BA NI DA IKO...

25

by @fareedaabdallah

BA NI DA IKO...

©Fareeda Abdallah

***

Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.

In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.

25)

Juyowa tayi da nufin ta koma ta mayar da saƙon tunda tana ta sallama ba'a amsa ba, karaf! Kanta ya bugi mararsa, don yana tsaye kusa da ita ne, ita kuma bata sani ba.

Da saurin gaske ta ja da baya, a tsorace. Ƙirjinta sai bugawa yake yi saboda tsoratar da tayi. Lokaci ɗaya kuma sai idanunta suka ciccika da hawaye, tana kallonshi yana mata wani irin murmushi mai wahalar fassara ta miƙa mishi ledar da ya bata.

"Ina ta sallama ba'a amsa ba. Babu kowa a gidan, ga shi."

"Ai dama na san babu kowa a cikin gidan Humaira."

Yayi maganar yana dariya, har lokacin bai daina shafa mararsa da ta buga da kanta ba.

Wani irin kallo tayi mishi, nan take ya lumshe idanunsa da sauri saboda wani yam-yam da ya ji a jikinsa kamar ana yi mishi waiwayi.

"Zan tafi. Ga saƙonka."

Ta sake faɗa a karo na biyu.

Ganin bai karɓa ba yasa ta ajiye mishi a gabanshi ta kama tafiya da nufin wuce shi. Damƙo hannunta da yayi da ƙarfi yasa ta waiga a tsorace.

"Menene?"

Ta tambaye shi a tsorace.

Dariya yayi mata da faffaɗan bakinshi.

"Kina jin tsoro ne Humaira?"

Ya tambayeta da sanyin murya.

Kafin ta amsa ya sake cewa

"Ki daina jin tsoro. Bazan cutar da ke ba. Ni ɗan'uwan Mamanki ne, baki gane ni ba?"

Da sauri ta ɗaga kai alamar eh. Har lokacin tsoron da ke fuskarta bai baje ba.

"Allah sarki... Dama ba lallai ki gane ni ba. Ni ƙanin mamanki ne ta gurin kishiyar yayan ƙanin gwaggon baffan baban maman kakarta, kuma ba a ƙauyen nan nake zaune ba. A birni nake, idan ta je Kaduna wasu lokutan muna haɗuwa da ita a sada zumunci. Mu je ciki in baki saƙo ki kai mata."

"Ni dai a'a...! Ban sanka ba. Ka ƙyale ni in tafi aiken da aka yi min."

Tayi maganganun cikin rawar murya.

Bai saurareta ba, ya fara jan hannunta tana turjewa, amma saboda ƙarfin ba ɗaya ba duk turjewar da take yi sai da ya shiga da ita har cikin falon gidan. Babu komai a ciki sai kayan fentin da ba'a daɗe da gamawa ba. Sai kuma wata suɗaɗɗiyar tabarma da aka shimfiɗa ta can gefe.

Kan tabarmar ya je da ita ya zaunar da ita da ƙarfi, har lokacin bai sake hannunta da ya riƙe ba. Yayi amfani da ɗaya hannunsa ya zaro kuɗaɗe masu yawa a aljihunsa.

"Kin gani? Ki tsaya ki saurareni na ƴan mintuna kaɗan. Duk yawan kuɗaɗennan zan baki su. Ko bakya so?"

"Eh"

Ta amsa da sauri, jikinta na ta karkarwa kamar an jona mata shoking.

"To tunda ba kya son kuɗi zan siyo miki kayan daɗi, irinsu tsire, balangun Abdulhadi, da kaza, da farfesun kifi. Ke har kilishi ma zan siya miki in dai kika tsaya na ƴan mintuna kaɗan, wani abu kawai zan duba a jikinki..."

Shammatarsa tayi ta fincike hannunta ta miƙe tsaye zumbur! Ta ɗaga ƙafa za ta fyalla a guje yayi saurin sa ƙafa ya taɗiyota. Kirif! Ai kuwa tayi mugun faɗuwa ta ci ta baki, tsananin azaba yasa ta buɗe baki ta kwarma ƙaƙƙarfan ihun da ya sa Halilu saurin tashi tsaye ya janyota a gigice ya taushe mata baki.

"Don ubanki ba ki da hankali ne? Asiri za ki tona min tun banyi miki komai ba? Ai kuwa na rantse da Allah yau sai na biya buƙatata a kanki. Dama tun kwanakin baya da na ganki a gidanku raina ya biya da ke."

Yana maganar ne yana waige-waige, har Allah yasa idanunshi ya kai kan wani mummunan tsumma da aka gama goge fenti da shi. Kamar kayan wanki haka ya ja ta kiiiii zuwa gurin tsummar, yana ɗauka baiyi wata-wata ba ya yaga tsummar gida biyu, rabi ya tamke mata baki gam, ta yadda duk ihun da za tayi bazai taɓa yin ƙarar da zai fita waje har ya janyo mishi hankalin mutane ba. Rabin tsummar ya haɗe ƙafafunta waje ɗaya ya ɗaure gam, cikin rashin imani da tausayi.

Kan tabarmar ya mayar da ita ya kwantar, jikinsa na rawa ya koma ƙofar gidan ya kulle. Sannan ya koma inda ya barta, yana kallonta zafafan hawaye na gangara a gefe da gefen idanunta, shi kuwa sai murmushi yake yi. A zuciyarsa babu tausayinta ko misƙala zarratin, sai ma wani farin ciki na musamman da yake ƙara lulluɓeshi.

Tana ji tana gani ya murɗe hannayenta ya cire mata riga, gurin zare mata dogon wandon da ke jikinta ne ya faffalla mata mari saboda gardamar da take ta mishi, tana ta miƙe-miƙe da harbinsa da ƙafafunta tana kai mishi duka da hannuwanta.

Yana tuɓe kayansa yake zazzaga mata bala'i kamar wata sa'arsa.

"Yarinya idan za ki nutsu gara ma ki nutsu. inyi miki a hankali cikin ƴan mintuna in sallameki kiyi tafiyarki. Idan kuwa ba haka ba ɓalla ki zanyi sannan inyi abinda naga dama da ke. Domin na rantse da Allah yau ɗinnan babu wanda ya isa ya hanani kashe ƙishin ruwana a kanki. Dama wancan ƴar iskar yayar taki sai yawo da hankali take min, tana cinye min ƴan kuɗaɗena, duk da dai itama ba ƙaunarki take ba, don na keta ki ba baƙin ciki za ta ji ba. Amma ko babu komai zan rage zafi a kanki kafin ita ma Allah ya ɗora ni a kanta."

Kamar mayunwacin zaki haka ya nufe ta gadan-gadan bayan ya gama tuɓe kayansa tumɓur a gabanta. Ita kuwa tsananin tsoron ganin ƙaton namiji zirr a gabanta abinda bata taɓa gani ba yasa ta runtse idanunta da ƙarfi, sai numfashi take ja sama-sama, zuciyarta na mata wani irin suya da raɗaɗi, babu abinda take tunawa a ƙwaƙwalwarta sai maganganun da Mamynta ke yawan faɗa mata...

'Humaira, kinga da gurin fitsari, gurin kashi, ƙirjin mace ba'a wasa da su. Kuma kar ki bari kowa ya taɓa miki a duniyar nan. Ko ni da nake mahaifiyarki idan ba da ƙwaƙƙwaran dalili na rashin lafiya ba Allah bai yarda in dinga taɓa miki ba. Kar ki yarda ko da wasa wani ko wata ta taɓa miki. Duk wacce ko wanda ya ce zai taɓa miki kar ki yarda, ko da mutum zai kashe ki ne kiyi iya ƙoƙarinki ki ƙwaci kanki ki gudu. Ba fata nake yi ba, idan mutum ya fi ƙarfinki ya taɓa miki gurare ukun nan, lallai idan kika samu kuɓuta kika dawo gida ki faɗa min, kar ki taɓa ɓoye min halin da kike da kike ciki. Ko da mutum ya yi miki barazana da wani makami akan kar ki faɗi abinda yayi miki idan kin koma gida lallai ki faɗa min, ni mahaifiyarki ce, babu wanda ya kai ni son ki a duniyarnan. Kuma babu wanda ya isa ya kashe wani sai Allah da ya halicci rai...'

Tunaninta ya katse lokacin da ya damƙo fatar ƙirjinta da ko alamun ƙirgan dangi babu ya murza da ƙarfi, duk a ƙoƙarinsa na fara samar ma kansa nutsuwa.

'La'ilaha illallahu, Muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam.'

Tayi salatin a zuciyarta, saboda wani azababben zafi mai haɗe da raɗaɗi da ya ratsa tun daga ƙirjinta har zuwa ƙwaƙwalwarta. Ta yi tsammanin mutuwa za tayi, ta yi tunanin wannan azabar irinsa ne azabar fitan rai da malaminsu ya ce ko mutum mumini ne sai ya ɗanɗana.

Shi yasa tayi salatin, saboda tana riƙe da hadithin da aka karanta musu cewa: Duk wanda kalmarsa ta ƙarshe a duniya salati ne zai shiga Aljannah.

Daga nan tunaninta ya tsaya cak!

*******

Bata ƙara sanin inda kanta yake ba sai farkawa tayi ta ganta kwance a gadon asibiti. Hannunta maƙale da ƙarin ruwa. Goshinta da yayi mata wani irin nauyi ta ɗaga hannunta mare ƙarin ruwa ta shafo da ƙyar, sai ta ji an naɗe da bandeji, gefen bakinta ma an saka bandeji.

Ta wulƙita ƙwayoyin idanunta a cikin ɗakin, ita kaɗai ce kwance akan gado, sai Mamynta zaune a gefe ɗaya tana karatun Alƙur'ani. Ko da ta ƙure Binta da kallo sai taga idanunta sun faɗa sunyi zuru-zuru kamar wacce tayi ciwo, ta rame sosai, kamar ba Mamynta ƴar gayu kyakkyawa da ita ba.

Binta ta yi nisa a karatun da take yi cikin nutsuwa har bata san Humaira ta farka ba. Kamar a mafarki ta ji muryar Humaira ƙasa-ƙasa ta ce

"Mamynaa..."

Da saurin gaske Binta ta ɗaga kai ta kalli Humaira, ai kuwa tana ganin idanunta a buɗe ta miƙe tsaye jikinta na kyarma, ƙiris ya rage Alƙur'anin hannunta ya faɗi tayi saurin riƙewa da kyau.

"Mamana... Humaira... Kin farka? Yanzu me ke miki ciwo...?"

Sai hawaye suka ɓalle mata kamar an buɗe famfo.

A hankali Humaira ta ɗaga hannunta ta ɗora akan na Mamynta. Ta buɗe baki za tayi magana sai aka buɗe ƙofar ɗakin aka shiga ciki da sallama, Aunty Halima ce, Matar Kawu Bala. Ganin irin kukan da Binta take yi ga ta tsaye a gaban gadon Humaira yasa ta ƙarasa gurin da sauri ƙirjinta na bugawa.

Ko da taga idanun Humaira a buɗe nan take ta fara hamdala tana godiya ga Allah da ya farkar da ita lafiya, bayan ta shafe kwanaki uku cif! bata san inda kanta yake ba.

"Sannu Humaira. Allah mun gode maka. Alhamdulillahi! Kina ji na Humaira?"

Ko da ta buɗe baki za tayi magana sai ta ji kaman an riƙe mata harshenta. Kawai sai ta ɗaga kai alamar tana jin ta.

"To ma sha Allahu. Allah ya ƙara sauƙi."

Sai kuma ta mayar da hankalinta kan Binta ta fara rarrashinta.

"Don Allah Binta ki daina kukan nan da kike yi, in dai ba so kike ita ma ki ɗaga mata hankali ki saka ta kukan ba. A tunanina godiya ga Allah ya kamata muyi da yasa ta fara lafiya kuma cikin hankalinta, duk abinda zai biyo baya yanzu ai me sauƙi ne. Kin ga ni bari in je in faɗa ma Likita ta farka."

Da sauri ta fice daga ɗakin.

Daƙyar Binta ta iya tsayar da hawayen da take yi, idanunta cikin na Humaira ga hawaye ga murmushi a fuskarta, sai ƙara ƙanƙame hannun Humairan take yi a ƙirjinta.

"Mamana... Na gode ma Allah da yasa kika farka cikin ƙoshin lafiya. Sannu kin ji? Yanzu ina ne yake yi miki ciwo?"

A karo na biyu ko da ta buɗe baki za tayi magana sai ta sake ji kamar wani abu ya riƙe mata harshe, ta sake yunƙurawa maganar ta ƙi fita. Sai tayi rau-rau da idanunta tana nuna ma Binta bakinta, tayi mata alamun ta kasa magana.

Duk yadda Binta ta so ƙwarara kanta ta kasa, kawai sai ta kifa kai a gefen gadon da Humaira ke kwance ta cigaba da sharɓen hawaye. A cikin wannan halin Aunty Halima da Likita suka tarar da ita.

"Haba Maman Baby. Na yi tunanin tunda Baby ta farka yanzu shi kenan kuka ya ƙare?"

Likita ya tambayi Binta.

"Ai in dai Binta ne ka ƙyaleta da abin haushi Likita. Kukan farin ciki ne take yi tun sadda ta farka har yanzu ta kasa tsayar da kukan."

Aunty Halima ta faɗi haka ganin Binta ta kasa cewa komai.

Ita ta kama Aunty Binta ta matsar da ita daga gaban gadon domin ba likita damar yin aikinsa.

Ko da ya matsa gaban gadon murmushi ya fara yi ma Humaira, sai dai duk yadda ta so mayar mishi da martani ta kasa, saboda damuwar kasa magana da tayi. Shi kuma bai damu ba ya duba hannunta mai ɗauke da ƙarin ruwa, yana yi mata tambayoyi tana amsa mishi da kai.

Ko da ya tambayi me ya fi damunta a yanzu? Kanta ta nuna mishi da bakinta, shi kuma sai yayi tsammanin ciwon da ke gefen bakinta ne yake damunta.

"Sorry ko? Duk za su daina yi miki ciwo amma sai a hankali. Ki kwantar da hankalinki. Za ki warke very soon in Allah ya yarda."

Kai ta ɗaga mishi, alamun ta ji.

Gurin Binta ya juya da har lokacin take sharar ƙwallah ya ce

"Kiyi haƙuri Maman Baby. Ki daina kuka. Ki gode ma Allah da ya tserar da yarinyarki ba tare da an samu nasarar lalata mata rayuwa ba. Duk abinda zai biyo baya yanzu me sauƙi ne, da an samu nasara a kanta shi ne abun zai ta damunki yana ɗaga miki hankali, saboda mummunan abu ne dai zai ta bibiyarta har girma, aure, ƴaƴa da jikoki. Ki gode ma Allah."

Yana gama faɗa mata kalaman bai saurari amsarta ba ya fice daga ɗakin.

"Au...nty... Humaira ba ta iya magana..."

Binta ta faɗa cikin kuka.

"Nima na lura da haka Binta, maganarta zai dawo in Allah ya yarda. Abinda nake so da ke ki kwantar da hankalinki, idan maganar bai dawo ba har aka sallame mu muka koma gida za mu cigaba da magani ne ai. Na bakin likitan nan ne fa, mu gode ma Allah da yasa wancan tsinannen bai samu nasarar lalata mata rayuwa ba. Alhamdulillahi! Allah ya ƙara tsarewa. Maganarta zai dawo cikin ƙanƙanin lokaci in Allah ya yarda."

Ta cigaba da rarrashinta da tausasan kalamai, suna cikin maganar sai ga Hajiya da Malam Balarabe sun shiga ɗakin. Ganin Humaira idanunta biyu ba ƙaramin farin ciki suka yi ba, sai da suka fahimci ba ta iya magana kuma sai jikinsu ya ɗan yi sanyi.

Sai kuma suka cigaba da tattauna yadda za su cigaba da nema mata magani in har maganar bai dawo ba har aka sallameta daga asibiti. Domin abu ɗaya da dukkansu suka yi tarayya akai shi ne: Rashin iya maganarta ba ciwon asibiti bane, duba da abinda ya faru ranar da mummunar ƙaddarar ta kusa afka mata.

******

Yadda Halilu ya dage yana murzar fatan ƙirjinta yana gurnani shaiɗan yana daɗa iza shi yana ƙayata mishi kamar ya damƙi ƙirjin budurwa, bai lura da sadda Humaira da ya danne ta buɗe idanunta ba.

Sai dai idanun sun ƙara wani irin girma ƙwala-ƙwala kamar an zazzago su, ga su jajaye sosai kamar an tara jini a ciki. Yana cikin shauƙi a lokacin ya fara ƙoƙarin ware ƙafafunta sai ji yayi ta damƙi wuyansa da hannayenta biyu, tayi masa wani irin mummunar shaƙan mutuwa kamar an naɗe wuyansa da rodi.

Nan take ya fara jan numfashi da ƙyar, ya ɗaga hannayensa biyu ya riƙe nata hannayen da ke wuyansa yana ƙoƙarin ɓamɓare hannayenta amma duk iya ƙarfinsa ya kasa, a taƙaice ma ko motsi hannayenta ba sa yi.

Cikin ƙanƙanin lokaci Halilu ya fara jiyo ƙamshin mutuwa... Sai ga Halilu yana kakari da zazzare idanu, ya gama sadaƙarwa ajalinsa ya zo kawai sai ji yayi anyi hurgi da shi an maka shi jikin bango.

Wahaltaccen ƙara ya saki saboda tsananin azaba. Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa ya kalli inda Humaira take, sai yaga tana kwance yadda ya barta, kamar ba ita ce tayi masa wannan masifaffen shaƙar ba, jajayen idanunta ƙwalala da ta zuba mishi yasa shi kawar da idanunsa da sauri.

Yana sake waigawa ya saci kallonta sai ya ganta a zaune digirgir tana ƙara zazzaro mishi manyan jajayen idanunta. Ai da saurin gaske ya miƙe tsaye duk da masifaffen azabar da yake ji a gaɓoɓinsa. Yana sake yunƙurawa a karo na biyu ai sai yasa gudu, habawa!!! ƙafa me na ci ban baka ba?! Kamar walƙiya ya fice daga ɗakin a guje.

Gidan da ke gaba kaɗan da gidan da Halilu ya shigar da Humaira, gidan wata Amarya ce mai suna Fatima. Da yake unguwar duk sabbin gine-gine ne. Ɗaiɗaiku ne akwai mutane a ciki.

Tun ihun da Humaira tayi na farko Fati ta ji, tsoro ne sosai ya kamata, ga shi mijinta ba ya nan. Ya tafi masallaci sallar magriba. Haka tai ta zagaye a tsakar gida hankalinta a tashi har zuwa sadda mijinta ya dawo.

Ko da ta sanar da shi abinda yake faruwa bai ɗauki abin da muhimmanci ba, sai daga baya da suka ji ihun da Halilu yayi, ai kuwa da sauri ya fita ƙofar gida Fatima ta zura hijabi ta bi bayanshi, gaba ɗaya hankulansu a tashe.

Sun ɗauki wasu mintuna suna zagaye ta bayan gidan, daga bisani kuma suka yi ƙumajin zuwa ta ƙofar gidan, sai suka ga ƙofar a buɗe, lokacin Halilu ya riga ya fice. Duk da haka basu shiga kai tsaye ba suna ta raɓe-raɓe da ƙatuwar sanda a hannun Awaisu mijin Fatima har suka shiga falon gidan.

Anan ne suka tarar da Humaira a kwance tana ta wasu abubuwa irinna masu aljanu, an kanannaɗe yatsun hannaye da ƙafafunta kamar kuturwa. Da gani an san aikin jinnu ne.

"Humaira? Wannan ai kamar Humaira ce ƴar gidan Anty Binta?"

Fatima ta faɗa da sauri tana ƙarasawa gurinta.

Duk yadda Awaisu ke ta gargaɗin tayi baya kar aljanu su make ta ƙin matsawa tayi, a jikinta ta rungume Humaira tana tofa mata duk wasu addu'o'i da suka zo bakinta. Sai da ta lafa da miƙe-miƙe da lanƙwasheta da ake yi sannan Fatima ta mayar mata da kayanta da ke yashe a tsakar falon, Awaisu ya saɓa ta a kafaɗa suka fice daga gidan.

Daga nan gidan Kawu Bala suka kaita saboda ya fi kusa. Daga can ne aka wuce da ita asibiti, sannan Anty Halima taje har gida ta sanar ma su Binta halin da ake ciki.

"Fyaɗe aka yi mata?"

Inna Ramatu da zancen ya shiga kunnenta ta zo gittawa tayi maganar da ƙarfi.

Babu wanda ya tanka mata a cikinsu. Kawai sai ta gyaɗa kai tayi gaba, a zuciyarta tana jinjina maganar da ta ji da kunnenta. Lokaci ɗaya kuma tana tunanin yadda za tayi amfani da wannan fyaɗen da aka yi ma Humaira ta tarwatsa duk wani cigaba ko ɗaukaka da zai faru da rayuwar Humaira da ita kanta Binta...

ƘARSHEN FREE PAGES. Masu son labarin su tura kuɗinsu a account ɗina da ke sama domin mu cigaba da tafiya tare. Akwai paid group a whatsapp da telegram