ABUNDA KE 'BOYE...

23

by @surayyahms

PAGE⏯️2️⃣3️⃣💫
Abunda Ke Boye(buk1).....
wajajen bayan sallan fajr ammi babba tafito sanye da hijabin datay sallah dashi ahnkli takr tafiya tana kifi kifi da idanunta yanayinta kamar na wacce kejin tsoro nan ta taho har kofar falon kawunta malam hamza

tsayawa tay cak abakin kofar tana tunanin irin kalmomin daya dace tabashi haquri dasu ko dama zai dan kyaleta yau taje tabawa bappa zaidu haquri dan ya maidata dakinta, dan gabaki daya zamanta anan gani take kamar cutarta akeyi awaje gashi izuwa yanxu jitake komi ya fara fita mata akai gara kawai taje ta dauki mataki tun kafin fatima ta gama kawo karshen zamanta a gidan mijinta da kuma rayuwar yaranta..

cikin sauke ajiyan zuciya tayi sallama afalon lkcin matarsa ne kawai a zaune akan sallaya tana lazimi..

tun daga kofar ta leƙa ganin baya ciki wani karamin tsaki ya kufce mata tabita tahaɗe rai batace uffan ba ta juya abunta ta koma dakinta tana kan sake sake aranta har saida karfe bakwai da rabi na safiya yayi kawunta bai shigo gidan ba and the more she waits the more lkci yana tafiya, tarasa abunda yakemata dadi, tasan inhar bata buga sammako ta same bappa zaidu a gida ba bazata iya samunsa akoina ba sai in har yamma yay inya dawo gida ita kuma sam bataso taje gidan bare makwafta suce ta dawo bikon miji ajinta yabi ya zuba..

ta shiga wani yanayin na ujula da tunani, can sai da karfe takwas ya kusa cikawa kafin taji sautin shigowar kawu wanda babu shiri ta taho ta samesa ko zama baiyi ba yaji sallamarta abayansa

"kawu ina kwana??

tafadi kanta na kallon kasa kamar mutuniyar arziki tanamai rusunawa

bai amsa ba ya mata wani irin kallo yace "ke kuma raihanatu me ya kawoki???

dan shiru tay kafin can tafara masa magana da sanyin jiki da taushin murya..

"kawu dama haquri nazo nakara baka,kai kanka fa shaidane wallh wallah nay nadamar abunda na aikata ma miji na duk sharrin shaidan ne.

ganin bai tanka ba adede nan ta fashe masa da wani irin makirtaccen kuka tana cewa "kawu dan Allah na rokeka kaji tausayi na kabarni naje dakaina yau nabashi hakuri kodan darajar yarana dana barsu acan sukadai batare da kowa ba nasan zai yafemin...babu ranar da basu zuwamin a mafarki suna bidana, dan Allah kawu kaji tausayi na..wallah sharrin shaidan ne, kuma nayi nadama
..tana fadin hakan tana kuka kamar ba ita ba.

bakinsa a bude yake ta kallonta ayayinda ta cigaba da kukan kamr dagaske nadaman tay

shide baice mata uffan ba face ganin yadda matarsa tafito da sanyin jiki tanata rarrashinta yasashi ya sauko snn sukayi magana yayi mata fada sosai
..snn yace yaune kawai zai iya bata izini tafita don neman gyaran aurenta amma muddin ya kasance bappa zaidu bai saurareta ba toh saidai fa duk su hakura su jira hukuncin da zai yanke nan gaba tunda sudin sunyi iyakan bakin kkrinsu na sasantawa shikuma bai basu fuska ba.  itade duk abunda aka fada cikin ladabi take amsawa da na'am.. suna kammala maganan ta fara shiri, aron kayan matar kawun nata ta amsa ta saka ajikinta tay kwalliya ta fito tawani shaa doguwar blue hijabi wajajen karfe goma saura tafita daga ita sai kudin motar ta nufi cikin gari

tun acikin abun hawa ta dinga lissafin yadda zata bi komi har ta iso wani sabuwar estate na masu hannu da shuni..

agaban wani katafaren gida aka sauketa ta ciro kudi ta bawa me adedeta snn ta nufi cikin gidan kai tsaye da karfi tahau buga gate din kamar tazo filin yaki,

mai gadi ya leko da zimman zai yi masifa saidai yana ganin itace yay maza yazo gabude kofar ta shigo ciki cikin rusuna kai yace ina kwana hajya?

wani dan uban walakntaccen kallo tamasa sama da kasa snn taja tsaki muryanta a dakile tace"Ramatu tana ciki? yace eh tana ciki..yana furta hakan bata jira ba kai tsaye ta wuce cikin gidan agaggauce.

wata babban falo ta alfarma ta ratsa ta samu lkcin masu aiko suna kan jera breakfast akan dinning table, cikin dauke kai ta wuce sama har bedroom din aminiyarta tana isa tafara bubbuga kofar tanacewa "ramatu.. ramatu..ramatu ni dan Allah kibude min kofa bani da lokaci sosai sauri nakeyi...,

hjy ramatu dake gaban madubi taci wani uban kwalliya na manyan mata ta saka cool orange shadda dayasha aiki daga sama har kasa tana kan karasa saka dan kunnen gwal dinta a kunnenta cikin mamko da kyabe baki tace "Ina xuwa..

wani expensive turare ta dauka ta shafe jikinta dashi kafin nan ta fito tana bude kofar kuwa sukaci karo ammi babba  atsaye wacce batace mata uffan ba ta wuceta ta shigo ciki ta tsaya cak a tsakiyar dakin tana huci ahankli..

juyowa hajy ramatu tay daga bakin kofar tace "ikon Allah, yau ga wani sabon salo. ke kuma raihanatu meye haka zako shigomin kamar an koroki ?

ammo babba tace kamar ya ramatu?

wani tuwon harara ta watsa tace "naganki gatsau agidana mana, badai bashi kikaxo nema ba dan inkudine wallah bazan iya bayarwa ba...ai kinsan da haka kikayi ganganci kika fasa magani me tsada sai kace ke kadaice me yara a duniya..

a hatsale ammi babba tace "aah dakata min ramatu karki sake ki gayamin maganan banza mana
..ke kinsan nafi karfin million goma. matsalar dana samu da mijina ne kawai ya tsareni da tuni anwuce wajen..

karasowa hajy ramatun tay tace ohhh dama can kina da hanyar fitowa kibada kudin shine kika bari zinariyar mace take cimana mutunci tana lalata mana suna agari sai yau kenan kikaga dama zaki wani bugamin sammako kamr nina miki asara???

cikin yatsina fuska ammi babba tace "abeg abeg is enuf..ni duk ba tashin hankali bane ya kawoni wajenki, eh naji na amince zan dauki asara kudi kuma zan bayar dashi amma bayau ba sai gobe, kinga dakyar na yaudare kawu cewa haquri canje bayarwa wa miji na na fito nan so dolene kawai kizo ki rakani mukoma wajen bokanki
inhar shida aljanunsa sun karya asirin nan ne da sukamin akan fatima gara insani dan wallh labarai marasa dadi suna zuwa min daga asibiti, na yadda fatima da mijina suke buga soyayyrsu kamar zasu hadiye juna, kuma ynxu haka duk iyayena an aika masa sunsha zuwa har gida suna basa hakuri akan ya maidano daki na amma kinga yay banza dasu baice komi ba...inde har dagaske aure fatiman zaiyi toh wallah gara shi in kashesa kowa ma yayi asarar miji..arzikinsa kuma ai gadon yaya na ne...bani da case!!dan wallah danayi zama da fatima a matsayin kishiya gara na mutu, ko shi ya mutu dan wallah wallah bazaiyu ba.

jikin hajiya ramatu har na ɓari ɓari tazo da sauri ta rungume ammi babba cikin buga shewa tace yawwa raihanatu sai ynxu kika farka a bacci, naji dadin wann maganan naki..ai dama can kece kika tsaya kina musu sanya da tuni an wuce wajen..

ammi babba na share hawayenta tace kawai ki dauki waya ki kira mana bokan kice masa muna zuwa ynxu, daga nan sai mu wuce banki nay drafting cheque na karbi kudin zuwa wajen bokan for now tunda kinga duka katunan banki na da wayana duk suna gidan mijina.

hajy ramatu tace Haba haba raihanatu kudin zuwa wajen boka ai bazai gagareni ba basai munje kinsha wahala a banki ba..ina da wasu kudi anan. jikinta na rawa taje ta bude mata drawer kudine sabbi aciki  famm wanda ba'a ma taɓasu.

da wani irin ido ammi babba ta kalleta tana karkada kai tace "hmmm ramatu kenan wato kina da  kudin kaini wajen boka amma kiban aro na biya bashi dayatsaya min a wuya kince sam baki dashi..hmm ai dama walakanci basai ka mutu ba.

cikin yatsina fuska haj ramatun tace wancan fa matsakrku ce banawa ba..badai zan baki bashi ba..wnn din ma inbaki so ai sai afasa dama inada inda zanje wallah

ammi babba tace a'a thisbis my only chance kawai muje inci abinci mutafi dan makahon yunwa nakeji daga nan sai mu wuce wajen bokan sharply kinsan dai ban isa injima awaje ba kawu zai fara min masifa

fitowa sukayi har dinning suka cin abincin suna labari akan lamarin dake afkuwa wanda rabi duk hirar bappa zaidu da fatima ne..

suna kammala ci suka shirya suka fita,tafiya ne me dan nisa cikin wani kauye 3-4hrs ne zai kaisu ya kuma dawo dasu.


fannin su ammi karama kuwa kusan kominsu acikin kwaciyar hankali da girmawa akeyinshi.
yau suke cika kwana shida a asibitin amma kowani rana jikin ayaana na improving sosai dan within this few days da aka mammata test har speciliast doctorn yazo dakansa ya dakatar da magananan kaita kasar wajen ganin jikinta yana samun sauki sosai..

presence din ammi karama da mutuncin da sultana take mata yasa tazama soo relaxed kwana biyun nan, babu wani abunda ta rasa, ko yake damunta.. maheer kullum zai siya mata su ice cream su sha tare da sultana, matsalar ta daya shine daga zarar taga ibaad sai taji kawai zuciyarta yana yawan bugawa da karfi taciki, duk dama baiya mata fada ko tsawa kwana biyun nan...amma itade haka kawai takejin mugun shakkarsa msmn dataga kamar har sultana ma haka takeji. ibaad baicika zama acikinsu ba, daga yazo few minutes yaci abincin sa, inya sata taci nata abincin ta koshi shknn zai fita masallaci ya kyalesu. life was calm and peaceful, badon ma suna jiran sakamakon karshe na kwajin da akayi ma ayaana ba da tuni an sallamesu sun koma gida.


wajajen karfe 12pm da rabi ammi babba da babban kawarta hajya ramatu suka iso wani karamin kauyen fulani acan tacikin jejin makiyaya wanda haryau da bukka suke yin gidajensu ajejin..

gaban wani katoton gida suka wuce mai babban zaure da dakuna kala kala kamr fadar sarki an zagaye gidan gabaki daya da katangar karare..

akofar gidan suka parker jeep dinsu snn suka shigo zauren gidan suka zauna akan tabarma after like 30 more minutes suna zaune wata babbar mace data toshe fuskarta da face mask ta fito ta wuce snn akamusu iso suma suka shigo ciki

shu'umin dattijo futuk ne tsiriri da farin gemu ke zaune akan kujerarsa ga kayan tsafi kala kala barbaje acikin dakin.

suna shigowa ya fara hangame baki yana kallon hajy ramatu dake mutumiyarsa ce sosai ya saba kwanciya da ita, da wani irin rangwadi hjy ramatun ta rusuna gabansa tana rausaya jiki cikin kashe masa murya tace"..malam nawa nina Allah yaza zamaninka malam ranka shi dade ina miko gaisuwata me dadi musmn ga kayan aikin ka masu dadi.

wani shuumin murmushi yay yace "hajy ramatu kenan gidan dadi, toh dani da kayan aikina masu dadi duk muna amsa gaisuwa...ku samu waje ku zauna inji meke tafe daku?

tana murmushi ta miƙe daga rusunan suna zama ammi babba ta hade rai daga baya bayan kawartan tace "malam ina wuni "wani irin kallo yamata snn yace "lafiya hajya...snn ya juyo da kallonsa kan hajy ramatu yace toh ina sauraranku meke tafe daki yau kuma?

...murmushi tay tace malam akan dai maganar mijinta ne,
kwana biyun nan gabaki daya abubuwa sun rikice mata harma ya koreta agidansa, snn munji labari soyayyarsa yake kwasa da wancan matar, harma syyn nasu ya dawo kamar sabuwa. shine mukace bari muzo muji kome ke faruwa.

cikin gamsuwa da bayanintan ya gyada kansa baice komi ba ya jawo wani katon tukunya ya kunna wuta akai hayakin na fara tasowa yafara sumbatu yana maganganu da hayaqin kamar wanda yake magana da asalin mutum da wani irin yare..

yana gama maganan wutar ya kashe kansa, nan ya tuntsire da wata mahaukaciyar dariya ya juyo ya kallesu duka yace "Asirin hana yuwar aure yana nan daram bai karye ba..saidai adduar da sukeyi da maganin kariya da suke karba shine yake saka asirin yake yin sanyi amma badon ya karye ba..kunyi daidai da kuka zo, idan da ba haka ba wata rana zakuji cewa sun sami wani lakani da zai warware musu sihirin.

cikin jin sanyin jin ance asirn bai karye ba ammi babba tace "toh malam dan Allah yanzu ya za'ayi ka kara zafafa abun nan a raba su,ya zamana baya son ganinta itama bata son ganinsa, su tsane juna..dan wallh ina cikin tashin hankli malam, matar nan ta kwace min mijinaz snn tazo ta kwace min yarana..tunda nabar gidansa yau kwana shida kenan amma ko sau daya yarana basu nemi ni awaya ba suna can atare da ita..nide ko ma miye ne kayi dan matar nan tariga tagama da rayuwar aure na.

shuumar dariya yay yace ki kwantar da hanklinki hajiyabai aure kam fa bazai taba yuwa ba..aljanun mu sunce babu aure a tsakaninsu wann shirmen da sukeyi duk zasuzo su dena kece matarsa na qaddara ,gidanki ne ke kadai zancen kshiya babushi ma a qaddararki.

wani dan uban murmushin bazata ammi babba tay tare da sakin wata katuwar ajiyan zuciya hummm masha Allah malam, ai iren iren maganan da nakeson ji kenan toh inde har hakane kuwa godiya nake Allah yakara maka basira nide yanxu ataimaka min dai na koma gidan mijina tunda kace bani da wata matsala da su anan gaba

cikin gyada kai yace 'angama' ke dai kije ki kwantar da hanklinki
aure fa babu shi aljanu sunce mana kece matar mutuwarsa..

wani irin murmushi ta karayi tanajin wani irin matsanamcin dadi na ratsata mata jikinta irin wanda ta jima bataji shi ba...

wani kullin magani ya ciro ya bata yace mata taje dashi ta jika a gora duk sanda zataje rokonsan ta kurkure bakinta da ruwan maganin babu makawa zai dawo da ita..

karban maganin tay tace masa nawa ne, yace aa kyauta ya bata

rusuna kai tayi tana masa godiya, nan hajya ramatu tace mata taje kawai ta jirata a mota bari itama tama bokan special godiya ata ciki.

bafulatin yana lumewa yar cikin dakinsa hajy ramatu ta sabi jiki ta bishi ciki suka rufe kofa

bata damu da salon karuwancin kawartan ba cikin kyabe baki ta fita can waje tana murmushi danyau bakaramin kwanciya hnklinta yay da taji batun bokan nan ba...

daga cikin dakin bokan kusan minti talatin yay yanakan durjan hajy ramatu sai can bayan har kura ya lafa snn yake gaya mata asalin maganan asirirrince...

cikin girgiza kai yace....hajiya 'ina tausayin kawarki dan gaba fa bazai mata kyau ba, da ace itama zata yi wayo irin naki tazo tana jiyar dani dadi nida aljanu na muna gamsuwa da romonta aida kuwa taga aiki da cikawa

hajy ramatu tace bangane ba malam dama akwai wata matsala ne?amma ai dazu naji kace mata komi lafiya, kuma aure bazai yu ba kode raihantu zata mutu ne???


yace a'a..bazata mutu ba, amma fa abunda zai faru agaba zata gwammaci da mutuwar ma tayi, dan kuwa wayancn mutanen nata sun rike Allah inkin lura shiyasa banfiye son mata aiki

,.magungunan dana baku na hana yuwar aurencan badan da baqaqen ifiritan aljani mukayishi ba da tuni sun kwanceshi. kuma ita waccan din datake gudun itace ma asalin matarsa ta qaddara, lokacin aurensu ne dai bazaizo musu da wuri ba, amma kuma fa manyan aljanunmu da suka shafa sama shekaru dubu daya suna harka sunce min zasuyi auren harma da rabon yan biyu atsakaninsu anan gaba.

a firgit hajy ramatu tamike tsaye cikin doka kirji tace "nashiga uku, haba malam...kace min wasa kakeyi dan Allah?...

jin yay mata shiru yana karkada kai tace...innalillah wa inna ilaihi rajiun lallai kuwa akwai matsala yanzu dan Allah ko kashe daya acikinsu bazakayi ba??...wnn abun inhar yazo ya faru wallah wallah raihanatu mutuwa zatayi

cikin kyabe baki yace.."ai kafin ta kashe wani acikinsu sai inta shirya mutuwar itama, ai suma ba azaune suke ba, mijinta yana can yana neman makansa kariya itama matar tana neman makanta kariya akwai kaikayi koma kan masheqiya ajikinsu, inhar dagaske kinason kawarki toh maza kijje kibata shawarar kartaje wajen wani boka da maganan kisa dan wallh kanta zai dawo, snn kiy duk abunda zakiyi ki rudeta ta cikagaba da yarda da cewa auren nan bazaizo yu ba. inba haka ba sakamakon da zata tarar fa mutuwa ne shima bamai dadi ba..

jikin hajiya ramatu a mugun sanyaye ta koma ta zauna tay jimmm....can kuma tace toh bakomi malam inaga mafita daya kenan.. in sha Allah bazan bari tasan asalin gaskiyar ba, sn inka amince zanyi kkri naga na shawo maka kanta inta yarda zatana jiyar da kai dadi saika taimaka arage mata wani abun ..niko haihuwar yan biyu acire shi acikin qaddararsu, fisabillah malam da wanne raihanatu zataji???

karamin dariya yay yace "babu komi kuje kawai...aiwnn magani dana bata zaisaka mijin ya maidata zuwa gobe. karku damu inyaso duk abunda kukeciki zanji daga wajen aljanu

godiya ta masa snn ta tashi ta tattare kayanta data zubar akasa ta saka ajikinta babu kunya ta fito ta same ammi babba acikin mota, wanda har suka iso cikin garin kano masifa kawai suke ma juna akan zina da bokan nan datakeyi anyhow batare da jin wani remorse ba..


duk wani salon wayo da iya magana hajiya ramatu tabi dan ta ganar da ita irin dadi da karfin buran bokan nan amma haka ammi babba takijinta sam tace na mijinta zaidu batagama iyawa da dadinsa bare na boka 

hardacewa kazanta bokan yake bata kuma har ta mutu bazata iya bude masa gindinta yaci ba.. haka suka sha musunsu har hjy ramatu tay give up, ta zuba mata idan while aranta kawai tausayin futuren raihanatun takeji bana kadan ba.

dukkansu sunsan bazasu taba iya zaman hada miji da fatima ba sabida sosaine tayi musu nisa wajen iya gayu, gata da kyau,da halaye me saurin shiga zuciyar namiji sabida ta iya girki ga tsafta ga sanyin tarbiya da iya magana.


wajajen 2pm suka iso gidan jaju ramatu, anan sukay wanka taci abinci, ko hutawa batay tay maza ta nemi gora ta zuba maganin aciki ta saka a leda tace zata wuce offishin bappa zaidu kawai bataci na xama ba.

hajy ramatu batace mata komi ba har sukay sallama ta wuce wanda tundaga gate din office dinsan akace mata ai ya fita da wasu muhimman bakinsa tun safe basu dawo ba..

da haushin haka tajuyo da Allah yaso ta ma ta amshi kudin abun hawa isashshe awajen haj ramatu, kai tsaye university ta nufa, tajeta har Department of law cikin cin sa'a kuwa yau maheer basugama lectures ba baifi 10min ne atashesu bama.

zama tay har saida aka tashe sun yana fitowa kafin ya daga wayarsa yakira ibaad yazo ya daukesa kawai sai yaji muryanta abayansa tana cewa maheer maheer kai maheer

Da dumbin mamaki ya juyo yana kallonta itama tana kallonsa ganinsa yanayinsa kamar ba abunda ke damunsa aranta tadinajin kamar ta dura masa ashar mai zafi ko ta tsine masa, musmn najin zafin yadda ya debi kashinta ya watsar sai sam bataga alaman kmr mheer yana da imani akanta ba

budan bakinsa kuwa babu gaisuwa yace "mummy meyakawo ki nan?? mugun hade rai tay amasife tace "meyakawo ni fa kace? hmm aidole ka tuhume ni maheer, tunda har kayi wata sabuwar uwar dayasa ni dana tsuguna na haifeka baka kason ganina a kusa dakai..kazubar dani a kwandon shara sabida fatima ko?...toh ni ai banida zuciya, duk yadda ka tsaneni ni uwarka ce babu wace macen da ta isa ta cire sonka araina, zuwa nay dama na duba lafiyarka amma tunda bakason ganina shkenan, 'na lura kanacikin koshin lafya maheer,. sai anjima...bari nakama gaba na kafin kay fushi ka zageni ko ka kadeni da mota marar hankali kawai.

rai amugun bace ta juya zata bar wajen da sauri ya jawo hannunta ta dawo baya cikin sauke murya yace "haba haba mummy nide ban tsaneki ba,
kuma ban mance ki ba infact kullum ma ina miki addua.....

cikin katsesa da haushi tace kana addua dan Allah ya raba ubanku dani ya kawo muku fatima gidansa ko?

wani irin makritaccen kuka tafashe masa dshi tace ...nasan nay masa laifi amma har ace iyayena sunata bibiyarsa har gida har office suna bashi haquri yana banza da su kam sam baimin adalci ba..duk cikinku inda kunsan abunda yarinyar tamin asararsa da saikun mata abunda yafi wanda na mata amma wai harkune kuke daurema babanku gindi yana tozartani..

wata karamar scoff ne ta kufce a bakinsa yace "but mummy that was too much..too extreme!!  haba mummy, ki amshi lefinki mana koda na rana guda ne..kwata kwata bai kamata ki dake yarinyar nan har haka ba..

kara fashewa da kuka tay tace "toh naji nayi leifi..nikuma da aka min asarar million goma ai dutse ce ni, bai kamata naji zafin asara ba..maheer i knw i overaccted but it pain me alot yakake son nayi..nifa baqin zuciyar babanka daka debo  shine matsalana dakai kuma shiyasa bazaka taɓa fahimtata ba...u have no idea what i went tru just to come out here nd see you ryt now...iyayena sun dau zafi, ku da babanku duk kun sakoni agaba, while everything is not entirely my fault nd you know that...

abunka da ɗa da uwa kukan datakeyin sosai yaji yana taba masa zuciyarsa sai baice komi ba ya kamo hannunta ya jawota gefe, suka zauna a inuwa ya fara lallashinta, ta rungumesa kyam sai wasu abun tausayi take masa.. dakyar tay shiru ya fara tambayarta asalin meye ne acikin kwalban har na 10million da ayaanah ta fasa mata

rantsuwa ta masa tsakani da Allah tace wai maganin aljanun kawartace da aka kawo musu shi tundaga china nd its worth 10mll sabida har da kudin shiping da komi aciki...ta dinga rantsuwa tana masa karya .har saida taga ya qamsu, yace toh mumy badamuwa zan gwada yi ma baba magana bt not ryt now sabida he is busy. sai zuwa da yamma inya dawo gida

tana share hawayenta tace "shikenan try for me' ya gyada mata kai yanajin tausaynta. daga haka ya rakata har gate in school tashiga adedeta sahu sai bai kara sanin ina ta nufa ba.

kirar ibaad yay awaya within 10min ya fito daga lab dinsu yazo ya daukesa suka wuce asibiti kamr yadda suka saba kullum, saidai wnn karon maheer was soo quiet thru out the jounery da tunanin maman san aransa wani bin sai yaji kamr kar ya amince da ita wani bin kuma tausayi kawai take bashi....


after few hours bayan sunzo asibiti sunci abinci sun koma gida, komi ya lafa musu, maheer bai sanar da ibaad meyake damunsa aransa game da mum dinsa ba har ya wuce wajen kwallo tareda friend dinsa su abdl gaffar, ibaad kuma yaje shi wani private libarary domin zurfafa karatu..

yau kwata kwata ammi karama da sultana da ayaanah ne kadai suka zauna a asibiti har yamma ya rufa sosai bappa zaidu yazo ya dubasu yaci abincin shima, at around 6:20 ya wuce gida shima, samu yay already su ibaad sun dawo har an shiga sallan magrib, yay alwala ya jonasu ya idar kenan wayarsa ya fara ringing sabon business patner insa ne sai yafito waje yana kan amsa wayar kenan sai caraf ammi babba ta hangosa daga cikin keke napep din tay marmaza ta fito da ruwan maganin ta kurba ta kurkure bakinta dashi..

nn ta sauko tana tahowa ta wajensa ahankli har suka ci karo dashi acikin duhun yamma tawani sha dogon hijabin da tun safe take yawo dashi...

ganinta ya saka ya sallame mutumin dayake wayar tun kan ta fara hauka ta zubar mai da mutunci dan yasan halinta sarai...

suna hade ido cikin sum sum tace mishi ina wuni yaa zaidu! muryan sa kasa kasa yace" ke kuma lafiya? a mugun makirce tabi ta zuba gwiwarta akasa tafara matse ido "haquri nazo nabaka. dan Allah dan darajar hajiya mama kayi hakuri, wallh nayi nadaman abunda na aikata ma yarinyar nan.. kawu na bai gaya maka anmin ruqiya ba? yaa zaidu wallah aljanuna ne  suka tunzura ni na aikata dukkan abun nan,i am not that wicked.. kayi wa Allah kayi hakuri ka maidani dakina and i promise u daga ynzu kocewa kay na rike yarinyar nan har abada kamr yar cikina zan rike maka ita,fatana maganan nan ya wuce tsakanin mu, duk abunda ya faru sharrin shaidu ne da sharrin aljanu na da sukeso su rabani dakai mijina...

adan tsime yace "aljanu? raihanatu ke yaushe kika taba yin aljanu...my friend pls i am not ready for all this nonsense talk ni karki tara min mutane kije kawai zan nemeki..

kuka tafarayi sai da taga ya hade ransa snn ta miƙe tsaye da sanyin jiki ta koma keke napep din tashiga suka bar wajen agaggauce.

maheer dake son dama yay seizing wnn chance din ya ma babansa magananta, ya fito kenan yaga zuwanta wajen sai ya tsaya daga bayansu yanajin duk abunda suka fada...

bappa zaidun na juyowa suka ci karo dashi da taushin murya yace "maheer lafiya? u almost scared me.

kan maheer a kasa yace i am sorry sir dama na fito ne sabida na maka wata magana privately sainaga ma kuna tarene da mummy shine na tsaya agefe

yace "yeah..so what is it dat u want to talk to me abt....

shiru yay sai can ya dago ya kalle baban nasa da sanyin murya yace "baba i dont mean to meddle in to ur marriage affairs..amma baa da kayi haquri da halin mummy ta dawo gidan nan..is already too much stress da muke daura ma ammi nauyin kulawa da ayaanah ga nauyin mana abincin safe da rana da dare koyaushe...in babu matsala ata wajenka i am begging on her behalf pls forgive her nd let her come back...

cikin katsesa bappa zaidu yace "is enough maheer, naji..kaje kay sallanka kawai, nd stay out of this.. i wll handle everything

..da ladabi yace yes sir i am sorry .snn ya wuce masallaci,

bappa yana tsaye awajen har saida aka fara karanta fatiha snn yabi jam'in aka karasa dashi. nd ever since then baice ma kowa komi akan issure din ba, yafita yabarsu bayan isha yay wanka yasaka plain jumfa data masa kyaun yana zuba uban qamshin hugo boss yabar maheer da ibaad agidan shikuma ya taho asibiti duna ammi karama da yara....

dake wekeend ne yau friday night sultana tana nan tare da su ayaanah a asbitin zata na kwana, har sai xuwa ranar sunday ko monday da safe da ake tsammanin zasu samu sallama snn su dawo gidan atare.

wajajen karfe takwas ya wuce ya iso, bayan sun gaisa ya duba jikin ayaanah snn suka fita waje suna hiransu tareda ammi karama, tunda raihanatun tazo sai yaji kamr abun dayayi ma iyayen nata yanata damunsa but he had no choice face yaxo yay shawara da masoyiyarsa fatima yajita bakinta koda hanklinsa zai kwanta.

suna zama acikin motarsa kuwa ya fayyace mata komi dayake ciki, itama sai ta bashi shawara akan kawai ya hakura ya dawo da matarsa, duk dama bayau aka fara ba amma tacemai yayi hakuri tunda yara sun fara saka musu baki aciki, ganin kamr she seems okay with it yasa ya amince amma bawai har ranasa ya so ya dawo da raihanatu gidansa yanxu ba. he wanted her to spend some months dan tasan ita bakomi bace a rayuwarsa, saidai tunda fatima ta lallabshi yaji maganan ma ya wuce mishi...

atake a daren kuwa ta sashi ya rubuta text message ma kawun ammi babba akan ya amince ta dawo gobe...

hirarsu suka kwasa mummsn akan tafiya conference da yake gabansu cikin sati mai xuwan nan...it was agreed that ranar tues zasu tafi su dawo thursday ran friday ko sartuday kuma ake saka ran hajy mama zata dawo mai gabaki daya, dan haka har ila yau ayaanah will still stay da su ibaad agidan bappa zaidu har sai sun dawo ranar thursdy din snn sai atafi da ita can gida.

wajajen karfe goma da rabi suka hakura da hirar har ya koma gida ita kuma ta dawo wajen cikin asibiti wajen yara.

washe gari sassafe kawun ammi babba ya kira mahaifinta ya masa bayani duk aka taru mata akai aka mata fada sosai can snn ta shirya kanta wajajen 10am na safiya ta wuce asibiti tare da daura dammarar korar fatima awajen dan ita tazauna da yarinyar kodan mijiinta ya kara aminta da ita har ta samu damar kawo masa batun kudi, dan ta riga ta qudura aranta cewa bazata taɓa daukar wann asarar da ayaanah tamata ba..
#SURAYYAHMS
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025