BA NI DA IKO...

21

by @fareedaabdallah

BA NI DA IKO...

©Fareeda Abdallah

***

Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.

In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.

21)

Har ta saka ƙafa za ta shiga ɗakinsu, sai kuma tayi saurin janye ƙafarta ta juya zuwa ɗan ƙaramin kicin ɗin Mamynta. Jikinta na rawa sosai ta ciro abinda ta ɗauka a jakar malamarsu ta ɓoye a kicin ɗin. Sai yanzu hankalinta ya fara tashi da abinda ta aikata, sai ga hawaye shar...

Da sauri ta sanya hannayenta ta ɗauke hawayen bayan ta jiyo muryar Mamynta tana ƙwallah mata kira.

"Oyoyo Mamynaaa.."

Ta faɗa da sanyin murya bayan ta shiga ɗakin.

Daga kan kujera mazaunin mutum uku da Binta ke kwance take ƙare ma Humaira kallo. Jikinta duk babu karsashi, ba kamar yadda ta saba dawowa ba.

"Mamana oyoyo. Me yake damunki?"

Ta tambayeta, sai kuma ta yunƙura ta miƙe zaune.

Humaira da take jin ta a ɗarare kamar Mamanta za ta ga abinda ta aikata a goshinta daurewa tayi ta ƙarasa ta zauna kusa da ita.

"Mamy... Yau a makaranta ne kaina yayi ta ciwo..."

Tana maganar a hankali. Kafin Binta ta ce komai sai ta cigaba da cewa

"Amma yanzu ya daina ciwon, an bani magani na sha a makaranta."

"Allah sarki Mamana."

Binta ta faɗa tana shafa kanta bayan ta cire mata hijabi da hula.

"Sannu! Allah ya ƙara lafiya Mamana. Amma kin tabbata kan ya daina ciwo ko in baki wani maganin?"

"Da gaske nake yi ya daina ciwo Mamy."

Humaira ta amsa.

Janyota tayi zuwa jikinta sannan ta fara cire mata kayan makaranta.

"Idan nayi miki wanka kika yi sallah da cin abinci sai ki kwanta da wuri. Na san har da gajiya ya janyo miki ciwon kan, idan kika samu isasshen huta za ki ƙarasa warwarewa."

Nan da nan Binta ta gama tuɓe mata kaya, ta barta da ɗan pant ta ɗauko ƙaramin tawul ta ɗaura mata. Suka fita tsakar gida Binta ta zaunar da ita akan ƙaramin kujera, ita kuma taje tana sirka mata ruwan wanka.

Ita dai Humaira tana zaune, duk inda Mamynta tayi nan take bin ta da kallo, babu abinda take tunani a zuciyarta sai

"Idan Mamynta ta gano abinda ta aikata wani irin hukunci za ta yi mata?"

Ta yi nisa a wannan tunanin Ramatu ta fito daga ɗakinta za tayi ma Halilu rakiya. Halilu almajirin Mahaifinta ne, irin almajiran nan da saboda tsananin daɗewarsu da ladabinsu har suka zama kaman ƴaƴan gida a gidan Malam. Tun yana ƙaramin yaro aka kawo shi, duk bayan shekaru biyu yake zuwa gaida mahaifansa ya dawo ga shi yanzu har ya kai shekaru ashirin.

Wani irin kallo da ya bi Humaira da shi yasa shi cin tuntuɓe da bokitin wankan Ramatu da aka ajiye a kan hanya.

"Subhanallahi! Yi hankali fa Halilu."

Ramatu ta faɗa, sannan ta kauda bokitin a hanya.

Ganin kamar hankalinshi ba ya kanta yasa ta mayar da idanunta inda yake kallo. Caraf! Suka haɗa idanu da Humaira da itama juyawarta kenan idanunta suka faɗa cikin na Ramatu.

Dogon tsaki ta ja kamar bakinta zai taɓa ƙasa. Ta aika ma Humaira wani kakkausan kallo, a tsorace yarinyar ta ɗauke idanu daga kanta.

"Uhmmm! Ai ina faɗa maka Halilu in dai wancan fitsararriyar yarinyar mai ƙwala-ƙwalan idanu ne baka ga komai ba daga fitsararta. Don ta ga baƙi a cikin gidannan ta ƙi gaishe su ai wannan ba komai bane a cikin munanan ɗabi'unta."

Ta ƙara jan dogon tsaki a karo na biyu, ta cigaba da surutun faɗi ba'a tambaye ki ba.

"Kuma ka san wani abu ne Halilu?"

Bata jira ya amsa ba ta cigaba da cewa

"A'amarin nata yana ƙara taɓarɓarewa ne bayan Allah ya haɗa ta da shaiɗaniyar uwa."

Tayi wata dariya irinta tsantsar rainin wayau. Sai ta kalli ɓangaren da Binta take kai da kawowa. Ta ƙara ɗaga muryarta sosai yadda za ta ɗaga ma Binta hankali ta cigaba da cewa

"Ai kai da ganin Kura an san za ta ci Akuya. Ƙaramin misali dubu yadda aka maida rayuwar yarinya ƙarama tun bata tafasa ba za ta ƙone, da kallon wannan ka san uwarta a kaɗan ne Allah ya tsareta da karuwanci. Uhmmm! Ai shi kam Malam Allah ya jarabce shi."

Ko kallo bata ishi Binta ba, balle har ta ɓata lokaci gurin maida mata amsa. Kamar ma bata san da wasu halittu a tsakar gidan ba, ta cigaba da hidimar gabanta.

Ita ma Ramatu jin ta taya ba'a siyar ba, ga Halilu da take mishi surutun bai tanka ba, sai ta sake jan dogon tsaki a karo na uku. Taja sanyayan ƙafafunta ta cigaba da tafiya zuwa rakiyar da ta fito da niyyar yi. Shi kuwa har ya fice a gidan bai daina satar kallon Humaira ba. Sama-sama suka ƙara yin sallama da Ramatu, ya fice daga gidan, zuciyarsa cike taf da tunani.

Wannan karon ziyarar da ya kai can ƙauyensu ya daɗe sosai kafin ya dawo. Saboda ya tsaya jinyar mahaifinshi, bayan doguwar jinya kuma sai Allah ya karɓi rayuwarsa. Mahaifiyarsa ta so yayi zamansa a gida tunda shi ne babban ɗa a gurinta aikuwa ya ƙi, a dole ta barshi ya dawo, bayan yayi mata alƙawurra masu yawa, ɗaya daga ciki shi ne lallai a ziyara na gaba zai je mata ne da labarin aurensa na jikar Malaminsa da yake nema.

A wancan lokacin da ya tafi, ya samu labarin Binta ta haihu daga bakin Ramatu. Amma bai taɓa katarin ganin ƴar da aka haifa ba, saboda babu shiri tsakanin Ramatu da Binta balle ya fake da haka ya je ganin ƴar.

Yau da ya ganta sai ya ji duniyarsa ta tsaya cak! na wasu mintuna... Da farko da ya ganta fa shi ya zata ƴar aljanu ce, saboda tsananin kyawunta... Fara sol da ita... Ga wasu dara-daran idanuwa farare kar kamar an ɗiga madara a ciki. Yadda take zaune tsaf a guri ɗaya a idanunsa ba ta ko motsi yasa shi zaton shi kaɗai ke ganinta.. Sai da Ramatu ta fara soki burutsunta sannan ya fahimci ashe ƴar gidan ce.

"Iko sai Allah... Taya akai Binta ta haifo ƴa mai kama da indiyawa?"

Ya tambayi kansa a fili.

Sai kuma yayi dariya, bayan ya tuna ita kanta Binta ai kyakkyawa ce.

"Amma gaskiya ƴarta ta fi ta kyau. Sosai ma... Wannan shi ne mai tashe kiyayi mai zamani."

Ya ƙarashe karin maganar yana dariya.

Har ya isa gida yana saƙe-saƙe a zuciyarsa.

******

"Keh! Hadiza"

Aunty Murja ta kira Hadiza, wacce ta riƙe hannun Humaira ƙam, tana jan ta don zuwa maɓoyar da suka saba zama su cinye mata abinci.

Ita kuma Humaira sai tana ɗan tirjewa kaɗan-kaɗan, kallon nutsuwa ɗaya za a yi ma Humaira a gane a tsorace take. Amma da yake kowa na musu kyakkyawan zato babu wanda ya gane a tsorace Humaira take, duk tsawon lokacin da suka ɗauka suna ɗauketa daga cikin ɗalibai sa'anninta babu wanda ya taɓa yunƙurin dakatar da su, sai yau da Aunty Murja ta dakatar da su da tsawa-tsawa a muryarta.

Ƙuuuuu...! Cikin Hadiza ya bada wani sauti a tsorace. Ƙara damƙe hannun Humaira tayi, ta juya baya tana kallon Malama, jikinta a sanyaye sosai.

Cikin nutsuwa Aunty Murjanatu take takowa har ta ƙarasa inda suke tsaye. Ta Kalli irin tsananin riƙon da Hadiza tayi ma Humaira, kanta tsaye ta saka hannu ta raba hannayensu. Tana kallon yadda Humaira ke jujjuya hannunta, alamun ta ji zafin riƙon ba kaɗan ba.

Aunty Murja ta ƙara ɗaure fuska tamau. Tana da son yara, amma fa idan yaro ya kaita bango ta iya horo mai tsanani. Shi yasa ɗalibai suna son ta suna tsoronta.

"Hadiza, me yasa kullum bakwa zama cikin ɗalibai ƴan'uwanku ki ci abinci?"

"Bbbbba komai Aunty."

Hadiza ta amsa da rawar murya.

"Daddddda yake Innarmu tana zubo mana abinci guri ɗaya ne shi yasa muke haɗuwa mu ci tare."

"Ku ci tare?"

Aunty Murja ta tambaya.

"To idan ana zubo muku abinci guri ɗaya me yasa kullum sai na ga almajirin da yake kawo ma Humaira abinci tun kafin shigowarku makarantar nan ya kawo mata?"

Shiru Hadiza tayi ba amsa, sai kawai ta sunkuyar da kanta ƙasa. Hankalinta a tashe, tsoronta ɗaya a tuhumi Humaira ta tona asirin duk irin zaluncin da suka ɗauki tsawon lokaci suna yi mata...

"Ba ni kwandon abincin in gani."

Aunty ta katse mata tunani.

Kamar ta ce baza ta bayar ba, sai kuma ta miƙa cikin sanyin jiki.

Aunty ta buɗe kyakkyawar kular abincin Humaira, sai taga lafiyayyar dafa-dukan shinkafa, da nama yanka biyu a sama. Sai dai abincin ƴar kaɗan ce, daidai cin Humaira.

Wani kakkausan kallo da Aunty ta aika ma Hadiza yasa kayan cikinta taruwa su ƙulle waje ɗaya.

"Wannan abincin daidai cin Humaira ne. Ina naku abincin da kika ce Innarku na haɗawa har da ita? Bayan haka kuma ita Maman Humaira bata san Innarku tana haɗo muku abinci bane da kullum sai ta aiko almajiri ya kawo ma ƴarta abinci?"

Tayi shiru tana zazzare idanu.

"Wallahi idan baki amsa min ba sai na tsinka miki mari..."

"Abincin... Abincin yana gurin Aliya."

Ta amsa a gigice tana ɗan ja baya.

"Mu je gurin Aliyar."

Tinƙis tinƙis Aunty ta bi Hadiza har maɓoyarsu, inda Aliya ke zaune dirshan ta cire hijabin jikinta tana jira a kawo mata abincin Humaira su cinye ita da ƴar'uwarta. Saboda samun guri ma yau ko garin rogon da suke zuwa da shi ƙin karɓowa sukai a gurin Innarsu.

Da yake Hadiza ce a gaba, kuma tana fara shiga lungun Aunty Murja ta ɗan tsaya a bayanta sai ta ji Aliya na zazzaga ma Hadiza masifa kan daɗewar da tayi, idanunta ya rufe ko lura da Aunty bata yi ba.

"Daɗina da ke wasu lokutan ke banza ce Hadiza. Kina sane dai yau ko karyawa banyi ba, yunwa nake ji sosai, kiyi ki taho da ita mu karɓe abincin shi ne za ki tsaya shashancin banza da wofi? Ina abincin?"

"Ga shi nan"

Aunty Murja ta fito daga maɓoyarta ta miƙa mata basket ɗin.

A tsorace Aliya tayi saurin miƙewa tsaye, kamar wacce aka hankaɗa baya, sai ta matsa da sauri tana ƙwalalo idanun rashin gaskiya. Idan ta kalli Hadiza sai ta kalli Humaira da take riƙe da hannun Auntynsu, sai kuma ta kalli Aunty Murja da take tsaye har lokacin tana miƙa mata basket ɗin Humaira.

Hannuwa biyu ta ɗaga sama alamun miƙa wuya, sai kuma ta fara ƙoƙarin kare kanta.

"Aunty Wallahi ba abinda kike tunani bane..."

"Ai kuwa dama ba abinda nake tunani bane Aliya Balarabe. Domin a tunanina shi ne kuna zaune da ƴar'uwarku da zuciya ɗaya, idan kuka keɓanceta daga cikin mutane kuna ba ta abincinta ne sai ta ci ta ƙoshi dam! sannan idan rage ta baku suɗin kwano. Ashe na yi kuskuren tunani, ba haka bane, idan kuka keɓeta abincinta kuke karɓewa ku cinye, ita kuma ko wane hali za ta shiga sanadiyyan yunwa babu ruwanku. Wannan wane irin zalunci ne?"

Ta tambaye su cikin tsawa.

Aliya da ta fi Hadiza tsoro ita ce da rawar jiki ta fara ba Aunty Murja amsa

"A'a Anty... A'a! Wallahi ba haka bane... Ki tambaye ta ma ki ji... Ke Humaira, ki faɗa mata muna baki abinci ki ci ko?"

Duk da zuciyar Humaira cike take da tsoronsu, sam ta kasa ba ta amsa. Jikinta sai rawa yake yi saboda firgici. Sai ƙara ƙanƙame hannun Auntynsu take yi kamar tana tsoron za su zo su ƙwaceta daga hannun Aunty.

Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Duk yadda Aliya da Hadiza suke ta ba Aunty Murja haƙuri ta ƙi saurarensu, nan da nan sai ga su a Ofishin shugaban makarantar.

Sai dai duk yadda aka kaɗa aka raya sun ƙi faɗan abubuwan da suke ma Humaira, sun kafe akan cewa abincinta kaɗai suke ɗiba su ci, shi ma ba kullum ba. Kuma duk ranar da suka ɗibi abincinta suna ɗiba mata nasu. Ita kuma Aunty Murja ta dage akan cewa zaluncin da suke ma Humaira ya wuce haka, duba da yadda gaba ɗaya yarinyar a firgice take da su.

Kuma a matsayinta na malamarsu sai a yanzu ne ma take tunawa ai an ɗauki lokaci mai tsawo da karsashin Humaira da ƙoƙarinta da walwalarta a makarantar suka canja gaba ɗaya.

A yanzu abinda ya rage shi ne Humaira ta faɗi gaskiyar abinda yake faruwa tsakaninta da ƴan'uwanta. Ita kuma ta kasa cewa komai, wannan kashaidi da yawan firgitarwar da suke mata har yanzu bai bar idanunta ba. A tsorace take da su biyun, tana ganin idan ta faɗa kamar za su kashe ta kamar yadda suka ce.

Al'amari dai tun yana faruwa a tsakaninsu har sai da kusan gaba ɗaya malaman makarantar suka taru a Ofishin. A lokacin ne da ƙyar Aunty Murja ta samu nasarar lallaɓa Humaira ta fara faɗin abubuwan da suke mata.

Gaba ɗaya malamai da shugaban makarantar sakin baki suka yi galala suna kallon Aliya da Hadiza, habawa! Su kuwa ganin da gaske ruwa ya ƙare ma ɗan kada ai sai suka fara rusa kuka, a zuciyarsu suke tsine ma Humaira da duk wani abu da ya danganceta.

Da fushi sosai a muryar Malam Habu ya daka musu gigitaccen tsawan da yasa suka ƙanƙame junansu suna sake fashewa da kuka.

"Ai baku yi kuka ba za dai kuyi. Wato a cikin makarantar nan ne har kun samu damar zuwa mana da almakashi kuna yi ma yarinya barazana ko?"

Da sauri cikin rawar murya Aliya ta ce

"Wallahi ba ni bace Sir. Hadiza ce..."

"Sir Wallahi ba ni bace. Ita ce tasa na ɗauko mata almakashin"

Hadiza ma tayi saurin faɗa da ƙoƙarin kare kanta.

Zancen wannan almakashi da aka ɗauko jakar Hadiza kuma aka tabbatar da shi a ciki shi ya ƙara zafafa almarin. Shawarwarin malamai akan hukuncin da za a yi musu ya rabu biyu.

Wasu suna ganin a hukuntasu kawai ba tare da an shigo da iyayensu cikin maganar ba. Wasu kuma suna ganin al'amarin ya yi girman da ya sha ƙarfin ace an hukunta su ba tare da sanin iyayensu ba.

"Gaskiya wannan babban al'amari ne Sir! Musamman da zancen kisa ya shigo ciki, ka dai ji abinda yarinyar ta faɗa, ko last week sun yi ƙoƙarin kashe ta, kuma a cikin makarantar nan. Babban abin damuwa da ban tsoro shi ne yadda yaran duk su uku babansu ɗaya. Ka ga kenan bisa ga dukkan alamu wannan ƙiyayya tasu ba a cikin makaranta ta fara ba, matsala ce da aka faro ta tun daga gida. Don haka babban adalcin da za muyi ma iyayen yarannan musamman mahaifinsu shi ne mu aika su zo a sanar da su abinda ke faruwa. Domin su gane ɓarakar da suka haifar a tsakanin ƴaƴansu lallai ta fara girman da idan basu ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki ba, to ba fata muke musu ba tabbas ko ba a nan makarantar ba al'amarin bazai haifar musu da ɗa mai idanu ba."

"Gaskiya ne Sir"

Sauran malamai gaba ɗaya suka goyi shawarar da mataimakin Principal ya kawo.

Ai kuwa nan take aka tashi malamai biyu aka aike su ƙafa da ƙafa zuwa gidan Malam Balarabe. Cikin sa'a sai suka tarar da Malam ɗin a gida, saboda a ranar ya tashi da ciwon kai.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya bi bayan malaman, duk da sun ce mishi ya bari zuwa washe gari sai ya je makarantar, tunda ba shi da lafiya. Amma ya dage kan lallai hankalinsa bazai taɓa kwanciya ba in dai ba ya je ya ji abinda ke faruwa bane.

Hankalinsa a tashe ya miƙe tsaye bayan gama jin abinda ya faru, sai kuma daɓas! Ya koma ya zauna akan kujera, da hannu bibiyu ya dafe kansa yana cewa

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Ya daɗe cikin shiru, ya rasa abin cewa, sai rarraba idanu yake yi a tsakanin Aliya da Hadiza. Zuciyarsa cike da mamaki da takaicin yadda ƙananan yara kamarsu suka iya haɗa kai suka yi tarayya wajen aikata zalunci mafi girma irin wannan.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Ya sake maimaitawa a karo na biyu. A kallon fuskarsa kawai za'a ƙara fahimtar matsanancin tashin hankalin da zuciyarsa ke ciki.

Principal da sauran malamai sai haƙuri suke ba shi, suna tausarsa da daɗaɗan kalamai na kwantar da hankali, har zuwa lokacin da ya ɗan samu nutsuwa.

Ya buɗe baki da ƙyar ya fara magana da yi ma shugaban makarantar da sauran malamai godiya.

"Na gode Malam Abubakar, na gode muku gaba ɗaya. Haƙiƙa na ji daɗi ƙwarai da kuka kira ni kuka sanar da ni al'amari mai girma irin wannan. In Allah ya yarda, zan ɗauki matakin da ya dace a ɓangare na. Sannan kuma ina haɗa ku da girman Allah yanzu a gabana kuyi musu hukunci mafi girma, hukunci irin wanda nan gaba ko da ba akan ƴar'uwarsu ba baza su ƙara tunanin kwatanta zalunci mai muni irin wannan ba."

Malam Hamisu, shi ne mai hukunta duk ɗalibi ko ɗalibar da tayi laifi mai girma a makarantar. Mutum ne da ya iya bada horo kala-kala ga ɗalibai, idan kuwa aka zo batun duka da bulala shi ne ƙarshe. Bulalarsa ta musamman ce, ɗaliban da suke matakin sakandire sun sha ɗauke bulalarsa, amma a washe garin ranar da suka ɗauke za su ganshi ya zo da wacce ta fi wancan da suka ɗauke azaba. Daga ƙarshe da suka fahimci kamar bulalai ne da shi masu yawa sai suka shafa ma kawunansu lafiya, idan ba wata mummunar ƙaddara da ba'a fata ba ɗalibai na matuƙar kiyaye laifin da zaisa a miƙa su gare shi.