PAGE 45
GANIN IDO 🥀🥀
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671
FREE-BOOK
PAGE 45
Murmushi kawai ya yi tare da amfani da ƙarfinsa ya riƙe hannayena sannan ya janyoni jikin sa yana mai bani warm hug. Laɓɓansa ya kai saitin kunnena cikin sigar lallashi ya shiga furtamin wasu kalamai masu daɗi da taushin da ban san lokacin da na haɗiye sauran kuka na ba na kwanta laƙwas a jikin sa ina saurarensa har ya yi nasarar lallameni na manta da laifinda ya mini wanda har yasa bana jin haushinsa sai dai yanayin jikina ina jin ba daɗi akan zazzaɓin da nake ji.
Miƙewa ya yi a hakanli ya ɗagoni muka wuce toilet ya barni nan nayi wanka na gasa jikina da kyau sannan na yi alwala na fito. Ina sallah na ji ana ƙwanƙwasa babbar ƙofar shigowa gidan gabaɗaya. Jallabiya ya zura ya tashi ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo hannayensa ɗauke da abincin kari.
Bayan na kambala sallar ya miƙomin alƙurni na karɓa na buɗe na karanta cikakkun shafuka biyu sannan na rufe na je na ajiye masa.
Sai da na gama shiryawa cikin doguwar riga da gyalenta na saka hula bayan na gama ɗaure gashin kaina, sannan na tsaya jikin mirror na ƙura ido ina kallon sa. Wannan mijin nawa a yanzu ya ƙware a tafiya dani, shi ne zai takalo fushina da kansa kuma daga ƙarshe shi ne wanda zai rarrasheni yasa na manta da duk wani ɓacin ran da yake zuciyata. Son sa nake...tabbas ina son sa sosai wanda duk abin da nake ji daga zaran na gansa nutsuwata ma nemanta nake na rasa.
Na jima ina kallon sa wanda shi sam bai ma lura dani ba akan yanda ya duƙufa yana aikin da na san baya rasa nasaba da kamfaninsa na Golden pathways Wanda kullum cikin aiki yake ba dare ba rana.
Da murmushina da kullewar idanunsa cikin nawa lokaci ɗaya ya kasance. Ai ba shiri na saukar da kaina a ƙasa cike da kunya ina neman yanda zan kare kaina idan ma ya tuhumeni da laifin kallonsa ina murmushi.
Kamar kuwa na sani. Rufe system ɗin ya yi ya ture duk wasu kayan aikinda suke gabansa ya taso ya zo gabana ya tsaya tare da riƙa gefen veil ɗina yana leƙa fuskata yana murmushi ya ce.
"Masha Allah...daga ganin wannan kallon da kike min kina murmushi na san cewa an yafe min laifin da na yi ko Bibina?"
Shiru nayi tare ƙara saukarda idona ƙasa sosai ina wasa da yatsun hannuna lokaci ɗaya ina jin wani abu yana mini yawo a ƙirjina.
"Mu je muci abinci?"
Ya ambata cikin sigar tambaya. Jinjina masa kaina na yi sannan na taka muka je muka zauna. Kaɗan na ci abincin domin har yanzu bana jin daɗi ina jin zazzaɓi. Kamar yasan abin da nake tunani domin magani na ga ya ɗauko ya bani, karɓa na yi na sha sannan na kwanta a jikin sa na lumshe idanuna kamar mai bacci.
Bayan ya kambala cin abincin ya tattara kayan ya kira Jadda sai gashi ta turo Taimiyyah ta tsaya can daga parlour ya bata kayan sannan ya rufe ƙofar ya dawo.
Wayata ya ɗauko ya miƙomin yana faɗin na kira Ammie domin ta kira bana kusa. Ina karɓa na kirata tare da yi mata sallama sannan na gaisheta.
Duk yanda na yi iya yina wurin ganin na sai ta kaina sai da Ammie ta tambayeni cewa mi yake damuna. Murmushi na yi kai tsaye na ce.
"Ammie yau na tashi bana jin daɗi ne, amma dai na sha magani, jikin ma ya sauka."
Cikin nuna kulawa daga can ɓangarenta ta ce.
"Kin tabbata?"
"In Sha Allahu Ammie. Ina su Mummy Sameera? Na ji duk wurin ya cika da surutu, ina kike haka?"
"Wallahy kin ganmu nan ana ta shiri wai Kebbi zamu je Huda ta haihu..."
Murmushi na yi na ce.
"Allah sarki! Aunty Huda ta gidan Mama Asma'u ko?"
"Ita fa. Ta haihu ta samu ɗan ta namiji kwana biyar da suka wuce."
"Allah sarki! Allah ya raya ya bata lafiya. Duk da su Mama da su Mummy Sameera za ku je?"
"A a. Kin san haihuwa ta uku ce yanzu ta yi, to shi ne Abbun ku yace ta shirya tun da haihuwa ta uku ce ba wani abu ba ne don taje ai za ta ji daɗi idan taga mahaifiyarta a kusa da ita. Shi ne fa ta rantse ta ce ba inda za ta je ai tun da ni gani yanzu ina nan ni ce uwar ta, saboda haka sai dai in je ita ba za ta je ba..."
Cikin jin farin cikin cewa yanzu Ammie na tana zaune cikin jin daɗi da walwala ba kamar can baya ba yasa na yi murmushin da har tana iya jiyo sautina don in ƙara tabbatarwa da kunnena na ce.
" Lafiya ƙalau kike zaune ko Ammie na?"
Jinjina kai ta yi tamkar ina a gabanta ta ce.
"Alhamdulillah Beenafah! Lafiya ƙalau nake zaune da Dr., matarsa, yaransa da kuma danginsa. Kowa lafiya ƙalau muke zaune dasu. Hajiya Asma'u ta mutuntani wanda babu abin da zance sai dai Allah ya ƙara mana hak'uri."
"Amin amin yah Allah Ammie."
"Kunyi magana da Aysha kuwa?"
Girgiza kaina na yi na ce.
"A'a. Mun kwana biyu bamu gaisa ba gaskiya.."
"To ki kira ta ki ƙara yi mata ya jikin Daddyn ku domin jikin nasa har yanxu ta ce sai a hankali."
"Tau ya yi Ammie In sha Allahu zan kira ta. Allah ya tsare ya kaiku lafiya....Ammie Bahrain fa? Kwana biyu ya daina cewa a bashi mu gaisa"
Sautin dariyarta na ji tana faɗin.
"Ai yanzu ɗana ya fara zama babban yaro. Yana gidan Hajiya Asma'u, tun shekaranjiya da Hashi ya zo su ka tafi tare. Hamza ne kaɗai a gidan nan."
Jinjina kai na nayi na ce.
"Hmmm! To ya yi Ammie, ai bari na kira mama Asma'un mu gaisa daga nan in ce ta bani shi in ji muryar babban yaro. Ina gaishe da Ya Hamza."
"Tau ya yi, In Sha Allahu za su ji, ki gaishe da Su Jadda da su Labiba."
"In Sha Allahu za su ji, ai jibi ma zamu koma."
"Ok! Allah ya nuna mana."
"Amin. Sai an jima."
Bayan na kashe na kamo numbern Mama Asma'u na gaishe ta sannan muka gaisa da su Bahrain, sannan na kira Mummy Sameera itama wacce in dai gidan lecture ce ta zaman aure da kula da miji to Mummy Sameera ba ta da tsara. Yanzu ma wannan kiran da na yi mata domin mu gaisa sai da ta tutseni da sabon karatun da ni dai kawai sauraren ta nake,domin ko wancan allon ban gama biye wa ba ballantana in wanke a yi min wani sabon karatun. Inda ma Allah ya taimakeni shi ne, Dayaa gabaɗaya aikinsa yake hankalinsa baya kai na ballantana ya saka ni a gaba da tambayoyi.
Bayan mun kambala daga ƙarshe na kira Aunty Aysha muka gaisa na yi mata ya jikin Daddyn kamar yan da Ammie ta ce domin wallahy darajar ta yaci da Aunty Aysha da babu abin da zai sa wai ni Beenafah na kira da sunan jin labarin lafiyar Daddy. Allah ya tsari gatari na da saran shuka wallahy. Allah ma yasa ya mutu ni ina ruwana. Mugu azzalumi wanda bai ƙware a komai ba sai zalunci.
"Subhanallah! Bibi..miye kuma aka miki na kuka?"
"Ba komai."
Kalmomin da na furta masa kenan, a raina kuma tambayar kaina nake cewa wai ashe kuka nake tunawa da irin zaluncin da Daddy ya yi a gare mu. Wata irin tambayar sa ce ta nemi hargitse tunani jin yan da ta jefo ta bagatatan da cewa.
"Miye abin da Mummy Sameera take faɗa miki naga kin nutsu sai murmushi kike?"
A ruɗe na ɗago na kallesa na ce.
"Na'am...Uhm! Ba fa komai. Kawai nasiha ce ta ke ƙara mini..."
"Nasiha Bibi? To akan me kenan?"
Hmm! Wai tashin service. To ni ko Karen hauka ya ci je ni an faɗa masa zan iya faɗin karatun da ta gama biya mini a yanzu? Ba zai ma faru ba. Mutumin nan ya iya bin diddigi kamar wani ɗan jarida wallahy.
"Bibi..."
Cike da neman agajin ya ƙyaleni da wannan biyar diddigin nasa na rausayar da kaina gefe tare da karyar da murya na ce.
"eyyah ba fa komai....ni dai wallahy bacci ma nake ji."
Jinjina kai ya yi yana murmushi ya juya ya koma kawai yaci gaba da abinda yake.
Ina ganin ya tafi na tashi naje na kwanta kawai na ci gaba da bacci wanda ban farka ba sai kusan ƙarfe huɗu na yamma sannan na tashi na yi sallar Asr sai ga shi ya dawo shi ma daga masallaci. Abinci na fara ci sannan muka shirya muka fita Zuwa wurin su Jadda.
Ina shiga bayan mun gaisa da Jadda na wani haɗe rai na ganin irin kallon da su Suwara ke mini wanda naga alamar idan na yi musu saku-saku za su kawo mini wargi.
Haka muka zauna da su wanda hatta Hairi sai da ta shiga taitayinta dani, bayan ya dawo masallaci tare da su Ya Emraan ba kunya ya kirani muka koma ɓangarenmu muka ci abincin dare sannan muka fito muka hau matattakala zuwa Rooftop ɗin su Jadda.
Ban san lokacin da wani kyakkyawan murmushi ya suɓuce min ba domin wurin ba ƙaramin burgeni ya yi ba. An ƙawata shi da shimfiɗu, kujeru da fitilu na alfarma. Wato ashe shiyasa suke ruffing irin wannan domin su riƙa hawo wa suna nishaɗi da dare.
"Wurin ya yi miki kyau ko?"
"Sosai wallahy, wurin ya burge."
Na faɗa ina mai wucewa da sauri na shiga tsakiyar su Taimiyyah da suka zauna akan wata kewayayyar shimfiɗa da aka saka mata wata fitila a tsakiya gwanin burgewa. Baki na tsalma a firar da suke muka ci gaba da firar muna dariya, daman dai babu abin da yayi min wani laifin da nake fushi, ni na yi fushi don kaina yanzu kuma na dawo na sake kamar bani ba.
Wuri Ya Mohaa ya samu gefen Jaddi ya zauna akan kujera suna fuskantar juna ya gaishe sa sannan ya gaishe da Jadda da su Uncle Mu'aƙƙib.
"Miyasa kuke rufin gidajen ku a nan da wannan sigar? Koda yake yanzu ma ga dalili ɗaya na gani tunda gamu a sama muna farin ciki..."
Miƙewa Suwara ta yi ta taje ta tsaya wurin Ya Emraan wanda shi ne ya yi tambayar. Yanda ya saka hannayensa ya riƙe zagayayyen ƙarfen da ya zamto garkuwa ga filin wurin ya tsaya yana kallon faɗin birnin itama haka ta yi sannan ta zuba ido tana kallon shi fuskar nan cike da annuri ta ce.
"Dalilin da yasa muke ruffing irin wannan shi ne; wannan ƙasar tamu ta kasance tana da zafi sosai saboda yashi da muke da shi da dai sauran dalilai..hakan yasa muke ginin ƙasa sannan mu rufe da ita ko muyi yaɓe ko kuma mu shafe da siminti kamar dai yanda Kaga namu yake, domin mu samu sauƙin zafi."
Jinjina kansa ya yi tare da sakar mata murmushi kamar yanda take masa ya ce.
" Uhmm! Da kyau. Gaskiya tsarin gidajen ku akwai burgewa sosai."
" Aunty Suwara Ya Emraan fa yana da mata har da yaro. Naga kin zaƙe sosai..."
Cewar Hairi wacce tun bayan da Suwara ta bar wurin ta je wurin Ya Emraan kunnen, idonta da baki da hanci ke kansu.
Waigowa ta yi cike da alfahari ta kalleta sai kuma ta waiga gun Ya Emraan ɗin ta kalle shi tun daga sama har ƙasa ta yi wani murmushin gefen baki sannan ta ce.
" Na sani. Amma ai ba haramun ba ne. Ba ki ji ko a cikin Alƙur'an mai girma Allah maɗaukakin sarki da biyu ya ce a fara ba, sannan uku, sannan huɗu. Sai kuma daga ƙarshe yace sai idan kunji tsoron cewa ba za ku iya adalci ba to sai ku zauna da guda ɗaya jallin jal."
Sosai Ya Mohaa ya mayar da hankalinsa a kansu yana wani irin murmushi a ransa yana ayyana cewa idan har hakan ya kasance gaskiya to haƙiƙa sai ya fi kowa farin ciki. Domin zumuncinsu tabbas zai ƙara ƙarfi.
Dariya muka fashe da ita cike da nishaɗi Hairi ta sake cewa.
" Idan kuwa haka ne, to lallai ki bini sau da ƙafa ki mini biyayya domin nice nan babbar Aminiyar sa, ƙawarsa mai bashi shawara."
"Masha Allahu! Ku ce sabon zumunci dai zai sake ƙulluwa a tsakaninmu..."
Gabaɗaya lokaci ɗaya kallonmu ya koma gun Ya Mohaa jin irin kalaman da Jadda ta gama faɗa a yanxu.
Ganin yan da kowa ya tsura ido yana kallonsa Har da Ya Emraan ɗin wanda saƙon idanuwansa kaɗai sun gama tabbatar masa da gamsar da shi cewa shima ɗin yana ƙaunar Suwara da gaske.
Hannayensa ya ɗaga sama yana murmushi ya girgiza kansa ya ce.
"Ban isa na ce a'a ba ai. If you do love her...i will be more happier than anyone here..Allah ya tabbatar mana da alherinsa."
Cike da wani irin jin alfaharin kalaman yayansa ya yi murmushi mai kyau ya kalle sa da su Jadda ya ce.
"Thank you for understanding..."
Suwara kuwa, tafin hannayenta ta saka ta rufe fuskarta wai ita taji kunya, daga nan ta gangara ta sauka ta wuce ɗaki.
Fira muka ci gaba da yi kowa ya baje ra'ayin zuciyar sa muna ta nishaɗi tamkar waɗanda suka ɗauki shekaru da sanin juna. Ba ma wanda yake ƙara bani mamaki kamar Ya Mohaa, na lura da shi yana da matuƙar sakin jiki a cikin ahlinsa tamkar ba wani mai babban matsayi wanda ake girmamawa ba.
"Taimiyyah Please ki kawo mana abin taɓa wa.."
Cewar Jadda tana mai kallon gefen da muke zaune. Kafin Taimiyyah ta miƙe har Hairiyyah ta miƙe tsaye tana dariya ta ce.
"Jadda ni ce wacce zan kawo...And ko yayi muku daɗi ko bai yi ba, sai kun sha domin ni ce nan wacce zan haɗa komai da hannuna, daman ai na fara koya ko Aunty Labiba?"
Dariya muka fashe da ita sannan Aunty Labiba ta jinjina kanta ta ce.
"Na san kin fara koya, but the true is,hannunki bai bi ba..."
Ya Mohaa na dariya ya ɗaga hannu sama ya ce.
"I will be the first one to taste everything...kuma ko bai yi daɗi ba, since favorite ce ta dafa, to dole kowa ya ci ya sha...Har Jaddi ban ɗauke masa ba."
Dariya muka yi wanda hakan ba ƙaramin ƙara hura mata kai ya yi ba ta gangara da sauri zuwa ƙasa.
Kitchen ɗin ta fara zuwa ta dudduba wanda ashe bata sani ba, dare da rana cikin aiki suke, musamman shayi da duk wani abu kayan ruwa da fulawa baya yanke musu a kitchen ɗin. Wata ƙila don gidan yana gidan mutane ne yasa haka oho.
Bayan ta ɗauko tray da taimakon wata daga cikin masu aikin kitchen ta jera Coffee, tsire da kayan snacks ta ɗauka tana dariya ta fito ta nufi rooftop ɗin.
Tana tafe tana lissafin yan da za ta shirga musu cewa ita ta ce ita haɗa komai ba kawai ta ji ta yi karo da mutum wanda da ace bai yi saurin saka zafin nama ya riƙe tray ɗin ba, tabbas da babu abin da zai hana masa tarwatsewa a jikinsa.
Cike da tashin hankali ta rufe bakinta da hannayenta tana zaro ido ta bar shi da tray a hannu tana faɗin.
"pp...Please I'm sorry...I'm sorry please!"
Tag ɗin shi da ya sance ya faɗo ƙasa ne ta yi saurin duƙawa ta ɗauko tare da glancing ta kalla rubutamin da ke jiki 'IG SUHAIB M. SAMI'. Miƙa masa ta yi still da damuwar abin da ya faru ta ce.
"Please I'm sorry!"
A hankali taga motsawar kyawawan lips ɗinsa yana faɗin.
"And ta ya ya kike so na karɓa bayan kin barni da kayan ki a hannuna??"
Jin Hausa raɗau a bakin sa ya ƙara ruɗata ba shiri ta miƙa hannun ta karɓa Tray ɗin sannan shi kuma ya karɓi Tag ɗinsa ba tare da ya ƙara kallon inda take ba ya haura ya wuce sama.
Jikin gini ta faɗa yaraf! tana mai jin yanda zuciyarta ke wani irin tsalle kamar za ta shiɗe tsabar yan da ta gigice wanda ta tabbatar da ace wannan trayn ya zube akan wannan haɗaɗɗen Kakin nasa babu abin da zai hana sa kifa mata mari. Bayan ta ɗauki tsawon lokaci a haka, daga ƙarshe ta lumshe idanun ta tare da sauke wata irin sassanyar ajiyar zuciya ta yi wani murmushi tana mai daidaita nutsuwarta sannan ta kama hanya ta haura sama.
Tana hawa idonta ya sauka a kansa inda yake zaune kusa da Ya Mohaa da Emraan suna magana suna murmushi.
Ajiyewa ta yi tare da samun wuri ta zauna tamkar wacce ruwa ya cinye. Lokaci zuwa lokaci take ɗaga ido tana kallonsa sannan daga ƙarshe ta kalli Taimiyya ta ce.
"Wane ne wannan naga ya shigo yanzu?"
Waigawa ta yi ta kalli Suhaib ɗin sannan ta dawo da Kallonta gare ta tana jinjina kai ta ce.
"Ahiy wai? Nan gidan yake shima, yaron Uncle Mu'aƙƙib ne. Yana wurin aiki ne shiyasa kika ga tun da kuka zo baku gan shi ba. Akwai Raihab da, su su Zayn...duk a wannan familyn suke wanda duk suna wurin aikin su, but da sannu In Sha Allahu watarana za ku san su gabaɗaya."
Kiran da Ya Mohaa ya yi mata ne yasa ta miƙe jiki ba ƙwari ta matsa inda suke zaune.
" Favorite...wannan Suhaib kenan. Ke kaɗai ce ba ki gaisa da shi ba."
Kallonta ya yi a tsanake sannan ya jinjina kansa yana murmushi ya ce.
" Akwai dai kam nutsuwa da hankali."
Bata san lokacin da ta sake waro ido ta kalle shi ba, jin wata iriyar magana mai harshen damo da ya yi. Ji ta yi ranta ya ɓaci da shi hakan yasa bata san lokacin da hawaye suka wanke mata fuska ba. A ruɗe Ya Mohaa ya janyo ta yana faɗin.
" Lafiya? Miye ya faru?"
Tambayar da kusan kowa ya jefa mata kenan lokaci ɗaya wanda hakan shi ne abin da ya ƙara tunzura ta ta fara kuka har da sauti. Cikin wata irin muryar sangarta wacce ta ƙware da ita ta ce.
"Zan hauro ne fa ban lura da shi ba na kusa kifa trayn da na ɗauko a jikin sa,shi ne na yi ta bashi haƙuri, shi ne yanzu ya tsaya yana faɗamin baƙar magana cewa wai akwai nutsuwa da hankali. To nufin ka kenan bani da hankalin da nutsuwa ko? tun da na kusa kifa maka abu a jiki."
Lokaci ɗaya ran Jadda da Uncle Mu'aƙƙib ya ɓaci suka rufe shi da faɗa musamman Jadda wacce bata iya ɓacin rai ba idan an taɓa ta, sai faɗin take.
" Yarinya baƙuwa wacce zuwan ta kenan ka ke so ka ɗaga mata hankali da shegen zafin zuciya da fushin da ka saba! Waye ba ya kuskure da har za ka dinga faɗa mata baƙaƙen maganganu daga zuwan ka? Tun da ta zo garin nan take farin ciki sai yanxu da ka zo kai kaga sarkin en rashin haƙuri za ka matsawa rayuwar ta. Kai duk laifin da kake idan an ce za'a riƙa tsaurara maka za ka ji daɗi ne??"
Ai fa yau ya shiga uku. Daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Laifin da ya yi mata ne tun wan can zuwan da ya yi shi ne kenan ba ta huce ba, akan wannan ɗan abun take neman hawaye masa kai.
Da sauri ya harɗe hannayensa alamar roƙo yana murmushi ya ce.
"Dan Allah Jadda ayi haƙuri...ni wallahy wasa nake mata, Ita ce dai ta ɗauka da zafi. Amma kuyi haƙuri..."
Kallonsa ya mayar gun Hairin wacce ke tsaye tana wani cika tana batsewa yana murmushi ya ce.
"I'm Sorry please...I'm sorry!"
Jikin Jadda ta koma ta lafe tare da lumshe idanun ta tana mai jin yanda zuciyarta ta sanyaya. Tabbas da ba ta fitar da wannan abin daga zuciyarta ta yi magana ba, da wata ƙila ko bacci ba za ta iya yi ba a yau. How comes zai kalle ta bayan duk irin haƙurin da ta bashi ya zo cikin mutane yana faɗa mata baƙar magana?.
Murmushi Ya mohaa ya yi bayan mun gama kallon dramar ya ce.
"Ba komai Suhaib. Ka yi haƙuri. Ita ɗin yarinya ce ƙarama.."
"No...Ba komai Yallaɓai. Ai ita ce da gaskiya, duk abin da ta faɗa haka akayi ba ta yi Ƙarya ba. Saboda haka ta yi haƙuri..."
Firar su suka koma yi yayin da muma muke tamu har kusan 1am Sannan muka yiwa kowa sai da safe. Ganin zan wuce yasa Ya Mohaa kiran sunana ya ce.
" Bibi.."
Waigowa na yi a darare na ce.
" Na'am."
"Ki je, ina zuwa yanzu kin ji ko."
Kallon kallo muka shiga yi ni da su Hairiyyah wanda shi kam tunda ya yi maganar ya juya suka ci gaba da magana da su Suhaib kamar ba shi ne ya yi maganar ba. Wucewa na yi daga ƙarshe ina mai ɗaure fuskata domin ko tsayawa ce musu sai da safe ban yi ba na je na shige na yi wanka na yi kwanciyata.
A hankali ɗaya bayan ɗaya suka shiga watsewa wanda wurin ya rage daga Jaddi sai Ya Mohaa.
Kallon Hammodin ya yi wanda a duk lokacin da ya yi ido biyu da shi sai ya ƙara jin wata irin sabuwar ƙaunarsa na ƙara kama shi. Cikin sanyin murya Jaddin ya fara masa magana da cewa.
"Gabaɗaya kanmu a haɗe yake. And kuma muna zaune lafiya ƙalau. Mi zai hana kaci gaba da zaman ka a nan kawai da kai da matarka? Mun rayu tsayin shekaru ba tare da kai ba, a yanzu ina so na ci gaba da ganin ka a kusa dani. Ka yi tunani, ina so ka dawo nan ka shiga cikin shuwagabanni ka ci gaba da tafiyar da siyasa ta tare da iyayenka da en uwanka tun da Kaga ni ƙarfina ƙara tafiya yake."
Ido ya ƙura sosai yana kallon kakansa wanda ya zo masa da wata iriyar maganar da bai san ma ta ina zai fara ba. Jin ya yi shiru yasa Jaddi ya ɗan ƙara matsowa gaba kaɗan yana mai ƙara fuskantarsa da kyau yaci gaba da cewa.
" Ka na ji ko Hammodi...Ba wai ina nufin yau ko gobe ba. A'a, ka bari sai lokacin da ka shirya,lokacin da ka ji zuciyarka ta aminta sannan. Idan kuma baka da ra'ayi, still I won't force you, Kawai a yanzu, I want feel your presence a duk lokacin da na bukata."
Murmushi ya yi yana mai jinjina masa kansa ya ce.
" Jaddi! I respect your opinion, Saboda nima ina jin yanda ka ke ji a ranka...I also respect politics domin a yanzu ina ciki tsumbul tunda har ku ahlina kuna ciki gabaɗaya. But ka yi haƙuri amma ba zan iya siyasa ba. Ba Layina ba ne ba ra'ayi na ba ne. Ni ɗin Engineer ne kawai wanda bai san komai ba sai aikin gine-gine da yin tituna. Yanzu ne na fara rayuwar aure Jaddi...Things will become more harder on me Idan na ce zan ƙara ɗorawa kaina wani nauyin. Ka yi haƙuri ba don na bijire wa umarninka ba. Amma ka barni na ci gaba da rayuwa a Dubai kamar yanda na saba, In Sha Allahu zan riƙa zuwa time to time ina duba ku domin a yanzu kun zamto nauyina kuna da haƙƙi a kai na, har abada ba zan taɓa barin ku ba, na yi alƙawari. I will always stay connected."
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na en wasu daƙiƙu sannan daga ƙarshe Mohaa ya ɗan ƙara matsawa kusa da shi tare da kamo hannayensa ya jimƙe a nasa yana mai ƙara kwantar da muryarsa sosai ya ce.
" kun shafe tsawon shekaru ba tare da kun san cewa ina raye ba. Haka nima na shafe tsawon shekaru ba tare da na san cewa ina da ku ba. To miyasa kake tunanin yanzu da na sameku zan iya ɗaukar dogon lokaci ba tare da na zo na ganku ba? Ina da kamfani wanda yake da rassa daban-daban kuma dole ni ne ke tafiyar da shi. sannan su kan su ƙannaina suna da buƙata dani a kusa da su domin su ɗin Amana ce a wurina. Barin duk waɗannan abubuwan kai tsaye ba abu mai sauƙi ba ne Jaddi. Ina fata za ka fahimce ni dan Allah!!"
Murmushi Jaddi yayi yana mai jinjina masa kansa ya ce.
" Ba komai Hammodi! Daman tun farko na faɗa maka cewa I won't force you. Waɗannan kalaman naka kaɗai sun gamsar da ni cewa hasashena Sam ba gaskiya ba ne, na cewa za ka iya barinmu. Allah ya yi maka albarka. Allah ya baku zaman lafiya da Zuriya ɗayyaba."
"Amin Jaddi. Na gode da fahimta. Allah ya ƙara maka tsawon rai da lafiya mai amfani da albarka."
"Amin. Ta shi ka tafi wurin matarka, dare ya yi sosai. Allah ya tashemu lafiya. Gobe ka fito da wuri zamu zaga inda na faɗa maka ka dubo ka gani"
Murmushi kawai ya yi domin kalmar "tashi ka tafi wurin matarka" ba ƙaramin dariya ta bashi ba. Miƙewa ya yi yana ƙara yi masa sai da safe sannan ya juya ya wuce.
*****
Washe gari kam lafiya ƙalau na farka ba tare da wata damuwa ba, domin jiya ban san ma lokacin da ya shigo ɗakin ba sai da na farka da asuba na ji ni a cikin jikin sa, kuma yana dawowa daga masallaci ya shirya suka fita tare da su Uncle Mu'aƙƙib wanda ban san inda suka nufa ba.
Bayan na shirya ni kuma na fito Kitchen muka ci gaba da yin aiki tare da su Suwara. Muna nan muna fira cike da nishaɗi Suhaib ya leƙo wanda da alama daga wurin motsa jiki ya fito sanadiyyar wata irin zufar da yake tsiyayarwa ga kuma kayan motsa jiki a jikin nasa.
Gaisawa muka yi da shi cike da mutuntawa ɗaya bayan wanda Hairi ce kaɗai wacce ta ɗauke kai tare da ƙara yin fuskar shanu tamkar bata taɓa sanin yan da ake dariya ba.
"Ke! so dangi..."
Ya faɗa yana mai kallon fuskar Hairi.
Ɗage kafaɗarsa ya yi tare da ware hannayensa alamar ko a jikin sa sannan ya kakkallemu ya ce.
"Ita ce ta min laifi, kuma ita ce ta tara min jama'a ta saka Jadda neman tono laifina na kusan watanni huɗu, sannan kuma still ita ke fushi...Taimiyyah!"
Ya ambata sunan ta daga ƙarshe yana mai kallonta ya ce.
"A bata breakfast ta kawo min ɗakina kafin na gama wanka."
Bayan ya wuce muka ɗauko firar muna ta tsokanar ta da ita muna dariya wanda ko kaɗan bata buɗe baki ta yi mana magana ba.
Bayan Taimiyyah ta gama haɗa abincin ta miƙa mata tana faɗin.
"Idan kika fita ta wannan ƙofar, ɗakin da ke kallon wancan garden ɗin can ne ɗakin sa.."
Wani irin ƙara ɓata rai ta yi kai tsaye ta ce.
"Ni fa ba zan je ba. Ku bai wa mai cikakkiyar nutsuwa da hankali ta kai mas.."
"Haba Hairi! Ki yi haƙuri mana. Kina ga fa har zubar da kansa ya yi gaban kowa jiya ya baki haƙuri. Shi ma ɗinfa Yaya ne a gare ki kamar su Emraan."
Cewar Aunty Labiba tana mai ɗan Kausasa Muryarta kaɗan ko Allah zai sa ta sauko daga Dokin zuciyar da ta hau.
Jin irin yan da Aunty Labibar ke magana yasa ta karɓi trayn ta tafi tamkar za ta kifa ta tura ƙofar ɗakin ta shiga kai tsaye. Within seconds ta gama ƙare masa kallo da ɗakin nasa wanda ya kai maƙura wurin haɗuwa sannan ta ajiye trayn a kan wani glass table tana wani Harararsa a kaikaice daga can inda yake tsaye jikin window yana Waya.
Ganin yaƙi ya tsinke kiran ballantana har ya yi noticing ɗin cewa ya ganta yasa ta Juya ta nufi ƙofa domin ficewa.
"Jira na ne ba za ki Iya ba?"
Tsayawa ta yi cak ba tare da ta waigo ba ta ce.
"To ai ga shi nan na riga na ajiye maka.."
"I LOVE YOU..."
A ruɗe ta waigo tana mai zuba idanuwanta ta kalle shi da kyau domin ƙara tantance mi ya ce a bayan idon ta.
Ta kowa ya yi ya tsaya a gabanta yana mata murmushin da tun a daren jiya idan ta kalleshi taga yana yin sa yake burgeta ya ce.
"Daman jiya har da haushin zancen ƙin auren da na yi ne yasa Jadda ƙara harzuƙa kuma ke ce kika janyo hakan. Saboda haka ina son ki, ina son ki, ina son ki. Yanzu sai ki san yanda za ki yi dani ki aureni."
Ƙirjinta na wani irin tsalle jin ta a wani irin yanayi, Muryarta har tana sarƙewa ta ce.
" Ka taɓa ji inda akace an kamu da soyayya daga dare zuwa safe?"
Jikin ƙofar ya jingina tare da tallafe hannayensa a ƙirjinsa yana kallon fuskarta wacce duk ta nuna rashin nutsuwa ya ce.
"Ana yi mana! Sau nawa ma akayi? Wa su ma ko ganin juna basayi kuma a ɗaura musu aure su zauna lafiya ballantana mu da tun a daren jiya son ki ya hana zuciyata sukuni..."
"To idan ni kuma bana son ka fa?"
"Ba zai ma faru ba....Tun jiya da kika ɗauko min Tag ɗina kika ruɗe kina ta bani haƙuri da kuma irin yanda kike ta satar kallona a Rooftop kina magana ta da Taimiyyah na gane cewa kema kin kamu da So na..."
Zuciyarta na wani irin pumping ta gimtse idanunta da ƙarfi tace.
" Ni dai ka matsa mini a hanya na wuce."
Janyewa ya yi ya koma gefe yana murmushi har ta fice da gudu tamkar za ta kifa tsabar yanda ta ruɗe take neman ficewa daga hayyacinta.
Har suka kambala breakfast ɗin gabaɗaya hankalinta baya jikinta, idan sau dubu ta rufe idonta babu abin da take gani yana mata gizau idan ba shi ba. 'IG SUHAIB' sunanda ke ta mata yawo kenan a brain ɗinta tsawon lokaci.
*******
A ranar Juma'ar da muka cika sati, a ranar muka shirya domin komawa gida, inda aka ajiye maganar Suwara da Ya Emraan daga zaran ya koma gida ya shaidawa sauran iyayensa. Sannan Ig Suhaib da Hairiyyah shima kamar da wasa sai ga shi ya kai maganar gaban su Jadda wacce daman ta jima da damuwar rashin aurensa, hakan yasa suka yi matuƙar farin ciki musamman da ya kasance Hairi ce zaɓinsa duk da cewa mahaifiyarsa ta so ta ɗan yi tirjiya sakamakon kasancewar Hairi ɗin 'ƴa a wurin Hajiya Batula. Sai da su Jadda suka tsawatar sosai sannan ta saki ranta ta amince itama.
Mun yi nishaɗi, munyi zumunci mai ma'ana a ƙasar Sudan wanda za mu jima wannan tarihin bai shafe a zukatanmu ba.
Tunda aka saka kayanmu a mota Suka fara koke-koke musamman Jadda. Bayan mun fito na riƙa hannun Suwara ina murmushi na ce.
"Zo ki rakani na hau Rooftop ɗin nan na bankwana. Wallahy wurin nan yana matuƙar bani nishaɗi."
Jinjina kanta ta yi tana murmushi ta ce.
"To shi kenan Aunty Beenafah. Muje daga nan sai na miki hotuna, kinga idan kin koma gida duk randa kika ji ina jin kewar Rooftop ɗin sai ki kamo ki yi ta kalla."
Sama muka haura har da Hairiyyah muna ta hotuna muna nishaɗi.
Kallon Ya Mohaa Jadda ta yi tana ta wani kuka ta riƙe masa hannu ta ce.
" Hammodi dan Allah karka barni.. "
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya ɗago hannun da ta riƙe shi da shi ya sumbata. cikin sigar rarrashi ya kwantar da murya ya ce.
" Ba zan taɓa barin ki ba Jadda...nan ɗin a yanzu shima ya zama gidana. Ba zan taɓa barin ku ba sai idan mutuwa na yi..."
"To ai kana iya jimawa baka waiwayemu ba Hammodi...I'm afraid.."
"Ba zan yi hakan ba Jadda. Da lokacin da kika so gani na, da lokacinda ma ba kya buƙata dani duk za ki riƙa ganina In Sha Allahu..."
Kallon Jaddi ta yi wanda shima duk ya yi wani iri ta ce.
"Alhaji miyasa ba zamu aura masa Noura ba??"
Wani irin waro ido ya yi a gigice ya ce.
"What!!"
Suma su Aunty Labiba a mamakance suka zuba ido suna kallonta, jin wata iriyar yasassar maganar da sam ba su tsammata ba.
Murya a karye ta ce.
"Ita ɗin er uwar ka ce Hammodi...ya kamata muyi hakan ko don ƙarfafar zumuncinka da en uwanka..."
Wani irin girgiza kai ya yi da ƙarfi tare da faɗin.
"This is a very bad Idea Jadda...ban shirya aure ba ni. Matata wacce nike da ita ta isheni komai...i can't do this to her."
"Hammodi!..babu wanda ya isa ya shiga tsakaninka da matarka. Duk kowa da yake nan yana sonta...amma dan Allah ka auri Noura..Alhaji! Mu'aƙƙib... Razia! Dan Allah kuyi masa magana mana! Ina so ya auri Noura. baiwar Allah ce mai matuƙar kirki da son ibada. Tun da Mijinta ya mutu yau kusan shekara uku kenan ta kasa samun farin ciki, ga marayun yara gareta. Ita ɗin 'ƴar uwar ka ce..."
Lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa ta shiga tsaka mai wuya domin har abada ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zai iya haɗa Bibinsa da wata macen ba. Wato a tare suka kitsa komai kenan? Tun da gashi babu wanda ya buɗe baki ya faɗa mata cewa wannan maganar da tayi ba akan daidaita take ba, Sam ba ta dace ba. Miyasa ma duk tsawon zamansa a gidan ba su kawo masa wannan zancen ba sai yau da ta kasance ranar rabuwar shi da su?
"Hammodi!!"
Uncle Mu'aƙƙib ya ambata sunansa a hankali sannan ya ci gaba da cewa.
"Tsawon shekaru baka tare da su. Alfarma Ƙwaya ɗaya! Ka daure ka cika musu ita dan Allah.."
Wai miye haka ne? Ya tambayi kansa ya yin da yaji ƙwaƙwalwarsa na neman zaucewa.
Daga irin kallon da Labiba ke musu kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa sam ba ta yi na'am da wannan maganar ba. Idan har zancen xumunci suke ai an gama ƙulla shi tunda ga shi kowa ya bayar da mutum biyu daga ɓangarensa. Gaskiya su Jadda ba su so gaskiya ba kuma muddin za ta faɗa masa ya ji to ba zai auri wata Noura ba.
Muryar Jaddi ya ji a tsakiyar kansa yana faɗin.
"Please kada ku matsa masa, idan ba ya so dan Allah kar ku matsa..."
Yana hango su Beenafah suna saukowa ya ƙara jin zuciyarsa ta sarƙafe da wani irin sabon ruɗani wanda ba shiri ya ɗagawa Jaddi Hannu da sauri ya ce.
"Please dan Allah ku bar wannan maganar, ga ta tana tahowa. Ku daina na roƙe ku....."
Da sauri na nufi mota da gudu ganin ya wuce kai tsaye ba tare da ya kira ni ba. Wata ƙila kuma fushi ya yi ganin na jima a sama ban sauko ba ya gaji da jira.
Ɗaga musu hannu na shiga yi ina murmushi kamar yanda suma suke min har muka fice daga gidan a raina ina jin wata irin kewar su tun ban bar garin na su ba.
Muna isa muka sauka wanda daman su Aunty Labiba daga nan Nigeria za su wuce, yayin da, ni, Ya Mohaa da kuma Hairi ne zamu wuce mu koma Dubai daga can ta wuce makarantar da take a Jami'ar Madina.
Hannuna Aunty Labiba ta riƙo idanunta cike da hawaye ta kalleni tana mai jinjina kanta ta ce.
"Ke ɗin Jaruma ce ta gaske Beenafah. Na yi imani daga inda kika faro da manyan jarabawowi har kika kawo nan to babu wani abu da zai tari gabanki wanda zai ba ki tsoro. Na gode da duk irin sadaukarwa da kika yi a gare ni Beenafah. Ina roƙon Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna ya ƙara muku danƙon soyayya a tsakaninku sannan ya ba ku zuria ɗayyaba."
Murmushi na yi mata yayin da nima ɗin na ji wasu irin hawaye sun ciko mini idona na ce.
" Amin yah Allah Aunty Labiba. Ina gaishe da Adeel da Hanan da su Hajiya....Aunty Nadeeyah. Ki barni na kiraki da shi na yau kawai. Allah ya kaiku lafiya ya sake sa da mu da alherinsa. Ina gaishe da su Dija."
Huggig ɗina Aunty Nadeeyah tayi itama da ruwan hawaye tab a kwarmin idonta muka yi bankwana. Duk budurin nan da muke yi Hairi na can tare da Suhaib suna ƙara zantawa yayin da Ya Mohaa da Emraan da kuma su Jaddi ke can suna wata maganar ta daban.
Su suka fara tashi sannan mu. Kallon Ya Mohaa na yi wanda duk ya yi wani iri wanda nasan bai rasa nasaba da kewarsu da yake ji a ransa. Tabbas ko ni nan wallahy rai na cike yake da kewarsu ballantana shi da ya kasance jinin su da ya shafe shekaru ba ya tare da su.
Hannu na kai na shafa gefen fuskarsa, cikin nuna kulawa na ce.
" Kana jin kewa ko? Uhm! Daman haka rayuwar take. Muna son masoyanmu muke rabuwa da su ba don hakan yana mana daɗi ba sai dai don wani dalili mai ƙarfi. Kamar dai yanda ka rabo ni da Ammie na wacce nake matuƙar ƙaunarta ba don na gaji da ita ba ba. To haka abun yake, Amma kuma a ko'ina suke masoyan namu suna zuciyoyinmu, ga kuma waya. Sannan idan an samu rarar lokaci, sai a yi ziyarci juna, in ma dai mu je, ko kuma su su zo gare mu..."
Ji ya yi lokaci ɗaya zuciyarsa na neman tarwatsewa tamkar gilashin da aka rotsawa falalen dutse. Hannayensa ya saka ya wani rungumoni har sai da na ji faɗuwar gaba ya riskeni jin wannan irin cakuma haka.
Shiru muka yi dukkanmu yayin da nake iya jiyo yanda zuciyarsa ke bugawa domin kunnena a daidai saitin ƙirjinsa yake.
Girgiza kansa ya fara a hankali tare da runtse idanuwansa tamkar mai tsoron kallon wani abu ya shiga tambayar kansa cewa. Miye yasa haka? Mi zai sa su yi masa haka? Sun san kuwa Wacece Beenafah a wurin sa? Akan me za su nemi su ƙirƙiri auren da wacce suke fighting akanta ma bata ƙasar? Auren nasa kwata-kwata kwana nawa ne? Miyasa wai mutane basa son a zauna lafiya ne...to ya ce mata me? Su Jadda sun bani mata don kawai su ƙara ƙarfafa zumuncinmu ko me? Ita ɗin fa yarinya ce ƙarama wacce bata san komai ba sai son a bata kulawa. Ta ya ya zai fara furta mata zancen wani aure alhali auren su ko shekara bai rufa ba? Impossible? Har abada abin da ba zai faru ba kenan? Da dai ya ɓatawa Bibi..to gwanda ya ɓata da kowa har abada....
✍️ OUM-AMEER ✍️