BA NI DA IKO...

BABI NA GOMA SHA ƊAYA

by @fareedaabdallah

BA NI DA IKO...

©Fareeda Abdallah

***

Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.

In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.

11)

"Idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri. Haukarki da na jure kwanakin baya, idan kika ce za ki maimaita min irinsa yau na rantse da girman Allah sai na yi ƙasa-ƙasa da ke a nan gurin."

Maganganun Malam da suka sauka a kunnen Ramatu kenan bayan ta dawo hayyacinta daga gigitar azababben marin da ya wanka mata.

Da saurin gaske ta ɗaga hannu ta dafe kumatun da take ji yana mata wani raɗaɗaɗa kamar an watsa borkonu a ɗanyen ciwo. Hakan bai mata ba, ko da ta ji azabar bai ragu ba sai kawai ta ɗora hannu akai a gigice za ta ƙwallah ihu...

"Kina cewa uhmmm! A bakin aurenki."

Malam yayi gaggawar faɗa mata haka cikin tsawa, bayan ya lura da abinda take shirin yi.

Ai kuwa da saurin gaske ta gimtse bakinta. Ta sauke hannuwa biyu akai ta ƙara damƙe bakinta, hankalinta a tashe da jin kalaman Malam. Tayi gaba a ɗimauce, kamar za ta bangaje Binta, sai kuma tayi baya da sauri tana girgiza kai. Kawai sai wasu zafafan hawaye suka silalo daga idanuwanta.

Wannan shi ake ce ma a dake ka a hana ka kuka, ko kuma ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Ko da ta tabbatar bayan tsayuwa da sharɓen kuka babu abinda za ta iya yi, kawai sai tayi gaggawar ficewa daga ɗakin tana harhaɗa hanya.

*****

"Uhmmm"

Binta ta faɗa.

Sai kuma ta ƙara da jan wata gajeriyar tsaki, ranta a ɓace da shi kansa Malam ɗin da duk wani abu da ya shafe shi.

Ƙasa-ƙasa ya kalleta, ya ga yadda fuskarta ya ƙara murtukewa sai kawai ya ji jikinsa ya ƙara yin sanyi.

"Binta..."

"Don ya Rasulullahi ka shafa min lafiya Malam."

Tayi gaggawar katse shi cikin sauri.

"Wai halan ba ka gani ne? Yadda tun da na shigo gidannan matarka ba ta so na ba ta ƙaunata?"

Ya kasa amsawa, sai ma kanshi da ya kawar gefe ɗaya yana cije baki.

"Uhmmm! Kai ma ka san ba ka da amsar bayarwa Malam. A wannan lokacin dai ya kamata ka sama ma kowaccenmu abinda ranta yake muradi. Ni da ake tsiyar domin nima na gaji da auren nan Wallahi..."

"Haba Binta."

Ya katse ta hankalinsa a tashe.

"Ki bari mana don Allah... me yasa kike min irin waɗannan maganganun? Kin san ina son ki..."

Da sauri ta katse shi da cewa

"A da kenan"

"Ba a da ba, har yanzu, har gobe, har zuwa ƙarshen numfashina bazan taɓa daina son ki ba Binta. Don girman Allah kiyi haƙuri ki yafe min."

Ya ƙarasa maganar a marairaice.

Ko tari bata yi ba, ko kallo ma bai ishe ta ba. A madadin tsayuwa saurarensa ma sai ta tsiri ninke kayan Humaira ƴan ƙwaranni da suke ajiye a gefe ɗaya.

"Ko so kike in durƙusa miki?"

Yayi mata tambayar yana ƙoƙarin kai gwuiyawunsa ƙasa.

"Ai sai kayi."

Ta faɗa bayan ta aika mishi wani mugun kallo, sannan ta fice zuwa falo, ta ƙyale shi a cikin ɗakin.

Kan kujera ta zauna tana karkaɗa ƙafa, alamun da ke nuna a cike take fam! ƙiris take jira tayi bindiga.

Can sai ga shi ya biyo bayanta zuwa falon, jikinsa a sanyaye. Kusa da ita yayi niyyar zama, ai kuwa ta miƙe da sauri kamar ya cuna mata wuta.

Ya buɗe baki zaiyi magana tayi saurin ɗaga mishi hannu.

"Malam za ka fita min a ɗaki ne ko kuwa ni in fita in baka guri?"

Ganin yadda take huci, yasa bai ja da nisa ba ya miƙe tsaye

"Kiyi haƙuri. Ni bari in fita."

Har ya kai bakin ƙofar sai ya waiga yana kallonta, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur saboda damuwa.

"Ina dai sake baki haƙuri Binta. Duk ɗan'Adam ajizi ne, ki saka a ranki wannan abinda ya faru ajizanci ne irinna ɗan Adam. Na yi miki alƙawari in Allah ya yarda irin hakan bazai sake faruwa ba."

Bai jira amsarta ba ya fice daga ɗakin ya ja mata ƙofar.

******

Ɗanɗana garin maganin tayi ɗan mitsili a harshenta, jin da tayi irin mai zaƙin nan ne duk da akwai gafin saiwoyi a cikin ɗanɗanon sai kawai ta cigaba da lasa a hankali, ɗanɗanon maganin ya yi mata daɗi sosai a bakinta. Daman ita kamar sha zumamu take, duk inda zaƙi yake tana gurin.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta lashe garin maganin hannunta, ta ɗaga ledar ta sake zazzagawa a hannu ta lashe.

A karo na uku ta sake ɗaga ledar za ta zuba a hannunta da saurin gaske Aunty Sadiya ta ƙwace ledar tana harararta.

"Haba Binta."

Tayi faɗa tana ƙulle bakin ledar.

"Yanzunnan fa na gama faɗa miki da nono ko madara ake shan maganin. Amma kuma kin tasa shi gaba kina neman shanyewa a haka."

Da dariya a fuskarta ta ce

"Wallahi Aunty Maganin ne daɗi, na kasa daina sha. Kuma wai a yadda yake da zaƙinnan ne zaiyi aiki?"

Ta tambayeta da mamaki a fuskarta.

"Ni fa kinsan na faɗa miki Aunty ba kasafai maganin mata ya cika aiki a jikina ba, tun ina Kaduna na tantance haka. Shi yasa ma kawai na daina asarar kuɗaɗena tunda basa min aiki..."

"Ke! Waɗannan magungunan da kike gani sun fita daban. Ba irin waɗancan karikitan magungunan da kike sha bane waɗanda baki san me aka haɗa da su ba.

Wannan haɗi ne na musamman Baba Habibu yake musu, kin san Malami ne, sannan kuma yana da sirrin magani da ya gada tun gurin kakanninmu, ga shi shima ya kusa mutuwa amma bai baiyana mana mu ƴaƴansa ba.

Kin ga waɗannan magungunan da kike rainawa? Ta ɗaga wani gorar coke da ruwan magani rabi yake a ciki, ta ɗaga wata ƴar mitsilar kwalba da haɗin maganin matsi a ciki, ta sake ɗaga ƙullin wani garin magani ɗan kucili, yawansa bai kai ɗaya bisa huɗun cokali ba. Ta ɗaga ƙullin garin maganin da tun farko Binta ta ɗanɗana sannan ta cigaba da yi mata bayani.

"Su fa ƴan birni gani suke kamar sun san magani, sai dai abinda basu sani ba asalin magunguna da masu bada maganin suna ƙauye. Waɗannan magungunan da kike ganinsu a haka Wallahi raina kama ki ga gayya kenan. Duk yadda Kawu Habibu ke gidanmu yana haɗa magungunan nan bai taɓa bani ba, duk da nasha yi mishi maganar ya bani inyi amfani da su, amma sai yai ta min hanya-hanya.

Sai da Kawunki ya ƙara aure tukunna, dangi suka samu labarin yadda Amarya ta zama linzamin da ke juya kowa na gidanmu. Shi ne fa afujajan Kawu ya aikon da su na gwada...

Uhmmm! Wallahi ba boka ba Malam in dai kika yi amfani da magungunan nan sai dai ke kiji tsoron Allah, kar ki cutar da mijinki da abokiyar zamanki. Amma fa in dai so kike miji ya zame miki bi ta zai-zai to waɗannan magungunan su ne cikakken bayanin bi ta zai zai. Kuma wani abin burgewa da magungunan shi ne ko mijinki yana neman matan banza ne, kawai kafin ki karɓi maganin za ki faɗa ma Kawu mijinki na leƙe-leƙe, akwai abinda Kawu zai haɗa miki a cikinsu da in sha Allahu mijinki bazai ƙara jin daɗin wata mace da ba ta aurensa ba, a matan auren nasa ma ke ce za ki zama zara a cikin taurari. (Waɗanda suke buƙatar maganin da gaske su min magana a karɓo musu daga ƙauye. 12k na magani, 1k na motar kawo maganin daga ƙauye. Tested and Trusted. ***.)

Ko kema Binta in banda kin bani labarin yadda Malam ya juya miki baya gaba ɗaya na rantse miki da Allah bazan karɓo miki magungunan ba. Shi kanshi Kawu Habibu in dai mace tana da kishiya, kuma yana da labarin suna zaune lafiya to Wallahi ko nawa za ta bashi ba ya taɓa yarda ya bada maganin, idan kuwa kika ci sa'a ya baki to ya dinga jaddada miki kalmar ki ji tsoron Allah kenan. Don haka kar ki kuskura ki ce za kiyi sakaci da magungunan nan, idan kuma kin san baza kiyi amfani da su ba sawuna a likkafa ki bani in koma da su..."

"Ah haba Aunty."

Binta tayi maganar tana dariya, sai kuma ta fara ɗauke magungunan tana mayar da su cikin ledar da Aunty Sadiya ta je da su.

"Sai da kika gama lasa min zuma a baki kawai kuma sai ki wani ce ga zance ga magana?"

"Toh na sani ko baza kiyi amfani da..."

"Zan yi ma Wallahi."

Binta ta katse ta da sauri.

"Na gode Aunty. Allah ya bar ƙauna da zumunci."

"Amin Amin."

Aunty Sadiya ta amsa tana miƙewa tsaye. Goyon Humaira da tun da ta je gidan ta goyata ta kwance ta miƙa ta ga Binta.

"Ita dai Humaira ta mori haƙuri, Allah yasa dai ta ɗore har girmanta."

"Amin ya Allah Aunty."

Bata ƙara jimawa a gidan ba tayi mata sallama ta tafi.

Ta tafi kenan babu daɗewa sai ga Malam ya yi sallama a ƙofar ɗakinta.

Amsawa tayi, amma a yangace, kamar ba ta so. Fuskarta babu walwala ko kaɗan take kallonshi da manyan idanunta bayan ya shiga cikin ɗakin.

Ledoji ne a hannunsa, cefane ne yau ya kawo mata da kansa. Duk da ya ji zafin asarar da Ramatu ta jaza mishi jiya yau ma haka ya sake buɗe bakin aljinu yayi cefane Rigi-rigi.

Daga inda take zaune ta gane ledojin da ya shiga da su cefane ne a ciki. Ai kuwa ta sake ɗaure fuska tamau, da ƙyar ta danne zuciyarta ta iya buɗe bakinta ta gaishe shi sau ɗaya.

Bayan gaisuwar kuma sai suka yi shiru, kamar baƙin juna. Shi yana saƙe-saƙe da neman bakin zaren ta inda zai kamo ya fara yi mata magana, ita kuwa ta ƙi bashi fuska balle har ya samu ƙwarin gwuiwa. Sai cika take tana batsewa kamar ya matse mata guri.

Daga ƙarshe dai gwanin ban tausayi kamar ƙaramin yaro Malam ya fara magana cikin kame-kame da in-ina.

"Umm... Amm... dama... nannnce... cefane..."

"Cefanen me?"

Ta katse shi muryarta a tsaitsaye.

"Duk da dai jiya da cikakkiyar hausa nayi maka bayani kamar baka fahimci abinda nake nufi ba ko Malam?"

Ta sake tambayarsa a karo na biyu.

Sai kallonta yake yi ya kasa amsawa, sai tsamo-tsamo da ya ƙara yi a muzance kamar an tsoma kazar hausa a tafasasshen ruwa.

"Ina sake faɗa maka na daina girki a gidannan Malam. Ko dai matarka ta dafa idan taga dama ta sammin in ci, ko ta dafa kar ta sammin, wannan duk matsalarku ce. Aurenka ne dai lokaci kaɗan..."

Kafin ta ƙarasa maganar ya fice daga ɗakin da sauri, ba tare da ya ɗauki ledojin cefanen ba.

Ai kuwa ta dasa masifa tana faɗan baƙaƙen maganganu, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Kamar yana saurarenta haka ta dinga maimaita mishi irin wulaƙanci da tozarcin da ya dinga yi mata akan abinda ko kusa ba ta da laifi.

Tana cikin wannan masifar ta ji sallamar Hajiya a ƙofar ɗakinta, sai kuma tayi ɗif! Kamar ruwa ya cinye ta. Hajiya da ta fahimci halin da ta shiga sai kawai ta shiga ɗakin ba tare da jiran ayi mata iso ba, fuskar Hajiyar cike fal da murmushi.

"Hajiya ina yini? Au! Barka da yamma"

Binta tayi gaisuwar cikin daburcewa. Domin ganin Hajiya shi ne abu na ƙarshe da bata yi tsammanin za tayi ba a wannan lokacin.

Kafin Hajiya ta zauna, sai da ta karɓi Humaira da ke ta ɓangala mata dariya, yarinyar akwai wayau, sannu a hankali har ta fara gane Hajiya da Mamanta, daman su kaɗai ne suke ɗaukarta a cikin gidan.

"Lafiya ƙalau Binta."

Hajiya ta amsa gaisuwar a nutse. Kamar an ce Hajiya ta kalli gefe, sai taga ledojin cefanen da Malam ya ajiye kamar yadda ya barsu. Sai ta kawar da kanta ta maida kan Binta, ta buɗe baki za tayi magana Binta tayi saurin riga ta cewa

"Kiyi haƙuri Hajiya."

Sai kuma tayi narai-narai da fuska kamar za tayi kuka.

"Hajiya ƙara ta Malam ya kai miki ko?"

Tayi tambayar a shagwaɓe.

"Laaa... a'a! Ni ba ƙararki Balarabe ya kawo min ba Binta. Tattaroni yayi dai takanas ta kano wai in zo in taya shi roƙon ki yafe mishi."

A bazata wata matsananciyar kunya ta lulluɓe Binta. Ai kuwa da sauri ta kifa fuskarta a hannun kujera tana murmushi.

Cikin nutsuwa da tausasa harshe Hajiya ta cigaba da magana

"Kiyi haƙuri Binta. Don Allah kiyi haƙuri, ki yafe mishi kamar yadda ya nema. Duk da na san an cutar da ke, amma daman duk wanda kika ji ance yayi haƙuri lallai an cuceshi ne. A matsayina na uwa a gareku gaba ɗaya ina roƙonki don Allah ki sake bashi dama ta biyu... Idan ya sake maimaita irin wannan kuskuren na miki alƙawarin ni da kaina zan goya miki baya a duk irin matakin da kika yi niyyar ɗauka a kanshi. Kin ji ko?"

"To shi kenan Hajiya. Babu komai. In Allah ya yarda komai ya wuce."

Malam da yake maƙale a bakin ƙofa ta waje bai san sa'adda wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta suɓuce mishi ba. Hannu biyu yasa ya dafe saitin zuciyarsa, fuskarsa cike da murmushi. A zuciyarsa yake godiya ga Allah da jera mishi kalmomin yabo, domin duk da ya ɗauko Hajiya bai taɓa tsammanin Binta za ta yafe mishi da wuri haka ba.

Yana tsaye a gurin yana sauraren nasiha da godiyar da Hajiya ta ɗauki wasu daƙiƙu tana yi ma Binta. Daga ƙarshe ta rufe duk maganganun nata da addu'ar Allah ya dauwamar da zaman lafiya, ƙauna, soyayya, tausayin juna da fahimta a tsakaninsu.

Bai ankara ba sai ganin Hajiya yayi ta fito daga ɗakin, tana riƙe da Humaira a hannunta. Ganinshi yasa ta buɗe idanu da yanayin mamaki, har ta buɗe baki za tayi magana sai kuma tayi shiru, saboda hannu biyu da ya haɗa yana ta yi mata alamun roƙon kar ta tona asirin tsayuwarsa a gurin.

Daƙuwa tayi mishi, sannan ta yafito shi alamun ya zo, tayi gaba, shi kuma ya bi bayanta da sauri.

*****

Ya ɗauki tsawon mintuna goma sha uku yana riƙe da tafukan hannayenta a cikin nashi. Idanunsa da nata a rufe tsam-tsam, sai wasu irin surutai yake yi da wani irin yare da sam ba ta fahimtar me yake cewa, yana ta fallatsa mata miyaun bakinshi mai wani irin wari kamar na barasa.

Aka ce ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba. Duk da gajiyar runtse ido da riƙe mata hannu da yayi, da gajiyar wannan wawwaran miyaun da yake ta fallatsa mata a fuska har a saitin bakinta. Ko kusa bata ji a ranta za ta karya ɗaya daga cikin dokokin da aka kafa mata kafin shigarta cikin kogon dutsen ba.

Ba'a shiga cikin kogon da takalma biyu sai ɗaya.

Ba'a shiga cikin kogon da ɗankwali ko mayafi.

Idan za a shiga ciki za a rufe ido ɗaya ne a bar ɗaya a buɗe, ana zuwa tsakiyar kogon dutsen kuma za a rufe idanun duk biyu ruf, sannan a dinga tafiya da ƴar gala-gala(Wani kalar tsalle tsalle da yara ke yi a ɗage ƙafa ɗaya a dinga tafiya da ɗaya).

Idan aka yi umarnin a zauna ba a cema boka komai, hannu kawai za a miƙa masa cikin runtse ido, shi kuma zai riƙe hannuwan ya dinga surutan tsafi, a cikin wannan lokacin ne zai karanci duk wata damuwa da ta kai mutum gurinsa.

Tana wannan saƙe-saƙen ta ji an yarfar mata da hannuwa da ƙarfi. Sannan cikin tsawa aka yi mata umarnin ta buɗe idanunta.

Ai kuwa tana buɗe ido tayi arba da jajayen idanun bokan da saurin gaske ta sunkuyar da kanta ƙasa, zuciyarta na wani irin bugawa da saurin gaske kamar zai fasa ƙirjinta ya fito.

"Kin zo ne akan yarinya mai suna Binta, Matar maigidanki ne. Kina ganin ita ce matsalarki, saboda mijinki yana fifitata a kanki. Sai dai abinda baki sani ba shi ne, Binta ba ita ce babbar matsalarki da ƙalubalenki ba, matsalarki ita ce wannan."

Yayi nuni da yatsarsa manuniya a jikin bango, kamar a tv sai ga hoton Humaira ya bayyana tar-tar. Tana kwance akan gadon Hajiya tana barci, sai murmushi take yi a cikin barcin. Kamar a saka hannu a taɓo ta. Lallai tsafi gaskiyar mai shi.

Waɗanda basa telegram na buɗe group ɗin Whatsapp. Kuyi payment don samun damar kasancewa a cikin group.