ABUNDA KE 'BOYE...

bonus

by @surayyahms

BONUS💫#surayyahms

tafiyar minti 12 ammi karama tay kafin ta iso wani kayattacen street tana tsayawa agaban wani babban fancy eatry store taga text message dinsa me sanyi daya turo mata na godiya da kwantar masa da hanklinsa datay...

murmushi tay ta karasa ciki ta siya wasu few abubuwan ci na yara snn ta fito ta nufi schl dinsu sultanan, she waited a bakin gate din schl din for abit,1.30pm na cikawa sai ga nan yaran sunfara fitowa

sultana tana hango motar ammi karama cikin gwalo ido ta zuba ihu tataho da gudu ta bude motar tabi ta shiga motar suna hade ido da karfi ta rungumeta sosai tana murnan ganinta..

favourite cookie da chocolates dinta data saya mata ta bata snn suka kama hanyar asibitin tana ci tana mata surutun su na school tanasata dariya har suka iso asibitin atare.

suna sauka ammi ta kama hannunta tabi ta rike babban basket din adayan hannunta suka wuce ciki, suka samu dede lokcin specialist heart consultnt din ya iso har ankai ayaanah wani daki dr din yanakan examining inta with few advanced devices. jikin sultana atake yay sanyi data ga hakan

ammi tajawo hannunta suka koma dayan dakin sa aka basun snn ta umarceta akan taje toilet ta wanke hannu da baki tazo taci abinci dan ta samu tay sallah akan lokci kafin su ibaad su dawo..

babu musu sultana tay hakan tazo ta samu ammi har ta zuba mata hot plate of coconut rice da turkey stew ga eggs da coulslow ga zobo me sanyi dama kuma baqar yunwa take ji dan tunjiya rabonta dataci abincin gida sai tarin snacks datake siya a school abubuwan har sun fara fice mata akai..

ammi tabarta a zaune snn taje ta karbo doguwar hijabin anty hauwa tanafara sallah agefe sultana ta zauna taci abincin sosaii kmr wacce ta jima bata samu ba, har ammi ta idar tazo tana tayata sunaci atare suna hira, kafin nn anty hauwa tazo itama ta debi abincin tana ci tana bawa ammi labarin yadda ake ciki da jikin ayaana da ire iren test test da likita yace dolene za'a mata su ayau dinnan, hakan yasa zuciyar sultana karyewa, sai atake taji komi ya fita mata akai ta mike taje toilet tay alwala tazo ta fara sallah sai jin hirarsu take tana dada jin tsoro da rauni na dada karya mata zuciyarta sosai...

Doc yace inhar suka gwada akaga ciwontan yay tsanani they may opt for more advance treatmnt a kasar waje koma amata heart surgery or sumtin of that similar kind itade batama gane me suke cewa dakyau ba.

tana idar da sallahn ta dawo tadan lafe ajikin ammi karama idonta yab yacika da hawaye batace komi ba har suka gama hira da anty hauwan, ta gama cin abincinta ta tatashi fa fita amsa waya awaje cikin gaggawa tabarsu subiyu azaune...

juyowa ammi tay jin yadda sultanan take dada shigewa jikinta, suna hade ido kuwa taga wai harta lumshe ido tafara zubo da hawaye da mugun mamaki tace ikon Allah kaga min shagwababbiya kinci kin koshi bari kizo jikina kiyi kuka ko?? da serious muryan kukan sultanah me tattare da wani irn frustration tace ammiiiii amma meyasa ke bazaki dawo maman mu ba?.

hawaye nakan zuba a idonta tace nifa wallh nagaji da mummynmu, itafa asalin muguwace bakiga abunda tay ma ayaanah bane da karfi tajeta shakure mata wuya tana buga mata cikinta, kullum sai tay fushi da su yaa maheer kuma takiyin mana abinci tabar mu sha yunwa kuma saitana ihu tana zaginmu duka damu da babaa..

Kallonta ammi karama ta dingayi da mamakin jin abunda take furtawa, kafin can takara jawota ta rungumeta ajikinta gently tadinga sassaita tana cemata tay shiru ta dena cewa hakan aikomi zai wuce..

sultana tana kukan sosai tace

ammi nide kawai ki amince zaki zamo mamanmu wata rana..

tana shafa kanta da tausayi tace in sha Allah sultana koda bana cikin gidanku i wll alwys be ur mother kinji ko

wasa wasa dakyar ta rarrasheta snn tafara mata few questions akan abubuwan da ya faru, wasu abun da bata gaya ma babanta bama duk saida ta gaya ma ammi karama, ammi was also very shocked to hear the full story, sai yanxu kuma tagane cewa ashe ba ma ayaanah ake son kawo hari ba asali tea din da ake shiryawan na bappa zaidu ne ake son saka masa asiri aciki

nasiha tay mata cikin hikima tace mata duk randa taga mamanta tasaka wani abu a abincin babanta karta sake ta barsa yaci, snn maza taje ta gaya masa dan kar wata rana ya mutu abarsu da kukan rashin sa,da iya ka wnn kalman ta dan razana zucyar sultana tareda cusa mata raayin zamowa very alert musaman akan abincin baban nasu.

..tun bayan nan tay shiru da tunanin abun aranta at same time tacigaba da rarrashin sultana har tay shiru batare da tace komi ba

suna zaune nurse ta shigo da ayaanah akan wheel chair cos she is weak nd drowsy tafiya ma bata iyayinsa sosai yanxu

suna hade ido sultana ta tashi taje ta dan rungumeta tanata bata haquri. ayaanah taji dadin ganinta sosai. nurse din tana ficewa ammi ta jawo su duka,ita ta gyara ma ayaanah position ta dora ta akan gado azaune ta sassaka mata pillow abayanta snn sultana ta zauna kusa da ita tana share hawayenta suna kallon juna...

kallon ayaana ammi karama tay cikin tausayawa tace "yan mata ya jikin naki?? ahnkli ayanah ta dinga kalonta ganin tamata mugun kama da ibaad bakinta na rawa rawa tace da sauki..

she introduce herself as a mother very gently to her, tace mata karta damu zata kula da ita..nd she wll be fine...wata nurse ce takara bude kofar tace ma ammi doctorn sun yana son ganinta yanxun a office dinsa dan zai tafi

kyalesu tay subiyun tabi bayan nurse, tana fita sultana tahau gaya mata cewa ai wann itace mummyn yaa ibaad kuma tana da kirki wata rana ma itace zata dawo mamansu..

ayaana batasha mamakin hakan ba sabida tariga taga kamanninsu sosai..kuma ta lura matar akwai kirki da sanyin hali

hira sukeyi daddaya it seem like duk ta kalle sultana saitaji kmr da addanta take hira...

cike cike ammi tay tabi ta karbo sauran drugs na ayaanah tana dawowa ta samesu suna hirarsu kadan kadan, atake ayaanah saita tsinci kanta dajin kunyar ammin ibaad musmn ma data lura kamar mutuniyar kirkice sam bata da hayaniya

...fresh fruit salad din data siyo ta bawa sultana da ayanaahn dan suna ci atare.

sai ita tafi tasamu anty hauwa acan waje daketa kkrin shirin komawa gida dantaje tay ma mijinta girki, nan tahau gaggaya mata abunda take harsashe bisaga labarin da sultana ta bata akan lamarin raihanatu, anty hauwa tace mata bakomi izuwa gobe zata bincika taji gaskiyan dan akwai wata kawar raihanatun datasani me son surutu tana aiki aitama anan asbitin amma sai goben zatazo kuma tasan duk yadda zatabi ga kwakwalo musu duk wani zancen raihanatu abakinta inde asiri ne ma zasu tabbatar tare da sanin kalar matakin da zasu dauka..ammi ta mata godiya ta bita rakata har waje sukayi sallama kafin ta dawo ciki..

samu tay har ayaana ta amayo dukkan fruits din dataci cikin kulawa ta karbeta a hannun sultanan ta kaita bayi ta wanke mata fuskanta da bakinta tass snn ta cire mata kayanta ta saka mata kayan asibiti sabo dall data karbo acan waje..

a very thick 3qtr gown green gown me round neck da guntun hannu tanata mamakin yadda taga ko gyarama ayaanan gashin kanta ba'a tabayi ba, she look neat in her body but very unkempt in her looks, sun jima a toilet da ammi karama tana gyarata, ayayinda ta aje kanta akan cinyarta tahau kitsa mata suman kantan into two pieces har saida tagama tass snn tadore mata jelarsa yasauka mata har gadon baya.

daga kayan asibitin da kitson duk bakaramin kara fitowa da kyaun ayaanah yay ba hannunta ammi ta kamo suka fito waje suka samu har sultana tay clearing wajen yay fess..ammi ta dauki ayaanah cak ta dorata akan gadon cikin lallami take tambayarta ko tanajin shaawar cin wani abu sai gabaki daya tama rasa me zatace dan batasan metakeji yanxu ba..

.....suna cikin tunanin irin

abincin da ayaanah zataci ya zauna mata aciki arund 2:30pm saiga sallamarsu ibaad tare da maheer dukansu sunsaka kananan kaya ajikinsu daya dada fallasa samartakansu. tun daga kofa ayaanah ta hade ido da ibaad saida suka karewa juna kallo snn tabi ta sunkuyar dakanta can kasa tanajin zuciyarta na buga akansa da bala'in karfi..

kallonta yake har suka karaso ciki suka gaida ammi, ayaana ta kara kallon ibaad ashagwabe as he was busy passing one lovely symphatethic look to her, cikin fahimar irin kallon tausayi dana sannun daya mata sukayi xhnging wani irin silent hrt to hrt soft glances at each oda batare da kowa yalura dasu ba, dama kuma hawayene fall ya cika idonta,daga can yadan girgiza mata kai ahkli da alaman kartay kukan saikuma ta shanye shi tasss tay shiruuuu..

satar kallon juna sukeyi har maheer ya taso ya iso gareta da fara'a ya tambayeta ya jiki itama babu yabo ba fallasa ta amshi ahankli tace da dasauki..

he was alwys so happy inyaga abincin ammi shiya fara zuwa gaban warmers yafara deban nasa dan yasan ibaad is a very picky eater, shidama bakomi yake son ci ba, besides yadda yake cin abincin sa very calm nd classy inkanajin yunwa bazaku shirya ba, dan ko ayanayin taunar ka ma kawai zai iyasawa kuyi fada dashi sosai awajen..

so he fetched his own seprt

yabar ibaad ma ya debi nashi, sunfara ci kenan wata nurse tazo tana gaya ma ammi cewa bazasu iya ma ayaana allura inbata sa komi acikinta ba ..duk da ammi ta mata bayanin yadda abincin bai zama acikinta amma still nurse din tace basuda wani option koyayane kawai asata taci abincin koda kadan ne...

while ayaanah dint say a word, tana zaune kusa da sultana da tun da tagaishe da yayun nata bata kara motsi awajen ba, babu yadda maheer baiy da ayaanah akan taci abincinsa ba amma taki sam...sai can da yagama cin nasan saiya fita dan yaga ko zai gwada siyo vanilla nd cokolate ice creams yaga ko zata iya sha,..

ibaad was eating his food slowly nd observing her, har sai da ya kusa kaiwa can karshe snn yasaka spoon dinsa yayita yayyanka eggs da namansa sukay kuci kuci, snnn ya taso dakansa yazo har ta kan gadon with an unreadable expression,

fusknsan nan amurde ya miqa mata sauran abincin nasa yace "try this one..ammi karama ta juyo ta zuba musu ido tanata kallonsu, tasan kowacce yarinya agidan na jin tsoron ibaad da har kamar zata masa magana tace masa ya kyaleta sai kuma tay shiru ganin kan ayanahn na kasa amma taga wai ta saka hannu takarba plate din daga hannunsa harta rike batace mishi a'a ba.

ajiyan zuciya ayaanan ta sauke duk a tunaninta zai juya ne yaje yazauna awajen zamansa not giving a damn kmr yadda ya saba sai kuma taga ya dada gyara tsayuwansa akanta kyam

suna hade ido taga ya zuba mata idonsa baya ko kiftawa ahnkli ta dau spoon dinsan tadebo iyakan nama da eggs wanda ya yayyanka mata da spoon dinshin tafara ci ahankli ahnkli..

kowa yana kallonta da mamaki har takusa cinyewa batay amai ba...ibaad ya ma sultana wani kallo babu shiri ta sauka a bakin gadon, yabi ya zauna awajen, yana zama yamata alaman ta dauko masa sauran abincin haka taje ta dauko, dakansa ya karba ya kara zuba mata one spoon of rice da two eggs da naman yasake rarrabawa sanda yay loma daya snn ya kara bata spoon din sai ta cigaba da ci ahankli

harsaida sukayi hakan sau uku yaga tafara fidda zufa agoshinta snn ya kyaleta ya miƙa hannu wa sultana ta kawo masa zallan ruwa na gora, ya bude yasha kadan ya miƙa mata itama ta sha ahnkli yace "good girl".suna kallon juna snn ya tashi awajen, hannunsa acikin aljihunsa kamar bashi ba...ya amshi plate din ya ajiye, yay excusing ammin shima ya fita waje..

har wani ajiyan zuciyar jin dadin ayaana taci abincin batare da tay amai ba ammi ta sauke, nan suka zauna kusa da ita suna jera mata sannu, jim kadan ibaad ya turo wata nurse daga wajen tazo tay ma ayaanahn alluran tasha kukan alluran dan yana mata zafi sosai hartagaji tay shiru kafin bacci ya daukata kanta akan kafar ammin..

after some time ibaad ya kira awaya yace ma sultana tafito suje gida tayi wanka ta canza kaya, bada son ranta ba tabishi shima wankan yaje yayi har 3pm ya wuce suna gidan maheer bai dawo ba. sultana tagama shirinta tsaf ta tattara kaya da zatakai ma ayaanah dakyar ma ibaad ya kyaleta suka wuce asibitin tare dan cewa yay ta xauna tay lesson dinta agida tajirasu har sai dare yayi sun dawo haka ta dinga masa kuka tana rokonsa dakyar yazo yaji tausayinta yace mata toh sutafi....

suna shiga asibitin ya ajeta aharaba ya shiga masallaci yay sallan asr yabi ya zauna yana bitan qur'ani abunsa .

sultana tazo ta samu ayaanah ta farka tana zaune shiru but she look abit okay, Ammi tana sallah itama taje tay alwala tafito tazo tafara sallahn agefe tanakan sallahn ne maheer ya iso da katon ledan wani eatry ahannusa kai tsaye ya isa ga ayanahn ganin kowa yana sallah ita dayane kawai a zaune akan gadon yana mata mrmushi ta mayar masa, kanta na kallon kasa tace mishi ina wuni? yace lafya pretty one..ya jikinki.. tace "da sauki...waje ya nema ya zauna kusa da ita yace "are u sure? ta gyada mai kai, cikin jin dadi ganin ta sake dashi yace ga ice cream nakawomiki..duk dama batajin shaawar komi amma ganin kkrin daya ke mata sai batace mai komi ba ta karba

nan kuwa idonta ya sauka akan inda dazu ta gantsara masa cizo wajen har yay jaaa tana daga kai taga yana murmushi da sanyi murya ta kalli wajen snn ta kalleshi tace" yaya..kayi hakuri..yace its okay pretty, amma inkinaso na yafe miki saikin shanye ice cream dinki kinji ko, tace mishi toh..bude mata yay ya bata ice cream spoon din hannunta snn yace "ina ibaad yake? girgiza kanta tay da alaman bata san inda yake ba...

dedenan ammi ta juyo suka kara gaisawa take tuhumarsa inda yaje tun dazu yace mata aikan babansa ya kai wani waje saiyabiya eatery ya siya musu abubuwan..duk sai yahau ciro musu duka kayan kwamulashe ya rarrrba musu, sultana tazo da nata suka zauna ita tadinga motivating ayaanah tasha abun dan bata taɓa sha ba...

the room was calm ibaad ne kawai baya cikinsu yana cikin masallacin asibitin yanakan karatu har saida yamma yay sosai daf magrib kafin nan sai ga bappa zaidu, shima direct frm work yazo ya dubasu yaci abincin daya rage snn akay sallan magrib dashi, shisai ya koma gida shikadai sai can arnd 10 na dare snn ibaad yashigo baiyi tsayuwr 5 mint ba yace musu duk tashi su tafi gida...

ammi kawai aka bari da ayaanah suka kwana tare wnda tun bayan zuwanta batay bacci me dadi ba saiyau sabida time to time takanji ammi ta farka ta gyara mata kwanciya ko ta kira nurse acire mata ruwa ko ta kara rufe mata jiki.....

washe gari tun asuba ta kira anty hauwa tazo tana duba mata ayaanahn ita kuma saita koma gidanta tay wanka ta shirya safiya school tay musu lafiyayyen break fast, kominta tay a tsanake anty safeera da uncle moh kowa yay jaje akan abunda ya faru da ayaanah, she left safiya under they care, bfore 7.30 ta dawo asbitin da hijabi ajikinta da breakfast din datayi musu wanda tasan dai zai ishi kowa....

sassafen kuwa ayaarin gidan bappa zaidun suka so hardashi kowa ya shirya zuwa school

sukazo suka samu ammi hartama ayaanah wankan tasa mata kayan da sultana ta kawo mata jiya, sun zauna agado kmr uwa da ya tana kan taje mata dogon suman kanta data wanke matashi yafita fesss fess yana baza qamshin olive oil data kawo daga gida harda su ribbon komi tamata shi neatly cikin kulawa.

suna shigowa tabisu ta tarba mai kyau tana murmushi tabi rusuna cikin girmawa tagaida bappa zaidu, kagansu agaban yaran kamr sunajin kunyar juna

amma kuma tsabar darajawa ne kawai datake kallonsa da shi

haka ta gaisa da kowa lovingly babu wani bambanci datake nunawa tsakanin yayanta da wanda banata ba.....

wanda ire iren hakan ne yake cima maheer tuwo akwarya, kullum ya tuna mamansa is mot even close to how respectful nd perfect ammin ibaad take sai yanaji kamar da ba ita ta haifesa bama.

haka kowa yama ayaanah ya jiki, ta amsa tabi ta gaida bappa zaidu, itade duk tafi jin sanyi aranta in ibaad ya mata magana koda kadan ne dan harga Allah shikawai take gani taji kanta very safe nd secure a duniyan nan yanzu..

duk da murdadden halinsa she knew he care so much abt her, cos she can feel it ryt in her heart cewa shi mutum ne mai saukin hali da amana ataciki.

haka ammi tay serving inkowa break fast dinsa..sultana tace sam tare da ayaana zata ci aka samusu kuwa atare

suna faraci ibaad ya dinga satar kallon ayanan da gefen idonsa har saida kallon nasa ya kara tursasata taci abincin sosai hartana zufa akanta....

30 min sukay kafin duk suka watse, bayan yaran sun wuce haka ammi ta rako bappa zaidu har waje yana ta mata godiya.

washe gari yana fita a masjid saiga kira daga mahaifin ammi babba dakyar ya dauka sukay magana baban nata ya bashi hakuri amma koda suka gama maganan sai yabi ya shashrntar da zancen nasun gabaki daya

time to time haka har office ake turo masa mutane suzo subashi haquri akanta har yazo ya dena

zamo musu available...

haka rayuwansu ya kasance very calm nd peaceful harna kwanaki uku, anty hauwa tay shige da fice duk saida taji sirrin ammi babba abakin kawarta nurse hasina, matar akwai dan uban gulma cewa tay yanxu ma bura uba ake kanyi me zafi tsakanin zinariya da ammi babba, wai ammi babban tace musu ita sam bazata iya biyan million goma cass banza bayan magani bai amfane ta da komi ba yarinya taje tafasa shi...

ammin ibaad dataji wnn batun bakaramin mamaki tasha ba wanda tun ranar suka fara neman mafitana kariya ma ayaanah da kuma ma yaronta ibaad ita da anty hauwa suketa kkrinsu batare da sanin kowa ba.

saidai daga uncle moh har anty safeera babu wanda yake zuwa asibitin bare ya lekasu..

saidai ayi waya sama sama kuma cikinsu basu taba cewa zasu gaisa da ayanahn ba, thinking she is some local looking village girl that is soo vulnerable nd needs help daga ita har mijintan suna da halin classism irin kanuna kai dan gayu ne wayayye sosai even above normal level of being emphatetic.

haka ammi take ta jigila ita kadai, ta kula da ayaanah snn tabi ta kula da su maheer, haka za tay musu abincin safe da rana har zuwa yamma kuma kullum ita take kwana da ayanah har suka fara sabawa da junansu sosai.

yawan zagowa asibitn da bappa zaidu yakeyi yana duba ammin karama da yamma har su jima suna hira a motarsa yasaka kananan gulmace gulmace ya soma yawo har izuwa kunnen ammi babba.

aranar da suka cika kwanansu na hudu a asbitin sai tafarajn kamar kanta zai fashe dan kirar kawarta nurse hasina dake asibitin ta dingayi tana mata questions kala kala akansu

aikuwa dake asalin magulmaciya ne nurse hasinan har hotonsu agaban mota suna tsaye saida ta dauka mata ta tura ma ammi babba awayar matar kawunta dan ta gansu a zahiri..

tabi ta kara shuga da maggi tace ai fatima kam tariga ta kwace mata mijinta da yaranta gabaki daya ynxu worshipin inta sukeyi, shiyasa su maheer ma ko tunawa da ita basu karayi ba

...kuma awajen fatima bappa zaidu yake rage darensa, snn koyaushe basu hira a waje sai acikin motarsa kuma basu taba gama hirar da wuri ba sai karfe dayan dare.

ta zuxxuƙaa ma ammi babba manya manyan karya me gigita zuciya duk tabi ta sakata takasa bacci. ko baccin kuwa yafara daukarta sai kaga ta firgita ta tashi ta zauna tana zage zage kamr me tabun hankli.

ranar yadda taga rana haka taga dare, gashi tana mutuwar son mijiinta dan duk duniya shine kawai yake rufa mata asiri,

washe gari sassafe ana idar da sallah zafin kishi ya debeta ta sabi jikn wai zataje asibitin tay musu tijara, aikuwa tana kaiwa kofar gida kawunta ya fito ya korota da bulala ta dawo cikin gidan tanata kuka tana zage zage har da yankar jiki da fadi ko wai za'a kaita asibiti dan tasamu ta gudu daga wajen..

haka ta gama sumanta ta farka dakanta kawunta kuma yace ko kunu yau bazata sha agidan ba tunda ita cikkkiyar yar daba ce

gashi kwana biyun nan bakaramin ubanta yake ci agidan cikin ruwan sanyi ba, yadda kasan tazo ta prison, ga abinci ga komi amma dan kadan sosai ake bata hakama bata da breakfast, na rana kawai ake bata..banda na dare. babu kuma fita waje, ko kirar kawaye, inzatay waya saidai ta sace wayar matar kawunta ta buya a bayan gida tayi

abun duniya yabi ya dameta ta rasa abunda yake mata dadi in just five days time din nan datay agida duk sai tabi ta zube kmr ciwo me tsanani tay, kullum tana fushi tana famar kulle kullen makirci da buhun cin mutuncin da zatay ma fatima. abu maficin ran ma ga zinariya ta sakota agaba, har tafara cewa ma zata zo gidan kawun nata da polisawa in har bata tura mata kudinta ba...

komi yabi ya tsaya mata akirji kullum ta zauna saitay kuka kmr ranta zai fita

kwana biyun nan ma taki sam taci dan abinci da ake batan sai kukan kawai take yawan yi,

matar kawun ne dataji irin wayar tashin hankli da dabanci da sukeyi da zinariya shine ta zaunar da ita ta mata nasihohi masu ratsa zuciya tareda bata shawara akan maza ta koma taje ta nemi mijinta gafara tun lokci bai kure bamata ba.

kuka ta dingai ranar kamar wacce taji wa'azin amma inaaa har cikin ranta so take taga ta bar nan, kuma koda zata bawa bappa zaidu badai tabayar dan nadama ba, saidan ta samu ta lallabashi ya bata koda half ne na kudin zinariya dan tasan yana nan yana kashe ma fatima fiye da haka..itama tana da wnn kudin amma ji kawai data bayar tay asara gara ay duk abunda za'ayi. gashi bata iya managin capital ba, miji zai dora mata business kafin kace wani abu ta cinye kudin tass itakanta bazata san metayi dasu. maganan da akey yncu ko yarta sultana tafita yawankudi a banki amma dake babansu na aka musu ido yasaka bata isa ta kwashe kudin yaran ba.

babban gudurinta shine inhar ta koma gidan sa wallah wallaj saita dau fansa akan fatima dan ynxu babu wani lungu da sakon da gulmanta baije ba akan cewa wai wata kyakkwan bazaura data fi karfinta a duniyanci ta kwace mata miji da yaranta harfa kiran layin matar kawuntan akeyi na msmn ana mata gori akan haka....

yau sassaafe da abun ya isheta taji kirjnta na zafi kamr zai fita, sai kawai taji gara taje ta roki kawunta ya barta taje ta bawa bappa zaidu hakuri tunda iyayenta sun sha kiranshi suna bashi hakuri amma haryau baizo ba.....

see you guys monday dan Allah ayi share

surayyahms ***