KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Suna cikin hira Husna ta tambayi Nafisa "Sis meya faru jiya na kiraki zan miki gulma naji wayanki a kashe?" Nafisa tace "Na kashe ne dan nasan Umar zai kirani" sai Husna ta jijjaga kai tace "Kai..keda guy dinnan dai bansan yanda zanyi defining kalan taku matsalar ba wallahi" Na'ima batasan lokacin da tafara yar dariya ba suka juya suna kallonta Husna na dariya tace "Allah kuwa, yanda kikasan numfashinsu ne ajikin na juna, su basu rabu ba, kuma matsalar taqi qarewa" Na'ima ta girgiza kai tace "Karma ace sai sun rabun, dan banason su rabu but it's high time su fahimci a ina matsalarsu take" Nafisa tace "Bazaku gane bane" Husna tace "Toh fahimtar damu yanda zamu gane din, guy dinnan kunason juna amma kullum matsalar yau daban ta gobe daban, Bobo get a break please" Nafisa bata amsa ba ta cigaba da shan yogurt dinta, Salma ce ta shigo dakin Na'ima ta dan kalleta ganin bazata wuce mate dinsu ba, ta qaraso bakin gadon ta tsaya tace "Sannunku" suka amsa Nafisa na cewa "Amarsu kinsha qamshi" Salma tayi yar dariya sannan ta cewa Husna "Dazu Yaya Adam ya shigo yana neman ki bakyanan" Husna tace "Eh munyi waya dashi ai" sai Salma ta juya tana kallon Na'ima tace "Wannan fa, daga Ina?" tsuka mai karfi Husna tayi tace "Kefa matsalata dake kenan, meye hakan kuma?" Nafisa ma ta juyo tana hararan Salma, sai Salma tace "Ha'a daga tambaya" cikin fusata Husna tace "Dalla to haka ake tambayan? Ji rainin wayo wai 'daga ina' " ta qarasa tana quoting maganar Salman da hannunta, sai Nafisa tace "Banida lokacinki Salma". Na'ima tayi tsuru tsuru ganin fada zai kaure akanta, tadan kamo gefen skirt din jikin Nafisa alamun su bari.

Sanin masifa da rashin hakurin Husna da Nafisan yasa Salma juyawa ta fice tana fadin "Kwaji dashi" Husna ta dan daga murya tace "Zamu hade ne, yar rainin hankali" sai ta maida hankalinta gurin Nafisa tace "Wallahi duk Laila ce take koya musu salon magana mai dauke da rainin nan, balle yanzu da tunda watan bikin ya kama suke sintirin yawo tare, idiots..." Nafisa tayi tsuka tace "Can gidansun zamuje daga nan, Mami harda min gargadin batason fada" Husna ta kyabe baki tace "Lailan ce sai kana mata zafi zafi" Nafisa tace "Ita tasa Salma ta fitar da wannan ankon mai kama dana 'yan iska ko?" Husna tace "Eh mana, ba don Mamma tace sai nayi ba su sun isa su sani nayi wannan kayan ne" Nafisa ta sake yin tsuka jin ranta yana neman baci tace "Wace gulman kika kirani za kimin din jiya?" Husna tace "ke jiya Farha ta sake hotunan wanda ta auran a insta" Nafee tace "Haba? Kice anata ruguntsumi babu ni kaddai" Husna tace "Kedai bari..5k comments a jiyan fa". 

Cikin zumudi suka fara maganganunsu da ya shafi Instagram wanda Na'ima ba ganewa take yi ba dan duk ta qosa su tafi kuma, jitayi duk ta taqura.

Bayan sunyi sallama dasu Mamma akan zasu tafi ta basu humra da turaren kabbasa sukayi godiya suka je wajen Anty itama, sama sama ta amsa musu, Husna ta rakasu suka fice, sun fito compound din gidan kenan suka hango Ahmad sunkuye cikin boot din motarsa yana neman abu , Husna tace "Tabb ga yaya can" Nafisa tace "Bari muje mu gaisa" riqo hannun Nafisan Husna tayi tace "Mamma ta kai qarata jiya, kuzo mu wuce tun bai dago ya ganmu ba" Nafisa tace "To inya juyo fa, kinga Na'ima zo muje" ta qarasa maganan tana riqo hannun Na'ima itama, Na'ima ji tayi kamar ta cewa Nafisan "Bazai juyo bama" amma ganin Husna yasa bata fada ba, haka dai ranta babu dadi suka qarasa wajensa da har zuwa lokacin yana duqen bai gama abunda yake ba, Nafisa ce tafara magana tace "Sannu yaya" sai ya dago ya rufe boot sannan ya juyo, idonsa bai sauqa kan komai ba sai Na'ima, suka sake hada Ido Na'ima tayi saurin kauda kanta ganin yau ma kallon ta yake yi, jitayi kafafunta na neman gagara daukanta gashi sai ta ganta wata qarama a qasansa dan Allah ya masa baiwar tsayi da qaqqarfan jiki, dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida hankalinsa wajen qannen nasa yana amsawa cikin muryarsa dake hana Na'ima nutsuwa yace "Yauwa sannu Nafisa, ya gida?" Nafisa ta amsa, cikin sanyin murya Na'ima tace "Ina wuni" tana kallon everywhere but not his face, dan motsa lips dinsa yayi wanda inba lura kayi ba baza kace murmushi yayi ba, yana nazarin yadda take escaping kallon fuskansa, a nutse ya amsa mata da "Lafiya" Husa tace "'Yar'uwarsu Nafisa ce Yaya, sunanta Na'ima..." sai ya sake kallon Na'iman yana nanata sunanta a zuciyarsa, a fili yace "I know" Na'ima ta dan juya ta kallesa ganin ya maida kallonsa wajen qannensa, within sakannin da basu wuce sha biyar ba ta gama kallon fuskansa a sace sannan tayi saurin kauda kanta kar ya juyo, Nafisa ce ta tambayesa  "Yaya Adam yana nan kuwa Yaya?" ya dan gyada kansa yace "Yana falo" hanyar bangarensu Ahmad din suka nufa, yadan bi bayan Na'ima da kallon gefen Ido kafin ya shiga motarsa ya tayar.

Sun tadda Adam yana Shirin fitan shima yana maqala link jikin hannun rigarsa, suka gaisa yace musu fita zasuyi shida Ahmad shima, tare suka fito ya musu sallama ya wuce gurin motan da Ahmad yake ciki yaja suka fice, suma tasu motar suka shiga suka bar gidan Husna na nan tsaye a compound ta daga musu hannu.

Isarsu gidan Daddy basu samu kowa a falo ba, sai basuyi azarbabin bin Mummy part dinta ba Nafisa tasa sukayi zamansu nan falon, basu jima da zama ba Mummy ta sauqo cikin shiga ta alfarma cike da qasaita ta qaraso ta zauna tace "Sannunku" suka gaisheta kan Na'ima na qasa dan tunda Mummy ta shigo taji kwata kwata Aura din matar bai mata ba sam, suna gama gaisawa Mummy ta dan kwala kira wata mai aiki ta shigo sai ta umarceta da ta kawo musu refreshments, sunanan zaune shiru babu me magana Mummy ta kalli Na'ima sannan tace da Nafisa "Ina kika samo wannan fa? Kawarkice?" Nafisa ta amsa da "A'a yar uwar muce" Mummy ta qarewa Na'ima kallo sannan tace "To sannu"

Laila ce ta fito daga wani qofa alamun kitchen ne a gurin, ta qaraso cikin falon ta zauna gefen Mummy tana kallonsu sama sama tace "Sannu fa" sai Nafisa ta dan juyo itama sama sama tace "Sannu" Na'ima ta dago kai ta kalli Laila zata gaisheta atake ta rasa me zata fada, ganin attachment da nails din da suke jikin Lailan yayi triggering wasu memories acikin brain dinta, tayi saurin sauqe idonta, Laila da kyawun Na'ima took her by surprise ta kalli Nafisa tace "Wannan fa, daga Ina?" Nafisa na jinta kuma bata kulata ba ta cigaba da kallon Tv kamar bada ita Lailan ke magana ba, Mummy ce ta amsawa Lailan tace "Nima yanzu nake tambayanta, wai 'yar'uwarsu ce, Inaga sai dai ta fannin Mamin tasu daga Nijar" 

Laila ta sake tambayan Nafisan tace "Daga gidan baba kuke ne?, Salma tananan?" Sai lokacin Nafisa ta juyo ta amsa coldly da "Eh" Laila tace "Yaya Ahmad fa?" Nafisa tace "Bansani ba nima" tasake juyawa tana kallon Tv, Na'ima dai kamar ta arce daga falon haka takeji, the atmosphere become toxic to her, daga Mummyn har Lailan tuna mata suke da wasu mutane a rayuwan ta da bata son tunasu kwata kwata yanzu. Jin Laila na tambayan Ahmad yasa Mummy tace "Ba kince zaki kirasa ba" cikin rashin da'a Lailan ta amsawa Mummy da "Toh na kirasa bai dauka ba ya zanyi Mummy, ni zuwa kawai zanyi da kaina in kaimasa cakes din, tunda bai dauki kiran ba" ta miqe tana turo baki ta sake tsuka ta wuce stairs su Nafisa na bin ta da kallo, Mummy tace "Ke kika sani ai" ta sake kwala kiran me aiki tace mata "Ki dan debo musu snacks din da Lailan tayi" ta amsa da Toh ta koma kitchen din bata jima ba ta dawo dauke da different shape of small pieces of cakes ta ajiye gabansu, basu ko taba plate din ba Nafisa ta fara miqewa tareda cewa "Mummy zamu wuce gida" Na'ima ta miqe itama tana mata sallama sai Mummy tace "Toh a gaida gida" da haka suka fice, isarsu wajen motansu afili Nafisa tace "Shegiya" juyowa Na'ima tayi zagin yayi tooking dinta by surprise tace "Haba Nafee" adan fusace Nafisa tace "Ke bakiga yanda shegiyar ke mana magana bane, wallah badan Mami ta gargadeni akan fada da Laila ba da watarana sai na zubar mata da haqora tas" Na'ima tadan ware Ido tace "Toh ba gashi har mun gaisa mun fito ba, komai dan haquri ne ai, keda ba wani haduwa kukeyi bama" Nafisa tayi tsuka suka shiga motan suka bar gidan tana mitan sai sun koyawa Laila hankali itada Husna, itadai Na'ima Allah Allah take su qarasa gida ta huta da wannan tunanin da suka zo ranta tun safiyar yau har zuwa barinsu gidansu Laila.