan in saɓar miki ba ki masa biyayya ko wuta ya ce ki faɗa ba dole ki shiga ba Sadiya tun da mijinki ne aljannarki tana ƙasan ƙafafunsa, kin samu Allah ya tarfawa garinki nono kin yi aure amma kike tada fitina da dai ban san ki da haka ba ko ƙawaye kika samu suke hure miki kunne?" Jin Baban ya dakata ta gane kamar ya bata damar magana hakan ya sa ta ce
"Baba tun da na dawo yana ganina fa ya tafi da mukullin a titi muka wuni sai yanzu ya dawo kuma bani da damar da zan nuna ban ji daɗin abin da ya yi min ba sai ya kai min hannu? Marina fa ya yi Baba yana ta faɗa wa iyayena maganganu... Cike da faɗa Baba ya katse ta ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba yana ta ɗora mata rashin gaskiya a ƙarshe ya ce idan ya ƙara jin wata magana ta ɓullo sai ya saɓar mata.

  Duk abin da ake Nasir yana ji, kawai murmushi yake saki jin Baba ya ce ta ba Nasir haƙuri a kan kunnensa ya ji haka ta buɗe baki ta bashi haƙurin cikin dashashshiyar muryarta, sannan Baban ya ce ta ba Nasir wayar tana jin yadda ya ringa ba Nasir haƙuri tamkar zai ari baki yana ta yi wa Nasir ɗin godiya kamar wanda ya masa kyautar kujerar makka.

  Juyawa kawai ta yj ta koma kan sallayar ta fara sallar magriba, tana saddaƙarwa da cewa wannan gidan auren kamar kurkuku yake a wajenta, sai dai ta san ba za ta dawwama a haka ba akwai ranar ƙin dillacin ta san ko ba jima ko ba daɗe sai Allah ya mata sakayya a kan zalincin da Nasir yake mata, ko da bayan ranta ne kuwa.



     Bayan ta yi har isha'i ya zo ya buɗe store ya ɗakko mata taliya rabin leda ya miƙa mata, karɓa ta yi ta nufi kicin ɗin ta shiga kunna gawayi don mahaifiyar Nasir ta yi uwa da makarɓiya ta hana ta kunna gas ɗin da Nasir ya saya tana amarya ɗan ƙarami, ta ce ita Sadiya bata dace da amfani da Gas ba saboda a gidansu da icce ake amfani. Dakyar ta samu gawayin ya kama ta ɗora tuwan zafi ta dawo falon, sai ta ji kamar ta rufe ido ta buɗe ta ganta a wata duniya daban. Tun da ya bata taliyar ya fice, ta gama dafawa ta soya manja ta zubo abincin ta ajiye ta ɗauki Kalifa ta ke ta wanke masa ido da baki tuni ya ware don dama yunwa yake ji, haka yake cin abincin kaɓr me saboda yunwa, ita kuwa kaɗan ta samu ta ci shi ma duk babu daɗi.

   Haka ta yi shimfiɗa ta kwantar da Kalifa ta shiga ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta saka rigar bacci marar nauyi ta yi addu'a ta kwanta har lokacin Nasir bai dawo ba, ganin an kawo nepa ta tashi ta saka cajin wayarta ta koma ta kwanta tana rungume da filo tana ta tunanin lamarin gidan aurenta, rana zafi inuwa kuma ƙuna, hawaye yana ta bin kumatun ta mafita take nema ita dai da za a ji damuwarta a magance mata da da daɗi amma babu mai saurarenka iyayenka kawai burinsu ka zauna a ɗakin miji daɗi da wuya ko da kuwa a wulaƙance ne.  Tana ta wannan saƙa da warwarar bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.

  Nasir sai wajen ƙarfe goma saura ya shigo gidan, yana can majalisa da abokai ana ta hira, yana shigowa ya rufe ƙofar gidan ya shigo gidan yana wani bada faɗi, sai kuma ya ga baiwar tashi bata ma falon tsire da coca colan da ya shigo da su ya zauna ya baje a falon ya cinye a shanye lemon ya tashi ya bar mata takarda da robar a wajen. Bayan ya gama abin da zai yi ya saka hannu a aljihu ya fito da wani ƙullin ruwan magani a farar leda ya tula ya shanye ya fito ya jefar da leda, kayansa ya cire daga shi sai singlet da ƙaramin wando ya haura kan gadon bayan ya kashe gabaɗaya fitilun. Kasancewar Kalifa a ƙasa take masa shimfiɗa a kan ƙaramar katifa da yake gidan ciki da falo ne, sai kicin da banɗaki kawai sai kuma ɗaya part ɗin inda ciki da falo sai ɗaki ɗaya wanda an fara ginin an kai linta amma ba a ƙarasa ba. Yana hawa gadon ya kwanta ya miƙa hannu ya shiga tashin Sadiya, cikin bacci ta ji yana buga mata ƙafa ta ɗago jajayen kumburarrun idanunta ta kalle shi ta cikin ɗan hasken farin wata da ya ratso ɗakin.

  Cike da gadara babu tausasa murya ya ce

"Haƙƙina na zo karɓa" Ranta ne ya sosu wai mutumin da ya gama ci mata mutumci har marinta ya yi amma yanzu kuma ya zo da wata buƙata, a kasalance irin na wanda yake cike da bacci da gajiya ta ce

"Dan Allah Abban Kalifa ka mini lamuni yau wallahi ba na jin daɗin jikina" Kamar wanda ta watsa masa wuta haka ya zaburo mata ya ce

"In baki taliya ki cika ƙundunki ki shi ne tawa buƙatar ba za ki biya min ba? To in dai wancan taliyar da na ga kin ajiye mini a ƙaramin filas ce kike yi wa ki je ki ɗauka ni nama da lemo na sha, idan kin cinye sai ki zo ina jiranki da alama ƙoshi ne baki yi ba shi ya sa kike mita" Cike da ƙosawa da kalamansa ta ce 


"Ni ba yunwa nake ji ba kawai dai zuciyata ce babu daɗi"

 Zaune ya miƙe ya saka hannu ya daki kan katifar kan gadon ya ce

"Ko zuciyarki da daɗi ko babu wannan ke kike sakawa kanki kuma ke kika ga za ki iya, ni dai yanzu haƙƙina dole ki bani tun da sadaki na bayar" Tun da ya yi wannan furucin bata ƙara furta komai ba ya cire kayan jikinta, babu wani ɓata lokaci ya shiga biyan buƙatarsa ya daɗe yana abu ɗaya sai da ya gaji don kansa ya ƙyaleta, ita kuma tana kwance kamar gunki don dama babu wani abu da take fuskanta a lamarin don damuwa ta gama yi wa zuciyarta katutu, shi kuma lamarin mu'amalar aure ana son gabatar da shi a lokacin da ake cikin walwala farinciki haɗe da annashuwa.




*IBRAHIM*

   Kafin ya ƙarasa gidan su Jidda ya haɗa uban gumi sharkaf abin ka da wanda ya saba rayuwa cikin AC gida AC mota AC office ma AC. 

       Ko da ya zo bai ƙarasa saitin gidan ba daga ɗan can gefe ya tsaya yana hangar ƙofar gidan, sai lazimi yake a zuciyarsa, yana addu'ar Allah ya sa ya dace.

  A can cikin gida kuwa Aliya ce take gwada wata doguwar rigar abaya maroon da takalmi haɗe da wata jaka sai murna take tana cewa

  "Gaskiya Kasim ya iya zaɓe" 

  Umma ta yi karaf ta ce

"Wannan ai za a je da shi, kin ga duk da ba mai arziƙi ba ne ai yana da wadatar zuciya, daga ganinsa irin mazan nan ne masu bautawa mace, kika dai yadda yake miki wahala komai ya samu ke yake yi wa"

  Aliya ta ce

"Umma ai wanna  da kike gani bawan mace ne"

Umma ta ce

"Ai tun da dai yana da karatun digirinsa digirgir kuma yana da ƙashin arziƙi daga gani, gashi yana sonki yana bauta miki tabbas in kika aure shi kakarmu ta yanke saƙa, wuyarta ya samu aikin gwamnati da takardun nan basa ai shi kenan kin zama babbar mace" Wani uban tsalle Aliya ta daka tana murna tana sanar da Umma Kasim ɗin ma ɗazu ya ce zai saya mata sabuwar waya. Da gayya suke ta maganganun nan da yada magana duk abin da suke Jidda tana jin su, ita damuwarta ma da jiya da daddare Abba ya tara su ya ce kowacce ta fitar da miji shi bai san cewa Jidda bata da wani tsayyaye ba, ita kuma tana jin nauyin sanar da Abban.

   Ta yi nisa a tunani Umma ta ƙwalla mata kira, tana fitowa ta saka ta wankin kaya, haka ta karɓa don dama yau Ummar ce ta hana ta zuwa islamiya saboda aikin gidan. Aliya ce ta gama saka kayan gabaɗaya a leda ta cewa Umma za ta je gidan su Amatullahi ta kai ta nuna mata Umma ta ce

"Yawwa maza kula ki je ki nuna mata kin kece raini kuma kina da mijin da xa ki aura na nunawa sa'a" Ta faɗa tana kallon saitin Jidda da ta duƙufa wajen wankin zanin Ummar. Ko da Aliya ta ɗauki ledar ta fito ƙofar gidan, Ibrahim daga can inda ya tsaya ya hango ta, kasancewar bai shaida ta ba sai ya taho domin yana son ya tambaye ta ko Jidda tana ciki, bai gane ta ba sai da ya zo dab da ita, ita kuma Aliya a lokacin da ya ƙaraso tana ƙoƙarin kara waya a kunne don Amatullahi take kira za ta ce mata gata nan za ta nuna mata kaya. Ganinsa ya sa ta fasa kiran wayar ta kashe tana ƙare masa kallo, tabbas ko daga bacci ta tashi ba za ta kasa shaida wannan fuskar tasa ba.

  Fuska ta yatsina tana masa kallon ƙwaf, shi kuma gabaɗaya kansa ya kulle da ya ganta don tabbas ya shaida ta ita wacce ta ciwa direbansa mutunci ranar nan. Gabaɗaya ma sai bakinsa ya ƙi bashi haɗin kai wajen yin sallamar da ya yi niyyar mata, bare a kai ga tambayar da zai mata a kan Jiddar tana cikin gidan.

  Aliya kuma sai ta shiga masa wani kallon raini tana yatsina, gabaɗaya sai ya tsargu da kallon nata amma sai bai ce mata komai ba, cike da mamaki da gatsali ta ce

"Oho sai yanzu na je ghana, kai duniya mutane sai a barsu, wato dai Allah ya tona maka asiri ashe dai ganin kana da kyau shi ya sa kake aron mota da kaya masu kyau kana yaudarar ƴaƴan mutane ko? Har da aron direba da yake janka a mota, wato ka zaci ba zan gane ka ba, to ta Allah ba taka ba wannan ai kai ne a wanki gara!" Ta faɗa tana wani zagaya shi, gabaɗaya sai Ibrahim ya kasa magana  ita kuma ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har da faɗin ɗan talaka dama bai iya samun wuri ba wato har da cewa wa yake nemanta lokacin da ta je wajensa a motar ashe dai duk kanwar ja ce shi ma dai talaka ne bai ajiye ba bai bayar ajiya ba.

   Shi dai yana kallon ta tsabar mamaki ma ya rasa mai zai ce.

   Ganin haka sai ta ce

"Shi ne ka lallaɓo koɗaɗɗun ƙafafunka da wasu tsoffin kayanka sa suka gaji da wanki, to wallahi ni na fi ƙarfinka ne, kar ma ka ɓata lokacinka wajen mini magiya ko roƙona don ina cikin mutanen da suke cewa da wuya ta kar su ai gwara daɗi ya kar su" 

   A can cikin gida kuwa Umma ce ta ce Jidda ta ɗauki bokiti ta fita famfon waje ta ɗakko ruwa ta ƙarasa wankin, da yake ruwan ya ƙare, duk da akwai mai ruwan da yake kawo musu ruwa amma saboda ta ga Abba ba ya nan ta aike ta ɗakko ruwan, haka ta ɗauki bokitin ta fito ba don ta so ba.


    Aliya tana cikin masa wannan maganar har wani nuna shi da yatsa take a daidai nan ne Jidda ta fito, sai da gabansa ya buga da ya ganta sanye take da wani blue ɗin hijabi har ƙasa hijabin yana da hannu sai bokiti a hannunta fuskarta babu walwala. Tun da ta fito kallo ɗaya ta musu ta wuce da yake wajen famfon kusa da gidan da yae kusa da gidansu ne ta tara ruwan ta ciko ta ɗakko.

  Ta zo za ta shige gida ganin abin da Aliya take yi wa Ibrahim sai ta ce

"Haba Aliya, a titi kike wannan ɗaga muryar?" 

   Cike da ɗaga murya ta ce

"An yi ɗin uwar pan shishshigi" Juyawa ta yi ta shige gidan, shi kuma kallon ta kawai yake yana son ganin gudun ruwanta, sai da ta gama masa ɗiban albarka ta ce

"To a yi gaba ko a samu wata dai amma wannan Aliyar sai Kasim!." Tana faɗa ta juya ta tafi tana wani juya mazaunan da su da babu duk ɗaya.

  Gefe ya koma yana ƙarewa jikinsa kallo yana mamakin cewa kenan dai shi talaka a wajen wani shi ba komai ba ne, sannan wasu suna ganin duk rashin mutuncinka in har kana da kuɗi to kai mai kirki ne in kuma baka da shi da kai da babu duk ɗaya, dama ya fahimci cewa Aliyar nan ƴar son banza ce don ranar ma a idanunta ya ga son banza ƙiri ƙiri.


  Ko da ta je gidansu Amatullahi nan ta shiga bata labarin Ibrahim suka ringa zaginsa suna ce masa matsiyaci, Aliya ta ce

"Oh har zan ce in yi saki na dafe da Kasim ɗina ashe dai ba arziƙi ba ne yake kirana tsiya ce"

  Amatullahi ta ce

"Humm! Ba ke kike cewa wani kyakkyawa ba ne"

   Aliya ta ce


"Ke dai bari a yau na gane cewa duk arahar kunu ta banza ce in babu gaya a ciki" Suka ci gaba da ɗaga kayan Kasim suna zuba masa albarka.

   Fitowar Jidda za ta ƙaro ruwa sai ta gan shi jingine da bango, amma sai ta masa kwarjini ya kasa mata magana har sai da ta ciko bokoti tana ƙoƙarin ɗakkowa ya ƙarasa wajen ya ce

"Kawo in taimaka miki" Kawai da ta juyo sai ta kasa hana shi kwarjini ya mata ta ga yana da kima da kuma kamala. Ɗakko mata ruwan ya yi har ya kawo ƙofar gidan, kasancewar ya saba ruwa a banɗaki sai dai ya tara ya yi wanka tunaninsa zai ji nauyin bokiti amma da yake soyayya yake yi wa bauta sai ya ji ko alamar nauyi babu kamar dai ya ɗauki bokiti mai auduga ne. Yana zuwa ya ajiye ya ɗago yana kallon ta cike da jin daɗin abin da ya mata ta ce

"Sannu da ƙoƙari na gode ƙwarai" 

  Wani daɗi ne ya cika shi kamar ya taka rawa jin muryarta tana masa godiya da jinjina masa.


  Har za ta ɗauki bokitin ta juyo ta ce


"Don Allah ka yi haƙuri abin da Aliya ta farfaɗa maka" Yana jinjina dattakon ta ya ce

"Ni dama ...am dama ke zan ce ta yi min magana da ke shi ne ... Ya faɗa yana inda -inda 

 
 Cike da mamaki ta kalle shi tsantsar mamaki yana bayyana a kan fuskarta ta ce


"Ni kuma?" Ta faɗa zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, ta san dai jiya ta yi ta addu'ar ita ma Allah ya fito mata da mai son ta wanda zai aure ta ya riƙe ta da daraja idanu ta ɗan runtse ta buɗe ta ce

"Lafiya dai ko?"


  Yana kallon yanayin ta ya ce


"Na zo don in bayyana miki soyayyata wallahi ina ƙaunarki da gaskiya tun daga ranar da na fara tozali da ke" Ya faɗa zuciyarsa tana zillo kawai gani yake ba za ta amince da shi ba saboda kyaun da yake da shi tun da da kunnensa ya ji ta ce bata son mai kuɗi kyakkyawa.

    Jidda kuwa jikin ta ne ya fara rawa kasantuwar abin ya zo mata a bazata, kuma dai mutumin ya birge ta musamman da ta ga cin mutuncin da Aliya ta masa bai biye mata ba duk da bata san abin da ya haɗa su ba sannan da taimakon ta da ya yi ya ɗaukar mata ruwa.

   Rasa amsar da za ta bashi ya sa ta ce


"Sai na yi tunani tukunna"
 
  Wannan furucin nata ya saka shi a wasi-wasi amma ya danne ya ce


"Babu damuwa Allah sa ki yanke abin da ya fi zama alkairi " Yanayin yadda ya yi maganar ya sa ta ji wani iri kamar dai bata kyauta masa ba kamar dai bai ji daɗin furucin ba.

 
 Bata ce masa komai ba ta sunkuya ta ɗauki bokiti har ta fara tafiya ya ce


"Jidda" Har tsakiyar kanta ta ji kiran sai ta ji tamkar shi kaɗai ne ya iya kiran sunanta daidai, sai dai bata san dalilin hakan ba, juyawa ta yi bayan ta ajiye bokitin ta ce

"Na'am" Ta faɗa idanunsu suna sarƙewa da juna da sauri ta yi saurin kawar da nata, kasancewar sai ta ji kallon da idanunsa suka jefe ta da shi ya sha bamban da kallon kowane mutum.

 
 Iska ya ɗan hurar daga bakinsa ya ce

"Ki daure ki bani phone no ki" Kamar ba za ta ce komai ba har ya cire rai za ta bashi sai ya ji ta fara karanto masa, nan ya shiga rubutawa a ƙaramar wayar da ya taho da ita. Tana gama faɗa masa va tare da ta jira cewarsa ba ta juya ta ɗauki ruwan ta shige gidan.

 
  Tsabar murna bai san ya isa bakin titi ba don ko wahalar tafiyar ba ya ji, wani irin farinciki da yanayi marar misaltuwa da yake ziyartarsa, haka ya yi kwanan farinciki amma dai ya kasa kiran wayarta don sai ya rasa mai zai ce idan ya kira.


    Bayan kwana biyu, har lokacin bai koma gidansu ba kuma bai kira ta ba, sai dai yana ta dakon soyayyarta. A ɓangaren Jidda tun daga wannan ranar ta ji ta damu da Ibrahim sai dai rashin kiranta a waya sai ta ji duk babu daɗi, tun tana jiran kiransa har ta cire rai, da ko baƙuwar no ta gani sai ta yi tunanin shi ne har dai ta cire rai daga kiran nasa. Sai da aka yi sati sannan watarana da yammaci yana zaune a ƙasan wata bishiya a wata unguwa yammaci ne mai cike da ni'ima sassanyar iska tana kaɗawa, yana zaune saman motarsa ya kamo sunan ya shiga kiranta, Jidda tana hura wutar da take tuwon dare ta fara jiyo ƙaran wayarta, amma bata je ta ɗakko wayar daga ɗaki ba. Har kiran ya tsinke bata je ba, Ibrahim kuma sai ya fara wata zufa hankalinsa ya tashi ya fara tunanin ko dai ta yanke shawara marar kyau a kansa, kuma da ya yi tunanin ai bata san numbersa ba sai ya ji hankalinsa ya ɗan kwanata a ƙara gwada kiran.

 
  Tunanin ta ma ko Salama ce ita ce idan ta fara kira bata san ta daina ba, hakan ya sa ta iza wutar ta nufi ɗakin, tana ɗaukan wayar ta ga baƙuwar no dama gidan babu kowa sai ita kaɗai duk sun fita gidan biki. Bata san mai ya sa ba amma sai da gabanta ya faɗi tana dannawa ta ƙara wayar a kunne.

    Sassanyar muryarsa mai amo mai daɗi da ita ya fara mata sallama, idanu ta lumshe kaɗan ta buɗe su bata san dalili ba amma sai ta ji ta yi farin ciki da kiran, bata san ko don ta daɗe tana jiran ya kira ta ba ko kuwa mene ne oho.

 
 Amsa sallamar ta yi sai ya ce

"Sunana Ibrahim ni ne kika ba numberki ranar da kika ɗauki ruwa" Wani murmushi ya kuɓuce mata marar sauti a zuciyarta tana raya da a ce ya san cewa bata da wani saurayi da bai wahalar da kansa wajen tuna mata ranar da suka haɗu ba.

 
  Cike da murnar da bata bari ta bayyana ta a fili ba ta ce

"Na gane ka"


  Ya ce


"Ya batun tunanin kin yanke hukuncin"

  Ta ce

"Hukuncin me?"

 Ya ce

"Hukuncin na cancanta ki kula ni ko ban kai ki kula ni ba" Maganarsa ta bata dariya hakan ya sa ta dara har yana iya jiyo sautin dariyar ta cikin wayar.

 
    Jingina ta yi da bango ta don dama a tsaye take ta ce

"Ban amince ba" Gabansa ne ya buga da ƙarfi a take ya ji gabaɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi, ɗan walwalar da ya tsinci kanaa sanadin magana da ita duk sun gaushe.

 
   Bata tantance ba ta ji saurin maganarsa cikin tashin hankali yana cewa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" 
 
  Bata san dalili ba sai ta ji zuciyarta babu daɗi ta ji duk ta damu da yanayin sa ya shiga bata san lokacin da ta ce


"Da wasa fa nake maka na amince" Daga ita har shi dariya ce ta ƙwace musu.

   Sun daɗe suna hira kamar sun saba daga bisani ta ce masa aiki take saboda ta ga abin nasa ba na ƙare ba ne, wayar ta ajiye ta fita ta ƙarasa tuƙa tuwon, sai bayan ta kallama aikin ta yi wanka ta zo ta ɗauki wayar ta yi saving no da IB tana ta maimaita hirarsu a zuciyarta.

    Washe gari tun da asubar fari Aliya ta ishe ta da cewa saura sati guda a kawo mata kayan saka rana, amma Jidda ta yi kamar vata ji ba daga ƙarshe ta ce Allah sanya alkairi amma sai Aliya ta ce baƙin ciki take. Ita kuwa ko da Abba ya sake tambayarta sai ta ce za ta turo wanda zai gaishe shi ya ce za a aiko suna shiri ne daga haka Abban bai sake tambayarta ba.


    Bini-bini waya da Ibrahim da Jidda har dai ta kai ta kawo yana zuwa hirar tsakanin magriba da isha, a hakan Aliya ta sha yanka masa magana wai laila ta ƙiya an koma caca. Ranar da ya zo ma kayan gwanjon ya sako abinsa, bayan Jidda ta koma gida Aliya take cewa wai wannan mai zuwa wajen nata matsiyaci ne.

       *BAYAN SATI GUDA*



    Ana ƙoƙarin kawo kayan saka ranar Aliya sai gobe, sai Ibrahim ya sanar da Jidda cewa zai aiko in ta amince duk da basu daɗe da haɗuwa ba, ita kuma ta yarda da shi ta yaba da halayyarsa don haka ta amince cewa ya aika a samu Abban nasu, lokacin da ya sanar da su Mummy cewa ya samu wacce yake so sun yi matuƙar mamaki sun yi murna ƙwarai . Daga haka ne ma ya samu damar saka kayan gwanjonnsa babu ɓoye-ɓoye ya ce saboda yana son ya auri mai sonsa da gaskiya ne ba wai don dukiya ba, basu san cewa yana amfani da kayan va ne saboda ita wacce yake so ɗin kuɗin basa gabanta.

    Ya fahimci Jidda tana son ss duk sa ya san nasa son ya linka nata. Bai san dalilin da ya kore mata ƙuduri da burin auren kyakkyawa ba.

   Tun da yake zuwa ko biyar bai taɓa bata ba, ko da Ibrahim ya sanar da ita za a je gaisuwar iyaye ta faɗawa Umma a kan ta sanar da Abba saboda tana jin kunya Umma ta ce


"Shi ma dai wannan zai kwasawa kansa jangwam, ko don talaka ne ai dama talaka ya saba da wahala" Jidda bata ji daɗin maganar ba amma babu yadda za ta yi.


    MAMAN AFRAH
     ***