Chapter 11&12
*DANGIN MUTUWA π₯*
A story of full hatred, vengeance of the spirit, betray, unconditional love and heart touching.
*STORY & WRITTEN BY βοΈ FATIMA ISA MANU π₯π»*
*( DR TEEMAH βοΈ )*
*( SAHIBAR JAJIRTATTU ππΌ )*
_______________________________
_Masu neman littafin *DANGIN MUTUWA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following din channel Ιi na dan samu_π***
___________________________________
COMMENTS SECTION
___________________________________
****
πͺ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*πͺ βοΈ
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Ζasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauΖi_.βοΈ*
____________________________________
*DIAMOND π STAR β*
*LADIESπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈ*
*(We stand together)*
π€π€π€
___________________________________
*PAGE 11 & 12*
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ππ«*
Kallon juna suka yi duk sun tsure, AYMA da ta gama rikicewa ne ta ce.
β Mutane biyu? Kuma masu muhimmanci, to waye ne?.β Tambayar da bata da amsa kenan.
Matsowa ya yi yana kallon bayan REYYAN din yanda yatsun suka fito, kana ya daga kai ya kalle ta yana cewa.
β Wannan fa yatsu shida ne?.β
Kallon shatin yatsu ta yi me kyau tana cewa. β Eh amma zai iya yuwa yatsu biyar din hannun ne, sai kuma na dayan hannun.β
β Kai ina ba haka bane.β
β Me ka ke nufi kenan?.β
β Ina nufin wanda ya yaguni REYYAN yatsun sa shida ne.β
β To ai MARWAN ma yatsun sa shida ne.β Ta yi maganar da mamaki kwance a fuskarta.
β To me hakan ke nufi?.β Ya yi tambayar da bayi da amsar shi.
A dakin ya yi sallah, dake ita bata yi hakan ya sa ta yiwa REYYAN wanka, tana masa yana kuka shi a dole an tada shi a barci, amma da yaga jini sai ya yi shuru bai sake magana ba.
Ganin kamar bai san da ciwo a jikin sa bane yasa ta cewa.
β Son bayanka baya ciwo?.β Ta yi maganar fuskarta dauke da damuwa.
β AMMIEY babu cizo.β
Dariya ta yi tana cewa. β Ba cizo ba, I mean babu ciwon da ka ke ji a jikin ka?.β
β AMMIEY babu.β
β Okay.β
Tana gama masa wanka suka fito yana dauke a hannunta, sai murmushi take yi duk da kuwa zuciyarta tsinkewa yake, ga kuma wani fargaban da take ji.
Da haka dai ta gama shirya sa lokacin har haske ya fito, duk in da tayi AMJAD na binta da kallo, bai san me ya sa ba haka kawai ya ji tausayin ta.
Kama hannun REYYAN ta yi kafin ta kalle πMJAD tana cewa. β Muje ko.β
Da haka suka fito.
Duk family members din suna waje, tana fitowa ido ya dawo kanta, kama hannun AMJAD ta yi da karfi tana jin yanda zuciyarta ke bugu da karfi.
Dubanta ya yi yana cewa. β Babu abunda zai faru sai alkhairi.β
Gyada masa kai kawai ta yi badan ta yarda ba.
Duban mutanen gurin ta yi gaba daya, lokaci daya kuwa zuciyarta ya tsinke, wasu zafafan hawaye suka fara wanke mata fuska.
Sai lokacin ta yarda cewa tabbas ta yi rashin mutane biyu masu muhimmanci.
A guje ta sake hannunta daga na REYYAN tana nufan apartment din ABU din ta.
Bin bayanta AMJAD ya yi yana kiran sunanta, bata ma san yana yi ba.
A parlon ta ja burki ta tsaya, kamar mutum mutumi haka ta koma, kallon gawar kawai take yi tana jin yanda zuciyarta wani abu mai dauyi ya tsaya.
A hankali take takowa zuwa gurin, gawa biyu ne a kwance an rufe da farin kyalle, a tsakiya ta tsaya tana kallon su.
Ko bata bude ba tabbas tasan wannan ABU ne, amma dayan ne take tsoron budewa.
Kama ta AMJAD ya yi, dago kai ta yi tana kallon shi, girgiza mata kai ya yi kawai.
A hankali ta taka zuwa gurin gawar, hannun ta na rawa ta fara budewa.
Bata san lokacin da ta saki wani kara ba tana ja baya, irin kisar da aka yi ma UMMIEY ta shi aka yi wa ABU din ta.
Kisar da ya fi muni a cikin kisa ukun da ake yi kenan.
Sai da suka yanke harshe kafin suka guntule hanci, sai suka kwakwule ido, suka barga kirjinsa suka cire zuciyar sa, sai suka zo kafa suka cire farce duka.
Kuka kawai take yi, lokaci daya kuma taji zuciyarta ya karaya da family gaba daya, ji ta yi bata yarda da kowa ba.
Ganin kukan da take yi ne yasa AMJAD jan farin kyalle ya rufe ABU din.
A hankali ya taka zuwa gurin dayan gawar yana shirin budewa, da sauri ta sa hannunta tana rufe fuskarta.
Yana budewa ya ja baya da sauri, yana kallon fuskan, baki na rawa ya ce. β RUMAISA.β
A razane AYMA ta bude fuskarta, sai a lokacin ta tuna bata ga RUMAISA a gurin ba.
Sabon kuka ne ya kufce mata, ita irin kisar da akayi wa AMMIEY aka mata, sai da aka cire kayan cikinta tas kafin aka kwashe gashin kanta gaba daya.
Hawaye ne suka zubowa a kan fuskan shi, wani bakin ciki ya mamaye ilahirin jikinsa, lokaci daya ya ji ya tsana family gaba daya, an kashe masa mahaifiyarsa, an kashe masa matarsa, yanzu kuma kanwarsa din da ta rage masa aka kashe.
INSPECTOR LAWAN da shigowar shi kenan ya kalle su yana cewa.
β Lawyer and general, yau kuma wa aka kashe?.β
Ko kula shi ba su yi ba, infact ma basu san yana yi ba, takowa ya yi har zuwa gurin da AYMA take ya sa hannu yana kama ta.
Saukan mari ya ji a kuncinsa na hagu da dama, da sauri AMJAD ya juyo yana kallon su.
A razane ya kalle ta yana cewa. β Ni kika mara AYMA?.β
β Bakai kadai ba har ubanka zan mara idan ka kuskura ka sake saka wannan kashin hannunka din a jikina.β
Shuru ya yi yana kallon ta, ganin yanda jikinta ke karkarwa ne yasa shi jin tsoro, ga idanunta din da ya bushe babu alamar hawaye ko kadan.
Juyawa ta yi ta taka zuwa gurin da RUMAISA ke kwance, bin jikinta ta yi da kallo.
Idanunta ne ya sauka akan yagunin da yake fuskarta, shuru ta yi tana kallon yagunin.
Wannan shi ne yagunin da aka yiwa REYYAN a baya, kuma gashi a jikin RUMAISA, kuma yatsa guda shida ne ba biyar ba, me hakan ke nufi kenan?.
Takowa ya yi zuwa gurin da take, kallon abunda take yi ya yi yana cewa. β Me hakan ke nufi?.β
β Ni ma dai ban sani ba.β Ta yi maganar tana rufe RUMAISA din, kana ta tashi ta nufa gurin ABU.
Ita har tsoron kallon shi ma take, ganin haka yasa AMJAD tahowa gurin da take, yasan sarai abunda take son dubawa, hakan yasa ya fara duba jikin ABU din.
Abun mamaki sai ga shatin yatsu hudu a kirjinsa.
Kallon juna suka yi, kafin AMJAD ya karewa gawar ABU kallo me kyau, kafin daga bisani ya tashi.
Fita suka yi a parlon har lokacin AYMA babu hawaye a fuskarta, sai ma dai jikinta din da ya dauka zafi sosai alamun zazzabi.
Kallon ta kawai suke yi, dan kowa yasan yanda take son ABU din ta, haka kuma sunfi shakuwa da RUMAISA a gidan, ko shi AMJAD da take kanwarsa basu shaku kamar yanda suka shaku da AYMA ba.
Direct dakin AMJAD ta nufa jikinta duk ya yi sanyi, tana tafiya kamar wacce babu laka a jikinta.
REYYAN ne ya biyo bayanta da gudu yana cewa.
β AMMIEY food.β
Ko jin shi bata yi bama har ta rufe kofar.
Juyowa ya yi yana kuka ya nufo gurin AMJAD da gudu.
HANIFAH ce ta zo ta dauke shi tana rarrashin shi, cizo ya mata a kafada yana kuka.
Da sauri ta sauke shi tana cewa. β Allah baka hakuri.β
Kama kafafun AMJAD ya yi yana cigaba da kukan shi.
KAWU AMADU ne yazo yana dafa AMJAD, kana ya soma cewa. β Ka shirya sai a sallace su.β
Gyada kai kawai ya yi yana daukan REYYAN suka nufa hanyar get din gidan dan sanar da LIMAN akwai janaβiza.
LIMAN yana kallon shi ya nufa hanyar masallaci dan yasan labarin gizo bai wuce na koge ba.
Ganin haka yasa AMJAD komawa cikin gidan, REYYAN sai zuba gwarancin shi ya ke shi daya.
Tunda ta shiga daki bata fito ba har aka kai ABU da RUMAISA, tabbas anyi rashin mutane biyu masu muhimmanci, dan duk mutuwar da ake yi babu wanda akayi kuka sosai kamar wannan mutuwar.
AMJAD ya kwankwasa kofa har ya gaji, gashi ya bar key din a ciki, haka ya koma dakinta ya kwanta.
Da ya ga bata da niyar bude kofar ne, sai ya nemo guduma ya fara bugawa kofar, tana ji ta mantar da shi, haka ya gama buge-bugen shi, da kyar kofar ta budu.
Tana zaune akan two seat ta daura kafa daya kan daya.
Kallon ta ya yi da mamaki yake cewa.
β Wai dama kina jina amma shi ne ki ka mantar da ni?.β
β Uhm.β Shi ne amsar da ta bashi tana kau da kai gefe.
Zama ya zo ya yi a gefenta yana kallon yanda taci kuka har ta gaji.
β AYMA?.β Ya kira sunanta a sanyaye.
β Uhm.β
β Kinci abinci?.β
Kuka ta fashe da shi tana fadawa kirjinsa, a hankali ta soma cewa.
β Ban san amfani na ba YA AMJAD, ban sani ba sam.β
Bai ce mata komai ba, cigaba da magana ta yi tana dago da kanta.
β Wai ni zasu kashewa ABU? Sun kashe min UMMIEY sun kashe min KHALIL, yanzu kuma RUMAISA, hauka suke ne ko omo suke sha, to Wallahi sai na nuna musu asalin two colour na, za su san ni suka taba, yanzu wasan ta faraβ¦
*FRIDAY AND SATURDAY BABU UPDATE NIMA ZAN HUTA π₯±π₯±π₯±π₯±π₯±π₯±*
*MORE COMMENTS MORE TYPINGπ*
_SIGN BY DR TEEMAHβπΌ_