BA NI DA IKO...

20

by @fareedaabdallah

BA NI DA IKO...

©Fareeda Abdallah

***

Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.

In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.

20)

"Ina kike ƙoƙarin guduwa? Don kin ga yau bamu zo munyi miki talala ba shi ne har kike ƙoƙarin gudu da abincin ko?"

Aliya ta tambayeta cikin kaushin murya, sai dai kuma a fuskarta da murmushi. Kuma ƙasa-ƙasa tayi maganar don kar masu zurga-zurga a gurin su ji me ta ce ma Humaira.

"Ba guduwa zanyi ba Anty Aliya."

Humaira ta amsa a raunane, idanunta ciccike da hawaye take ɗan waige ko za ta ci sa'ar samun wanda hankalinshi zai kai kan abinda yake faruwa a tsakaninsu, cikin malamai ko ɗalibai.

Sai dai babu wanda ya kalle ɓangaren da suke tsaye ma, domin a bayyane yake a makarantar an san Aliya da Hadiza babansu ɗaya da ita. Da wannan dalilin kuwa don an gansu tare a killace ko suna tafiya babu wani malami ko daga cikin ɗalibai da yake tunanin za su iya cutar da ita.

Da ƙarfi da mugunta Aliya ta damƙo tsintsiyar hannun Humaira ta miƙar da ita tsaye. Ta ƙwace kwandon abincin da ke hannunta, tana riƙe da tsintsiyar hannunta tana matsewa tana tsungulinta ta ja ta suka fara tafiya.

"Na rantse da Allah tari kika yi sai na yanka ki da wannan sabon rezar da yake cikin jaka na."

Aliya da ta tsuguna kamar tana gyara takalmi ta faɗi haka ga Humaira a saitin kunnuwanta.

Da ƙyar ta iya ɗaga kai a wahalce. Ko kafin su isa inda suke ɓoyewa su cinye mata abincin basket ɗinta ita kuma su haɗa ta da garin rogon da kullum suke zuwa da shi idanunta sun kaɗa sunyi jajur!

Da rashin tausayi Aliya ta yarfar da hannuwanta, ai kuwa ta tafi da baya ta faɗi daɓas akan ciyayi. Tsananin buguwan da tayi yasa ta buɗe baki za ta yanka ihu, Hadiza da ke zaune kusa da ita da saurin gaske ta taushe mata baki da hijabi.

"Kina cewa 'uhmm' Saina shaƙe miki wuya kin mutu kowa ya huta."

A tsorace ta dinga mirgina kai alamun baza ta ce komai ba.

Sai da aka ɗauki tsawon lokaci Hadiza tana taushe da bakinta sannan ta sake mata baki.

"Koma can gefe ki tsuguna don ubanki."

Ta faɗa mata haka cikin tsawa.

Da rarrafe Humaira ta ja gwuiwa ta matsa can inda aka nuna mata.

Tana ji tana gani suka buɗe kular abincinta, doya ce da aka soya ta da ƙwai gwanin ban sha'awa a idanun mai kallo, doyar ta naɗi ƙwai sosai. Da saurin gaske ta haɗiye miyau muƙut! Mamynta ta san tana tsananin son doya da ƙwai, shi yasa mafiyawancin lokuta take yi mata ta aika mata da shi makaranta, sai dai kuma yanzu an ɗauki tsawon lokaci ko an kawo doyar akan idanunta Aliya da Hadiza suke cinyewa tas! Ko ladan ganin ido basa sammata.

Ƙasa ta saukar da idanunta, ganin yadda suke saka lomar doya da ƙwai suna lumshe idanu, irin alamun daɗi ya kai daɗi.

"Keh! Humaira! Za ki ci?"

Aliya ta tambayeta tana miƙa mata wani guntun ragowar doya da ke hannunta.

Da saurin gaske ta ɗaga kai, jikinta na rawa

"Eh! Eh! Zan ci... Don Allah ki sammin."

Ta faɗa cikin kyarmar murya.

"Zo ki karɓa"

Aliya ta ce mata.

Miƙewa tayi da sauri ta taho, sai dai tana isa kusa da Aliyar ta miƙa hannu za ta karɓa kenan tayi saurin lunƙuma doyar a baki. Su biyun kuwa me za suyi ba dariya ba.

Ita kuwa Humaira duk yadda ta kai ga dannewa a yanzu ba yadda ta iya sai da ta fashe da kuka.

"Za ki tona mana asiri ne don uwarki?"

Hadiza ta daka mata tsawa ƙasa-ƙasa.

Duk da ta ji tsoro, ta kasa daina kuka. Saboda baƙin cikin lokaci mai tsawo ne ya haɗe mata a zuciya.

Ƙyallin hasken Almakashi sabo dal da Hadiza ta fito da shi a cikin jakarta da ya ratsa idanunta shi yasa ta dafe bakinta a tsorace tana zare idanu tana girgiza kai. Ta ɗaga ƙafa za ta fara ja da baya Aliya tayi saurin damƙo kafaɗunta.

"Zo nan! Wallahi idan baki mana shiru ba da ki tona mana asiri gara ta yanka ki ki mutu mu huta da takaicinki."

Tana maganar tana nuna ma Humaira wuyanta da za a yanka.

Tsabar tsorata, yasa Humaira ta tafi luuu kamar za ta suma, saboda duk muguntar da suke gwada mata basu taɓa yi ra'ayil aini kamar da gaske za su yanka ta ba sai yau. Tsananin firgita yasa numfashinta ya kusa cayawa cik!

Da saurin gaske Hadiza ta mayar da almakashin cikin jaka ta ɓoye shi tsakanin littattafanta, ita kuwa Aliya da hannu ɗaya ta ɗauki gorar ruwan Humaira da suka rage kaɗan a ciki ta watsa mata a fuska.

Nannauyan ajiyar zuciya ta ja, sai kuma ta buɗe ido a firgice ta fara rarraba idanu a tsakaninsu.

"Don Allah... Kar ku yanka ni."

Ta faɗa a rarrabe, ƙarara idanunta ke bayyana yadda take tsoron mutuwa.

A daidai lokacin aka kaɗa ƙararrawar komawa aji. Da sauri Aliya ta durƙusa a kusa da Humaira ta juya mata baya.

"Hau baya in mayar da ke ajinku."

Da yake ba yau ne ta fara goya ta bayan sun zalunce ta ba, ba tare da tsoro ba ta je za ta hau bayan.

"Ke dallah tsaya in goge miki wannan mummunan fuskar naki kafin ki hau."

Hadiza ta faɗi haka tana harararta.

Bata ce komai ba, tsayawa tayi guri ɗaya tana kallonta da manyan idanunta da suka canja launi har ta goge mata fuskarta tas! In banda jan da idanunta suka yi ba wanda zai ce tayi kuka.

"Hau mu je."

Ta faɗa tana harararta a karo na biyu.

Sun kusa isa ajinsu Humaira sai Aliya ta canja hanya zuwa Ɗakin bada magani na makarantar

"Barin kaita a bata maganin ciwon kai. Kin san malamar nan tasu da bala'in sa ido. Tana ganin idanunta ya yi ja yanzu za ta fara mana tambaye-tambayen banza da wofi. Idan muka karɓo maganin kai tsaye sai mu ce kanta ke ciwo."

"Haka ne kuma! Kin yi dabara."

Hadiza ta faɗa tana murmushi.

Bayan sun karɓa mata maganin sun ba ta ta sha, sai suka mayar da ita ajinsu. Ai kuwa suna bada baya ta kifa kanta akan kujerarta ta fara hawaye, sai riƙe ciki take yi tana juye-juye ita kaɗai.

Yunwa take ji, yunwa ba ƴar kaɗan ba. Saboda zalunci yau ko garin rogon da suke ba ta ta sha basu bata ba. Da yake Humaira tana da kyakkyawan mu'amala da kowa a cikin ɗaliban nan da nan suka rufu a kanta. Ba matan ba ba mazan ba, kowa tambayarta yake me yake damunta.

Sai dai ta kasa amsa ma kowa, don bata san me za ta ce musu ba. Kukanta kawai ta cigaba da yi tana juye-juye, da saurin gaske Jamila yarinyar da suka fi shaƙuwa da ita a ajin tayi saurin fita ta kira malamarsu.

Ko da Aunty Murjanatu ta zo hankalinta a tashe, da kulawa ta rungume Humaira a jikinta tana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. Sai da ta ɗan rage kukan da take yi, sannan Aunty ta fara tambayarta me yake damunta.

Habawa...! Ba sai ta sake ɓallewa da kuka kamar an buɗe famfo ba. Tsam Aunty Murja ta kama hannunta suka fice daga ajin zuwa Ofis ɗinta. A kan kujerarta ta zaunar da ita, ta buɗe jakarta ta ciro ma Humaira lafiyayyen fura da nono da aka zuba a ɗan wani kofi mai murfi, ta buɗe kofin sannan ta miƙa mata.

A tausashe ta fara yi mata maganganu cikin rarrashi da kwantar da murya.

"Kiyi haƙuri Humaira Balarabe Sani. Ko me yake damunki ba kuka ne maganinsa ba. Ki daure, ki taushi zuciyarki ki faɗa min abinda yake miki ciwo in karɓo miki magani. Amma kafin nan ina so ki sha wannan furar, yanzu zan dawo sai ki faɗa min abinda yake damunki."

Aunty Murja bata jira ta amsa ba ta fice daga Ofis ɗin.

Jikinta na kyarma saboda tsananin yunwa ta kafa a baki, ai kuwa bata cire kofin daga bakinta ba, sai da ta shanye furar cikin kofin duk yawansa.

Nannauyan ajiyar zuciya ta ja ta sauke na samun nutsuwa. Mintuna biyu tsakani sai kuma ta fara kalle-kallen cikin ofis ɗin. Ba yau ne ta fara shigowa cikin Ofishin ba, amma bata taɓa tsayawa ta ƙare ma Ofis ɗin kallo irinna yau ba.

Can sai idanunta ya sauka akan jakar Auntynsu da ta bari a buɗe, ai kuwa sai ta hango gora da ruwa a ciki. Kamar ana tunkuɗa hannayenta da sauri ta janyo jakar, da farko ruwan ta ɗauka ta sha sosai sannan ta rufe ta mayar da ragowar.

Gurin mayarwar ne idanunta ya hango mata wani ɗan ƙaramin gwangwani mai kyau a cikin jakar, da sauri ta zura hannu ta ɗauko, ta fara jujjuyawa a hannunta tana kallo da idanu.

Bata san ko miye ba, kawai dai ita ɗan mitsitsin gwangwanin ya yi mata kyau a idanu. Tana cikin wannan yanayin sai ta ji motsin malamarsu za ta shigo, a maimakon ta mayar da abin da ta ɗauka, sai tayi saurin cusa gwangwanin a aljihun wandonta.

"Aisha Humaira Muhammad Sani."

Aunty Murja ta kira sunanta da murmushi a fuskarta.

"Ina fata yanzu kin shirya faɗa min abinda yake damunki?"

Aunty ta tambayeta.

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa yatsun hannayenta, kamar baza tayi magana ba. Can kuma sai ta ce

"Aunty dama cikina ke min ciwo. Amma yanzu da na sha fura na ji sauƙi."

"Kin tabbata?"

Aunty ta sake tambayarta. A zuciyarta kuma tana haɗa lissafin ɗaya bisa biyu.

"Da gaske na ji sauƙi Aunty."

"To ma sha Allah! Allah ya ƙara sauƙi. Za ki iya tafiya aji, ga ni nan shigowa."

Har ta fara tafiya sai Aunty Murja ta kira sunanta. A tsorace ta waiga, duk a tsammaninta Aunty ta ganta lokacin da ta ɗaukar mata abu a jaka ne.

Sai kuma tsoro da fargabanta ya baje lokacin da Auntyn ta ce

"Aisha Humaira yau Mamynki ta aiko miki da abinci kuwa?"

Nan da nan idanunta suka cicciko da hawaye saboda tunawa da abinda yayyenta suka yi mata. Kamar za ta ce ba'a aiko mata da shi ba, sai kuma ta ji tsoron kar Aunty Murja ta tura sakon me yasa ba'a aiko mata abinci ba zuwa ga mahaifiyarta. Don haka ta ce

"Ta aiko min da shi."

Har ta yi shiru sai ta sake cewa

"Ban ƙoshi bane. Shi yasa cikina yake ciwo."

"Ina basket ɗin abincin naki?"

Ta sake tambayarta.

A yanzu sai da muryar Humaira yai rawa kafin ta ce

"Yana... yana... yana gurin Aunty Hadiza."

"Ok...! Je ki aji."

Aunty ta bata umarni.

Humaira ta daɗe da tafiya Aunty Murja tana zaune cikin tunani. Ta rasa dalilin da yasa shanye kofi guda na furar da yarinyar tayi ya tsaya mata a zuciya.

"Sai ka ce wacce ta zo makaranta bata karya ba?"

Ta tambayi kanta a fili.

"Akwai wani abu. Tabbas! Kuma zan bincika."

Ta sake faɗa a fili.

Sai kuma ta watsar da tunanin ta tattara takardun da za ta buƙata ta wuce ajin da za ta ɗauke su darasi na gaba.

*******

Duk sadda aka tashi makaranta, akwai hanyoyin da suke a fili inda mafiyawancin ɗalibai suke bi idan za su tafi gidajensu.

Amma a ɓangaren Hadiza da Aliya da Humaira da suke tilasta mata tafiya tare da su basa bin hanyar da kowa ke bi, sun fi bi ta yanke, ta cikin gonakin jama'a.

Ba don komai suke hakan ba sai don su ɗauke hankalin mutane daga kan duk abinda za suyi mata. Ko yanzu ma suna ɓace ma idanun mutane Hadiza ta ja tunga ta tsaya, ta watsa ma Humaira wani mugun kallo sannan ta ce

"Uban waye bawanki a cikinmu da baza ki karɓi ɗan iskan basket ɗinki da jakunkunanmu ki riƙe a gurinki ba?"

Dama tun da suka taho ɗari-ɗari take yi, don ta san ba ƙaramin aikinsu bane su cire tsumagiyar sa maigida tsalle su tsuttsula mata a ƙafafunta.

Da saurin gaske ta kwashi jakunkunan ta goya a bayanta, duk da sun mata nauyi saboda text books ɗinsu duk suna ciki, haka ta dinga tafiya tana jan ƙafafu sai da suka kusa ɓullewa babban hanya sannan suka karɓi jakunkunansu.

Suna tafiya kamar maganar arziki suke yi Aliya ta cigaba da jaddada mata maganar da kullum sai sunyi mata bitarshi kamar karatu.

"Muna sake gargaɗinki dai Humaira. Wallahi Tallahi idan kika kuskura kika faɗa ma wani ko wata abinda muke miki na lahira sai ya fiki jin daɗi. Za kiyi mamakin irin masifaffen azabar da za mu gana miki."

"Uhmmm! Ai ke ce ma kika tsaya wani ɓata lokaci a kan jan kunmenta. Idan ta isa ta tona asirin namu mu gani."

Tayi ƙwafa mai ƙarfi, ta cigaba da magana

"Ki faɗi abinda muke miki kin ji ko Humaira? Hmm! Ai Wallahi kashe ki da nace zanyi kina ga kamar wasa da gaske ne zan kashe ki."

Ita dai Humaira bata ce komai ba, kanta yana ƙasa, a zuciyarta take addu'ar Allah yasa kar su haɗa mata da murɗe kunne wajen kashaidin. Sai satar kallon hanya take yi har suka isa gida. Suna shiga, ta fyalla a guje zuwa ɗakin Mamynta tana ƙwallah mata kira...