BABI NA GOMA
BA NI DA IKO...
©Fareeda Abdallah
***
Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.
In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.
10)
"Me kike nufi Binta?"
Malam ya tambayeta, hankalinsa a tashe da jin irin maganganun da ta caccaɓa masa.
"Kika ce zaman kanki kike yi, me kike nufi?"
Ya sake tambayarta da damuwa.
"Hmmm!"
Ta ce da murmushi a fuskarta.
"Malam kenan."
Ta sake faɗin haka, har lokacin murmushin da take yi bai bar kan fuskarta ba. Hannu ta sa ta ɗauko Humaira tana mata wasa, kamar baza ta sake magana ba, sai kuma ta ce
"Ai kuwa zaman kaina nake yi"
Tayi shiru sai kuma ta cigaba da magana.
"Ya sunan auren da miji bai san ci da shan matar da yake aure ba?"
Ta saka idanunta cikin nashi, lokaci ɗaya duk wani annurin fuskarta ya ɗauke ɗif.
"Tunda na haifi Humaira ka taɓa siya mata pampers? Ka taɓa siya min klin ɗin da zan wanke kayanta? Ka taɓa bani ko kwabo idan ba ta da lafiya?"
Taja nannauyar numfashi ta sauke, ta cigaba da magana cikin ɓacin rai, baƙin cikin da ta kwasa na wofintar da ita da al'amarinta da yayi yana dawo mata a zuciya.
"Duk ka ajiye waɗannan ma gefe ɗaya. Tsawon waɗannan watannin da ka daina raba kwana da ni kai kuma ba saki na kayi ba ko sau ɗaya ka taɓa tunanin ya nake rayuwa idan buƙatar ɗa namiji ya taso min?"
Sanyi jikinsa yayi, sanyi sosai kamar wanda aka sheƙa ma ruwan ƙanƙara. Lokaci ɗaya ya saukar da kanshi ƙasa, yana jin kunyar haɗa idanu da ita.
"Kai a tunaninka tunda kana kawo abinci, kuma matarka tana girki, ai nima dole zan ci abinci... Amma abinda ka manta shi ne kai ke aure na ba Ramatu ba, duk wasu hakkokina a kanka suke ba a kanta ba. Don haka hakkin in ci, in sha, a kanka yake. Ka taɓa tsayawa a gaban idanunka an zuba abincina an kawo min?"
Tana zuwa nan a maganganunta sai ta miƙe tsaye, ta saɓa ƴarta a kafaɗa, ta zo za ta wuce shi ta shige uwarɗakinta sai ta tsaya a saitin shi ta ce
"Dama tun kwanakin baya na faɗa maka, duk wani hakkin mace a cikin zaman aure na san shi. Ko tsufa nayi ba na jin zanyi zaman haƙurin da idan banyi wasa ba zan ja mu wuta ni da kai, balle kuma da ƙuruciyata. Kafin in haifi Humaira kai ma ka sani ƴaƴa uku na bari a wani gidan, ka ga kuwa don ita ɗaya baza ta riƙe min ƙafafu a gidanka ba. Duk tsawon lokacinnan da ka ga na zauna na zuba muku idanu watanni huɗu nake jira ya cika, domin shi ne ƙayyadadden lokacin da aka ce mace za ta iya jure rayuwa ba tare da mijinta a kusa da ita ba. Lokacin yana cika zan miƙa ka kotu Alƙali ya karɓa min takarda ta."
Tana gama faɗin haka ta shige ɗaki tana juya mazaunai.
Malam ya bi ta da kallo hankalinsa a tashe. A zabure ya miƙe tsaye, har ya kama hanya zai shiga cikin ɗakin sai kuma ya fasa. Fita yayi daga falon da sauri, ɗakin Ramatu ya nufa kai tsaye har yana harɗe ƙafafunta.
Ko sallama bai samu sararin yi ba sai da ya isa tsakiyar ɗakin.
"Ramatu? Kina ina?"
Ya ƙwala mata kira bayan ya ga ƴaƴanta ne zaune a tsakiyar falon sun yi kaca-kaca da shi da ƙasusuwan nama.
"Malam? Ka dawo? Ina zuwa."
Ta amsa daga can cikin ɗaki. Sai ga ta ta fito da sauri, ɗankwalinta a hannu tana ƙoƙarin ɗaurawa. Idanunta ƙozai-ƙozai ko kwalli bata saka ba.
"Malam lafiya kuwa? Irin wannan kira sai kace wanda aka biyo?"
Ta tambayeshi tana zazzare idanu.
Har ya buɗe baki zaiyi magana, sai kuma ya kalli yaran da suka zuba musu idanu, su kalle shi su kalli Innarsu. Sun baza kunnuwa suna jiran ya faɗa su samu na kwashewa a ƙwaƙwalensu.
"Ku wuce ku tafi ɗakin Hajiya yanzunnan"
Ya faɗa musu hakan cikin tsawa.
Ai kuwa ƙananan a guje suka fita, Zainab da Zakiyya da suka kasance manya kuwa tafiyar laƙaiƙaita suke yi har suka fita daga ɗakin.
Zainab ɗakin Hajiya ta wuce kamar yadda aka yi musu umarni. Ita kuwa Zakiyya ƙofar ɗakin ta maƙale, ta kasa kunne tana sauraren abinda za a ce. Daman ita ne kamar Ramatu ta yi kaki ta ajiye, kuma sai aka yi sa'a duk wasu munanan halayen Ramatu ta kwashe tsaf, har da ƙari. Shi yasa duk cikin yaran ita ce ƴar da Ramatu ta fi so da tsananin ƙauna.
"Ɗazu na aiko da cefane mai yawa. Me kika dafa mana?"
Malam ya tambayi Ramatu a nutse, bayan wata sashe ta zuciyarsa ta bashi shawarar ya bi komai a sannu.
"Hmmm kai dai bari Malam. Ai yau mun ci biredi mun yaga leda. Kanwa ta kar tsami ƙwarnafi ya kwanta. Kai baka ga yadda yara suka yi kaca-kaca da ɗakin ba? Allah dai ya ƙara buɗi Malolinaaa..."
"Amin. Me kika dafa na ce?"
Ya sake tambayarta, yana ƙoƙarin danne wani mahaukacin ɓacin rai da yake yunƙuro masa.
"Fate-faten dankalin turawa da nama da ƙashi da dagargajajjen ƙwai."
Ta amsa kai tsaye, da wani ƙayataccen murmushi a fuskarta. Don ita duk a tunaninta sunan abincin da ta faɗa ya bayar da cikakken ma'ana irin na ƴan birni masu kalolin girke-girken ƴan gayu.
"Muje turakar naka mana Malam. Dama fa yanzu nake cewa na san duk inda kake kana hanyar shigowa gida, in gama shiryawa in tafi maka da abincinka can, to ashe ma ka dawo. Mu je in biyo ka da abincin."
Tayi maganar haɗe da nufar gurin kwanonin abincinsa da ta jera a babban farantin silba ta aje can gefe ɗaya.
Ko da ta ɗauko ta juyo, sai taga har lokacin Malam yana tsaye a inda ta barshi yana kallonta da wani irin yanayi da ta kasa ganewa.
"Malam za ka ci abincin a nan ne? Idan a nan za ka ci sai in share yanzun..."
"Buɗe abincin in gani.
Ya umarce ta kai tsaye.
Farantin ta ajiye a ƙasa. Ta ɗauko kwanon samira da take zuba mishi abinci ta buɗe, sai ga wani irin abinci ya bayyana lakakaf a cikin kwano. Shi ba faten da aka zuba masa ganye ba, shi kuma ba faten da yayi kama da na doya ba. Wannan wani irin yanayi yayi mare kyawun gani a idanu, saboda asalin faten ma ya yi ruwa sosai.
Kuma wani shirme da tayi amma ita a ganinta salo ne gurin yin girkin shi ne, naman da ya aiko da shi na Rago ne, akwai ƙashi da yawa a ciki, har da irin ƙananun nan masu kamar Kwalba. Bata wani tsaya ta ware ƙashin ba ta juye gaba ɗaya akan faten dankalin da bata taɓa yi a tukunyarta ba sai yau, tana yawan gani dai a fakaice idan Binta za tayi ma Malam.
Ƙwai rabin kret da ke cikin cefanen kuwa bayan ta dafa, ta ɓare, ta zuba a baho, tafin hannunta tasa ta dagargaza ƙwan ta dinga mutsukawa tana cakuɗawa sai da ya zama kamar gari, sannan ta juye a cikin faten dankalin, ta dinga juyawa da ludayi tana tuƙawa da muciya tana sake farfasa gudajin dankalin har sai da ya haɗe yadda take so.
Jikinta ya ɗan fara sanyi ne ganin duk yadda ta ke ta kururuta daɗin da faten yayi yaranta sun kasa sakin jiki su sha duk kuwa da yadda suke da mugun cin abinci. Hadiza da ta matsa tana son sha kuwa sau biyu ƙashi yana kakare mata a maƙogwaro, daƙyar suke fitowa bayan ta ci uban wahala har tana amai. Don haka suka bi duk abincin da ta zuba musu suka dinga tsince naman ciki suna cinyewa. Ƙashi idan mai taunuwa ne sai su tauna su watsar a tsakar ɗakin.
Ganin yaran sun kasa sha, kuma wannan haɗe-haɗe ta tabbatar idan ya kwana zai lalace yasa ta tattara ragowar da yaran suka kasa sha ta zuba a kwanon silba, ta ƙara kaɗan a ciki ta ce Zakiyya tayi gudu ta kaima Aminiyarta Safiya ta dawo. Ta san duk kwaɗayinta Safiya ta dame ta ta shanye, ko za ta sha faten nan ta tsure da zawo ta san bazaiyi kwantai a gurinta ba.
Zakiyya ta dawo daga kai faten kenan, babu jimawa Malam ya shiga ɗakin.
Wani jiri da ya nemi kifa Malam da ƙasa yasa babu shiri ya dafe jikin bangon da yake kusa da shi. Hankalinsa ya ƙara tashi da ganin irin asarar cefanen da Ramatu ta ja mishi, don shi kam wannan abu mai kama da zawon dankali ko ɗanɗanawa bazai iya yi ba, ballantana har ya ci shi a matsayin abincin dare.
"Saboda Allah Ramatu tunda kike a gidannan in banda zuwan Binta na taɓa kawo miki dankalin turawa na ce kiyi fate?"
"A'a"
Ta amsa tana zumɓura baki. Sai kuma ta haɗe girar sama da ƙasa don kar ma ya ce zai kawo mata wargi.
Ganin ɗaurewar da tayi sai mamakinta ya ƙara kama shi.
"Amma dai kin san wannan abun da kika kira faten miye da miye asarar cefane kika yi min ko? Tunda akwai mangyaɗa a gidan me yasa baki soya dankali da ƙwan ba? In yaso shi kuma naman kiyi farfesun shi..."
"Haba Malam!"
Ta katse shi da ɓacin rai a muryarta.
"Shi kenan kuma ni bazan yi abu ka yaba min ba? Haka ake yi? Na ga dai girkin nan nima fa na iya shi, tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta. Kuma ma da ba makoyi ai gwani da ya ji kunya..."
"Haka ne"
Ya katse ta. A lokaci guda kuma yana dafe kansa da ya ji yana mishi wani irin ciwo kamar ana buga mishi guduma.
"Me yasa idan kika dafa abinci ba kya saka ma Binta?"
Da saurin gaske ta kalle shi, jin da tayi yana maganar Binta. Abinda ta manta rabon da yayi.
'Kar dai a ce aikin da Baba yayi akan Malam ya fara sanyi?'
Ta tambayi kanta a zuciyarta.
Sai kuma ta fara faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.
"In ji Bintar? saboda munafuka ce ita za ta ce maka ba na ba ta abinci? To ko da ma ace bana zubawa in aika mata da abincin ita me yasa ba ta fitowa ta ɗiba da kanta? Tunda dai ai ta san a tukunya nake barin ragowar abinci..."
Yana dafe da bango, ya fice daga ɗakinta zuwa nasa. Bazai iya da wannan hayagagar ba, in dai ba so yake ya faɗi a gurin ba.
A hankali yake tafiya saboda jiri da yake ɗibansa har Allah ya sa ya isa ɗaki lafiya bai faɗi ba. Ya daɗe zaune cikin shiru, numfashi yake saukewa a hankali, idanunsa a lumshe.
Kamar an buɗe mishi idanun zuciyarsa da ya daɗe a lulluɓe cikin duhu, sai tunani yake yi, na yadda shi da kanshi da hankalinshi, ya biye ma zugar Ramatu ya juya ma Binta baya.
Amma kuma bai taɓa tsammanin Binta za ta shaƙa sosai har haka ba. Ya zaci ko da ya ce ta bashi lokaci ya huce shi kenan ta tsaya zaman jiranshi, ya zaci kawai duk sadda ya huce ya waiwayota za ta karɓe shi hannu bibiyu, saboda ita mai haƙuri ce. Ashe ba haka al'amarin yake a ɓangarenta ba.
Yau tun da ya tashi da safe Binta tai mishi tsaye a ƙahon zuci. Sai tunaninta yake yi, da tunanin kyawawan lokutan da suka gabatar a baya tare da ita. Shi yasa ya kashe kuɗinsa yayi wannan cefanen, domin in dai ranar girkinta ne ta san duk salo-salo na yadda za ta sarrafa kalolin abinci irinna ƴan gayu. Ba ta ko tambayarsa me za'a dafa, duk yawan nama ko ƙwai ko dankalin da zai kawo ta san yadda za ta sarrafa su a nutse, kuma su bayar da ma'ana yadda ake so.
50% discount ga mutane 20. Akwai wata baiwar Allah da ta biya 10k ga masu karatu 20. Don haka masu saurin hannu su tura 500 ta 5407827015, FCMB, shaidar biya ta ***.
A mafiyawancin lokuta ma cefanen da ya zaci an ƙarar da shi a ranar, sai washe gari ko bayan kwana biyu idan girki ya zagayo kanta zai ga ta sake yin wani salon girkin na daban da ragowar wancan cefanen.
"Binta akwai tattali da iya sarrafa abinci."
Ya faɗa a fili. Sai kuma yayi ɗan murmushi. Ya yi kewarta, kewa ba kaɗan ba.
Ya wulƙita idanunsa a lungu da saƙo na ɗakin yana kallon yadda su kansu kayan ɗakin suka fice a hayyacinsu, saboda rashin samun gyara da ƙalƙala irin na ta.
"Binta akwai tsafta."
Ya sake faɗa a fili.
A hankali ya tashi ya zauna, yana tunanin yadda zai rarrashe ta ya shawo kanta cikin ƙanƙanin lokaci. Domin Allah yana gani shi da kansa da hankalinsa bazai taɓa iya sakin Binta ba.
Miƙewa yayi ya canja kayan jikinsa. Daga manyan kaya zuwa jallabiya mare nauyi na barci. Ya ɗauki turarukansa kala biyu ya feshe lungu da saƙo na jikinsa, turarukan da tunda ya daina shiga harkar Binta ya daina fesa su idan zai kwanta, ya maida su ma'ajiyarsu yana murmushi.
Fita yayi a ɗakin ya nufi ɗakin Binta, a ransa yake ta tsara kalaman da zaiyi amfani da su gurin rarrashinta. Yana daf da shiga ɗakin, Zakiyya da ta fito daga ɗakin Innarsu za ta je bayi ta ga wucewarsa.
Haɓa ta kama cikin mamaki da haushin Babansu a ranta.
"Shi ma dai Baba gaskiya ba ya kyautatawa. Wannan matar tasa kaman wata ƴar gwal ya kasa fita harkarta."
Tayi maganar ƙasa-ƙasa, da salon yadda Innarta ke yawan faɗe a gabanta.
Tana tsaye tana kallonsa har sai da taga shigarsa ɗakin Binta, akan idanunta ta ga ya rufo ƙofar. Ai kuwa bayin da bata shiga ba kenan, ta juya da sauri domin ta je ta kaima Innarta rahoton abinda ta gani.
*****
Duk da ta gama shirin yin barci amma bata kwanta da nufin yin barcin ba. Shimfiɗe Humaira take yi, cikin rashin sa'a sai ita ma barcin yayi awon gaba da ita. Wannan dalilin yasa sakaye ƙofarta kawai tayi, bata sa sakata ba.
Tana cikin barci kamar a mafarki kawai ta ji an ruƙunƙumeta.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"
Ta faɗa a fili, sai kuma ta buɗe idanunta da sauri a tsorace.
Ƙamshin Malam ta fara shaƙa, kafin tayi arba da fuskarsa a cikin ɗan taƙaitaccen hasken ɗakin. Ɗaure fuska tayi tamau, a zuciyarta take jinjina ƙarfin hali da ƙoƙarinsa.
"Miye haka kake yi Malam?"
Ta faɗa a fili. Sai kuma ta fara mutsu-mutsu tana ƙoƙarin ƙwace jikinta.
Tunawa da Humaira da ke kwance a gefenta yasa ta fara ƙirjinta ya buga daram! Da sauri ta waiga kan gadon tana neman inda ya aje mata jaririyarta.
"Kin ganta can, na ɗan matsar da ita ne kawai."
Ya amsa a tausashe, bayan ya lura da waigen da take yi.
Inda ya nuna mata ta kallah don tabbatarwa, sai taga Humaira na barci cikin nutsuwa, ya tare gabanta da bayanta da filo, don taji kamar mamanta ce a kusa da ita.
"Zan tashi, don Allah ɗaga ni."
Ta faɗa bayan ta gaji da mutsu-mutsun ƙwacewa shi kuma ya ƙi sake ta.
Ɗaga ta yayi kamar yadda ta buƙata, ita kuma ta miƙe tsaye. Sai kallonta yake yi cikin kayan barcinta jajaye masu kyau sosai, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur! Ɗan rungumeta ɗinnan da yayi shi kaɗai ya san halin da yake ciki.
Zuwa tayi za ta gitta ta gabanshi yasa hannu ya janyo ta da sauri, yana daga tsaye ya haɗe ƙirjinta da nashi. Yana jin yadda na shanunta suka ƙara cika da tsayuwa ƙam, domin babu bireziya a jikinta. Ba wanda zai ce ta taɓa shayarda yaro ɗaya ma balle huɗu.
"Haba Amaryata... Kiyi haƙuri ki yafe min mana don girman Allah..."
Malam ya faɗa a tausashe, ya wani karyar da kai yana kallonta abin tausayi kamar ƙaramin yaro matashi.
"Yafiyar me kake nema?"
Ta tambaye shi da sakakkiyar murya. Sai kuma tayi murmushi, ta shafa gefen kumatunsa yadda take masa yawancin lokuta
"Ba ka yi min laifin komai ba Malam..."
"Binta idan kin isa ki ci min girki a gidannan Allah ya tsine min albarka."
Muryar Ramatu ya ratso kunnuwansu daga can falo cikin tsawa da hargagi.
Kafin ɗaya daga cikinsu yayi wani yunƙuri tuni Ramatu ta yaye labulen ɗakin ta cuso kanta ciki, sai huci take yi kamar kububuwa.
"Idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri Bin..."
Idanun Ramatu sun rufe bata ga sadda Malam ya raba jikinsa da na Binta ba. Bata ga sadda ya nufo ta a haukace ba, sai saukar wani ƙaƙƙarfan mari ta ji a kuncinta na dama da gefen kunnenta na daman... Ɗif! Ji da ganinta ya ɗauke na wasu daƙiƙu.