Chapter 19&20
*DANGIN MUTUWA 🔥*
( The family of death ☠️)
A story of full hatred, vengeance of the spirit, betray, unconditional love and heart touching.
*STORY & WRITTEN BY ✍️ FATIMA ISA MANU 🥀🌻*
*( DR TEEMAH ✍️ )*
*( SAHIBAR JAJIRTATTU 💃🌼 )*
_Masu neman littafin *DANGIN MUTUWA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following din channel ɗi na dan samu_👇***
___________________________________
COMMENTS SECTION
___________________________________
****
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
____________________________________
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
___________________________________
*PAGE 19 & 20*
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
Sake warcewa ya yi yana cewa. “ Wai AYMA are you out of your sense? Me hakan ne, ki duba yanda yaron nan ya ke kuka saboda wannan ihun, kuma ai..” gagara ƙarasa maganar ya yi lokacin da idanunsa ya sauƙa akan yarinyar.
Duban AYMA ya yi yana nuna yarinyar da hannu ya ce. “ Waye wannan?.”
Kallon abunda ya ke nunawa ta yi, kana ta ce. “ Daughter na ne.”
“ Ok.” Ya fad’a, kafin ya duba gurin da su KARIMA suke, waɗan da tuni sunyi shuru suna kallon yarinyar, kana ya ce. “ Yau dai na taimake ku, idan kun ga dama gobe kuyi kalan shigan da ku ka yi yau, za mu ga waye zai taimake ku a hannunta, get out my friends.” Ya ƙarashe da d’aga murya.
Da sauri suka fita a parlon har suna buge juna.
Dawo da kallon shi ya yi kan AYMA yana cewa. “ Yar waye?.”
“ Nawa.” Ta fad’a a gadarance.
“ Yar waye?.” Ya kuma maimaitawa.
“ Nawa.” Ta sake fad’a tana juya kai gefe ganin kallon da ya ke bin ta da shi.
“ AYMA kar ki bari na kuma maimaita tambayar dana miki a karo na uku.” Ya yi maganar yana zuba mata sexy eyes din shi.
Turo baki gaba ta yi tana cewa. “ Nawa…”
“ AYMA!!!.” Ya kira sunanta da ƙarfi, wanda hakan ya sa ta tsorata lokaci daya, yarinyar kuma ta farka a razane tana kuka.
“ Yarinyar ALIYU BAFFA ne, wanda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.” Ta fad’a da sauri.
Sausauta murya ya yi yana cewa. “ Shi ne ke za ki ɗauke ta, bayan kin san yanayin yanda gidanmu ya ke.”
“ Babu yanda zan yi ne, ya bar min amana ne.” Ta fad’a kamar za ta yi kuka.
Takawa ya yi zuwa gurin yarinyar wacce tun ɗazu take kuka, ɗaukar ta ya yi yana cewa. “ Me sunanta?.”
Kallon yanda suka yi kama da yarinyar take, kafin ta ce. “ Ban tambaya ba.”
Murmushi ya sakar mata yana cewa. “ REYYANA.”
“ Sunan ya yi sosai.” AYMA ta fad’a tana kallon yanda tsanar yarinyar ƙarara a idon REYYAN, kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce. “ REYYAN me ya faru?.”
Kamar jira ya ke a tambaye shi, kawai ya fashe da kuka mai ƙarfi yana cewa. “ AMMIEY ace ABBIEY ya shuke ta.”
Da mamaki AMJAD ya ke kallon shi, a ransa kuwa tunawa ya yi da matar shi ALIYAH, ita ma haka take da mugun kishi idan ta kalle shi da AYMA suna tsaye, ko suna magana, ranar kwana za ta yi tana kuka, ko taki cin abinci, gashi yanzu yaron ta ya ɗauka.
Ta san sarai me ya ke tunani hakan ya sa ta ce. “ REYYAN ai ƙanwarka ce.”
Da sauri ya ke cewa. “ Ah ah ba shonta Allah.”
AMJAD ne ya ce. “ Okay me ta maka?.”
“ Ba shonta ne kawai.” Ya fad’a yana sauƙa a kan gujeran ya ruga da gudu zuwa waje yana kuka.
Da kallon mamaki suka bisa, kusan a tare suka ce. “ Namiji da kishi kuma?.”
Kallon juna suka yi, kafin AMJAD ya ce. “ Kamar yunwa take ji.”
Ƙarɓan ta AYMA ta yi tana nufan bedroom, AMJAD kuma ya yi hanyar waje gurin REYYAN.
Ana idar da sallan isha kowa ya fara rufe ɗakin shi, saboda an tsorata da kisan da akayi, baka jin komai a gidan in ban da kukan tsuntsaye dake cikin lambu.
Gaba daya mazan gidan suna zaune a parlour duk sunyi shuru, kowa da irin tunanin da ya ke.
Chan da shurun ya yi yawa ne KAWU BELLO ya ce. “ Ni dai sai nake ganin kamar da alamar tambaya akan wannan family.”
KAWU AMADU ne ya ce. “ Ni ma Yaya yanzu na fara tsorata gaskiya, lamarin nan kamar da tambaya, kullum fa ɗauki day-day ake mana.”
MARWAN ne ya kalle su, kafin ya sunkuyar da kai, cikin ransa kuwa cewa ya ke ‘ Babu mai gaskiya a cikin ku ai, sai ku ta shan wahalan. ‘
NAJEEB da ba wani magana ya ke sosai ba, tun da aka tafi da mahaifinsa bai kuma yin magana ba, shekaransa daya da AMJAD, amma har yanzu yaƙi aure, shi dama RUMAISA yake so, sai kuma aka kashe ta.
Kamar ba zai yi magana ba kuma, sai ya ce. “ Ina laifin ayi sauƙan Al-qur’ani Baba.”
Shuru suka yi kafin chan KAWU BELLO ya ce. “ Hakan ma ya yi, sai ayi gobe ko jibi ko?.”
Gyaɗa kai suka yi alamun sun yarda, kafin Baba ya ce. “ Babana yaushe ne shari’an naku?.”
Sunkuyar da kai ya yi yana cewa. “ Baba sai On 6th September In Sha Allah.”
“ To idan anyi shari’an za ka koma aikin ka ko?.”
“ To dai sai abunda suka yanke.”
“ To Allah ya bawa mai gaskiya, gaskiyar shi.”
Da Amen gaba daya suka amsa, kafin kowa ya tashi ya nufa hanyar ɗakin shi.
Yana shigowa ya tarar tana faman zubawa HANIFAH masifa, tana yi kamar zata dake ta.
Da sauri ya iso yana cewa. “ Me kuma ya faru?.”
Kuka HANIFAH take tana cewa. “ Yaya Wallahi bani ɓace sharri kawai suke min…”
Buge bakinta AYMA ta yi tana cewa. “ Idan ki ka kuma cewa bake ɓace HANIFAH sai na kashe ki a gidan nan.”
Kallon ILHAM ya yi wacce ta rakube a gefe tana kuka, ga REYYAN da REYYANA waɗan da suka natsu, da alamu dai tun ɗazu ake masifar.
Mai da kallon shi ya yi kan HANIFAH yana cewa. “ Me ki ka yi?.”
“ Yaya videos din ILHAM ne da wani, ni kuma bansan mutumin ba.” Tana maganar tana kama bakinta wanda tuni ya fara jini.
Duban AYMA ya yi yana cewa. “ Video kuma?.”
Da sauri ta ce. “ Ba video zaka ce ba, videos zaka ce,,, ban da ƴar iska ta san waye mutumin fa, kuma ita ta tura ILHAM hotel din.” Ta yi maganar tana noshin HANIFAH da ƙafa.
Kukan ta ya sa mutanen gidan fitowa suna nufan gurin su.
Da gudu Mamarta, wacce ake kira da Anuty Larai ta nufo su tana cewa. “ AYMA kashe ta za ki yi?.”
“ Ai ta cancanta kisan ne, ƴar iska kawai.” Tana faɗan hakan ta kai mata noshi a ciki.
Ihu HANIFAH ta saka tana cewa. “ Wallahi Anuty bani ɓace.”
“ Idan ki ka kuma cewa bake ɓace, HANIFAH idan ban kashe ki ba ki canja min suna.” Ta fad’a tana hararan Anuty Larai din.
Cike da masifa Matar KAWU BELLO ta ce. “ Ai idan HANIFAH ce komai ta aikata zan yarda, dama ai barewa ba ta yi gudu ɗanta ya rarrafa ba.”
Dayar Matar KAWU YA’U ne wacce ake kiranta da ANUTY AMARYA, Mahaifiyar ILHAM da NAJEEB ita ta ce. “ Me ya samu ILHAM din na ganta a rakube haka tana kuka?.”
Sai yanzu idon su ya kai da ILHAM din, Yayanta NAJEEB ne ya ce. “ ILLY me ya faru.”
Kukanta ne ya ƙaru tana buya a jikin labulen.
Idan akwai abunda NAJEEB ya tsana a duniyar nan shi ne a taɓa masa kanwarshi daya tilo,,, kamar wanda aka hura sai gashi a gaban ILHAM din.
Da gudu AYMA ta isa gurin su tana cewa. “ Yaya NAJEEB kar ka buɗe ta.”
Da mamaki ya ke kallon ta, kafin cike da masifa ya ce. “ Me ya same ta?.”
“ Ga can wayata a gefen REYYAN ka ɗauka ka gani.”
Kallon mara gaskiya ya bita dashi kafin ya nufa gurin wayan ya sa hannu ya ɗauka.
Dake wayan babu security, hakan ya sa ya kunna.
Baka jin komai sai kukan ILHAM tana cewa. “ Dan Allah ka barni, Yaya NAJEEB Anuty AYMA dan Allah kuzo ku ceceni.” Da sauri ya kashe video yana kallon mutanen parlon, waɗan da jikin su ya yi sanyi.
Duban AYMA ya yi yana nufo gurin su, ba shiri ya wankawa ILHAM mari, yana k’ok’arin fuzgota a cikin labulen.
Sake tare ta AYMA ta yi tana cewa. “ Yaya ka tsaya ka ji..”
Bata gama rufe baki ba itama ya wanka mata mari, duk da hakan bata bari ba ta sake rike shi tana d’aga murya ta ce. “ Ka bari zan muku bayani.”
“ AYMA idan ki ka bud’e baki ki ka sake magana sai na miki ba dadi.” NAJEEB ya fad’a yana ture ta gefe.
Buguwa kanta ya yi a jikin kujera, kafin ka ce me tuni jini ya fara zuba.
Da gudu AMJAD da MARWAN suka nufo su, AMJAD ya rike AYMA, shi kuma MARWAN ya kama NAJEEB yana cewa. “ Ka bari mana tun da ance ka bari.”
Kukan ILHAM din ne ya sa suka yi shuru, tana kuka ta soma cewa.
“ Yaya Wallahi aike na HANIFAH ta yi zuwa hotel din, kuma…kuma cewa ta yi naje gurin ƙawarta zata bani abu na kawo mata, ni ban san waye bane a hotel din, shi…shi…shi ne sai…ya rufe ko..k’ofa, kuma dama kafin naje na kira ANUTY AYMA a waya… amma network ya hana naji me take cewa, ni.. na mai da ce..cewa ta yi na je, shi ne na shiga ɗakin.” Ta ƙarasa maganar tana fashewa da sabon kuka.
Kowa tun da jikin shi ya yi sanyi, Anuty Amarya kam kuka ta fashe da shi.
Kafin ka ce me tuni MARWAN ya zuba tsalle ya fara dukan HANIFAH, ta ko ina kawai kai mata naushi ya ke.
Babu wanda ya hana shi, sai ma taya shi da ABDUL ya yi, sai da suka mata -jina kafin suka bar ta ganin ko d’aga hannu bata iya yi.
Zame jiki kowa ya fara yi yana nufan dakin shi.
Parlon ya rage AMJAD, AYMA, MARWAN, NAJEEB, sai ILHAM din da ta ki fitowa ta zauna tana kukan takaici, sai HANIFAH da take kwance kwance kamar gawa.
Ɗaki AYMA ta nufa tana ɗauko hijab babba, ta zo tana rufe jikin ILHAM din da shi.
Kana ta kama ta suka nufa ɗaki, tana tafiya tana ɗingishi…
*SIGN BY DR TEEMAH✍🏼*