22
22)
"Malam Hamisu? Bismillah fa"
Shugaban Makaranta Malam Habu ya kira shi da nufin ya zo ya hukunta su Aliya.
Ai kuwa nan take suka ƙara fashewa da ƙaƙƙarfan kuka. Duk da bai taɓa dukan ɗaya daga cikinsu ba suna da labarin irin azabar da ke cikin bulalarshi. Hankulansu bai ƙara tashi ba sai da ya fita ya dawo da wata doguwar bulala murtukekiya kamar ta dukan dabba.
Nan fa suka sake zubewa a ƙasa suna tumami da ban haƙuri, sai rantse-rantse suke yi akan baza su sake ba. Idan suka sake duk hukuncin da aka ga dama ayi musu.
"Ai baza mu jira ma ku sake ba. Shi yasa za'a hukuntaku yanzunnan, yadda nan gaba ko da kuɗi aka haɗa ku baza ku sake aikata irin wannan zalunci da son zuciyar ba."
Malam Hamisu ya yi maganar a fusace.
Ko a jikinsa duk da ga Mahaifinsu a zaune haka ya riƙo hannun Aliya da take babba, ya fara shimfiɗa mata bulala a gadon baya. A tare ita da Humaira da tsoro ya cika ma ciki suka fashe da kuka.
Da saurin gaske Aunty Murja ta ja Humaira ta fice da ita daga ofishin. Suna tafiya zuwa ajinsu suna jin muryar Aliya tana ƙwala gigitaccen ihu kamar za ta shiɗe.
Ita kanta Hadiza duk taurin zuciya irin nata tun kafin azo kanta har ta fara fita a hayyacinta, ba tare da saninta ba har fitsari tayi a wandon jikinta don tsananin firgici da tashin hankali.
Duk irin ihu, burgima da numfarfashi sama-sama da Aliya ke yi Malam Hamisu bai saki hannunta ɗaya da ya yi ma mugun damƙa cikin nashi ba don kar ta kuɓce sai da yayi mata bulala ashirin. A hakanma ya tsaya ne don Shugaban makarantar ya ce a barta haka.
Yana fara nufar inda Hadiza ta rakuɓe tana ɓare-ɓaren jiki ai kuwa sai ta ƙwalla ihu ta yanke jiki ta faɗi, sai kuma ta fara wani irin harbe-harbe da lanƙwashe lanƙwashen ƙafafu tana sambatun kar a sake a taɓa musu goɗiyarsu. A tunaninta idan tayi aljanun ƙarya Mal Hamisu zai ƙyale ta.
Sai dai rashin sani ya fi dare duhu, abinda bata sani ba shi kanshi Malam Hamisu kamar aljanin yake. Ai kuwa da fisge-fisgen da take yi da komai haka ya damƙo hannayenta biyu ya matse a hannunsa ɗaya, ya fara zabga mata bulala a bayanta da mazaunanta kamar wanda aka aiko shi, tun tana dannewa tana matsewa ita nan aljanu yake duka a bulala na bakwai ta buɗe baki ta fara kwarma ihu tana kururuwa da tsalle-tsalle, bai saki hannunta ba sai da yayi mata bulala ashirin da biyar.
Tun a bulala na ashirin Malam Habu yace ya ƙyale ta, shi kuwa ya dinga maimaita
"Bar ni da ita ranka ya daɗe, ai na yi bulala shida ba ita nake samu ba aljanunta ne, don haka sai na yi mata madadinsu."
"Ni ce... Wallahi tallahi ni ce. Na rantse da girman Allah ƙarya nake yi ba ni da wasu aljanu... Na tuba! Na bi Allah na bi ku... Don girman Allah ka ƙyaleni kar ka kashe ni. Bazan sake ba..."
Ire-iren kalaman da Hadiza tai ta furtawa kenan cikin ihun kuka, duk da haka bai ƙyaleta ba sai da ya kai ashirin da biyar.
Bayan wannan hukunci da aka yi musu sai da aka haɗa musu da dakatarwa na sati biyu cif! Da sharaɗin duk ranar da za su dawo su tabbatar sun zo da Mamansu da Babansu.
Godiya mai yawa Mal Balarabe ya sake yi, ya karɓi takardar dakatarwar tasu, ya tasa su a gaba suna tafe suna tangaɗi da jan ƙafafu ya tasa su a gaba suka tafi gida.
Ramatu tana tsakar gida tana surfe geron da za tayi fura sai ganin yaranta tayi sun shigo a jigace a magauce kamar sun yi haɗarin mota.
Hankalinta a tashe ta saki taɓaryar a ƙasa, ta ƙwala kiran sunayensu a gigice ta nufi inda suka zube a tsakar gidan suna rusa kuka.
Isarta kusa da su ya yi daidai da shigowar Malam cikin gidan, da jakunkunansu na makaranta a hannunsa, yana isa kusa da su bai ce komai ba sai watsa musu jakunkunan yayi a jikinsu. Babu alamar tausayin yaran ko kaɗan a fuskarsa, sai ma yayi haramar zagayesu ya wuce zuwa turakarsa.
"Malam lafiya? Me yake faruwa? Me ya faru da su?"
Ramatu da tayi saurin shan gabansa kafin ya bar gurin ta jera mishi tambayoyin hankalinta a tashe.
Wani kakkausan kallo Malam ya aika mata. Ya haɗiye miyau muƙut!
"Kauce min daga hanya Ramatu."
Ya faɗa mata da wani irin murya mai kauri da salon ba da umarni.
Har ta yi kamar za ta kauce saboda tsoratar da tayi. Sai kuma ta ja tunga ta tsaya ta riƙe ƙugu, a tunaninta ta yaya zai dawo mata da yaran da a saninta makaranta suka tafi, ba lokacin tashi ba, kuma ya dawo da su cikin mawuyacin hali, sannan ya ce bazai mata ƙarin bayani kan abinda ya faru da su ba? Itama ta tamke fuska tamau.
"Kamar yaya in kauce maka a hanya Malam?"
Ta harare shi ƙasa-ƙasa.
"Ya hausar in kauce maka a hanya bayan ka dawo min da yara cikin mawuyacin hali? Ai kuwa dai ba wani kauce maka a hanya da zanyi, ni gaskiya sai ka faɗa min abinda ya faru da yarana..."
A fusace ya ɗago hannu, kamar zai gaura mata mari, sai kuma yayi saurin runtse idanunsa yana janyo duk wata addu'a da ta zo bakinsa. Allah ya sani haushin Ramatu yake ji, haushinta ba kaɗan ba. Ba don komai ba kuwa sai don sanin da yayi wannan abinda ya faru kaso saba'in cikin ɗari laifinta ne.
'Mummunar tarbiyar da ta ɗora gaba ɗaya yaranta a kai na tsananin tsanar Binta da ƴarta shi ya fara jan gorar busar da zuciyar ƴaƴan har suka iya aikata wannan ɗanyen zalunci akan ƙanwarsu da suke uba ɗaya.
Har gobe Ramatu ta kasa yin hankalin iya yiwa bakinta linzami idan hankalinta ya nemi gushewa akan kishi. Har yanzu Ramatu ta kasa danne zuciyarta ta daina zagi da tsine ma Binta da ƴarta a gaban yaranta. A taƙaice ma, Ramatu tun yaranta suna ƙanana ba ta shayin faɗa musu ko wace irin mummunan magana akan Binta da ƴarta.
A yanzu kuwa da ƴaƴanta suka girma, su ne manyan abokan shawararta akan duk wasu hanyoyin da za ta bi wajen ƙuntata ma Binta da ƴarta. Da irin wannan mummunan hali na Ramatu ta yaya kan ƴaƴanshi zai haɗu? Ta yaya Ramatu za ta gane mummunar illar da tayi ma kanta da tarbiyar ƴaƴanta akan kishi? Kishin banza da wofi.
In banda shirme ma irin na wasu matan idan za suyi kishi me yasa baza su tsaya a kawunansu ba? Me yasa suke saka ƴaƴansu a cikin abinda bai kamata su shiga ba? Me yasa mata ire-iren Ramatu baza su danni zuciyarsu su raini ƴaƴan kishiya tsakani da Allah ko don inganta tarbiyar ƴaƴansu ba? Ko ma ba don haka ba, shin mata masu hali irinna Ramatu suna da tabbacin za su rayu da ƴaƴansu? Idan ma sun rayu da su ɗin, suna da tabbacin ƴaƴan nasu za su zamo masu jin ƙai a gare su sanyin idaniya a wurinsu?
Akwai mata da yawa da a ƙarshen rayuwarsu ba arzikin ƴaƴansu suke ci ba, arzikin ƴaƴan kishiyoyinsu ne. Ba fata yake yi ma Ramatu da masu hali irin nata ba idan hakan ta kasance ta ya za su tsinci alkhairi a gaba bayan basu yada a baya ba?'
Girgiza kansa yayi, fuskarsa na bayyana zallar takaicin halayen Ramatu da tun da ta canja bayan ya ƙaro aure har yanzu ta kasa gyara halayenta gaba ɗaya. Sai ta yi kamar za ta canja zuwa mutuniyar kirki, idan ta aikata wani abun kuma sai yaga ai kwata-kwata Ramatu ba ta ma da niyyar canjawa.
Kafaɗunta ya riƙe cak! ya matsar da ita gefe ɗaya. Yai wucewarsa ɗaki ba tare da ya mata ƙarin bayanin komai ba. Ya barta sake da baki tana bin shi da kallo, ranta a ɓace.
Wahalallen nishin da Hadiza ta ja da ƙyar ta sauke shi ya dawo da ita hayyacinta. Da sauri ta ƙarasa gurinsu tana jera musu sannu akai-akai kamar za ta ari baki. Ɗaya bayan ɗaya ta kama su da lallaɓawa ta kwantar a tsakar ɗakinta. Ruwan zafi ta ɗebo ta fara gargasa musu jiki, su kuwa sai wash-wash suke yi suna kuka gwanin ban tausayi.
*******
Ɗaya bayan ɗaya yake kallonsu, daga bisani kuma sai ya kafe idanunshi akan Ramatu, a zuciyarsa yake jinjina ƙarfin halinta.
Tun a jiya da abin ya faru bayan zuciyarsa ta sauka, kafin ya kira Binta yayi mata bayanin abinda ya faru ita Ramatu ya tarar har ɗakinta ya bata labarin abinda ya faru gaba ɗaya. Duk da ya san halinta da goya ma yaranta baya ako wane al'amari da ya faru, a wannan karon ya yi mamaki matuƙa gaya ganin yadda tayi tsalle ta dire ta ce atafau bata yarda da wannan abinda ya faru ba.
"Sharri ne... Idan duk jikina kunne ne bazan taɓa yarda Aliya da Hadiza sun aikata wannan muguntar ba. Haba! Haba!! Yaran duka-duka nawa suke? Su dai kawai malaman makarantar sun haɗa baki da uwar Humaira an ƙulla ma ƴaƴana sharri anyi musu hukunci da zalunci..."
"Ki daina cewa anyi musu sharri Ramatu."
Ya katse ta da sauri, yana ta ƙoƙarin dannar zuciyarsa kar su raba hali ga yara a falo.
"Ba'a zalunce su ba, a gabana a gaban sauran malamai da shugaban makarantar aka maida bayanin abinda ke faruwa. An tambayi Aliya da ita kanta Hadiza babu wacce ta musa abinda suka yi..."
"Yo dama taya za su iya musawa bayan an taru kansu anyi musu taron dangi ana zaginsu da muzantasu kamar sunyi kisan kai? Allah ya isa! Wallahi Allah ya isa!! Wannan mugun duka da aka yi ma yara na zalunci bazan taɓa yafewa ba..."
Sai kuma ta durƙusa a gurin ta fasa ihun kuka.
Ganin ba ta da niyyar fahimtarsa yasa shi ficewa a ɗakin da sauri. Ransa a ɓace da abinda Ramatu tayi masa ya nufi ɗakin Binta, ya tarar da ita tana ta fama da Humaira da take zazzaɓi tun da ta dawo daga makaranta.
"Me yasa baki faɗa min in siyo mata magani ba?"
Ya tambayeta da damuwa a fuskarsa.
"Kayi haƙuri. Da yake muna da maganin zazzaɓi sai kawai na bata ta sha. Dama a niyyata idan jikin nata bai sauka ba zuwa dare sai in faɗa maka a kaita allura."
Binta tayi maganar a tausashe.
Ajiyar zuciya ya sauke, yana jin ɓacin ransa na sauka kaɗan-kaɗan.
"Allah ya ƙara sauƙi. Mu je falo, ina so inyi magana da ke."
Ko da suka je falon bai ɓoye mata komai ba na daga abinda ya faru. Da farko kasa magana tayi, sai hawaye da take ta sharewa akai akai, fuskarta na bayyana matsananciyar damuwar da zuciyarta ke ciki.
"Kiyi haƙuri Binta. In Allah ya yarda hakan bazai sake kwatanta faruwa ba. Zan ɗauki matakin da ya dace, su ma can malaman sun sha alwashin ƙara saka ido sosai a mu'amalarsu..."
"Babu komai. Duk hakan ma bazai faru ba Malam. Ina ganin gara in canja mata makaranta kawai, tun kafin wata rana a kawo min gawarta."
Tana gama faɗin haka ta duƙar da kai ta cigaba da sharar ƙwallah.
Maganganu masu taushi ya dinga faɗa mata, da alƙawurra kala-kala na irin matakan da zai ɗauka don daidaita tsakanin yaransa gaba ɗaya. Sai dai har ya gaji da magana Binta bata ƙara ce mishi uffan ba! Ya fice daga ɗakin hankalinsa a tashe, jikinsa a sanyaye.
Tun jiyan bai ƙara saka Ramatu a idonsa ba sai yanzu, jiyan kuma ita ke da girki. Amma ko abincin dare bai gani ba balle yasa ran ganinta a shimfiɗarsa.
Haka aka wayi gari babu abincin kari balle na rana. Ko da ya aika Zakiyya ta ce mata ina abincinsa? cewa tayi
"Ki faɗa masa ina jiyyar ƴaƴana da aka kusa kashe su a gabansa bai ɗauki mataki ba. Abinci ne banyi ba, ko na dare ma bazan yi ba. Ke ki faɗa masa girkinma na ajiye sai ƴaƴana sun ji sauƙi."
Da yake kuma Zakiyyan girma ne ba hankali ta cika ba, yadda uwar ta biya mata haka ta zo ta karanta ma uban. Bai ce komai ba sai girgiza kai da yayi. Ko da ya je ɗakin Binta ita ma hana shi abinci tayi, a cewarta tana fama da kanta baza ta iya da tashin hankalin Ramatu ba.
Ransa a ɓace ya wuce gurin Hajiya, barci ya tarar da ita tana yi. Bai tashe ta ba ya fice daga ɗakin, a ƙarshe ma ya fice a gidan gaba ɗaya. Sai teburin mai shayi ya je aka dafa masa lafiyayyiyar indomie da ƙwai. Yaci yayi nak! Sai da ya idar da sallar isha'i sannan ya nufo gidan, zuciyarsa cike da saƙe-saƙen yadda zai ɓullo ma Ramatu da ƴaƴanta.
Yana shiga gidan, ya ci karo da Shamsiya ta fito daga banɗaki. Yafitota yayi, da tsayayyiyar murya yayi mata umarnin ta kira masa Ramatu, yana jiranta a ɗakin Hajiya yanzun nan.
Da kanshi ya leƙa ɗakin Binta ya kira ta zuwa ɗakin Hajiya. Sannan ya wuce zuwa ɗakin Hajiyar ya zauna, kafin shigowarsu ne ya fara bata labarin duk abinda ya faru.
Binta da ta fara amsa kiran, ta shiga ɗakin ne ta tarar da Hajiya tana kakabi da sallallami, ba ƙaramin girgizata labarin yayi ba. Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, abu ne da bata taɓa tsammanin yaran za su iya aikatawa akan bare ba ma balle wacce suke jini ɗaya.
"Ai kuwa lallai ya zama dole bayan hukuncin da aka yi musu a makaranta kai ma ka hukunta su a gida. Domin su ƙara gane girman munin abinda suka aikata, bayan haka kuma sai mu ƙara janyo su a jiki, mu bisu da addu'a da nasiha, da misalai na yadda ake tafi da rayuwa a sauƙaƙe don cin ribarta."
A daidai lokacin Ramatu ta shiga ɗakin da sallama ciki-ciki. Fuskarta a ɗaure tamau, domin ta daɗe tsaye a bakin ƙofa, duk abinda Hajiyar ta faɗa ta ji da kunnenta. A zuciyarta take ƙudurta gogayya da ko uban waye a cikin gidan matuƙar aka ce za a sake taɓa lafiyar jikin ƴaƴanta.