BABI NA GOMA SHA SHIDA
BA NI DA IKO...
©Fareeda Abdallah
***
Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.
In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.
16)
Jikinsu ta ƙara haɗewa guri ɗaya, ta kamo kansa ta kwantar a ƙirjinta. A hankali take shafa gashin kansa, da murya ƙasa-ƙasa ta ce
"Waɗanda suke goranta maka akan abinda suka san ba ka da iko a kai, su ya kamata su shiga damuwa ba kai ba Malam. Domin abinda suke yi maka tamkar suna fito na fito da Ubangiji mai ikon bayarwa da hanawa ne, ka ga bayan nuna jahilcinsu a fili da suka yi, to fa lallai su shirya karɓan ƙalubale daga Allah ta inda basu taɓa zato ba."
Ta ja ajiyar zuciyar zuciya ta sauke, ta cigaba da magana a tausashe
"Sau da yawa za mu kasance muna tsananin son wani abu, amma wannan abun samuwarsa a gare mu ba alkhairi bane. Shi kuma Ubangiji Almusawwiru da yake ako wane lokaci ya fi son ya ba bayinsa musamman zaɓaɓɓu abinda bazai zama silar halakarsu ba, sai ya hana mu abinda muka roƙe shi muna so, ya musanya mana da abinda ya fi zama mafificin alkhairi a gare mu ba tare da saninmu ba.
Kayi haƙuri Malam. Ka kwantar da hankalinka. Ka ƙyale masu yi maka gori su cigaba da yi. Ka kyautata ma Allah zato, ka roƙe shi da yaƙini. Kasa a ranka idan da alkhairi a haihuwar ɗa namiji cikin ƴaƴanka tabbas zai baka, lokaci ne kawai baiyi ba. Idan kuma bai baka ba kasa a ranka babu alkhairi tattare da hakan. Ka cigaba da godiya ga Allah, ka saka ma ƴaƴanka mata albarka... Kayi musu addu'a mai kyau... Su zama ababen alfahari a gare mu iyayensu, al'ummarmu, da addininmu na musulunci."
Saboda tsananin daɗin da maganganunta suka yi mishi baisan sadda ya ƙara matseta a jikinsa ba, ya ɗago kansa ya sumbaceta a laɓɓa, ya ƙura mata idanu yana mata kallo mai bayyana tsananin son da yake mata.
"Na gode Binta."
Ya faɗa a hankali.
"Na gode da tunatarwa... Allah yayi miki albarka. In Allah ya yarda, daga yau bazan sake ƙorafi akan haka ba."
Ya faɗa da yanayin jin daɗin maganganunta da samun nutsuwa.
Hannu yasa ya ɗan matsa tausasan mazaunanta, sai kuma ya kai bakinsa daidai kunnenta ya fara raɗa mata wasu maganganu masu girma. A hankali fuskarta ya faɗaɗa da murmushi, can kuma sai ta fara dariya a sakalce tana ƙoƙarin ƙwace kunnenta, ai kuwa sai ya fara mata cakulkuli.
Yadda take ƙyaƙyata dariya, tana ɗan babbanƙarewa shi ne abinda ya ƙara kunna shi, ai kuwa daga wasa sai al'amarin ya fara juyewa zuwa gaske. Kasancewar Binta lafiyayyiyar mace ce, ga ƙuruciya, sannan ba ta wasa da shan ƴaƴan itatuwa, kuma tana yawan shan maganin sanyi, shi yasa ako wane lokaci Malam ya ce kule za ta ce Cas!
*****
Sau uku tana sallama a ƙofar ɗakin amma ba'a amsa ba. Har za ta juya, sai kuma tayi tunanin ɗaga labule ta leƙa, watakila barci take yi. Tana leƙawa sai ta ganta a zaune dingirgir, ta ƙura ma ƙasa idanu, ga Zakiyya zaune a gefenta tana yayyanka ƙyallaye.
"Assalamu alaikum"
Ta sake maimaita sallamar da tayi da ɗan ƙarfi, don ganin za su amsa ko baza su amsa ba.
Ga mamakinta kuwa basu amsa ba, sai ma tsaki da Zakiyya tayi ƙasa-ƙasa. Ita kuwa Ramatu ta ƙara haɗe girar sama da ƙasa tayi murtuk! Har lokacin bata ɗago kai ta kalli Binta ba.
"Uhmmm!"
Binta ta ce cikin takaici.
Har za ta isar da saƙon da ya kaita ɗakin sai kuma ta kasa danne ɓacin ranta, wani hali da ta koya tun sa'ilin da Ramatu ta zige Malam ya juya mata baya.
"Innar Zakiyya kenan. A ganina ko da gaba muke yi tunda har na sauke kaina ƙasa, na nema miki amincin Ubangiji ai ya kamata ki amsa min. Amma babu komai, duk da baku amsa ba mala'ikun Rahama da suka fi ku sun amsa min, don haka Alhamdulillahi.
Dama zuwan ba nawa bane, Malam ne ya ce in kira mishi ke, yana ɗakinsa yana jiranki."
Tana gama faɗin haka bata jira ko Ramatu za ta ce wani abu ba ta fice daga ɗakin.
Sai da aka ɗauki mintuna biyu, sannan Ramatu ta ja wani dogon tsaki kamar bakinta zai taɓi ƙasa.
"Aikin banza aikin wofi, ai Wallahi babu inda za ni. Idan shi Malam ɗin ya matsu da abinda zai faɗa min, ya zo har nan ɗakina ya same ni. Munafukai kawai."
Ta haɗa duk su biyun ta zaga, sai kuma ta ƙara jan tsaki a karo na biyu.
*****
Yana tsaye ya gama shiryawa, Binta ma tana tsaye a gabansa tana fesa masa sababbin turaruka kala biyu da ta siyo mishi tsaraba a Kaduna. Hular da zai sa yana kanta, ta kafa hular a kan ɗankwalin da ta ɗaura, sai ta ƙara kyau a idanunsa, domin shi a gurin Malam duk abinda Binta tayi mai kyau ne, kuma yana mata kyau.
"Wai kuwa kin faɗa ma Ramatu ina son ganinta?"
Ya tambaya, lokacin da take ɗaura masa agogo.
"Na faɗa mata."
Ta amsa
"Amma ina ga kila wani abin ne ya mantar da ita."
Ta sake faɗa don rufa ma Ramatu asiri, ganin an kwashi fiye da Mintuna ashirin babu Ramatu babu alamarta. Tun kafin yayi wanka, ga shi har yayi wankan, ya gama shiryawa.
"Ka zauna. Bari in sake sanar da ita."
Har ta juya za ta fita ya kira ta.
"Ƙyale ta kawai. Ko idan na dawo sai muyi maganar, yanzu lokaci ya ƙure..."
Buf! Sai ga ta ta banko labulen ƙofar ta shigo kamar wacce wani abu ya biyo. Har lokacin babu walwala a fuskarta. Sai a lokacin Binta ta lura da wani mugun rama da fuskar Ramatu yayi kamar wacce tayi amai da gudawa cikin dare. Idanunta gaba ɗaya sun faɗa ciki, fuskar nan ƙozai-ƙozai, alamun ko tsaka tsami bata samu yi ba balle uwa uba wanka.
"Ga ni."
Ta faɗa a tsaitsaye. Bayan ta aika ma Binta wani kakkausan kallo.
"Nima ga ni."
Malam ya faɗa da irin salon da tayi mishi magana.
A yanzu duk su biyun ta haɗa ta aika ma mugun kallo kamar ƙwayoyin idanunta za su faɗo ƙasa.
"An ce kana son ganina, idan kuma ba ka da abin faɗa ni ina da abinyi."
Ta sake faɗa cikin fushi.
Lokaci ɗaya ranshi ya fara ɓaci, tsaf ya karanci take-takenta. Don haka shi ma sai ya matse fuska. Ya buɗe baki zaiyi magana Binta da ke tsaye kusa da shi tayi saurin kama hannunsa. Ta matsa sau biyu, alamun kwantar da hankali a yaren soyayyarta, sannan ta sakar masa hannu tana mishi murmushi.
Ajiyar zuciya ya sauke, ya mayar mata da martanin murmushinsa, sai kuma ya matsa ya zauna akan kujera.
"Zauna"
Ya umarci Ramatu.
Sai da ta gama harare harare tana magana ƙasa-ƙasa ba sa jin me take cewa sannan ta zauna.
Binta ta kama hanyar barin ɗakin ya dakatar da ita.
"Ina za ki je min da hula a kanki?"
A tare su biyun suka yi dariya. Ita kuma Ramatu ta ƙara ƙulewa, ta cika tai fam! Ƙiris take jira tayi bindiga.
"Zo ki zauna, ai maganar da za muyi har ke ta shafa."
Kafin ta zauna, sai ta cire hularsa ta kafa mishi a kai, ta daidaita zaman hular, sannan ta zauna a gefensa.
Shiru ya ratsa gurin na wasu daƙiƙu. Malam sai kallon Ramatu yake yi yana karantar yanayinta, ga shi Binta ta hana shi magana, kawai sai ya girgiza kai.
"Dama Maganar kayan gado da kujerun Zainab ne..."
"Ni dai gaskiya tsakani da Allah ana gwada min iyakata da rashin adalci a gidannan. Saboda Allah za'ayi maganar auren ƴata sai a ce sai an shigo da wasu Karere?"
Da baki a ɗan buɗe yake kallonta.
"Waye Karere anan gurin?"
Ya tambayeta bayan ya kasa haƙuri.
"Ga ta nan kuwa a kusa da kai!"
Ta amsa gatsal, ba wani tsoro a muryarta.
"Idan gaskiya ne ai sai ta jira idan bikin nata ƴar ya taso sai tayi uwa tayi makarɓiya. Don haka gaskiya Malam ka barta ta fita."
"Babu inda za ta je. Sai dai idan ke ce za ki fita..."
Ai ko kafin ya rufe baki har ta fara tafiya zuwa waje.
"Na tafi. Idan girki ya zagayo kaina ma yi maganar."
Bata jira cewarsa ba ta fice daga ɗakin.
Baki buɗe suka bita da kallo har ta ɓace ma idanunsu, zukatansu cike da mamakinta. Kamar haɗin baki, sai kuma suka yi dariya a tare.
Dariyar da ya sauka da wani irin raɗaɗi a kunnen Ramatu da ta maƙale a bakin ƙofa tana son jin maganar da za suyi bayan idanunta.
"Wai kin san dama akan me na ce ki kira min ita?"
Malam ya tambayi Binta bayan sun tsagaita da dariyar.
"A'a!"
Ta amsa da murmushi a fuskarta.
"Ina zuwa."
Ya faɗa, sannan ya shiga cikin ɗakinsa.
Can sai ga shi ya fito hannunsa riƙe da baƙar leda. Ko da ya kwance, kuɗi ne masu yawa a ciki. Ya miƙa ma Binta ta karɓa, sai ya fara yi mata ƙarin bayani.
"Waɗannan kuɗin kayan Gado ne da kujeru da Katifa da za a siya ma Zainab. Dama na kira uwarta ne don in ji shawararta na inda ya kamata a siyi kayan. Amma tunda ta ƙi tsayawa ta saurare ni, na fita hakkinta. Ki riƙe waɗannan kuɗaɗen a gurinki, nan da sati biyu sai ki ɗauki Hajiya ku tafi Kaduna ku siyo kayan a can..."
Da wani irin matsanancin fushi da ɓacin rai Ramatu ta ɗaga ƙafa za ta koma cikin ɗakin, sai wata magana da Zainab ta faɗa mata a safiyar ranar ya dawo cikin ƙwaƙwalwarta kamar a lokacin take faɗa mata.
'Innarmu ko za ki kashe ni da duka bazan daina faɗa miki gaskiya ba... Ki ji tsoron Allah, ki ji tsoron ranar da Baba zai kama ki dumu-dumu kina yi musu laɓe... Kin dai san halinsa sarai... dama yaya lafiyar giwa balle ta yi hauka...? Ki rufa mana asiri... Sannan ki rufa ma igiyoyin aurenki asiri... Ni dai don Allah ina sake roƙon kiyi haƙuri ki kwantar da halinki ayi bikinnan lafiya, ki ƙyale Binta da Babanmu suyi abinda za suyi, watarana sai labari...'
Sanyi jikinta yayi lokaci ɗaya, a madadin ta shiga ɗakin Malam, sai kawai ta juya ta wuce zuwa ɗakinta. Gaba ɗaya hankalinta a ɗugunzume.
Duk da Zainab ta faɗa mata ita ta fi so Babansu ya ba Binta kuɗin siyayyar da zaiyi mata, a yanzu da ta ji da kunnenta Malam ya ɗauki kuɗin da bata san iya yawansu ba ya damƙa ma Binta, sai ta ji ranta ya yi mugun ƙuntata.
Ta fara sambatu a fili kamar wata zararriya.
"Wannan ma ai rainin wayau ne da rainin hankali... Ta ya za a ce auren ƴata a rasa waɗanda za suyi mata siyayya sai kishiyata? Kishiyar da ba ƙaunata take yi ba? Idan ta siya mata munanan kaya fa? Ko kuma ta ɓoye rabin kuɗin ta siya mata kayan rabin kuɗi? Gaskiya da sake."
Hijabinta ta zura ta ce ma Zakiyya tana zuwa, duk da bata tambayi Malam za ta je unguwa ba haka ta fice daga gidan.
*******
Lubabatu yayar Ramatu ce da suka haɗa uba ɗaya. Amma da yake mahaifiyarta ta bar gidansu Ramatu tun Luba na ƙarama, kuma ta tafi da ita, sai bata girma a nan cikin gidan Ubanta ba.
Ko da aure ya kawo ta garin Kasuwar magani kuma sai ya zama babu wani shaƙuwa sosai tsakaninsu da ƴan'uwanta. Ita ce ma ke yawan bibiyarsu su suna share ta. Sai dai kuma ita wayayyiyar mace ce, a Zariya ta girma, shi yasa idanunta ya fi na ƴan'uwanta buɗewa. Tana da yaranta biyar duka maza.
Tana da ilimi da zurfin tunani, shi yasa duk ƙananan maganganu da gutsuri tsoma irinna su Ramatu ita ba ta da shi. Daga ƙarshe ma da ta fahimci halinsu sai kawai ta fara janye jikinta daga gare su, ta kama kasuwanci da tarbiyar ƴaƴanta ka'in da na'in.
Ɗan Adam da ba'a iya masa kuma sai suka fara surutun tana gudunsu ƴan'uwanta, don ta ga tana samun kuɗi, kuma ga arzikin ƴaƴa maza da Allah yayi mata. Ita dai tasa auduga ta toshe kunnuwanta, wanda ya zo gidanta suyi zumunci, ita kuma duk abinda ya faru na daɗi ko akasinsa za ta je tayi musu jaje.
Kai tsaye Ramatu gidan Luba tayi ma tsinke. Bahaushe ya ce in tabi daga-daga na ƙurya ka sha kashi, ranar wanka ba'a ɓoyen cibiya.
Cikin kuka da shessheƙa Ramatu ta gama kora ma Luba labarin duk abinda ya faru tsakanin daren jiya zuwa wayewar garin yau.
Shiru Luba tayi cikin tunani, a zuciyarta take mamaki da takaicin yadda Zainab da Ramatu ta haifa ta fi ta hankali da hangen nesa. Wannan shi ne kuyanga ta haifi uwargijiyarta.
Da farko ta so ta rufe Ramatu da faɗa, amma sai tayi tunanin a wannan dokin zuciyar da Ramatu ta hau faɗa ko tashin hankali bazai sa ta fahimce ta ba.
Don haka kafin ta ce komai ruwan zafi ta tsiyaya a babban kofi, ta haɗa ma Ramatu tea mai kauri, sannan ta ɗauko wani ƙaton biredi ta ajiye mata a gabanta.
"Na san da wuya idan waɗannan damuwoyin sun sami barinki kin karya a nutse. Ki sha shayi, ina zuwa. Bari in soya miki ƙwai ki haɗa da shi."
Bata jira cewar Ramatu ba ta fice daga cikin ɗakin. Duk cikin ƴan'uwanta ba wacce bata san halinta ba, ita Ramatu a cikin halayenta akwai son banza, tana jin daɗi taga ta yi kwance kwance tana cin abin hannun wani, bayan ita kuma nata sam ba ya ciwuwa.
Ƙwai biyar ta soyo ma Ramatu ta aje mata a gabanta.
"Ki ci abinci a nutse. Barin sallami Baban Hamza in zo muyi magana."
Ko kafin ta sallami mijinta ta dawo Ramatu ta shanye shayin nan tas, ta ci Rabin biredi, ƙwan ma ta cinye tas! Har ta kishingiɗa akan ledan ƙasan ɗakin Luba tana mayar da barcin da bata samu yi jiya ba.
Dariya kawai Luba tayi ta ɗauke kofi, ragowar biredi da farantin da ta soya mata ƙwai ta fita zuwa tsakar gida ta kama harkokin sana'arta.
Tun misalin ƙarfe tara da rabi na safe, Ramatu bata farka ba sai ƙarfe sha ɗaya da Rabi. Lokacin hankali da nutsuwarta ya dawo jikinta. Bayan ta wanke fuska da baki, Luba ta ajiye mata gorar zoɓo da kunun zaƙi sannan ta fara yi mata nasiha da faɗa a fakaice, tana nunar mata illar abubuwan da take aikatawa, Waɗanda maimakon a sami daidaito da maslaha, sai ƙara damalmala al'amuran take yi.
"Kin ga dai yanzu ina amfanin zuciyar da kika yi? Ace kuɗin kayan ɗakin ƴarki da ya kamata ace ke ce jagaba a komai, a ɗauka a damƙa ma kishiyarki? Babban abinda nake so ki gane shi ne duk abinda haƙuri bai bada ba, rashin haƙuri bazai bada ba.
Ko kina so ko bakya so Malam Balarabe mijinki ne. Idan kuwa aka ce miji a sauƙaƙaƙƙiyar harshe ana nufin shugaba a gare ki, jagoranki, Ubangidanki.
Ta ina Shugabanki zai tausaya miki ko ya ƙaunaceki alhali babu girmamawa tsakaninki da shi? Duk girma da shekarunki ace baki iya magana ba Ramatu? Kina sakin maganganu kwaɓal kamar kin ci kashi ta ina zai ƙaunace ki? Ɗan kissa da kisisinar nan da ko wace mace take da salon irin baiwarta ke baki iya ba Ramatu? Binta da take ƙaramar yarinya ƙanwar ƙanwar bayanki ta fi ki fahimtar halin mijin da kika kwashe shekaru masu yawa da shi, gaskiya kin bani kunya Ramatu."
Shiru ya ratsa tsakaninsu na wasu daƙiƙu.
"Da gaske ne da ake cewa zaman aure sai da haƙuri. Amma haƙurin da ake faɗa ana ƙarawa bai kai yadda ake kururutawa ba. Rayuwar aure rayuwa ce mai daɗi da sauƙi, amma ga mace mai fahimta da sanin ya kamata. Kamar zaman duniya ce, idan kika ɗauketa da sauƙi, ta zo miki fiye da sauƙaƙawar da kike hange, idan kika ɗauke ta da zafi, sai ta zo miki fiye da zafafawar da kike hange.
Akwai tattaunawa a cikin aure Ramatu, ke da mijinki ku zauna ku tattauna matsololin da yake damunku. Idan ke ce da matsala kiyi ƙoƙarin gyarawa, idan shi ne da matsala ki faɗa mishi cikin tausasa harshe da iya magana, sannan ki haɗa da addu'a. Cikin sauƙi sai kiga Allah ya tanƙwara miki shi ya gyara duk abinda kike yi masa ƙorafi akai.
Duk da na san a cikin mazaje akwai marasa fahimta, musamman mazajenmu na ƙauye. Idan kika bi mutum ta lalama bai gyara ba, sai kiyi haƙuri, ki ci gaba da addu'a Allah yasa ya gyara, sannan ki ƙara da roƙon Ubangiji ya cire miki damuwa da al'amarin. Kin fahimce ni?"
Sai da ta ja nannauyar ajiyar zuciya sannan ta amsa da
"Na fahimce ki Yaya Luba. Kuma in Allah ya yarda zan gyara duk kura-kuraina."
Har ta yi shiru sai ta sake cewa
"To yanzu ta wace hanya kike ganin zan ɓullo ma batun siyen kayan ɗakin Zainab ɗin?"
"Wannan ki barshi a hannuna. Na san Balarabe mutum ne mai fahimta, zan zo har gidan naku sai muyi maganar, bama zan nuna masa kin zo kin faɗa min ba."
"To shi kenan Yaya Luba. Na gode."
Suka sake yin shiru, can sai Luba ta cigaba da magana
"Akwai matar da garin laɓe ta jiyo miji yana faɗa ma kishiyarta ya sake ta, kuma malamai suka tabbatar da ta saku. Ke ma irin abinda kike muradin ya faru da ke kenan ko?"
A kunyace Ramatu ta sunkuyar da kai, kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki don kunya. Domin da farko da ta ji Luba bata yi mata faɗa akan laɓen ba, ta zaci har ta bar gidan baza a tada maganar ba.
"Da gaskiyar bahaushe da yace duk ƙazantar da ba'a gani ba tsafta ce. Sannan abinda ido bai gani ba zuciya baza ta kai kanta ba. Laɓe ɗabi'ar kishi ce irinta jahilan mata na baya Ramatu. Ina haɗa ki da girman Allah ki daina, ba don ni ba, don Allah za ki daina."
"In Allah ya yarda... Bazan sake ba."
Ramatu ta amsa a kunyace.
"Idan kin je gida ki turo min Zakiyya."
Godiya mai yawa ta sake yi ma Luba, ta fita gidan da farin ciki. A zuciyarta take ji kaso sittin bisa ɗari na damuwarta ya yaye.
*******
Ko da girki ya zagayo kan Ramatu ta yi iya ƙoƙarinta ta danni zuciyarta, kamar yadda Luba ta bata shawarwari.
Wani abin burgewa da tayi har a gurin Malam shi ne yadda ta iya sauke kanta ƙasa ta bashi haƙurin abinda tayi masa ranar da ya aika kiranta.
Da mamaki ya a fuskarsa ya ce ya yafe mata. Haka ta kwana ɗaya cikin biyu na girkinta yana ta mamakin canjawarta, duk da yayi farin ciki sosai, amma bai zaƙe da yawa ba don ya san halinta.
Daren kwana na biyunta ne har sun kwanta shi ya yi nisa ma a cikin barci ta tashe shi. Yana buɗe ido, sai yayi saurin wartsakewa saboda ganin yadda ta kunna haske tar a cikin ɗakin.
Tana zaune a tsakiyar gado, tsirararta haihuwar gyatumarta. Da yake tana da ƙiba sai tayi wani shirim da ita.
Da sauri Malam ya kawar da kansa daga kallonta, ƙirjinsa na bugawa. A zuciyarsa yake addu'ar Allah yasa lafiya.
"Ramatu me ya faru?"
Ya tambayeta a ɗarare, bayan ya daure ya kalli fuskarta da yake ta maiƙo cikin haske.
Karyar da kanta tayi, a tausashe ta ce
"Malam gani nayi har zan fita kwanakin girkina biyu babu abinda ya shiga tsakaninmu na auratayya... Bayan kuma da can baya ba haka kake min ba."
Ta faɗa kai tsaye, a zuciyarta take tunano yadda da kunnenta ta jiyo irin sambatu da kukan da yake ma Binta idan suna auratayya.
Tana fata ita ma yau dai ta gwada irin salon Binta da har yake saka shi kuka, ita ma ta dinga sambatu da ihu mai ƙarfin da Binta za ta jiyo daga nan har cikin ɗakinta.
"Lafiya kalau Ramatu. Kawai dai ba na jin yin auratayyar ne. Kuma in banda abinki, ai ba wannan karon ne kika taɓa yin girki har kika gama ban kusance ki ba."
Yayi maganar yana sake kwanciya.
"Amma ai ba haka kake ma Binta ba."
Ta yi suɓul da baka wajen faɗin haka.
Kallonta yayi na tsawon daƙiƙu, kamar bazai ce komai ba sai ya ce
"Ya akai kika sani?"
Zuwa yanzu ta kai maƙura wajen gajiya da kwane-kwane. Kawai sai ta ce
"Da kunne na rannan zan je bayi naji kana mata kuka da sambatu kana faɗin irin daɗin da kake ji idan kana tare da ita. Kuma kusan kullum idan girkinta ne in zan je bayi ina jin ka... Nima ai mace ce, kuma matarka, gaskiya bazan yarda ba ni ma sai kayi min yadda kake mata..."
"Laɓe kike mana kenan Ramatu?"
Ya tambayeta a zafafe. Sai kuma ya miƙe zaune.
"Kalar zaren ai ba kalar yadin bane. Don haka ki cigaba da laɓe kina sauraren yadda nake yi da Binta, ke kam bazan yi da ke ba..."
"Wallahi baka isa ba Malam, bazan yarda ba. Ni gaskiya sai ka bani hakkina"
Ta faɗa kai tsaye, sai kuma ta fara matsar ƙwallah.
Ya kalleta, tayi wani shirim akan gado ba ko kyan gani. Nonuwanta har ciki, ga wani irin maiƙo da take yi kamar ta shafa mangyaɗa. Bai san sadda yayi tsaki ba ya ce
"Ai sai ki ƙwaci hakkin naki idan kina da ƙarfi."
Tsam ya sauka daga kan gadon ya koma falo. Tsawon lokaci yana jin ta tana kuka da ƙananun maganganu.