TAZARA

Chapter 3

by @reza12

TAZARA

©By S-Reza...✍️

My Whasop Chanal

Chapter 3️⃣

Mutumin ya ce "Kaga bari ni na raba wannan matsalar, akan ɗari biyar dai ai ba kayi faɗa da Mace kuma yarinya ba". Ya fara ƙoƙarin saka hannu ya ɗauko kuɗin Abida ta ce "Malam barshi kawai, idan ma cutata yayi Allah ya isa ban yafe ba, kuma in sha allahu sai wannan shagon naka ya lalace, mugu kawai mai halin mugaye". Ta na faɗa ta ɗauki ɗari biyun da Fantasy ɗin ta, tayi waje, tana jin yadda mutumin nan ke kiran ta akan ta zo ya bata ɗari biyar ɗin amma sai ƙara sauri take. A bayan gidan su Yusra ta same shi yana jiranta. Tana zuwa suka tafa ya ce "Ina tsaye anan Yakubu ya fita, muyi sauri kar ya dawo?" Ya fad'i hakan ne domin shima Yakubu baya son ana zuwar masa gida, duk da cewar shi ba mugu bane, amma ya hana a dinga zuwa gidan kwata-kwata, kuma hakan ya faru ne ta dalilin matan nasa, sun faɗa masa iya waɗan da zasu dinga zuwa kuma ya yarda. Hakan yasa basu tsaya duba kuɗin ko nawa bane suka shiga cikin gidan. Ɓangaren mai shago kuwa mutumin ya dinga duba jikinsa bai ga kuɗi, tun yana ɗaukar abun wasa har dai ya ajiye wayarsa a gefe. Mai shagon dai ya tsaya yana kallon sa. Nan kuma ya fito waje gurin da ya tsaya, sannan ya sake dawowa cikin shagon duk ya fita a haitacinsa. Kamar zaiyi kuka ya ce "Yanzu fa na shigo da kuɗi nan, ko minti ɗaya ba'ayi ba?" Mai shagon ya ce "A'a fa, sai dai ko a hanya ka zubar amma idan har a cikin nan ne zaka ga kayanka". Sosai bawan Allan nan ya shiga damuwa harda hawaye domin kuɗin na da yawa, kuma yanzu ya ciro su zaiyi amfani da su. Sai da yayi tunani sosai ya gane cewar wannan yarinyar ce ta ɗauka, domin ko lokacin da ta ɗauki kuɗin yaji ta goge shi, sannan kuma ai da tana da gaskiya lokacin da ya ce zai biya zata tsaya. Ya tambayi mai shagon ko ya san yarinyar. Ya ce shima yau ta taɓa ganinta. Gashi kuma bai gane fuskarta ba. Haka dai mutumin ya bar shagon yana ta Addu'ar Allah ya haɗa shi da ita.

Ƙofar palon gidan a buɗe suka same shi hakan yasa suka shiga suka zauna. Abida ta kai kallonta kan kujerar dake kusa da ita mai cin mutum daya, ta sake kallon kujerar da kyau. Tashi tayi da sauri ta ƙarasa gurin tana kallon wannan ƙaramar rigar da ta gani a jikin Hafsa jiya da daddare. Bayan kujerar ma sai ga hijjab dinta a yashe. Hakan yasa ta kalli Abbati da hankalinsa ke kallon katun ɗin dake tv show din gidan. Tashi tayi ta nufi cikin gidan tana kiran sunan Yusra kasancewar sun ɗan yi sabo da ita, domin kafin su yi aure tana janta a jiki, itace dai take kwace wa, har abu ta sha bata, ko ta ce tazo taje su kwana tare a ɗakin su. Ɗakin farko shine na mai gidan, kuma a rufe yake, hakan yasa ta nufi ɗakin Saddiƙa. Tun kafin ta ƙarasa ta fara jiyo sambatu. Abbati ya kai kallonsa ganin yadda take tafiya kamar zata kama barawo. Hakan yasa ya bi bayanta. Ƙofar a buɗe take, hakan ne ya bata damar shiga ɗakin tayi mummunan gani. Yusra ce da Saddiƙa sai Hafsa kowacce tsirara suna lashe-lashe. Ai kuwa nan take ta tsorata ta rusa ihun da ya dawo da hankulan su ga bakin ƙofa. Suka yi ido huɗu da Abbati da Abida. Shima kawar da kai yayi ya kamo hannunta suka fito daga gidan gaba ɗaya. Basu tsaya a ko ina ba sai da suka yi nisa da gidan kafin ya tsaya yana kallon yadda duk tabi ta tsorata. Kalmar da ta fara fita daga bakinta itace "Mai kenan suke yi haka Abbati?" Tayi maganar tana kafe shi da ido, kuma har lokacin a tsorace take. Abbati da shima ɗin cike yake da mamakin abun da ya gani ɗin ya ce "Babu ruwanki da abin da kika gani, kiyi kamar baki ga komai ba". Ta haɗiye wani yawu ta kawar da kai. Sai cen ta sake cewa "Tsirara fa suke babu kaya a jikinsu gaba ɗayansu, kuma su da suke matan aure, kuma ita Hafsa mai ya kawo ta gidan, to wallahi sai na fadawa Baba Manu ko Uncle Mugu". Ta ƙarasa tana yin gaba. Ya san halinta, hakan yasa yayi saurin riko mata hannu

ya ce "Ke wawiya ce, baki da hankali, yanzu idan kika je to me zaki ce musu?"

"Zan faɗa musu abun da na gani ba".

"Me kenan kika gani?"

Ta hararesa. Kafin tayi magana ya ce "Mu koma gida, kawai mu dinga ajiye kuɗin mu a gurin mu ba sai mun bawa Kowa ba, saboda kar ma wani ya gani a samu matsala.  Haka suka kama hanyar gida suna tafiya yana musu hira har suka ƙaraso ƙofar gidan marayu. Sai a lokacin ma tsoron abun da ta gani ɗin yake dawo mata.

Ihun da Abida tayi ne yasa gaba dayansu tsorata suna kallon ƙofar palon. Ita Saddiƙa ma tayi tunanin ma Yakubu ne ya dawo sai kuma taga Abida da Abbati. Duk da haka sun tsorata, amma ba kaman da farko ba. Kafin ma su gama saka kaya sun bar gidan. Haka cikin sauri Hafsa ta saka kaya tana yi tana kuka dama ba'a san ranta tazo ba, sun mata dole ne da kuma alkawarin abubuwa, ita kuma da yake mabuƙaciya ce shine ta yarda. Haka ta fito palo ta saka rigar da dama Yusra ɗin ce ta bata. Duk da suma a tsorace suke, amma bai hana Yusra daka mata tsawa ba ganin ta kasa natsuwa. Ta ce "Wai ke meye haka, kina abu kamar wata mara wayo, saboda wannan yaran sun gammu shine duk kika tashi hankalin ki, an gaya miki sun isa suyi wani abu ne?". Hafsa ta ce "Anty ina tsoron kar ta fadawa Baba Manu ko Uncle Gali ne, wallahi ina tsoro, ni dai gida zan tafi na bata hakuri, kuma ba zan sake zuwa ba". Ta na faɗa tayi hanyar waje ta na kuka. Suna kiranta domin su bata kuɗin mashin ma amma ina kuka take yi bil haƙki da gaskiya. Saddiƙa ta ce "Shi yasa tun farko na faɗa miki bana son alaƙarki da wannan figigiyar yarinyar, na rasa uban me kika gani a tare da ita, shigiya mai kama da alƙalamin rubutu, ita ba gaba ba kuma ba baya ba, yanzu ga abun da kika jawo mana, aikin banza aikin hofi". Yusra ta ƙarasa kusa da kishiyar tata ta ce "Ba zaki gane bane wallahi, haka kawai zubin yarinyar ke burge ni, gata dai babu komai tana nan kamar alu, amma wallahi ina son zubin nata". Ta ja tsaki ta ce "Bana son irin wannan wasan, kar ki ƙara, domin ba zan jure ba?" Yusra ta yi dariya ta ce "Sorry ba wai so irin wanda nake miki ba, ai kece ɗaya tilo a zuciyata, ina dai so ne ace mun jawo ta cikin wannan tafiyar domin itama zata bada gudun mawa".  "Ta yaya babu gaba babu baya ɗin?" "Eh, ba gaba babu baya ɗin amma ko kin san irinsu sunfi abun al'ajabi?" Saddiƙa da hirar ke ɓata mata rai ta ce "To ni bana so, kuma kema bana son na ƙara jin kina maganar ta, wallahi raina ɓaci yake, ji nake kamar na fasa ihun kuka". Yusra ta ce "To an gama love. Yanzu dai meye abun yi?" Saddiƙa ta ce "Ba ke kika ce kin san yadda zakiyi da ita ba, ni dai karta ƙara zuwa gida na, idan ba haka ba Allah watarana sai na mata duka, idan ma saboda wannan gaɓon yaron ne take rashin kunya yanzu da aure na, Yakubu zan sa yaci min ƙaniyarsa". Yusra ta ce "A'a bama za'ayi haka ba, nasan halin Abida ba zata faɗa ba, Abbatin ne kawai abun ji, amma shima nasan yadda zanyi. Haka dai suka shiga gyaran gidan kafin suka fara girki. Sunayi suna labarin hajiyoyinsu, wacce tafi sakar musu kuɗi da wacce tafi kishi da mai jarabar tsiya. Yusra da Saddiƙa ma'aurata ne wanda ƙungiyar su ta ƴan neman jinsi suka ɗaura musu aure da yardar su, suna da uwar ɗaki wacce ita ce ta buɗe musu ido, kuma ta koya musu wannan harkar saboda rashin ƴanci da suke da shi. Wannan dalilin ne yasa suka auri miji ɗaya wanda kusan komai na auran su ne su kaiwa kansu, domin hatta gidan ma nasu ne, kowa yasan yadda suka shaƙu amma babu wanda yasan abun da suke aikatawa harda kuwa shima mijin nasu.

****

•Anty Hinde

Yau tun safe har kusan ƙarfe biyu babu wanda ya kawo mata ziyara, abun har mamaki yake bata. Ita da bata rabo da baƙi ƴan gidan su yara ko manya. Sauri take ta ƙarasa girkin da take yi kasancewar yau juma'a da wuri zai dawo, kuma idan har ya shigo gidan nan bata gama girkin ba ta shiga tara. Ta na girkin zuciyar ta na wani gurin. Sannan tana tunanin ko mai yasa har yanzu babu wanda yazo. Kuma tana tunanin su Abbati. Ta san halinsu ko zasu dawo gidan nan ba yanzu ba, domin gaba ɗayansu suna da zuciya, dan ma ita ce, da gidan wata ne ake musu wannan abun da yanzu sun manta da ita. Ko a ina suka samo kuɗin da zasu bata ajiya. Bayan ta gama girkin ne ta sauƙe ta zuba masa nasa, kafin ta juye sauran a kula, ta zuba wani a wata kular saboda tasan dole sai wasu sunzo kafin dare. Ƙasan gadon ta taje ta ciro wayar da babu wanda yasan tana da ita. Ta kunnata kafin ta kunna data ta shiga YouTube. Gobe sati biyu da yin hira da shi, hirar da akayi minti arba'in kawai amma har yau ta kasa gama kallon saboda tsoro da rashin lokaci, yau take da burin ta ƙarasa kallon tunda babu baƙi. Jikinta har rawa yake yi ta kunna vedio ɗin ya ɗora daga inda ta tsaya. Ta na kallon vedio ɗin ta na kuka tana jin yadda yake magana Kamar ba shi ba. Bana shekara uku kenan rabonta da shi, amma ya chanja, ya zama wani daban mutum. Tambayar da akayi masa ne yasa zuciyarta bugawa tana sauraron amsar da zai bayar. Mutumin ya ce "Malam Saif (Saifullahi) "Shin yaya batun iyali, mutane nata magana akan cewar baka da aure, wasu kuma suna cewa kana da aure, shin menene gaskiyar maganar?" Saif yayi murmushinsa mai tsada, wanda a lokacin da suke tare idan yayi take jin kamar duk duniya babu wanda ya iya murmushi kamar sa. Ya gyara zama ya ce "Maganar iyali babu, nayi soyayya kuma na gama ba zan sake ba, mace ɗaya naso kuma ita zanta so har ƙarshen rayuwata. Yana faɗa yayi shiru. Mai tambayar ya buɗe baki zai sake masa tambaya ya ɗaga masa hannu yana sunkuyar da kai. Koda ya ɗago kansa idanunsa sunyi jaa! Ya ce "Abar wannan tambayar na gama da ita. Anty Hinde taji zuciyarta ta harba da ƙarfi, take wani irin kuka ya kufce mata, ta tsayar da kallon ta kifa kanta a tsakanin gwuiwoyinta. A fili ta ce "No Saif dan Allah kaje kayi aure kaman yadda nima nayi, karka cuci rayuwarka, please Saif!. Bayan ta gama kukan ta ɗauko wayar tana cigaba da sauraran hirar. Sosai kukan yaki tsayawa tana jin yadda yake magana da natsuwa da burge wa kaman yadda ta san shi tun a baya. Lokaci ɗaya ta fara tunanin mai yasa bata da Iyaye, mai yasa wannan dalilin ya hana ta samun burin ranta. Shin ina iyayenta, mai tai musu da suka zaɓi kawo ta gidan marayu, shin ma tana da iyayen ko bata da su. Kamar a cikin tunani taji an fauce wayar daga hannunta, lokaci ɗaya ta miƙe tsaye har tana ƙwarewa da kukan da take yi. Lokacin da tayi ido biyu da shi sai taji kamar hajijiya ce ta fara juyawa da ita tsabar tsoro da tashin hankali, irin kallon da yake mata ya tabbatar mata da cewar ya dade a tsaye yana kallonta. Sai yanzu ta tuna da ashe bata rufe ƙofar ba. Idonsa ya mayar kan wayar yana kallon wanda ke jawabin.  Idan bata manta ba, wannan shine karon farko da ya kamata da wani laifi mai girma tun auransu, sai dai ƙananun laifuka wanda dama shi ba'a rabo da yi masa su, kuma su ɗin ma haka zai jibgeta to bare kuma ga mai dalili. Take makogaronta ya bushe, hawayen suka tsaya, ta sunkuyar da kai ƙasa tana jiran jin abun da zai faru. Gali ya ce "Waye ya baki waya?" Ya faɗa da wata murya mai wahalar fahimtar abun da ya ce zabar yadda ta fito da wani irin sauti mai rikitarwa. Take jikinta ya fara rawa ta kasa magana, domin bakinta a bushe yake. Da ƙarfi ya ɗauke ta da wani irin mari ya ce "Dan uban ki waye ya saya miki waya da har kika buɗe YouTube ban sani ba? Na ce waye ya saya niki?" Ya faɗa yana ƙara mata marin, yana kuma kallon videon da take kalla, wani irin kishin da bai san yana da shi bane ya taso masa, duk da bai san Saif ba, amma yadda yake kuka ya tabbatar masa da cewar zata iya sanin sa. Lokaci ɗaya kukan da bata san daga ina ya fito ba ya kufce mata, kuma har lokacin ta kasa magana. Hakan ya ƙara tunzura shi. Ya ɗagota ya yi ball da ita ya ce "Shigiya munafuka, ashe duk wannan shiru-shirun naki na iskanci ne, ashe munafuka ce ke ko? to daga yau zanyi maganinki, kuma sai kin faɗa min inda kika samu waya ko wanda ya saya miki?" Take ya cire layin wayar a gabanta ya karya su yasa a aljihu. Sannan ya ce "Wayar kuma zuwa zanyi na sayar da ita, kuma wallahi ina nan dawowa zaki san ni kike munafunta, sai kin faɗa min wanda ya baki ita, shigiya ƴar iska munafuka". Yayi waje fuu zuciyarsa na zafi. Yana fita ta zube a gurin ta fara kuka mai harufa. Gefen bakinta ya fashe ga kanta da ke mata ciwo. Daga layin har wayar Saif ne ya bata su, shekaru uku kenan babu wanda yasan tana da wayar. Tun lokacin da suka rabu ta daina samun sa a waya, haka zata shiga fecbok tai ta kallon hotunansa, gurin chatting kuwa yayi blocking ɗin ta, shi kansa account ɗin ma daga baya aka rufe. Haka za tai ta rubuta sunansa ko zata ga sabon account ɗin sa amma babu. Duk wani gurin da zata iya cin karo da shi ya toshe, tasan cewar ya samu labarin auranta ne. Bata taɓa kawo cewar zata iya samunsa a YouTube ba, kasancewar bata yin YouTube ɗin, domin tun da ta rabu da shi fecbok kadai ta ke yi shima. Kuma har wannan Lokacin bata taɓa saka data ba, amma zata yi komai da layin, hakan yasa take ɗan shiga YouTube ɗin lokaci zuwa lokaci tayi kallo.  Bata san komai a kai ba, sai dai taiyi ta kallon video, a haka taci karo da wannan hirar tasa wacce ta kusa sumar da ita a lokacin. Tana cikin tunanin taji ana sallama, hakan yasa ta tashi da sauri ta saka hijjab tayi waje. Rabi ce ɗaya daga cikin matan da aka aurar dasu tare, kallo ɗaya tayi mata tasan cewar a kwai matsala. Tun ma kafin Anty Hinden ta zauna ta fashe mata da kuka. Hakan yasa gabanta ya fad'i ta kawar da tata damuwar ta ce "Rabi meye haka kuma, kuka fa, kenan kuka kika zo yi a gidan nawa ko, so kike nima na fara ko yaya?" Ta faɗa tana jin tata damuwar na taso mata, ga ciwon kan ta kamar ana ƙaro shi. Jin haka yasa Rabi share hawaye ta ce "Anty Hinde na gaji, wallahi ba zan iya ba, gara na shiga duniya na nemi gurin da zanyi rayuwa yafi min irin wannan cin zarafin, Anty Hinde har fa ta kai yanzu Sani ya fara duka na saboda na tambaye shi kuɗin abinci, Anty wai ni haka rayuwata zata cigaba da tafiya har na mutu kenan, Anty Hinde zan samawa kaina ƴanci, ba dai sunce kome za'ayi wa mutum kar ya kai musu ƙara ba, to ba zan kai ba, amma zan samawa kaina mafita". Ta ƙara sa tana fashewa da kakan mai ɗaci, wanda sai da itama ta fashe da kukan. Hannu ta kai ta shafa gurin da bakinta ya fashe, tana tuna tun lokacin da Gali ke dukanta, tun kafin ta zama matarsa, har yau bata wuce duka ba, duk da bata aihu ba, amma ta zama uwa ta cancanci a raga mata. Ta rungume Rabi a jikinta suna kuka tare. Ita kanta Rabi ɗin abun ya so bata mamaki jin tana kuka. Anty Hinde ta ce "Rabi wannan auran shine gatan ki, yafi miki mutunci da alkairi akan abun da kike hange, rabi mu ɗin ba kamar sauran mutane bane, a kwai tazara mai tsayi a tsakanin mu da su, mu haka tamu rayuwar take, amma abun da na yarda da shi cewar zaman auren yafi duk wani abu da za muyi, dan haka dan Allah kiyi hakuri, bana son na ƙara jin batun guduwa duniya, domin bamu da kowa, bamu da komai, su ɗin dai sune ahalin mu, sune ƴan uwanmu". Rabi ta ce "To Anty haka zan zauna yana dukana kamar jaka, abinci nan ba isarmu yake ba, idan nayi magana sai duka da zagi fisabilahi a haka zamu rayuwa?" Anty Hinde ta share hawaye ta ce "Rabi ki fara yin sana'a, zama haka ba zai miki ba, ba komai bane ake dogara ga Namiji musamman ma dai mu da ba ɗaya muke da saura ba, dole ki nemi naki, kuma ki daina yawan tambayar sa abu duk shi yake jawo wannan fadan naku, na san halin Sani mutum ne wanda baya son surutu, dan Allah kiyi hakuri. Yanzu dai ga abinci ki tafi muku da shi, dan Allah ki yi haquri, ranar Lahadi kizo zan baki aron kuɗi dubu biyar ki fara yin wani abu da shi wanda kika san zai rufa miki asiri. Haka Rabi take ta godiya, ta zuba mata abincin a kula sannan ta bar gidan. Sannan ta zuba mata wani taci ta ƙoshi ta sha ruwa. Ta tashi zata tafi kenan sai ga wasu yaran kusan su biyar sun shigo gidan. Rabi ta tafi tana ta godiya. Take suka shiga gaidata tana amsa wa da sakin fuska. Har cikin zuciyarta take kallon gaba ɗaya ahalin gidan a matsayin ahalinta, a duk lokacin da take cikinsu tana tsintar kanta ne a cikin farin ciki. Tashi tayi ta zubo musu abinci a tire biyu, ta raba yaran biyu ta ce suci amma a hankali. Suna ci suna hira da ita...📝

Please kuyi mana like and shering

S Reza