Chapter 7&8
*DANGIN MUTUWA 🔥*
A story of full hatred, vengeance of the spirit, betray, unconditional love and heart touching.
*STORY & WRITTEN BY ✍️ FATIMA ISA MANU 🥀🌻*
*( DR TEEMAH ✍️ )*
*( SAHIBAR JAJIRTATTU 💃🌼 )*
___________________________________
_Masu neman littafin *DANGIN MUTUWA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following din channel ɗi na dan samu_👇***
___________________________________
****
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
____________________________________
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
___________________________________
*PAGE 7 & 8*
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
“ Ai koma mai take yi yanzu kam ya ci ace ta iso, tun ƙarfe sha biyu fa muna nan, kuma kunsan idan har yau bamu shiga nan gurin ba duk abunda muka yi ta wargaje.” AMJAD ya faɗa.
“ To wai ina AYMA ne?." MARWAN ya yi tambayar.
Bai gama rufe bakinsa ba suka ji tana cewa.
“ Sorry na tsayar da ku, SON ne bai yi barci da wuri ba.”
Kallo daya AMJAD ya mata yana jan tsaki.
“ Kasan na tsana tsuki kuma naga shi ne sabon abun da ka fara.” Ta yi maganar tana watsa masa kallo.
“ Ki hanani idan kin isa.”
“ Zan hanaka kuwa sai na nuna maka na isa har na wuce.”
“ Mtsw kin isan ne ki ka kasa yin…” Haɗiye maganar ya yi kawai yana saka hannunsa a aljuhun wondonsa.
“ Ai zaka iya ƙarasawa ba sabon abu ba ne a gurina, ka saba faɗamin.”
“ Dan Allah ya isa haka, sai ka ce baku girma ba har yanzu, tun kuna yara kuke faɗan nan har aka muku aure amma baku dai na ba, wai sai yaushe zaku dai na ne?.” MARWAN ya yi maganar a hassle.
“ Sai lokacin da ta daina raina ni.”
“ Ni ma sai lokacin da ka daina min gori da tsuki.”
“ Mu zuba mu gani.”
“ Eh din a zuba a gani, za muga waye da nasara.”
“ Mtsw.”
“ AMJAD ka daina min tsuki.”
“ Baza’a dai na ba AYMA.”
“ Wallahi kunyar ABBA nake ji da REYYAN da sai na kassara ka.” Ta faɗa kamar ta yi kuka.
“ Ko za’a gwada ne? Sai ki ajiye kunyar a gefe kizo mu gwabza.”
“ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un!!! Wai dan Allah ba za ku yi hakuri ba, ita zuciya kai zuciya haba YA AMJAD, ka ringa hakuri mana.” RUMAISA ta faɗa.
“ Ai ni bazan sake yin magana ba, idan sun ga dama su bari idan sun ga dama kar su bari, kan su ake ji, ga lokaci kuwa sai ƙurewa ya ke.” MARWAN ya ida faɗar hakan yana hararan su.
Shuru suka dan yi, kafin AYMA ta iso gurin ƙofar tana saka yatsarta, a hankali ƙofar ta soma buɗuwa.
MARWAN ne ya fara shiga sai RUMAISA, kafin AYMA, AMJAD na mara musu baya.
Wutan lungun ne ya fara ɗaukewa, ko tsoro babu a tare da su haka suka nufa cikin ɗakin. A bakin ƙofar suka tsaya suna jiran AYMA ta buɗe.
Kallon ƙofar ta yi tana cewa. “ Wani ya shigo nan gurin.”
A razane suke kallon kofar da mamaki, RUMAISA na cewa. “ Ta ya?.”
Kallon ta AYMA ta yi tana cewa. “ Anyi k’ok’arin buɗe kofar ne, amma an kasa.”
“ Kenan akwai wanda ya iya buɗe kofar sirrin bayan ke?.” AMJAD ya tambaya yana kallon AYMA.
“ Dama kafin BAFFA ya rasu ya faɗa mana ai, bayan ni akwai mutane biyun da zasu iya buɗe kofar sirrin, amma ba zasu iya buɗe kofar ajiyan sirrin ba.” A cewar AYMA.
“ Akwai aiki kenan a GANDARA’S family.” MARWAN ya faɗi haka yana kama kugu.
Daura hannunta AYMA ta yi a jikin kofar, haske ne ya mamaye kofar na wasu seconds, a sannu a hankali kofar ya fara buduwa.
MARWAN da RUMAISA ne suka fara shiga, kafin AYMA, AMJAD ya zo zai shiga kofar ta fara haske sosai.
Da sauri AYMA ta ce. “ Kar ka shigo ka tsaya, akwai robber a jikinka shi ya sa.”
Shafa jikinsa ya yi yana cewa. “ Babu komai fa a jikina.”
“ Ka duba mai kyau akwai robber a jikinka.”
Sake shafa jikinsa din ya yi yana ɗago kai ya kalle ta, kana ya ce. “ Babu fa AYMA.”
“ Akwai.”
“ To a ina?.”
Fitowa ta yi daga ɗakin tana isowa gurin shi, rigarsa ta daga tana saka hannu ta zame belt din jikin wondon sa, sannan ta jefar tana cewa.
“ Ni narasa me ya sa kake saka belt bayan an hanaka.” Ta faɗi hakan tana jan shi suka shiga.
Ƙofar ne ta rufe kamar ba’a taɓa yin kofa a gurin ba.
Babban apartment ne wanda ya ɗauki su gujeru da gado, amma duka an rufe da fararen kyelle, ga kuma kura da ya yi yawa, babu wuta a bangaren, hakan ya sa suka kunna wayoyin su.
Direct wani ɗaki AYMA ta nufa, AMJAD ma nan ya nufa yana haskawa da torch.
Fara buɗe gujerun MARWAN ya yi yana haska ko ina, ja baya ya yi da sauri yana ihu.
Da gudu suka fito suna nufo shi, haska gurin suka yi, RUMAISA na cewa.
“ Gawa kuma a nan bangaren?.”
“ Kuma kamar ya dade da mutuwa.” Cewar MARWAN.
“ Amma me ya sa bamu taɓa kallo ba sai yau?.” AYMA ta faɗa.
“ Hakan na nufin zamu samu nasara kenan, tunda har an fara bayyana mana wasu abubbuwan.” Cewar AMJAD.
AYMA ce ta ce. “ To amma gawar waye wannan?.”
Shuru suka yi, kafin AMJAD ya nufa gurin laptop din su.
Kunnawa ya yi, nan da nan haske ya kunnu. “ AYMA me password din?.”
“ AAMRR.”
Kallon ta ya yi yana cewa. “ Me hakan ke nufi?.”
“ Farkon sunayen mu ne.”
“ Waye dayan R din?.”
“ Ina ruwanka?.”
“ Babu kam.” Da haka ya saka password din.
Nan laptop din ya nuno masa duk shige da fitan dake gidan, tun daga safe har zuwa dare.
Wani baƙin mutum ne ya wuce, da sauri ya yi stop yana zooming, sake zooming ya yi yana kallon bayan mutum din.
Ganin hankalin shi yana kan laptop ne ya sa su suka iso suna kallo.
MARWAN na cewa. “ Kamar bayan KAWU nake gani.”
“ Ni ma haka nake gani.” Cewar RUMAISA.
Kallon AYMA suka yi wacce tuni mamaki ya daskarar da ita, zuciyarta na harban tara-tara, kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce.
“ Ba kama ba ne tabbas wannan bayan ABU na ne, kenan me hakan ke nufi? ABU ne ya ke aikata kisan nan ko waye?.”
CCTV camera ne ya ɗauke, da sauri AYMA ta fara bubbuga kan laptop din ko zai dawo.
Rike ta AMJAD ya yi yana cewa.
“ Me hakan? Ce miki akayi shi ya ke aikatawa ne?.”
Kamar ta yi kuka take cewa. “ To me ya fitar da shi da daddaren nan idan ba shi yake kisar ba?.”
MARWAN ne ya yi murmushi yana cewa. “ AYMA daɗi na da ke zuciya, za ki yanke hukunci ba tare da kinyi bincike ba.”
“ Hmm shi kenan amma bari kuji idan har shi ne ya kashe min UMMEY na sai na kashe shi da hannuna, zan manta da shi din mahaifina ne na kashe shi.”
“ Whatever yanzu dai mu tafi a nan gurin.” AMJAD ya faɗa yana kashe laptop din, kana ya kama hannun AYMA.
“ Sake min hannuna Malam.”
“ Bazan sa ke ba Malama idan kin isa ki ƙwace.”
“ Ku kam Allah ya shirya ku idan masu shiryuwa ne.” MARWAN ya faɗa yana rufe gawar.
Girgiza kai RUMAISA ta yi alamun sun fara gajiya da su.
Fita suka yi a ɗakin suna bin lungun da zai sada su da ƙofar fitan, nan ma AYMA ce ta buɗe kofar suka fita.
“ RUMAISA zo na raka ki sai na tafi.” AYMA ta faɗa hakan tana kama hannun RUMAISA.
Fuzge hannun ya yi yana kama hannunta me kyau, kana ya ce.” MARWAN ka raka RUMAISA sai ka wuce ɗakinka.”
Gyaɗa masa kai MARWAN ya yi yana saka RUMAISA a gaba suka wuce.
Ɗaga kai ta yi tana kallon shi, kafin ta sauke idanunta akan hannunta, a hassle ta ce. “ Ka sake ni na tafi na bar yaro shi kadai.”
Bai bata amsa ba sai ma jan hannunta din da ya yi yana nufan part na sa da ita…
COMMENTS AND SHARING PLS🤝🥰
*SIGN BY DR TEEMAH✍🏼*