ABUNDA KE 'BOYE...

25

by @surayyahms

⏯️2️⃣5️⃣💫
Tunda taji anrike mata hannun tatsaya cak tareda juyowa da uban sauri, wani irin kallon juna sukeyi har ya shigo cikin kitchen din tana ganin ibaad ne tawani fauce hannunta anashi dawani irin hucin tsana me zafin gaske, ibaad yay sama da idonsa yana kallon kwayar idanunta bayabo ba fallasa yace mummy lafiya meye faru, metayi kuma?

wani irin zazzafar huci ta saki tanamai hararsa upandan tunma be gama rufe bakinsa ba cikin hatsala tace "me kuwa zai faru banda satar nama da na kama wann walakntacciyar yarinyar tana min...

da mamaki yace sata kuma amma mummy..sai kuma yay shiru baice komi ba ya juya yana kallon ayaanahn data dan sunkuyar dakanta can kasa tana zubda hawaye sosai jikinta na mugun rawa rawa.

muryansa na fita ahnkli salon rashin son ya tsoratata yace
"..ke kuma meya kawoki nan?

lumshe idonta tay dan bata san da kuka ya kufce mata ba ahnkli muryanta na rawa tace "ruwaa..a kawai nazo debewa ni wallah ban mata sata ba

."..zai magana da mugun sauri ammi babba ta karakawo hannu zata jawota gaba danta falla mata mari yasake yin wuf ya rike hannun yace mumy pls wait mana let her answr all the questions dan Allah,"...yana sake mata hannun ransa abace yakara kallon ayaanah yanamai tuhumarta akan abunda ya kawota kitchen din,..duk ta rude sai takasa bashi kwakwarn bayani tana kuka itade cewa take bata dauka mata namanta ba"..

a mugun masife ammi babba tace "ibaad bangane kana wani tambayrta ba, nayi maka kama da wacce zata maka karya ne? okay naa pls lets look at her hands tunda baka yarda da ni ba..ahaukace takamo duka hannun ayanahn tanamai nuna masa maiko maikon naman, amugun zafafe tace kagani ko? inda ba namar tazo sacewa ba ta ina wann maikon zai fito? toh wallh walh saina miki shegen duka, dan ni gidana ba amin sata, kuma ba'a min karya, saidai kikoma can kauyenku inda kika fito da wann mummunan dabiar taki ta mayunwata barayin abinci, ai inma kwadayi kikeji saikizo kicemin wanda nabakin ne bai isheki ba, i will undrstnd you dan nasan babu a house, gidan miji babu tabbas, makwabta sai ɗaiy-ɗaiy..amma tunda kikace ke satar abinci zakiyi agidan nan toh wallah saina ci ubanki kuma bazan taba kyaleki yauba har sai anbiyani nama na da kikaci...

ayaanah tafara kuka sosai har tana jan shsheka cikin rudewa tace "Umman sultana kiyi hakuri ni wallah ban miki sata ba ruwan sha fa kawai nazo debawa zan kai ma sultana..

tace "da Allah kimin shiru, bakin samu ana bin bayanki ba?last week kinmin asarar dumbin kudina anbi bayanki, yanxu kuma wato bari ki tsiromin da halin bera to badai agidan nan ba, yau ko abiyani ko kaf masu daure miki gindin suzonan sugani snn suji cewa ke babban barauniyace kuma makwadaicya...

kuka kawai ayanah takey dan duk wyannan maganan ji take kamar sun mata nauyi..

ibaad yace" mummy dan Allah kiyi hakuri..if u cant let her explain herself properly atleast let her apologise to u"

ya kalle ayanan ransa a mugun bace yace "ke kuma mekike jira da bazaki bata hakuri ba tunda ai naman kikazo sata saiki bata haquri
...ayaana ta kara fashe masa da kuka batace komi ba ta tsuguna kasa cikin masa biyayya tace "yace ince miki kiyi hakuri. wai bazan kara ba..

ammi babba tace kan facalin bala'i wato shine ma yace kice min inyi haquri?kuma ma bazaki kara meye ba..ki fada da bakinki...kowa anan ya shaida cewa ke barauniya ce

ihun datake mata yasa sultana tafara shako muryansun daga kan stairs dan already tafara tahowa dubata, sai ta tsaya cak idonta ya ciko da hawaye ata bakin kofar kitchen din tanamai jin bakin tsoro karta shigo ciki asata ta fadi gaskiya yaa ibaad yasan ita ta saci naman ya casata...

ihu ammi babba take ma ayaana akai tana cewa ki fada masa da bakinki cewa sata kikamin..ke barauniya ce..say it ryt now!

ayaanah tana kukan sosai da wani irin taurin kai tace nifa wallah ban miki sata ba..ni ba barauniya bace...ai ban dauka miki abunki ba...

da mamaki ammi babban tace ohh dan ubanki karyan zaki ci gaba damin? toh wllh inhar baki furta cewa kinmun sata agabansa ba yau dinnan sai anbiyani nama tareda dukkan wasu abubuwana da kike min asararsu ai ba ubanki bane ya bani su...

haka kuwa ayaanah taki sam ta furta komi sai kuka takeyi daga tsugunen daf da shi
ayayinda kukantan yake daga masa hanklinsa yanasamai rauni taciki bana kadan ba..

wani irin ruwan balai take saukar musu tana cewa ''ko abiyani nama na kona miki dukan mutuwa, shegiya makira kawai barauniyar abinci, ke abubuwan ma sun miki yawa wai shege da hauka...if u want me to forgive u just open ur mouth and admit it cewa ure a big thief..ole..oloriburuku barauniya...young anini...

tanakan maganan ayanah na tsugune agabanta tanakan kuka itama sam takiyi shiru sai cewa take ni ban miki sata ba wanda hakan bakaramkn dada mugun hatsala ammi babba yakeyi ba...

can cikin lumshe tare da budewa da comanding voice dinshi me sanyi yace mummy please is enuf. fuskarsa a dore yabi yakalle ayaanah yace ke tashi kibar nan wajen ynxn nan..

da wani irin mugun gudu ayaanahn ta miƙe daga tsugunen ta fita waje tanata kuka sosai harta tawuce sultanan abkin kofa ma bata sani ba, can waje gaban pool din taje ta tsuguna tanata kuka tanajin kamr ta gudu ta koma wajen ummanta

ruwan masifar ta dawo akansa tana kallonsa kamr wacce zata falla masa mari tana huci "'and what was the meaning of that ibaad? kai waye da zaka ce min enuf agaban yarinya
...bayan kana kallo yarinya tana karya kiri kiri zaka kuma wani ce mata ta tashi ta tafi dan tsabar ka rainani ko? hmm ko da shike ba lefinka bane, uwarka ai ita take mulki agidan nan shiyasa kaima kaje har kauye ka kawomin wata sabuwar annoba fitinanniyar yarinya barauniya, wacce a kwana biyu kawai da tazo saida tabarar min da abuna dat is worth 10million naira, yau kuma gashi tahau tsince min nama acikin abinci..

toh wallah wallah tunda abun naku rainin wayo ne ko ka biyani kudi na ko in ma yarinyar nan dukan kudi na inyaso saika kira uwarka kace mata tasaka bappanka yasake ni yau ya aurota..yan bura uba kawai macuta...inka ga maganan nan tawuce toh wallh biyana akayi inba haka ba kuwa saidai kafitar min da barauniyar nan agida na yanxu, ni bazan iya ba, ga asara, ga sata da karya, ga uban raini, haba da wanne zanji, inde bazaka biya ba tou muzaba mugani saidai in bazan kara hada ido da yarinyar nan agidan nan ba wallh sai na mata dukan million goma tare dana kudin nama da sata..


sosai idanunsa yay jaa yana jin ammi babban harta gama balbalin bala'inta akansa

muryan sa adan dakile yace mummy toh kiyi hakuri.. azafafe cikin katsesa tace wallah ni ba uwarka bace dan kuwa bakasan darajata ba..

cikin lumshe ido da budewa yace okay fine nawa ne kudin naki. i will pay u back..amma dan Allah karki tabata...her medical condition is quiete...

tace "i do not care abt that stupid conditon of hers, banason ji, in taga dama ta mutu mana nina kawota duniya ne ehhhh?..aini bakasan halin da tasaka ni aciki ba dake ni ba uwarka bace duk bai dameka ba..if u want her to breath in dis house u shud just pay my money ryt now.

ahnkli kuma a dakile yace okay..shikuma naman nawa taci miki..

....cikin yatsinawa tace dubu dari cass na saya turkey dina, kuma duka za'a biyani...baice mata komi ba yaciro babban wayar samsung dinsa daga cikin aljihunsa ya bude daya daga cikin microfinance app dinsa da kwanan nan akayi legalizing masa yasa biometrics nasa for swift transfer, acct din na buduwa Allah yaso shi sai yaga cassh limit din transfer dinsa ksan 15million naira ne kacal sumwhat beyond what she is even asking him for.

idonsa nakan wayar yace"wani banki ne?

wani rau tay da idonta looking desperate nd very wicked babu dandanin kunya acikin kwayar idanunta tace masa" "zenith bank..yace ok acct number, acikin sauri tana yatsinawa tahau gaya masa digits inta yana rubutawa har snn full sunanta ya fito atake atake yasaka mata cak cak kudinta dats 10million 100k yana gama nuna mata receipts taga kudin yashiga atake tajaa masa wani dan banzan tsaki

tace..mtsw aikin banza aikin wofi,.. ka kyauta makanka, danni wallah gaba takaini gobarar titi a jos, daga nan inkunga dama kucigaba da daure mata gindi tana abunda taga dama agidan nan nide wallah bazan taba daukar wani asara ba...nd pls if u want to test my patient ibaad kaje kadau wayarka ka gaya ma kawunka ko uwarka cewa kabiya ni kudina, nikuwa zan dawo maka da kudin amma wallah wallah ibaad, duk abunda nazo nayi ma yarinyar nan kasani kaine ka jawo.

wani uban tsaki taja masa snn tabarsa awajen yana tsaye baice mata uffan ba cikin shanye bacin ran dake cinshi a kirji yafito yana tafiya calmy da duka hannunsa acikin aljihun sa,yana steping wajen kitchen din kuwa yakalle sultana agefe ta rakube da jikin bango tanata matse ruwan hawaye zuciyarta na bugawa da sauri sauri

suna hade ido ta dan firgita, fuskansa a mugun daure yace "ina ayaanah take?muryanta na rawa tace tafita waje inaga tana can wajen pool tana ku...
...tun bata karasa gaya sauran ba yadauke kansa yanufi wajen pool din shima walking very gently kamar ba abunda ke damunsa

samu tay tadukunkune kanta waje guda tana rabza uban kuka, dan babu abunda takeji arnt kamr ta gudu taje wajen ummanta ynxu.

kuka takeyi abar tausayi tabi tacusa kanta atsakankanin cinyoyinta har ya iso wajen bataji steps insa ba saida taji qamshi tare da dirar inuwarsa akanta snn ta dan dago cikin sauri, suna hade ido tay maza tamiƙe tsaye  da hawayen a fuskarta, jikinta a sanyaye sosai. shide baice mata komi ba sai tabita tsuguna kasa  agabansa da ladabi itama tay shiruu.

idonsa akanta yace keee kin taba cemin kinason kici wani abu agidan nan na hanaki?

cikin giragixa kai da muryan kuka tace mishi aa..adan masife yace toh uban meyesa zaki je har kitchen inta ki daukar mata nama, ke kika aje ne da zakije ki dauka? nd when has dis nonsense start..

hawaye na zuba a idonta tace wallah ni ban dauka mata komi ba..

yace "Dont u dare lie to me.

jin yadda yafada hakan da bacin rai yasa ta kara fashe masa da kuka me sanyi

cikin controlling emotions dinsa yana kallonta anitse yace "inkin san kinyi abu marar kyau, just admit it.. bawai kina yin karya ba. dan da ace baki dauka ba ta ina har hannunki zai samu maikon namanta?ni bana son karya. i hate lies in any form...

tana girgiza kai tace amma wallah ba karya nake maka ba..

batare da ya daga maya murya ba yace ohhh just shut up ina magana caraf kema kina amsawa irinke gaki me taurin kan nan ko? to ai me taurin kai baya sata..dan shiru yay.. snn yakuma cewa kee kalleni nan. hawaye na zuba a idontan ta dago ido ta kallesa "yace kinaji, araunce tace masa ehh..

da wani irin stern voice yace dont you ever..kar inji ko na sake ji ko ma sake ganin kin sake taɓa abun wani, inde abu banaki bane just take ur hands off it idan ba hakaba nidakaina zan miki shegen duka agidan nan..nd when ever ure wrong just admit it, nd shut up...ki tashi kiban waje kar kuma na sake ganinki kina kuka anan wajen....


tana zubda hawaye sosai ta mike kanta na kallonn kasa jikinta a sanyaye ta doshi kofar main mansion din tana budewa ahnkli kuwa caraf suka hade ido da maheer tare da sultana suna saukowa kusan atare..

wani cak ya tsaya da sultana abayansa dan already yazo ya sameta tana kuka anan ya tuhumeta shine ta gaya masa cewa ai mummyn su ne tay ma yaa ibaad da ayaanah masifa wai akan dan ayaana ta dauka mata namanta a kitchen ynxu..

cikin idanunta dake fidda hawayen ya kalla tay saurin sunkuyar dakai kasa, tuni jikinta ya bata hala shima yaji komi shikennn yanxu kowa zaina mata kallon barauniya.

wani sabon kuka taji yaxo mata batace mai komi ba ta wuce sama da sauri tay sashensu tanajin nauyi da kunya sosai ..

tausayinta yaji ya kamashi da can har zai fita waje ya same ibaad din dan yaji sauran bayani saikuma ya fasa kawai yabi bayanta dan ya lallasheta

shortly after sun wuce sama shikuma ibaad ya dawo gidan  room dinsa direct ya wuce ya zauna abakin gadonsa jin kirjinsa na masa zafi sai ya shafa fuskansa ahankli cikin rasa gane abunda yake masa
dadi. cikin raya wani abu aransa ya dauki wani sabon atm card dinsa da ake yawan saka masa school fees dinsa aciki ya saka a wallet dinsa kafin nan yabude closet dinsa ya canza kaya zuwa wasu casuals masu kyau snn ya dau key din mota da sauri yay waje, within few minute yay driving kansa out of the mansion zuwa wani katon exclusive unisex boutique...

daga dakin kuwa sultana sam takasa zuwa kusa da ayanah sabida guilty consience najin cewa itace me asalin lefin ita sato naman sukaci tare, kuma har ga Allah tana tsoron ta fadi gaskiya agaban yaa ibaad sabida bata kaunar ya bugeta ko ta shiga red list insa na makaryata agidan. she cudnt help but to feel guilty nd sad, agefe taja ta tsaya tanata satan kallon ayanah yadda ta matse kanta acan dungun gado tanata kuka ahankli

maheer ne ya nufo inda take yana kallonta da tausayi har ya zauna agefe daf da ita bata dago fuskarta ba.

muryansa na fita ahnkli da sigar lallashi yace "pretty one, zaki iya min magana "can we talk? wani uban shiru ta masa tanakan kukanta saida yakara memeta hakan snn ta gyada masa kai yana murmushi me sanyi ya kara matsowa daf da ita ahnkli yace toh prettyna pls gayamin meyafaru mana, ko ibaad din ya miki wani abu ne?

idanunta na kallon kasa suna fidda ruwa ahnkli cikin muryan kuka tace"..aiyaqi ne yaji abunda zan fada, yace wai na mata sata yanata min masifa kuma wallah ni banmata sata ba..

jawota yay jikinsa yace shuhsh its okay, kidena kuka hakan nan kinji ko, ai sultana tagaya min iya abunda ya faru..so just chill ,ire iren wannan kananan mistakes din dama are bound to happen..shima i will talk to him zai gane cewa ba halinki bane its just a mistake ko?

tana sharewa hawayenta tace "nifa banaso ka gaya masa komi ai ya riga yamin fada kuma nace masa bazan kara ba, kawai kabarshi .nide tsakanina da Allah ai nasan ban mata sata ba..

yace hakane pretty one nd dats what matter ynxu dai kidena kuka kishare hawayenki kinga ankusa kirar sallahn magrib ni zanje nay alwala then we wll talk later ko?.

ahnkli ta gyada masa kai tanata mamakin irin kirkinsa harya fice bata dena kallon inda yabi ba..

yana ficewa a dakin wani irin shiru ne ya ratsa tsakaninsu da sultana..haka kuwa basu ce ma junansu komi ba, ayaanah tagama share hawayenta ta tashi sum sum ta shiga bayi domin yin alwala...cikin rasa nay sultana sai tafice a dakin ta koma can dakin quest dinsu tay nata sallahn awajen ta cigaba da zama dan batasan ta ina zata fara bawa ayaanah haquri ba..she neva had any close friend or sister, duk wnn abubuwan datakeji na quilt da tsoron fadin gaskiya danta wanke wata yau ne tafarajin jinsu aranta dake duk zamanta da causin sisters din nata baifi insunje weknds a family house ba kuma dama da kulthum kawai tafiye yin magana.


Dagata dayan bangaren kuwa tun biyar da rabi zainab Arifa tagama daukar wanka ta saka wata xpensive saudi arabian abaya classy handwoven frm safiya abdallah of saudi, shikadai kawai ta siya jiya da suka dawo daga 5days business trip to paris din da sukaje ita da babanta, daga wnn bakin abayan sai sabon bag pack dinta na school data dawo dashi, she feels like she needed to buy clothing gifts nd more chokolates da zata bawa kawayenta rukky da nala tsaraba dan haka yamma liss taci wani irin kwalliya da sabon abayan ajikinta,only herself and her closest two maids wato elizabeth da aqeela zasuje wata private boutique dan ta siya kayan tsarabtanta acan.. daga ita sai driver a katoton benz jeep, maids dinta kuma suna biyota a wani motar shima benz din ce amma ba jeep irin nata ba..

tunda suka kamo hanya idonta yake stiff akan customised wayarta tanakan daddanawa time to time haka tana yagar chokolate dake gefenta tana kaiwa baki..

wajajen 6pm aka iso dasu gaban unisex boutique din har snn ta daga ido jin sun tsaya,
expensive original designer mall ne just few cars are packed outside da basufi guda biyar haka ba

she likes coming to this place sabida it has great customer service kuma babu tarukucen hayaniyan yaran kananan millionaires gashi wokers din suna treating customer kmr royalty, a treatmnt she soo much adore on her self.

suna tsayawa maids dinta suka sauko da sauri elizabeth ta bude mata mota muryanta kasa kasa tace "kishiga ciki kigani idan customers sunfi shida aciki just come back here lets move nafasa shoping din, then you wil oder evrythin for me online idan munkoma gida.

cikin ladabi Elizabeth tace yess maam. snn tq shiga ciki taje ta samu kusan mutane takwas ne ma acikin mall din biyu yan mata sauran kuma duka maza but she was stunned to see ibaad among them kuma yana tsaye ata sashen mata...

tun kafin su hade ido dashi tay sauri ta dawo waje har jikinta na rawa ta kwankwasa ma zainab arifah windon mota wanda saida ta ja mata aji ma kafin ta bude..

tace "excuse me maam'

batare da ta kalleta ba tace "what is it...spill.. quickly....

cikin gyaran murya elizabeth tace i have both gud news nd bad news maam...

batara da ta kalle ba tace "really...okay bad news first..

elizabeth tace okay maam i am afraid yau fa mutane takwas ne acikin store din

cikin yatsina fuska zainab arifah tace ohhh gosh...and the gud news?...

elizabeth tana murmushi tace "Ders someone inside that i think u may be intrested to see.

da mamaki zainab arifah ta juyo tace...and is that person my father?

....tace noo maam wanann mutumin na hoton dake gaban mirron ki ne fa wanda har yazo ranar kukay dinner??

da wani irin gwalo ido tace'you mean ibaad?

..elizabeth ta gyada kai..wani jan ajiyan zuciya zainab arifah tay tace "okay come quick, xoki ban jakana akwai pressed powder aciki, nd is my face okay? the shadows, the coutour, the blush..look at me dakyau..ina aqeela? aqeelan tana matsowa tace u guys shud tell me did i look beautiful...my lips okay? nd what abt my dressing...oh my god cant believe ibaad is in here...cikin bude ido da lumshewa da wata irin shauqi ahnkli tace i can wait to see him, ina ce dai nayi kyau??

zuga kyanta suka hauyi dan sunsan inba haka sukayi ba bazata sauko suje ciki akan lokaci ba.

elizabeth ta kawo mata jakarta ta ciro original fenty-X lead base made refined powder takara shafawa a fuskarta tay wani irin dau farin fatar tan yakara fitowa sosai

hannu ta miƙa wa elizabeth ta rike kmr yar sarki snn ta sauko kasa ahankli bisa kan 6inchess bouchra jarrar high heels dinta in shiny silver colour da dan karamin luxury side bag dinsa da yay complemting bakin abayantan sosai.

ahnkli take takawa suna binta a baya kamr wata yar sarki, wanda tun kafin ma sukai kofar wajen gabanta yake dukan tara tara dan ita kanta bata san wani irin mahaukacin ciwon so kwakwwlrta yake ma ibaad ba, he feels like the air she is breathing ryt now..dan tunda akace yana ciki sai taji gabaki daya bata da wani sauran nitsuwa ajikinta gabaki daya..

ata fannin ibaad din kuwa tunda ya shigo store din bai dauki komi ma kansa ba iyaka ma ayaanahnsa kawai yake tattara kayan sawa, dan gabaki daya tunanin ayaanahn ne ya gama cikke masa zuciya da kwakwalwansa, he feel much more guilty each time yaji ammi babba tana mata ihu dawasu irin walakantattun kalamai..sai yana ganin kamar hala duk lefinsa ne dayay shiru ya kyale ma su bappa zaidu aikin kulawa da ita while shi baida ma lkcin kansa.,duk sanda ammi babba ta zagi ayaana har ransa abun yake qonasa, nd he is very sure is bcos she have nothing of her own agidan, komi ara mata akey awajen sultana shi yasa har akelaka mata sharrin sata  take kuma yawan zaginta da sunan walakntaciya tare da kaskantar da ita akan kudi da wasu irin mugayen kalamai na cin fuska da gorin talauci....

Da abubuwa  dayawa aransa yashigo wajen, nd he picked mostly ready made wears ne wanda yasan zatana amfani dasu ne atake, 21 pieces of items sets da yasan zasu iya cika atleast 5 shopping bags. "abayas, inner wears, hijabs, shoe, casual wears, dana cream nd personal cares.

attendant din dake binsa abaya tana tayashi yana gama picking komi dayakeso tagama tattarawa masa duka kayan.

sungama kenan zasuje wajen biya yaji antaba shi akafada slightly yana juyowa suka hade ido da zainab arifah tana wani irin murmushi tace"Hi.. surpise to see me?yamata kallo daya cikin dauke idonsa yace "nop"
..nervously tay giggles tace well nikam i am suprise to see you musmn ma anan sashen mata..so, how have u been?ashe ka dawo gari shine banji labari ba, nd u dont even pick my calls..yamata shiru baice komi ba dan normally in rashin mutuncinsa ya tashi u go talk tire har kagaji bazai kulaka ba

...babu shiri ta fara zuba masa surutu tanamai tambyarsa abunda ya kawosa nan and who he is shoping for..harda zagewa wai zata tayashi,

daga haka yafara amsata daddaya..karshe ma yace mata yagama siyan abunda zai saya gida zai wuce ynxn nan

kamar mayya haka ta dinga binsa with queastion upon question har yakai sashen maza, ya dauki one pieces of perfume dama yanata neman turaren da zai rike guda daya as his own personal signature sai caraf kuwa yaga xerjoff naxos of Xerjoff’s 1861 collection, which is inspired by Italian heritage anyishi da pure notes of Tobacco leaf, Vanilla, Tonka nd bademorth, asalin turarene na namaza daya amsa sunansa turare yana da wani irin nanniyar masculine scent mai kama jiki da jimawa acikin kaya da tunani.

saboda tsadar turaren yasa bai kara daukar wani abu bayanshi ba duk surutun da zainab arifah takey asking him series of questions abt his shopings nd travels bama ji yake ba har suka kai kan counter

aka fara hada masa kayansa in difrent bags sai kallon kayan takeyi sounding confused take cewa "is it for ur sisters? ai kasan nima kanne na ko?toh meyasa bazaka jirani na kara musu da nawa gifts din akai ba inyaso sai muje gidan atare mukai musu..

shareta yay yaki kuma ya mata bayanin komi, amsarsa daga eh sai A'a.. karshe data matsa masa son sanin kayan waye sai yay saurin katseta da cewa sauri yakeyi zaije yaja sallah a masjid, haka tay masa taurin kai ta saka aka tarkata kayan biscuits da su chokolates aka kara masa akan kayan nasa aka bisa waje dashi, and she was soo pissed off da aka bishi dashi harmotan shikuma yay kyauta dasu atake awajen, duk da uban tsadarsu hakan kuwa ya bawa workers dintan kyauta bai tafi da ko daya ba.

bataji dadin hakan aranta ba,
ranta a dagule ta matsa ta matsa har saida manager na sales tay breaking normal protocol aka shiga computer aka dudduba mata sizes din kayan daya saya just to make sure wa sisters dinsan ya siya.

luckily enuf ta samu duk kayan they fits safiya's age whom is his blood sister. sai dataga haka kafin nan taji sanyi ta sissiya abunda zata siya snn suka kama hanyar dawowa gida

suna isa gidansun ko leke iyayenta batay ba ta kwanta akan makaken princess themed gadonta ta mika kafa elizebeth tazo ta rusuna kasa tana cire mata shoes din data hau kan gadon dashi, aqeela kuma tana unboxing duka kayan tsarabar tana shiryasu in a more fancy gift bags, while ita tana kwance tanata kirar layin mujaheed  all the way from south africa dan ya kara tabbatar mata if safiya is around that size and age, hira kadan sukayi da mujaheed din dan dama mashi kawai take iya fadan komi, duk da dabiarta na nuna classisms daya mata katutu. anan yake sanar da ita cewa kakansu hajy mairo mai tuwo ma zata dawo wann asabar din. kusan saura 4days ma kenan.

wani dan uban dadi taji aranta dataji hajy mairon zata dawo atleast she will get to spend more nd more time a gidan ran sartudays yadda taga dama batare da mamanta ta matsa mata ta dawo gida da yamma ba.


kamar wata mayya haka saida ta siya wani expensive botle na
Maison Francis Kurkdjian Amyris Homme perfume, a Fresh, woody, and very refined perfume. which According to Viora London is more classic Parisian ambrosia. perfect for sum one who is polished, intellectual and quietly wealthy kamar ibaad inta. da wata apple smart watch da niyyar kai ma ibaad su kyauta ranar asabar intaje tarban kakanta hajy mairo mai tuwo.

gani take tunda bai karban ma sister dinsa dukkan tarkacen chokolates inga ba ai dolene ran asabar ya amashi wayann kuma yasaka ajikinsa.

kafin ta gama waya da mujaheed maid dinta sun rage mata rabi daga kayan jikinta daga nan tashi kawai tay taje wanka, tay sallan isha ta tsalleka magrib sabida kyuwa, fav coffe dinta kawai aka kawo mata yaji madara tasha snn ta jawo computerta ta cigaba da karatu..

Daga nan gidan bappa zaidu kuwa ibaad na dawowa gida ya samu already maheer yana jan sallahn magrib a masjid dan haka aje bags din shpping din kawai yay akan gadonsa yay alwala yawuce masallacin shima ya jonasu

ayanah tana zaune a daki da tunanin irin saukin kai da kirkin da maheer ya nuna mata a case din satan nan, wanda har wajajen bayan isha kuma sultana bata leko dakin ba, ita tun tana fushi da ita harma abun yazo wuce mata, ganin ita dayane a dakin yasa tafara tunanin yin wanka...

dede lokacin an gama sallan isha'i kenan ibaad ya lallaba yashigo dakinsa inda ko taba bags din shoping din baiyi ba saiga maheer nan ya tura kofar dakin da sallama ya shigo kai tsaye.

idonsa kuwa na sauka akan shoping bags din yace woahhh damn..so may shoping bags.. and what are all these for? kuma kayan yan mata...wait man..did u go for shoping witout me..

ibaad yanakan cire takalminsa yace yeah, is for the girl..

maheer yace "what??amma meyasa? i tot sultana had enuf kuma she is ok dat they can share..ko dan sabida abunda yafaru dazune shikenan kuma kaje ka siya mata kayan sawa

ibaad zai magana maheer ya hade ransa sosai yace...look ibaad ayaanah fa yarinyace..nd so what if she took a piece of meat frm a pot..wann halin kowani yaro yanayinsa gigin kuruciyane ba dabiarta ba..i think both you and mummy are overly reactiive over this girl's issure, toh meye aciki dan ta dauki nama a kitchen taci?

cikin dakatar dashi ibaad yace "Dat is the problem maheer..i do not want her taking food or things..weda freely or stolen. beside i am very sure bata dauki wani nama ba, ka ma dena cewa waita dauka, dan nasan wallahi bata dauka ba.

baki bude maheer yace" 'harfa wallahi kakecewa.. hmm okay, tell me, why did u scold her then..

calmly yace "i know why
snn banason muja wani dogon surutu anan kawai kayi hakuri inhakan did not sit well with u. amma dan Allah kana duba condition inta..wancan karon ma kusan hakane ya faru yarinyar nan tun batagama farfadowa da jimami ba tazo gidan nan snn tasake shiga wani damuwa, nd then jiya ne kawai muka dawo da ita daga asibiti after spending 7 days in admission sai kuma in sake zuba ido adaketa akan namar da batama dauka ba?

cikin sauke ajiyan zuciya maheer yace "toh naji, hmm but you dont have to pay mummy with cash you knw.., sultana tagaya min duk yadda kukayi,she asked u to pay for damages nd u sent her the money, ibaad,..dat was rash nd stupid of you..in ita mummyn bata da hankali sai kai ka biye mata? yau in kuma baba yaji wann maganan me zakace masa?..i get that u want to protect her at all cost amma badai ta haka ba....kaima fa kasan halin mummy, farkon xuwanka gidan nan kaima batay kkrin kawace kudin abincinka agidan nan ba ne?.. son zucyarta yay yawa, inkana biye mata wallah sai kaga ta dawo da hakan kamr wani hanyar cuta da caca. dan haka ni zanje in ce mata ta maida maka kudadenka kawai yanzu nan ko wallah na hadaku duka da baba.

juyawa yay zai fice ibaad ya riko hannunsa da sauri da fuskan magiya yace maheer please Dan Allah kabari..i know what i am doing. kuma nasan inda kaine a position dina zakayi abunda yafi haka, kai bakasan ya mukayi da mummy dazu ba...i desprately want this girl to have a small moment of peace ne shiyasa ma nabada kudin bawai dan bani da hankali ba, please kaji tausayinta mana duk abunda ya faru da ita abaya akauyensu is still taunting her emotionly nd she is sick. wallah i will give twice as dis amount dan kawai a kyaleta, inkuma bawai so kake kajawo mata wani fitinan da zai saka ciwonta ya dawo full blown heart failure bane dan Allah kabari. let bygones ne bygone. let ur mum have peace in her marriage too,  tunda na rabasu lafya pls karkay involving bappa aciki just let it go for the sake of the girl.

kallon cikin idon ibaad din maheer yaketay all this while yana reading all the sincerity dats coming out of it..

idonsa atake yay jaaa jikinsa sai yay sanyi sosai.

ahnkli ya kwace hannunsa ana ibaad din yace "okay fine..for the sake of the girl, amma badan haka ba da wallah bazan kyaleta da kudin nan ba...excuse me!!

yana fadin hakan yay waje jin hawaye na tarowa a idonsa yana shiga dakinsa ya zauna abakin gadonsa dan jiyake zuciyarsa na masa wani irin zafi sosai da sosai daga bisani ya tashi yay wanka da niyyar zai kira ibaad ya rakasa gidansu abdl gaffar suje sharply ya amshi assignmnt dinsa ya dawo gida yayi.
#SURAYYAHMS

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025