Kuncin zuci
by @bintuuu
Daren ranan after maghrib suna zaune falon Mami itada Nafisa, ipad ne a hannunta tana game don tunda suka dawo gidan bata bude wayanta dake ajiye cikin box dinta ba, Hira sukeyi jefi jefi da Mami dake zaune itama tana kallon hiran da akeyi cikin Tv a tashar BBC, Mami tace da nafisa "Baby kina jira sai nace kije ku gaisa da iyalan uncles dinki ko?" Nafisa ta dago kanta daga danna wayan da take yi kwance a kujera tace "Mami I thought tunda za'ayi bikin nan basai naje bafa" Mami na kallonta tace "Ke tunaninki bazai baki kije ku gaisa kafin ku hadu a gurin bikin ba ko, for a week now na zuba miki Ido ai" sai Nafisa tayi shiru batace komai ba Mami ta cigaba "Gobe ki shirya kuje tareda Na'ima ku gaishe su and that's final" ta amsa da "Yes Mami"
Sai Mami ta maida hankalinta kan Na'ima da ta ajiye ipad din nata jin Mamin na magana, tace "Habibti, gobe kuje gidansu Baba ku gaishesu" cikin sanyi Na'ima ta amsa da "toh Mami in Sha Allah" bayan sunyi sallahn ishansu nan falon tareda Mami suka sauqa downstairs suka bar Mamin a side dinta.
Zama sukayi anan falon Nafisa na turo baki ita a dole abunda Mami ta sa suyi bai mata dadi ba, Na'ima ta kasa shiru tana murmushi dan yanayin Nafisan dariya ma ya bata tace "Nafee it's just ziyara fa, what's the harm in that? Beside, ba kince yayun Abba bane su din" Nafisa ta bata rai tace "Eh..amma Mami ce take taqurawa sai munje alhalin su ba wani zuwa gidan nan suke ba,
tunda muka dawo kinga yaran gidan sunzo gaisheta ne?.." Na'ima batace komai ba, Nafisa ta cigaba "Har gwara ma su yaya Adam da Anty Fatima sai dan dama dama Husna, Amma 'ya'yan Anty da Mummy fa ba wanda yake zuwa gaishe da Mami" Na'ima da bawai saninsu tayi ba, tana dai jin labarin su wani lokaci a bakin Nafisan, sai ta dan gyara zama tace "Yaran Anty sune twins da Salman da za'ayi bikin nata ko?"
Ganin Na'ima ba wani saninsu tayi ba yasa Nafisan cewa "Kinga yaya Ahmad, wanda sukazo rannan to shine babba a gidan Baba, forget it bari na miki dalla dalla, su Abba su hudu iyayensu suka haifa that is Babba sai Abba sannan Daddy and last dinsu Anty Amnah, to gidan baba yana da mata biyu da Mamma sannan Anty, yaran Mamma sune yaya Ahmad, Anty Fatima, Husna sannan Ummi sai kuma yaran Anty wanda Salma itace fari sannan twins Safiyya da Sumayya" Na'ima ta gyada kai alamun fahimta at the same time idanun Ahmad neh suka fado mata arai ta dan yi stiff tana tuna yanda yake kallonta dazu.
Nafisa ta cigaba "Sai gidan Daddy kuma, kinga yaya Adam shine babba wanda shi mahaifiyarsa ta rasu so practically he was raised by Mamma tareda yaya Ahmad, Mummy ce matar Daddyn ita kadai, ita kuma yaranta akwai Anty Murja, Anty Ummi sannan Laila ce autarsu, to anty Amnah kam kin santa ai" Na'ima ta gyada kai tace "Nagane" Nafisa tace "Mami itadai kayi ta zuwa gaishesu kamar wa'enda akayiwa mutuwa" sai Na'ima tayi murmushi tace "To ai 'Yan'uwan ku ne Nafisa, ya zama dole" Nafisa tace "Ni ba gidan Baba bane banason zuwa, gidan Daddy ne, Mummyn ce ba sauqi a lamarinta" yar dariya Na'ima tayi tace "Kijiki sai kace wata sa'arki" Dariya itama Nafisan tayi tace "Bazaki gane bane".
Abba ne ya shigo tareda samarin gidan dawowansu daga masallaci kenan su Na'ima suka gaishesu, nan kowa ya nufi dinning dan yin dinner Mami ta sauqo itama, Na'ima ce tayi serving dinsu, dan tun farkon zuwanta gidan Mami kan sata itama tayi serving a table din so that she could feel at home, hakan yazame musu al'ada ko ita ko Nafisa sune servers in an zauna cin abinci, Abubakar ne ya bubbude flask din ganin babu tuwo yace "Anty yau ba'ayi mutuminki tuwo ba" Na'ima data koma ta zauna tayi murmushi tace "Abu tsokala ko" Abba yana fara'a yace "Tuwo abunso ne ai Abu" Abubakar yace "Inaaa, Abba munfi gane yaren shinkafah" akayi dariya gaba daya.
Bayan sun gama cin abinci aka koma main falon ana hira, su Na'ima suka tattare kwanikan suka wankesu a kitchen sannan suka koma falon aka cigaba da hiran dasu, Al'adan gidan ne yawanci dare ana zama ayi hira in ba dai ranan da Abba ya gaji ba ko kuma yana da wani muhimmin uzuri ba, Morning ne dai ba'a cika haduwa ba dan kowa yana da lokacin tashinsa, so breakfast ma kowa da lokacin yin nasa.
Washegari...
Na'ima ta fito daga wanka ta zauna kan stool nan gaban madubi, cire hulan wankan nata tayi tafara taje gashinta da ya kasance mai santsi da laushi, har wani curls yakeyi gashin nata tsabar laushinsa. Taje gashin take while tana kallon kanta cikin madubin, idonta ne yakai kan bakin wani tabo a gefen kafadanta gashinta ya dan rufeshi, ta qurawa gurin ido acikin mirror takai hannu tana tattare gashinta daya sauqa kafadunta har zuwa bayanta, wani babban tabo ne ya bayyana sosai a gurin mai kama da yanka anyi dinki, takai hannu ta shafa kanshi tana tuna dalilin jin ciwon, komai yana dawo mata cikin brain dinta kamar yanzu glass din da aka jefon ya yanketa a wajen, idanunta ne suka ciko da hawaye takai hannu ta sharesu still wasu ma suka sake gangarowa.
Tana cikin share idanunta Mami ta shigo dakin, sai tayi saurin kauda kanta gefe tana goge idanun nata, qarasowa Mami tayi ta dafata, ahankali tace "Na'ima" juyowa Na'iman tayi ta cigaba da share hawayenta , Mami tayi shiru tana kallonta sai kuma ta kama hannunta ta jata suka zauna bakin gado, cikin kwantar da murya Mami tace "Na'ima fadamin meke damunki?" Muryan ta na dan rawa tace "Babu komai Mami" shiru Mamin tayi tana kallonta sai kuma ta sake cewa "Kinason komawa wajensu ne?" da sauri Na'ima ta jijjaga kai tace "A'a Mami" sai kuma ga wasu hawayen, Mami ta dan rungumota tana shafa dogon gashinta tace "It's okay dear, it's alright..... everything is going to be fine kinji" tana jikin Mamin ta gyada kanta, Mami tacigaba "I won't let things be repeated again in sha Allah, we will do anything to protect you, ki kwantar da hankalinki kiyi karatun ki kinji, this is your home too..talk to me duk lokacin da kike buqatan someone to talk to" Na'ima ta dago daga jikin Mami tana gyada kanta sai Mami tace "Now wipe those tears, you had so much ahead to live for in sha Allah, stop wasting your tears kinji" Na'ima ta sake gyada kanta tace "Toh Mami" sai Mami tace "In bakyason fitan ma kiyi zamanki ki huta" tayi murmushi tace "A'a Mami zanje"
Mami ta shafa kanta tace "Toh tashi ki shirya" miqewa tayi ta nufi wardrobe dinta Mamin ta bita da kallo zuciyanta na karyewa ta miqe ta fita daga dakin.
Na'ima na cikin saka kayanta Nafisa ta shigo cikin shirinta tace "Har yanzu wai baki shirya ba?" Na'ima ta kalleta tace "Gashi fa inayi" sai Nafee ta zauna kan gadon tana kunna wayanta, bayan Na'ima ta gama saka kayan ta fara neman veil din da zata yafa jikin light blue doguwar rigan jikinta na atamfa daya sha beadwork, ta bincika bata samu wanda ya dace ba acikin jerin veils dinta na cikin wardrobe din sai kawai ta jawo babban box dinta da ta dawo dashi daga England tafara bincikawa aciki, idon nafisa ne yakai kan wayar Na'iman dake cikin kayan, ta miqa hannu ta dauka tace "Bobo ni lafiyanki kuwa da baza kiyi amfani da wayarki ba" Na'ima dake abun gabanta tace "Nafee to wa zan kira?" Shiru Nafisan tayi sai kuma tace "To ai ba kira kadai akeyi da waya ba akwai abubuwa da dama" Na'ima na rufe box din tace "Duk ina yinsu da Ipad plus laptop dina ai" bayan ta mayar da box din ma'ajiyansa ta qaraso ta karbi wayar nata dake hannun Nafisan ta jawo bedside drawer ta jefa Nafisa na bin ta da kallo.
Sun fito zasu tafi Nafisa ta jefawa Na'iman key tace "Kiyi driving dinmu yau kema" sai Na'ima tayi dariya tace "kinfa sani hannuna bai gama fadawa ba" Nafisa ta bude side din mai zaman banza sannan tace "Ai sai kinayin a hankali zaki qware din" da haka Na'ima ta bude driver seat ta shige itama, haka tayi driving din Nafisa na qara nuna mata yanda zatayi, kuma balaifi ta iya din.
Isarsu gidan Baba bayan maigadin ya bude musu gate din babban mansion din Na'ima tayi parking, ta fito tana dan bin gidan da kallo ganin yafi nasu Mami girma, shigansu babban falon gidan suka samu babu kowa sai mai aiki dake faman goge goge suka gaisa da ita sai Nafisa ta tambayeta ko su Mamma na nan, ta amsa da Eh tana sashinta.
A falonta suka samu Mamman, Na'ima ta dan tsurawa kamilan Matar Ido ganin kamarta daya da Ahmad, bayan sun gaisheta ta amsa da "Lafiya nafisa, yakuka baro Mamin ?" Nafisa ta amsa da "Lafiya, tace agaisheki" Mamma ta amsa tana kallon Na'ima tace "Yarinyar wajen Mamin naku ce wannan ko" Nafisa tace "Eh Mamma itace, sunanta Na'ima" sai Mamma tace "Ma sha Allah sannu Na'ima,ya zaman qasar tamu, ba kamar nijar ba ko?" Na'ima ta dan sunkuyar da kanta tana jin yanayin ta wani iri aduk lokacin da aka dangantata da Nijar, gurin da bata ma taba sanin inda yake ba balle taje, murmushi tayi tace "Alhamdulillah" bayan Mamma tasa an kawo musu drinks da snacks suka dan taba hira game da karatunsu sannan suka miqe Nafisa tace "Mamma zamu je gurin Anty" tace "Toh Nafisa" sai Nafisan ta sake cewa "Husna tananan kuwa?" tace "Bansani ba ku duba dakinta , dan dazu tace min zata je gidansu course mate dinta" Nafisa ta amsa da Toh sannan tayi gaba Na'ima na biye da ita suka fice daga falon Mamma. Bayan sun fito daga part din Anty wacce suka gaisa da ita sama sama dan mace ce wadda nukurci ya cinye mata zuciya bata cika fara'a ba, batasan Na'ima ba kuma bata damu da tambaya ba har suka fice, dakin Husna suka shiga suka sameta kwance kan babban gadonta, tana ganinsu ta miqe ta danyi ihun murna sannan ta riqo hannun Nafisa.
Nafisa ta fusge hannunta tace "Dalla sakeni bayan kinsan nadawo amma ko kizo"
Husna tace "Bobo Dan Allah kiyi hakuri school ne ta riqeni amma kina raina wallahi" Na'ima ta dan kalli Husna jin kalman "Bobo" a bakinta, dama Nafisa ta fada mata sunan dasuke kiran juna ne itada Husna.
sai Nafisa ta kyabe baki tace "Bawani nan" dariya Husna tayi ta juya tana kallon Na'ima tace "Sannunki da zuwa" Na'ima tace "Yauwa sannu" ta qarasa zata zauna kan resting sofa da ta gani a dakin Husna ta riqo ta tace "Mu qarasa gadon yafi dadin zama" sai Na'ima ta girgiza kai zata zauna Husna ta riqe hannunta ta jata kan gadon da Nafisa ta hakimce akai ta miqe kafafu harda cire gyale. Bayan sun gaisa Husna ta kawo musu yogurt me sanyi babu cups haka ta miqawa kowannensu a hannu ta hau gadon itama riqe da guda daya, tana kallon Na'ima ganin itadai bata santa ba ta juya tadan taba Nafisa tana mata sign da Ido alamun "Wacece wannan?" a fili Nafisa tace "Na'ima ce fa wadda na baki labarin muna tare a Oxford" Husna tace "Ohhh cousin dinki dinnan?" sai Na'ima ta hada Ido da Nafisa, waskewa Nafisan tayi tace "Eh ita" Husa tace "Ma Sha Allah, she's so beautiful" ta juya ya kalli Na'ima ta sake cewa "Sis, you're so beautiful" Na'ima ta sauke idanunta tana dan murmushin kunya batace komai ba, sai Nafisa ta dan daki kafadan Husna tace "Dalla kina sa ta kunya" Husna tayi dariya tace "Aiiii...sorry" .