BARIKI DA KUD'I

Chapter 9&10

by @pinkyjay

💦💦💦💦💦💦

💄BARIKI DA KUD'I 💸

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Following this link to join my whatsapp group 
***


hot love ❤‍🔥care 🤗and romantic 💋story 

*Daga Alk'alamin Pinky Darling 💋Mrs Jay *


*BOOK ONE *  PAGE *  3⏩4
B'angaren Samha kuwa washegari ta shirya kayanta tsaf ta fito Inna Talatu na zaune bakin murhu tana dama koko tace "Inna Talatu ni zan tafi sai kuma na dawo." Wani kallo ta watsawa Samha kana tace "Idan ke tafi Allah ya had'a ki sa masifar da bazaki iya d'auka ba,  garin yin BARIKI da KUD'I, 


ki samo cuta mai karya garkuwar jiki. " Wata dariya Samha tayi kana tace  "Walaka tare dake da y'ar ki kwartuwa, jahila kawai wacce batasan annabi ya faku ba Ina yimiki addu'ar tsawon rai saboda Allah ya gwada miki cigaba a rayuwata da kika wargaza saboda mugunta da son zuciya, 

Allah baya barin zallunci tun a nan duniya \wasu ke fara karb'ar sakamako kafin aje lahira. " Tana gama fad'ar haka ta  fita gidan,  


Inna Talatu tace "idan ke ce me bayarda da sakamako don ubanki a bani sakamakona yanzu shegiya y'ar tasha mai zubin mayu Wallahi na tsane ki kamar yadda na tsane Uwarki. " Samha kuwa tana jinta saboda tana nan tsaye bakin soron gida,  

zama tayi ya sha kuka sosai kafin tayi addu'a ta kama hanya tafiya takeyi sosai har ta bar cikin gari ta fito bakin hanya inda ake hawan mashin ya kai mutum ya shar mota,  ta jima tsaye kafin ta samu mashin ta hau bazato ba tsammani mota ta kwashe su ita da mai mashing, 


ta zubar dasu gefe,  "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji 'un! ." Shine abinda  abinda kakeji  cikin sauri Najib da Aman suka fito Mota Abba da Mommy duk sun fito,  direban mashing babu abinda ya same shi Samha ce kanta ya dake dutse, hannunta kuma da mashing ya dannesa,  

cikin tashin hankali suka sakata mota Abba ya ce su juwa zuwa cikin gari a kaita hospital saboda ta suma ga jini dake zuba sosai,  Aman kuwa duk ya rud'e saboda ko mage bai tab'a bugewa ba,  kasa jan motor ya yi Najib ne yaja motar,  Abba kuwa KUD'I ya baiwa mai mashing d'in 


kana suka bi bayansu Aman sai addu'a yake yi Allah ya sa kar y'ar mutane ta mutu har suka isa hospital d'in sa da gudu nursing suka karb'e ta zuwa ciki Dr suka shiga bata taimako bayan sun tsayar da jinin dake zuba,  

Basu fito ba sai kusan awa biyu da rabi Dr na fitowa Aman yace "Ina fatar komai lafiya.? " Murmushi Dr Z ya yi kana yace "Lafiya lau Alhamdulillahi  komai lafiya nan zuwa yamma zata falka sai dai akwai wata matsala da bana fata zata Iya falkawa cikin tunaninta zata Iya falkawa ta manta komai saboda buguwar data samu, 


sai dai  duk abinda ta iya zatayi komai amma bazata Iya tuna ko wacce ita, ba, amma fa Ko wane lokaci tunaninta zai Iya dawowa don ko yanzu da za samu wani d'an uwanta Ko wanda ta sani hakan zai taimaka mata sosai. "


Writer Bey Pinky Darling Mrs Jay