RUWA CIKIN COKALI

Chapter 18

by @mamanafrah3028

***



*RUWA CIKIN COKALI* 
(Ya ishi mai hankali wanka)
 
                  
                NA


         MAMAN AFRAH

 
.        *Daga marubuciyar* 
  *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* 
      *****

           BOOK 1

         PAGE 1️⃣5️⃣



SADIYA
  Tun da Baba ya fita ta fara zuwa tana gaishe da matan gidan cike da girmamawa, duk cikin ƴaƴan gidan babu mai haƙuri da ladabi da biyayyar Sadiya tamkar dai ba a gidan take ba, don Sadiya daban ce a cikin ƴaƴan gidan ta kowane fanni. Lokacin sa ta je ta gaishe da Mama Habiba har za ta tafi Mama wacce ta ɗauki Kalifa ta ɗora cinya tana cewa
"Tun da dai baka son in ɗauke ka to zan maka saki uku"Ta faɗa tana dariya shi ma dariyar yake duk da bai san manufar maganar tata ba amma dai ya gane wasa take masa. Mama Habiba ta kalli Sadiya da take zaune kusa da ita ta ce
"Sadiya ki ci gaba da haƙuri a gidan aurenki, ki sani aljanna kike nema duk wani abu da namiji zai ƙunsa miki na baƙin ciki da ɓacin rai to ki sani wannan ɗacin da za ki ji a zuciyarki idan kika danne Allah zai baki ladan haƙuri sannan shi aure dama ɗan haƙuri ne, ita aljanna ba a samunta ta sauƙi, kuma duk ko da a ce mutum ya tauye maka haƙƙi ko yana maka abubuwa da gangan idan ka yi haƙuri wataran za ka ci riba. Na sanki da haƙuri to ki ci gaba wataran in har muna raye za ki ce na faɗa miki domin sai kin ga sakamakon haƙuri da juriyar da kika yi" Sadiya ta ɗago kai ta kalli Mama Habiba idanun Sadiya suka cika da ƙwalla tana jin Mama Habiba tamkar dai mahaifiyarta Mama Habiba tana mata abin da Mamarta bata mata, tana nusar da ita abubuwa masu yawa. Cike da rawar murya ta ce
"In sha Allahu Mama, na gode sosai ina alfahri da ke" Hannu Mama ta kai ta dafa kafaɗar Sadiya ra ce
"Babu komai Sadiya haƙuri ba ya taɓa yin tawa ko kuma a ce ya ƙare ita dama rayuwar cike take da ƙalubale, kowa da jarawabarsa haka kowa da ƙaddararsa wata ƙaddararta rashin samun mijin auren, wata kuma ta samu amma  kuma babu kwanciyar hankali, wata kuma kishiya ce matsalarta ta hana ta sakat ta hana ta zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta kange komai ta hana ƴaƴanta su wayata" Sadiya kai kawai take gyaɗawa kamar ƙadangaruwa don ta san duk abin da Mama take faɗa haka yake!.
  Suna cikin hakan ta ce ta je ta yi alwala, alwalar ta yi ta dawo ɗakin ita ma Mama ta yi suka tada sallah shi kuma Kalifa yana zaune yana cin biskit ɗin da Mama Habiba ta ɗakko ta ɓarw ta bashi. Bayan sun idar Mamar ta ci gaba da mata nasiha a kan kishiyar da za a mata tana ta nuna mata yadda za ta yi ta zauna lafiya duk da ta san Sadiya bata da hayaniya kuma tana da kawar da kai amma dai dole ta ƙara koyawa kanta juriya kasancewar yanzu abubuwa za au sauya idan da mijinta ne matsalarta yanzu kuma wata za ta shigo gidan kuma ba a san da mai za ta shigo ba, galibi ko yawanci mata ba wai suna tsoron kishiya ba ne sai dai suna tsorob da mai za ta shigo? Shin zaman lafiya ne zai kawo ta ko kuma kawai zuwa za ta yi ta hargitsa gidan, wata sai ta fitar da matar gidan kuma ta zo ta bar gidan, shi ya sa kishiya kala-kala ce wata ta zaman lafiya wata akasin haka.
  Sadiya ji take tamkar a cikin ƙwaƙwalwarta Mama take kissima maganganun, don sosai suke shigarta, duk da kasancewarta wacce ta taso a gidan kishiyoyi har huɗu amma dai shi zaman aure makaranta ce mai zaman kanta da babu wacce za ta fane sai wacce ta yi auren, kazalika kishiya ma abu ce mai zaman kanta da babu wacce za ta fahimci zama da ita sai wacce aka yi wa duk da ba a taru zan zama ɗaya ba, tun da ita Sadiyar shaida ce tun da gashi yanzu kishiyar mahaifiyartw ce take nusantar da ita. Ba wai don tata mahaifiyar bata gidan ba, tun da da ta gaishe da Mamar ta je wajen Mama Habibar.

   A ɓangaren Baba tun da ya yi turus ganin babu motar Nasir sai abubuwa da dama suka shiga masa gizo a ƙwaƙwalwa ya shiga saƙa da warwara sai dai idan zuciyarsa ta kissima masa abu marar kyau dangane da kawo Sadiya gida da Nasir ya yi sai ya yi saurin kawar da hakan, yana ƙara faɗawa kansa cewa ba da wata manufa Nasir ɗin ya kawo ta ba, tun da idan ya tuna fuskar Sadiya ai ya ga babu wata damuwa ko alamar ɓacin rai sannan ya ga Sadiyar ta murmure ta yi kyau abin ta babu wata rama ko yanayin da ya saba ganinta a can baya, ya ƙara haɗa hakan da cewa Nasir ne yake vata kulawa bai san cewa ita ce ta samarwa kanta mafita ba da taimakon Kaka, duk da ya san da maganar amma dai bai san sana,a ce mafarin komai ba, sana,a ce ta kaita ga wannan ɓigirin na walwala da mirmurewa don ta wuce jira a bata da kanta take yi wa kanta abubuwa babu ruwanta da jiran a bata bare a wulaƙantata, tun da wasu mazan masu son abin hannunsu wanda basa ɓanɓaruwa basa son sauke nauyin iyali wansa ya rataya a wuyansu suna yin hakan ne don sun gaji da bani- bami na mace koyaushe a ce ana buƙatar wani abu daga gare su amma in kina sana,a za ki ga sauyi domin ke kanki sai kin san akwai bambanci da ka ɗauki abinka da kuma bambanci da a baka.

    Ba a taru an zama ɗaya ba amma dai Allah shi kaɗai ne ba ya gajiya da a roƙe shi.
     Baba ya jima yana ɗan kaiwa da komowa gani yake kamar sai Nasir ɗin wani waje ya je ya dawo, har sai da ya kama hanya zai koma cikin gidan sai dai jin liman ya yi kabbarar harama sai ya nufi masallacin yana bazama riga kamar zai tashi sama, botocin da ya gani da ruwa ya ɗauki ɗaya ya yi alwala da sauri, saboda dama bai ƙarasa alwalar da yake yi a gidan ba, da ya ji Nasir ya zo ya fita.  cikin masallacin ya shiga sa,arsa ɗaya liman ya ja doguwar sura shi ya sa ba a wuce shi ba. Tun da ya yi kabbarar shi dai gashi nan ne yana sallah amma dai sheɗan ya yi wa tunaninsa linzami don kawai bai ankara ba sai ya ji ya tafi tunani, kuma tunanin ba a kan komai ba sai a kan kawo Sadiya gida da Nasir ya yi. Tun da aka kai sujadar ƙarshen Baba ya daddage yana addu,a yana cewa
    "Allah ka sa Nasir ba da wata manufa ya kawo yarinyar nan gida ba, Allah ka taimake ni kar ya ƙara min wahala a kan wacce nake sha ta riƙon ƴaƴan nan Allah ka dube ni ka bani ɗa namiji wanda zai tallafa mini ya ɗauki ɗawainiyata" Har aka kusa yin sallama bai ɗago ba sai can ya ɗago ya fara tahiya. Ko da aka idar babu wani azkar da ya yi shi ne na farkon tashi tsaye a masallacin, tamkar dama jira yake a idar shi ya fara fitowa daga masallacin idanunsa a ƙofar gidansa amma babu alamar motar Nasir don a tunaninsa ko zai dawo. Tsabar ya saka abin a ransa takalmin ma a juye ya saka yana jin wani maƙocinsa yana masa magana wanda ya fito daga masallacin amma bai waiwaya ba bare ya amsa don shi gani yake yana cikin gagarumin tashin hankali na rashin sanin matsaya kuma takamaiman maganar zuwan Sadiya.
    
    
      Yana shiga gidan ya fara ƙwalawa Sadiya kira tamkar zai fasa gidan, bai ma damu da sauran wasu ƴan matan da basa gidan ba, don shi dama tarbuyar ba damunsa ta yi ba shi dai damuwarsa ya aurar da su ya huta kuma bai damu da nagartar miji ba sannan ko da mai zuwa wajen ƴaƴan ne bai damu ya ga wani nutsatstse ko wanda ya san mai yake ba babu ruwansa da nakasun mutum.
      Sadiya wacce Mama Habiba ta kawowa tuwon ta da aka kasa aka bata ta tsoma hannunta kenan ta ɗauki loma za ta kai baki Baba ya ƙwala mata kiran da ya sa ta ji wata irin faɗuwar gaba, da sauri ta mayar da tuwon hannun nata ta miƙe tsaye tana amsawa amma bai daina kiran ba ita gabaɗaya ma ya tada mata hankali ba ita kaɗai ba hatta Mama Habiba tsaye ta miƙe tana zulumin anya lafiya?   Mama Talatuwa ma mahaifiyar Sadiya gabanta ne ya faɗi dama tana ta tunanin inda Sumy ta tafi har yanzu babu ko da ƙurarta kuma yanzu bayan Sadiya ta sanar da ita da Nasir suka zo amma ta san kowa ya ji yanayin kiran da Baba yake mata to ba na lafiya ba ne, don duk wanda ya san Baba to ya san wannan muryar tasa ta ɓacin rai ce.
     Mama Talatu a zuciyarta ta ce
    'Ko dai wani laifin Sadiya ta yi Nasir ɗin ya kawo ƙarar ts, Allah sa dai ba a kan maganar aurensa ta yi wani abun ba, haka kawai muna zaman zaman mu za ta tada mana zaune tsaye' Ma ta faɗa tana kasa kunne don jin mai zai biyo baya domin ta san a wannan hargagin da Baba yake to tabbas maganrsa sai kowa ya ji don bai iya faɗa a hankali ba.
     Sadiya da ta fito jiki sanyi ƙalau tana tafiya kamar ƙwai ya fashe mata a ciki, abubuwa da dama suna mata kai kawo na saƙa da warwara amma ta rasa makamar da za ta kama na dalilin wannan kiran da Baba yake mata.
     Cike da masifa ya ce
    "Sadiya mai kika yi wa Nasir?" Tambayar ta saka zuciyarta tsinkeww ƴaƴan hanjinta suka hargitse tana zare ido cike da tsoro ta ce
    
    "Baba wani abun Nasir ya ce na masa?" ,Ta tambaya kamar zuciyarta za ta fasa ƙirjinta ta fito. Baba takalminsa ya ciro daga ƙafa wanda na hagun ne amma a ƙafar dama tun da garin sauri ya sako a baibai  da takalmin ya shiga nunata sai kuma ya ɗaga takalmin ya yi kanta zai kai mata duka da sauri ta tashi ta yi baya don dama da ta zo tsugunnawa ta yi a gabansa, Mama Habiba da sauri ta ƙaraso ta shiga tsakani gabaɗaya kowa ya fito ya yi carko-carko don yanayin yadda Baba yake hargagi babu abin da zai sa mutum ya kasa yunanin sakin Sadiyar aka yi kuma wani babban laifi ta aikata.
     Kalifa ma fitowa ya yi hannunsa duk miyar da yake cin tuwo ɗaya hannun kuma riƙe da ƙaramar wata roba da Mama ta zuba masa tuwon don dama a nata ta ɗauka masa ta ba Sadiya sauran.
     Baba ya ce
    "Ina tambayarki kina tambayata",
    Tana girgiza kai ta ɓuya a bayan Mama Habiba ganin kamar zai duke ta da takalmjn sai kumfar baki yake.
Mama Habiba tana bashi baki cike da jin haushin ta ya saka hannu ya matsar da ita gefe guda yana nuna ta da takalmin hannunsa ya ce
"Na sha faɗa miki ki fita sabgata da ta ƴaƴana amma rawar kai ya hana ki" Bai jira cewarta ba ya matsa kusa da Sadiya ya ce

"Uban mai kika masa ya kwaso ki ya dawo da ke gida?" Cike da rawar baki da na jiki ta ce

"Wallahi Baba iya sanina ban masa komai ba, ina zaune ina ba Kalifa kunu ya shigo muna hira da shi har yana dariya ya ce in zo mu zo mu gaishe da ku" Shiru ya yi yana nazari don wani ɓangare na zuciyarsa ya fara raya masa cewa ko dai da gaske babu abin da ta masa ko dai ya je wani waje ne ya dawo amma kuma hankalinsa ya ƙi kwanciya da hakan. 

  Cike da tuhuma ya ce

"Kuma kin tabbata babu wani tsohon laifi da kika masa? Ai sau da dama ana yi wa mutum laifi sai yake tarawa rana ɗaya ta yi hukunci" Kia kawai take girgizawa domin yanzu Baba ya ƙure duk wani ƙwarin gwiwarta musamman da yance ko tsohon laifi ne aka tara, tun ba a je ko ina ba sai ta ji gabaɗaya gidan ya gundure ta, kai a rayuwa a ce gidan mahaifinka baka da kataɓus ko ikon zuwa ka ji daɗi sai dai koyaushe ana tsoron mutuwar aurenka kamar a kanka aka fara aure, bayan aure babu inda aka haramta mutuwarsa sai dai kawai sakin halattacen abu ne da ubangaiji ba ya son sa saboda a duk lokacin da aka yi sakin aure sai al,aeshin ubangiji ya girgiza.

  Jifa ya yi da takalamin gannunsa sai lokacin ma ya gane ashe ba daidai ya saka takalmin ba, yana jan wani uban tsaki ya gyara saka takalmin, gabaɗaya bashi da wata nutsuwa, waya ya ɗakko a aljihunsa ya shiga dokawa Nasir kira sai dai ba a cewa a kashe amma dai wayar bata shiga da alama dai Nasir ɗin ya saka lambar Baba a wani waje da baban ba zai same shi ba ko dai black list ma ya daka shi oho. Ya kira ya yi sau goma amma waya bata shiga ba, ƴan gida sai ƙusƙus ake, Mama Talatu tana daga bakin ƙofar ɗaki ko yawu ta kasa haɗiya tana fargabar ko dai Nasir ya saki Sadiya idan kuwa haka ne tabbas nata auren ma yana cikin jalala kamar yadda Baba ya sha jadda da mata a baya cewa matuwƙar dai ta zuga Sadiya ta kashe aurenta to tata igiyar auren ma tana cikin wani hali.
  A zafafe ya ce

"Kira min shi in ji dalilin kawo ki gidan nan da duhun magriba ya tafi babu wani ƙwaƙƙwaran bayani" Duk ta rikice da masifar Baban hakan ya sa ta ma manta da batub wata waya. Sai da ta tuna sannan ta ce

"Am na...na... bar wayar a gida" Baba da ƙarfi ya ce

"Allahumma ajirni fi musiba" Kai Sadiya ta sunkuyar tana jin zafin furucinsa, sai kuma cike da gargaɗi ya ce

"Bari in jira a yi ishsha,i idan har bai dawo ba ki jira nawa hukuncin" Na'am ta yi da maganarsa bai yi wa kowa magana ba ya juya fuuu ya yi ɗakinsa. Juyawa ta yi za ta koma ɗakin Mama Habiba ganin Mama Sa'ade tana mata wata dariyar ƙeta, sai kuma ta ji Mama Talatu ta kira ta hakan ya sa ta jiya alkalar tafiyar tata zuwa ɗakin Mama Talatun. Tana zuwa ƙofar ɗakin Mamar ta juya ta shige ɗakin Sadiya ta mara mata baya, Kalifa kuma Mama Habiba ta tafi ɗakinta da shi, tana shiga Mamar bata wani damu da halin da take ciki ba ta ce


"Sadiya mai kika yi wa Nasir ya dawo da ke gida?" Sadiya ta amsa tambayar sa har ta gaji da amsawa kamar yadda ta ba Baba amsar cewa babu abin da ta masa haka ma ta ba Mama amsa. Amma Mama ta ringa bala'i tana faɗin akwai dai wata a ƙasa domin ai ruwa ba ya tsamu banza, sai dai duk rantse -rantsen da ta yi Mamar bata yard ba.

  Zuwa can aka kira sallar ishsha,i ta fito ta wanke hannu ta sake wata alwalar, tana jin da za ta gifta ta gaban Mama Bilki tana mata habaici, wai sun zama ɗaya da sauran yaran gidan da ake yi wa gorin rashin samun miji Allah ya ƙara tun da yanzu ita ma ta dawo zaman zawarci. Bata ce komai ba illa iyaka ta wuce ta shige ɗakin Mama tun da dai yanzu abin ya haɗe mata biyu wato rana zafi inuwa kuma ƙuna. A tsanake ta yi sallar ta ta ringa kai kukan ta wajen ubangiji a cikin sujadarta don ta san shi kaɗai ne zai yi mata mafita ta alkairi kuma shi yake tafiyar da dukkan lamuranta. Baba tsabar damuwa da ɗorawa kai babu abin da ya ci don har da man shanu da ya siyo wanda ya ce zai ci tuwo amma tsabar rashin nutsuwa ko kallon kwanukan tuwon da aka ajiye masa bai yi ba. 

  Ana yin sallar ya shigo gidan, don tunaninsa ma da ya fito daga masallacin zai ga motar Nasir amma shiru maƙatau babu shi babu alamarsa. Kiran Sadiya shi ne sallamarsa, lokacin Sumy da sauran wanda basa nan duk sun dawo, kowa kunne ya kasa don ya ji mai Baban zai ce, Sadiya wacce ta amsa ta taso jiki yana rawa Sumy dama tun da ta shigo take faman yada maganar ganin Sadiya da dare don ta san dai ruwa ba ya tsami banza. Tana fitowa Baba ya ce

"Wuce mu tafi in mayar da ke ɗakin ki" Cike da marairaicewa ta ce

"Baba ina jin fa zai dawo" Ta faɗa don ganin Baban bai mayar da ita domin a ganinta matsawar dai ya mayar da ita ba ƙaramin raini zai ƙara janyowa mata a wajen Nasir ba ta fi so ya dawo da kansa tun da a iya saninta bata masa komai ba, amma dai ya kamata da a saurara a ji ta bakinsa amma kamar zubar da kima ne namiji ya maido mace gida da kansa kuma a mayar da itw, sai dai shi Baban babu mai faɗa masa ya ji. Cike da hargowa ya ce


"Wane shegen ne ya ce miki zai dawo, da a ce zai dawo ai da tuni ya dawo amma har an yi ishsha babu shi babu labarinsa, dole ki koma ɗakinki shi ne mutuncina da kwanciyar hankalinki " Da to ta amsa masa ba don ranta ya so ba sai dai don babu yadda za ta yi, takalmi ta saka ita tsabar ɓacin rai ma ta manta da Kalifa da yake ɗakin Mama Habiba.


     Maganar Baba ta katse mata hanzari da ya ce
"Ina Kalifan yake?" Fitowar Mama Habiba riƙe da Kalifan ne ya dakatar da Sadiya daga bashi amsa, shi ya karɓi Kalifan ya yi gaba Sadiyar tana biye da shi Mama Habiba tana bin ta da kallo cike da tausayawa. Suna fitowa ya tare wani mai napep tsayawa ya yi wani matashin saurayi ne wanda kansa yake rawa ya ƙure kiɗa sai rausaya kai yake haka suka shiga Baba ya faɗa masa inda zai kai su suka tasamma gidan Nasir.



ALIYA
   Sai da ya yi da gaske wajen yaƙi da zuciyarsa ganin tsananin razanar da ya yj bata bayyana ba duk da ita Aliya ta fahimci ya tsorata, tana tunanin to da shi mene ne nufinsa da har zai yi tunanin ba za ta  ga abin da yake ɗauke da shi ba, tun da dai aure ai zama ne na dindindin ba ya buƙatar ɓoye-ɓoye don duk abin da aka ɓoye watarana sai ya bayyana. Wani yawu ya haɗiye muƙut yana ɗan wayincewa ya ce

"Yau ban yi sallar asuba ba har gari ya yi haske" Ya faɗa har lokacin ba ya cikin nutsuwarsa wani kallon tsantsar tsana Aliya take binsa da shi ganin haka ya fara jan mazaunai har ya zo bakin gadon, yana zuwa ya sako ƙafafunsa ƙasa har lokacin sai jan zanin gadon yake yana rufe jikinsa tamkar dai wanda ba ya ƙaunar a ga ko da cinyarsa ne bare kuma wancan babban wuri da ya san ya adana sirrinsa a wajen wanda babu wamda ya san da hakan sai mutane ƙalilan.

   Tsaye ta tashi a kan ƙafafunsa da suke barazanar gaza ɗaukar gangar jikinsa sabosa ji yake kamar ba zai iya taka su a kan ƙasa ba bare har su kai shi zuwa wani waje. Gabaɗaya ya naɗo zanin gadon ya cire shi daga kan gadon, ya shiga ɗaura zani tamkar wata mace sai da ya ɗaura ya ji wani ɗan kwanciyar hankali ya saukar masa tamkar dai yana rayawa a ransa cewa Aliya bata ga komai ba tunanin hakan ne kaɗai yake ganin zai saukar masa da nutsuwar da har zai iya fuskantar ta.

  Ya ɗan sassauta murya ya ce

"Ki yi haƙuri Aliya na far miki ba tare da amincewarki ba wallahi kin san ba zan iya haƙuri ba, bare har na jure a daren farkon ki a gidana matsayinki na mallakina wani abu bai shiga tsakaninmu ba pls ina roƙon ki mini wannan afuwar!". Ya faɗa yana haɗa hannunsa wajen roƙon ta. Ji take tamkar ta samu mashi ko tsinin wuƙa ta raba ransa da gamgar jikinsa, tsantsar tsanarsa ta ninku a zuciyarta, ninkuwar da bata jin akwai ranar da farashin ta zai yi ƙasa.

  Bai jira cewarta ba don ya ga ta zaɓi masa kallon tuhuma da tsana a kan ta furta masa kalamin da yake son ya ji ta faɗa ko ya san inda ya dosa. Ya ƙara kalallame murya ya ce


"Mu je ki gasa jikin ki kin ji Aliyata, mu yi wankan tsarki mu yi sallah lokaci yana ƙurewa" Kamae wanda za ta fasa ɗakin saboda ƙaraji haka ya ji tashin sautin maganarta tana faɗin

"Kasim ya isheka, ka riƙe wannan daɗin bakin da kake yi kai kanka ka san ni Aliya babu wani daɗin bakinka da zai yi tasiri ba, abu na farko da zan faɗa maka shi ne na tsane ka ba na ƙaunarka ka yaudare ne zan ma iya cewa ka damfare ni" Gabansa ne ya shiga dokawa da ƙarfi ya fara tunanin wace irin baƙar rana ce, shi dai ya san bacci take lokacin da ya gabatar da sunna bare ya ce ko abin da ya yi ne bai gamshe ta ba wato bata samu abij da take buƙata daga gareshi ba kasancewarsa na namiji ba.

  Cike da fargaba ya ce
"Haba Aliya kar ki manta soyayya ce ta gina alaƙa ta da ke fa...


Hannu ta ɗaga masa ta hanyar dakatar da shi ta ce

"Ya isa! Na ce ya isa haka, ni ba wasan kwaikwayo nake yi ba idan wasan kwaikwayo kake so za ka iya kunna su Adam zango da Ali Nuhu idan a ɓangaren mata ne kana iya kallon Momi Gombe, ni Aliya a gaskiya nake faɗa maka magana babu wasa a ciki na tsane ka ka yaudare ne Kasim ashe kai mata-maza ne???" Da sauri ya kalle ta har zanin gadon da ya nannaɗa a jikinsa yana neman suɓucewa da sauri ya riƙe ya ce


"Aliya ban ɓoye miki hakan ba sai don na ga ba wani nakasu ba ne hakan, tabbas an haife ni da baiwar mata -maza amma kuma an yi maganin wannan larurar tun ba yanzu ba wannan wajen ma da kika gani wajen ɓangaren matantakar ne da likitoci suka yi min aiki har suka ɗinke wajen, sannan wajen ai ya zama ma bashi da wani tasiri tun da ni namiji ne can ma na fi ƙarfi ta ɓangaren maza, za ki ga ma ko breast ɗina sak na maza ne bai fito irin na mace ba, kin san shi mata -maza ana samunsu da breast su girma sak na mace sannan al'aurarsu ma waje biyu ne ɓangaren mazantaka da kuma ɓangaren matantaka sai dai kowa da ɓangaren da ya fi ƙarfi" Ganin ta zuba masa ido tana sauraron abin da yake cewa sai hakan ya bashi tabbacin tamkar dai abubuwan da yake faɗa suna shigarta hakan ya da ya ɗora da faɗin.

"Idan har aka yi wa mata -maza aiki su ma za su rayu kamar kowane mutum wanda ba mata-maza ba, sannan suna haihuwa kamar kowa daɗin daɗawa ba a gadon haihuwar mata maza, wato a ce mata maza ya haifi wanda yake mata maza" Idanu ta runtse don idan tana jin kalmar mata -maza ji takr kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, gashi ya karɓe ɗan budurcin da take alkintawa tana jin yadda ƙasanta yake mata zafi da raɗaɗi amma sanin jinsin Kasim ya daƙushe kowane ciwo da take ji, tabbas don ya shammace ta amma da bai isa ya karɓi budurcin nan ba


      Lokacin da ta runtse idanunta babu abin da take hangowa sai Jidda kwance a lallausan gado, mai kyakkyawar shimfiɗa da zanin gado mai laushi, tana kwance a lallausar fatar Ibrahim. Hakan ya sa da ta buɗe idanun sai ta ga Kasim ya zama wani baƙiƙƙirin. Idanu ta ɗaga sai ta ga ashe ma wandonsa ya shimfiɗa a kan gadon ya gabatar da sunnar a ka don tana iya hangar abubuwa masu wuyar faɗuwa a jikin wandon. 

  Juyawa kawai ta yi ta fita wanka ta yi amma na farin ruwa wato wanlan janaba, tana gamawa ta ɗauro alwala ta fito, a bakin ƙofa suka ci karo da Kasim ya matsa mata ta wuce, sallah kawai ta yi ta sake sauya wata rigar ta koma falo ta zauna ta harɗe ƙafa, har ya gama abin da zai yi ya zo ya yo sallar ya koma ya zauna a kan sallayar ya jingina da bango. Wajen ƙarfe tara ya fito ya zo ya ce

"Aliya mai za ki ci" Ko kallo bai iishe ta ba, ya ɗauki filas ɗin ruwan zafi a kicin ya jona ruwa a kyatil ya kunna ƙaramin gas ɗin ya ɗauki ƙwai guda uku ya fasa ya saka maggi da albasa ya shiga soyawa don shi ba ya jin ma zai iya cin wani abu. A lokacin da yake kicin lokacin ne kiran Umma ya shigo wayar Aliya Umma da ta ƙule a ɗaki saboda kar baƙin da suke tsakar gidan su ji wayar da za ta yi don Abba ya fita, bayan Aliya ta ɗauka Umma ta ce

"Aliya ya fita Kasim ɗin?" Aliya ta ce

"Umma babu inda zai je yana nan fa" Umma ta ce bari na kira ki an jima" Tana faɗar hakan ta kashe wayar. Shayi ya haɗa mata ya ajiye a gabanta da wainar da ya yi amma ta saka ƙafa ta ture kofin shayin ya zube ta saka ƙafa ta taka wainar, wannan abin da ta yi ba ƙaramin ƙonawa Kasim rai ya yi ba har ta ga gabaɗaya fuskarsa ta sauya, amma sai bai ce mata uffan ba ya ɗauke ya zo ya gyara wajen, ɗaki ya koma ya kwaso kayan shimfiɗar ya wanke ya shimfiɗa wani zanin. Ganin goma ta yi ya saka takalminsa ya fita daga gidan ko magana bai mata ba.

  Don yanzu zuciyarsa ta fara masa wasi-wasi a kan Aliya ya ga abin nata ba na ƙare ba ne, ya san a iya saninsa Aliya ita ta amince da aurensa ba ya manta ranar da aka kai mata kayan saka rana yadda ta yi ta gode masa kamar ta goya shi amma yanzu komai ya sauya tun daga ranar da aka kai kayan lefe kenan dama abin hannunsa take so ba shi b?

  Ko da ya fita wuri ya samu ya zauna a waje ya kira Salis yana faɗa masa cewa Aliya ta ga halittarsa tana masa tijara sannan ya faɗa masa abin da ta masa da ya mata girki.
 
  Salis cike da ɓacin rai ya kawo wani zagi mai maiƙo ya danƙara ya ce

"Wai wannan yarinyar mai take nufi da kai, ya za ka je kana neman zama matar kana neman bata matsayin naka da Allah ya baka na namiji, ai mace ita ce a ƙasan namiji amma kana neman mayar da kanka wani nusari, a wannan zamanin har ta samu namijin da zah shiga kicin ya sama mata abinci amma take neman ta yi wasa da damarta na lura Aliya ba albarkar zaman aure take nema ba, wallahi jiya sai da na zo na kwanta abin da ta maka a kunnen abokanmu ya ɓata min rai" Kasim kamar zai yi kuka ya ce

"Wallahi na ga abin nata ba na ƙare ba ne abin ma kamar dai ci gaba yake" Suka ci gaba da tattaunawa.


   Aliya kuwa yana fita ta ɗaga wayarta mai fashashshen screen ta shiga kiran wayar Amatullahi, bayan ta ɗauka ta ce

"Ƙawata amarya wato an kwana ana kwasar amarci shi ne yanzu da aka wartsake aka kirani" Ta faɗa cike da zolaya Aliya ta ce

"Dalla can malama rufewa mutane baki ana ga yaƙi kina ga ƙura, mutumin da ya min fyaɗe" Amatullahi ta fashe da dariya ta ce


"Batun nawa dai ya zo wato an ci amarcin dai ai ni dama na san duk wayon amarya dole sai an sha manta" Wani tsaki Aliya ta doka ta ce


"Idan kika ƙara ambaton amarcin nan sai mun ɓata, na kira ki ne in faɗa miki wani sabon tashin hankali da na tsinci kaina a ciki"


 Cike da ɓacin rai ta ce

"Subhanallahi Allah rabamu da tashin hankali ni fa dama jiya ganin kina kumbure-kumbure shi ya sa ban tsaya yi miki sallama ba, saboda na ga sai ki mini rashin m... Aliyanta katse ta da faɗin

"Amatullahi Kasim mata maza ne" Amatullahi zaune ta tashi daga kan doguwar kujerar da take kwance a falon gidansu tana mai saka hannu ta toshe bakinta ta ce


"Mata maza fa? Ke yanzu Aliya duk bita da ƙullin da kike yi wa mutumin nan sai kin bishi da sharri?" Aliya cike da haushi ta ce

"Wai sharrin mai kike nufi? Ina miki maganar tsakani da Allah mata maza ne Kasim amma kina wani batu" Amatullahi ta ce

"Innalillahi mun shiga uku, kuma kika zauna a gidan Aliya?" Aliya ta ce


"To ya zan yi?" Amatullahi ta ce

"To ke ba shikann ba kin samu maƙalar rabuwa da shi sai ki ce ya yaudare ki bai sanar da ke ba in ya so kin ga kin samu hanuar yakice shege daga rayuwarki dole ya sake ki tun da babu wacce za ta zauna da mata maza, kin ga burinki yana dab da cika na auren mijin Jidda tun da ba uwa kuka haɗa da ita ba, sannan ba uba kuka haɗa ba bare a ce ya hakan ya haramta" Dididim gaban Aliya ya buga a take ƙwaƙwalwarta ta fara mata safa da marwa lokaci guda wani abu ya ɗarsu a zuciyarta, sai dai furucin Amatallahi ya katse matq hanzari in da ta ce


"Ina fatan dai babu abin da ya shiga tsakaninku, don mar a je yin abu sau ɗaya ya ɓata miki abubuwa dubu!" Aliya cikin rashin fahimta ta ce ban gane ba?"

 Amatallahi ta c

"To idan yi ɗaya an samu ƙaruwa fa kin ga ko sakin ki ya yi ya barki da jelar goyon ciki da reno"


   MAMAN FRAH
    ***