Mafarin kunci
Da gudu ya banko kofar kamar zai ballata yana haki ya in karasa kusa da Ejazz daya shake ta tamkar zai kashe idanunta duk sunyi jajur,baka da hankaline zaka kashe ta ne ya fada yana banbare shi daga gareta,kuka kawai ya koma gefe ya saka saboda yadda yake jin zuciyarsa kamar ana hura wuta ana hadawa da fetur shikaam abin yayi mishi yawa bai san ina zai saka kansa ba,Amma ce tayi karfin halin cewa kayi hakuri Ejazz bawa baya taba iya tsallake kaddararsa Allah na tare dakai Kaji ta juya ta fita tana fadin shamsu a fadawa mutane rasuwan bara nasa a dora ruwa akaita makwancin ta,haka sukayi ta fita daya bayan daya daman sun shiryama hakan shiyasa mutuwar bata wani dakesu ba ba yau bane farko Auncle shamsu ne karshen fita ya dafa shi kafin ya wuce kayi hakuri haka kaddararka tazo addu'a zakayi ba kuka ba Ko kallonshi beyi ba bare yasan ran amsa saboda kanshi a kulle yake wata irin kaddara ce wai wannan
π€π€π€π€π€π€π€π€π€π€π€π€
RUGAR ARDO BALLE
A zaune take kofar Ιan dakin ta zabga tagumi bata san wannan karon sharrin da INNA zatayi mata ba sam bataji karasowar ta ba sai Jin Sanda tayi tsakiyar kanta da sauri ta dago shanyayyun idanun ta ta zuba mata su kara rangwala mata sandar tayi aka ke arr daina kallo na da idanunki kaman na mujiya a wurin shegiya mayya kin tashi kin tafi man kiyyo ga nagge can najira Ko kuwa Sai... kiyi hakuri Inna ta fada tana saurin mikewa ta kama hanyar fita waje, haka ta bita da zagi shigiya baΖar kaddara yunwar cikin ki ma ya isheki haka zanyi ta azabtar dake har ki kasa moruwa munafuka.
π€π€π€π€π€π€π€π€π€π€π€π€
Domin Jin wata kaddara ce ke bin Ejazz kuma wacece inna da kuma yarinyar nan,kubiyo mu a shafi na gaba taku har kullum,plss a ringa comments da like dan bamu karsashiπ₯° Ina sanku masoyana
NEENARH