ABUNDA KE 'BOYE...

26

by @surayyahms

Susum writer:

⏯️2️⃣6️⃣_ABUNDA KE ƁOYE💫_

Surayyahms

https://www.arewapen.com/book?id=68b893fa83afa58b60006705

***

***

wajajen 8.30pm maheer ya kammala wankarsa yafito direct ya tsaya atagaban gadonsa kuqunsa daure da thick white towel da wani dankarami daya riqo ahannun shi yanamai dabbing ruwan jikinshi slighly, wayarsa dake kan vanity table ya daga yana daga tsayen ya rubuta short text mssg ma ibaad akan zai rakashi gidansu abdl gaffar ynxu, yana gama tura masa text din yawuce gaban standing mirror yana kallon kansa a madubi not giving much tot ma yadda yaga duk ya xube kwana biyun nan yay kwafa kafin nn ya jawo kayan shafe shafensa yahau shafawa a smooth healthy skin dinsa ya taje kansa yay fess..

sharply ya saka wasu kananan kaya da hadadden jacket akai yafesa turarensa me qamshi kafin nan karfe tara yacika har ya fito waje,

kai tsaye yaje ya bugawa ibaad kofarsa, yana tsaye awajen after like 7 min sai gashinan shima ya fito sanye da rigar sanyi ta hoodie ajikinsa irin clean pure white colour innan da wandon blue jean da white sneakers duk sunyi matukar kyau har bazaka iya saurin bmbmce waya yafi haduwa dan kuwa danyen shekarun samartakansu na nunawa sosai..

Suna ficewa agidan bada jimawa ba saiga sultana tayo sashensu, ahnkli take tahowa tana waige waige looking so scared but dertemined to come nd tell ibaad the truth dan tun dazu abunda tama ayaana ya hanata sakat yana samata fargaba...

deciding tay gara kawai taje tagaya ma ibaad gaskiya inyaso ko dukan ta zaiyi still dai zataje tabawa ayanahn haquri halama taji tausayinta ta yafe mata.

tun bata karaso kofar dakinsan ba taji kirjinta yana bugawa da wani dan uban karfi kamr zai fita,acikin dauriya ta tsaya saida tay tsayuwr kusan minti biyu kafin ta tattaro courage ta fara buga kofar ahnkli har saida ta lura kmr a kulle yake snn ta koma ta duba na yaa maheer shima ganin da alama duk basu nan yasa tasauke wani maqudan ajiyan zuciya tare da barin wajen da bala'in sauri, direct ta koma quest room din ta cigaba da zamanta anan cikin sanyin jiki da tunani duk hanklinta ba akwance ba musmmn inta tuna cewa ita tay satar naman, kuma ayaanah bata tona mata asirinta ba har awajen yaa maher tay shiru...all this feelings are very new nd weird to her, ko karatu ta kasa yi sabida damuwa cos she tot she cud have defended her too, sosai taji babu dadi aranta data bari jin tsoron ibaad datakeji ya hanata yin abunda ya dace wa ayaanah dazu.

bangaren ayaanahn kuwa kusan komi ya wuce mata dama ita bamai saurin riko bace, she was calm abit musmn ma data shiga bayi ta watsa ruwan dumi ajikinta tay wanka tazo ta canza kaya.

tun bayan iddar da sallan ishai tabi ta kwanta time to time haka abun daya farun na dawowa mata ranta but she still wonders haryaushe ne sultana zatadena buya ta dawo cikin dakinta ta kwanta, tadauki tsawon lokaci tana wnn tunanin har tazo tadena tunanin qaddarar rayuwarta dana ummanta ya dawo mata afresh wasu silent hawaye na zuba a idonta tanaji kmr mafarki takeyi ba gaskiya ba. inta tuna irin mugun halin baban ta, da kuma irin zafin dataji da addanta ta mutu sai kuma tay shiruuuuu thinking maybe duk abunda ya faru dasu hala shine musu mafi alheri.

tama kasa iyayin tunanin makomar rayuwarta anan gidan musmmn tare da ibaad, da kuma mutane daban daban datagani wasu masu kirki, wasu mugaye. ganin tunanin zai iyafin karfin kwakwalrta sai ta dauki qur'anin gefen gadon ta mike zaune da pillow a kirji tarufe dogon gashin kanta da mayafi tahau karanta suratul Rahman ahnkli tanayi tanamai tuna nasihohin ummanta da na addanta game da rayuwa. tasan duk yadda akayi dolene kawai tay hakuri ta daure snn ta amshi sabuwar qaddararta, da wn sabuwar rayuwar, da kuma wayannan sabbin fuskokin dake zagaye da ita ynxu, duk dama aranta bata taɓa tsammanin hakan zai zo ya tunkareta adede wannan mayucin shafin qaddatararta bayan ta rasa addanta a duniyan nan ba.

karatun qur'ani ta dingai tana hawaye tana kuma tunaninsu har saida taji sanyi snn ta aje qur'anin ta kwanta cikin sauke ajiyan zuciya mai nauyi..

gidan was quiete babu motsin sultana bare na ammi babba dan tunda ta amshi kudin ibaad ta biya zinariyar mace kudinta sai taji sakat, yau wuni tay a dakintan suna waya da babbar kawarta hajiya ramatu banda zage zage da kulle kullen makirci gameda tafiyar da mijnta yay da ammi karama babu abunda sukeyi..

wani irin zugata Hjy ramatun tay akan karta sake takyale fatima ta cuceta a banza duk tsiya ta sake karban million goman nan ahannunsa kota halin kakane dan ta huce takaici.

bangaren su ibaad kuwa tunda suka fita wajen abokai ba su da dawowa gidan ba sai can wajajen karfe sha biyu saura na dare, they all came back very tired nd glad they went out dan spending time da sukay da abokan nasu awaje sosai yadan rage musu wani family tension acikin zukatansu...

washe gari da sassafe tun kafin aje sallahn fajr

sultana tay sneaking ta dawo dakin ta samu ayaanah nakan bacci sai tay maza ta cire kayanta tashiga bayi tay alwala bayan ta fito ne tazo ta tasheta akan tay sallah, kafin ayaana ta gama sauka daga gado taje tay alwalah tafito tazo ta samu har sultana ta fara nata sallahn sai kawai ta jonata itama bayan sun gama ne sanyin Ac ya buga ayaanah sosai ta fara wani irin tarin sanyi dayaki tsayawa, tun suna matsewa har sultana tafara jera mata sannu sannu dakyar ayaanan tasamu ta kwaco numfashinta tace mata ita ruwa zata sha ta kawo mata ruwa..nan kuwa sultanan ta fito da uban sauri danta neman mata ruwan dumi duba da anriga anhanata shan ruwan sanyi musn da sassafe.

lkcin daf ana fitowa daga sallahn fajr ammi babba daga farkawan ta dinga kwadawa layin bappa zaidu kira akai akai kamr yaqi amma sai ji take akashe, wani irin baqar kishi take taji duk ya cika ta taciki ta kasa tabuka komi sai juyayi dan tun batason tasaka zarginsa aranta na kasancewa tareda fatima har abun ya fara samun waje acikin zuciyarta,

sallan ma yau a daddafe tay shi tabita zauna akan sallayar ranta a mugun dagule tanata rubuta masa text message akai akai akan ya kirata tana son magana dashi.

bayan sallanh fajr maheer ne yafara shigowa gidan da sauri sauri akan zai haura sama yay wanka yafara shiri dan yana da 8am on d dot test yana kuwa shigowa ya hango sultana da flask din ruwan zafi ahnunta tana sauri sauri, gyaran murya yay abazata tatsaya cak tay freezing musammn ma da suka hade ido dashi saidai

ganin shidayane anan taji gara kawai ta fito fili tagaya masa gaskiya akan case dinta da ayanah inyaso shi sai ya ma yaa ibaad din bayani gameda abunda ta aikata ma ayaanahn jiya na boye asalin gaskiya

karasowa tawajen sa tay da mugun sauri tun kafin ta fara gaishesa yafara tuhumarta me zatay da flask din ruwan zafi da sassafe, tuna masa tay cewa an hana ayaana yawan shan ruwan sanyi ne da safe shiyasa taje kitchen ta kawo na zafin.. cikin gamsuwa da hakan ya juya zai wuce ya haura dakinsa sai tayi caraf takira sunansa."ya maheer can i talk to you??..da mamki ya juyo ya kalleta ganin ta sako fuskar tausayi yace"..ke kuma meyene badai zakice min bazakije schll yau ba? cikin i ina tace a'a yaa zanje,i iii just want to talk to u abt sumtin, nd i promise it wont take time

..dawowa yay one step back kusa da ita yace ehen inajinki

dede nan ibaad ya shigo gidan shima basu lura ba da tunanin kar ya katsesu saiya tsaya ata can bayansu batare da yay motsi ba, sultana ta sunkayar dakanta kasa ahnkli tace yaa maheer, zan gaya maka wani abun amma dan Allah don't judge me, ya mata kallon go ahead, tace..toh dama jiya ne nace ma ayanah muje waje musha iska sai naje kitchen sai naga soyayyan turkeyn da mummy ta ajiye shine na dauki guda uku nazo na bata guda daya nasata dole itama taci dan muyi hira, itafa batace ma zataci naman ma nine na dingace mata sai taci.. nd. and...it was bcos of me she also came to fetch water,shine kawai naji wai mummy ta kamata tanata ce mata barauniya, yaa maheer ..its totally my fault, wllh bata daukar ma mummy komi ba,..

dedenan ta fara hawaye ahnkli

tace "kuma ai naga yaa ibaad ne aciki shiyasa naji tsoron nagaya ma mummy asalin abunda ya faru a lkcin...can you pls tell him da it is not her fault?i feel really bad for putting her into dis mess.

....baki a bude maheer ya dinga kallonta sai can yace ohh dama kece munafukar da kika dauki naman shine kikay shiru saida aka gama cin mutuncin yarinya zakizo kina wani min bayanin karya daga baya?

tana budan baki zata amsa taji taauuuu ya dauketa da mari batasan sanda ta sake flask din akasa ya fashe da karfi ba. lkacin kuma lekowar ayaana ta wajen kenan jin karar fashewar flask din yasata ta razana ta koma da baya tadan tsaya acan nesa tanata kallonsu.

ta inda maheer yake shiga batanan yake fita ba. daga kuma ta budi baki zata sake magana sai ya kara wanka mata mari, saida ya mareta sau uku, snn kuma yabi ya zare mata ido ya hanata yin kuka...

yace munafuka kawai me baqin hali, u had all the chance to tell me d truth tun jiya aike na samu anan kina kukan makirci kikaki min karya konima tsorona kikeji a lkcin? muguwa kawai ai sainaci ubanki kika sake aikata irin wnn halin nd ure very stupid for telling me not to judge u

ayaanah was teriffied dataga irin hukuncin da maheer yay ma sultana dan duk tunaninta ay shine namiji me tausayi da saukin hali agidan, sai taga kmr ma yafi ibaad masifa da mugunta, dan duk tsiya dai tasan ibaad saidai yace zai daketa intay wani abu amma haryau dai bata taba ganin ya aikata hakan ba.

cikin tsananin razana sultana take kuka at same time tabi ta toshe bakinta kamar yadda ya umarceta dan baison kukanta yajawo hanklin mamansu har sai yagama masifeta, masifan yake mata saidai tunda ta juya baya taga ibaad na tsaye ata bayansu atake tafara jin kamar numfashinta na tafiya tsabar tsoronsa datakeji kmr zata yanki jiki ta fadi ta suma

..shide baice komi ba harsaida maheer ya gama fafala mata mari ya masifeta tasss snn yazo ya karbeta a hannunshi yace masa yay mata uzuri

aima tay kokari ma datazo tagaya gaskiyan he shudnt dicredit her like this..

sama sama yace mata karta kara yin hakan, snn tana fadin gaskiyarta koda a gaban wayene, jin tsoronsa is not an ezcuse for her to hide things, and this shud serve as a lesson to her,..

haquri ta dinga basu, har ibaad din ya sallameta batare da ya mata wani zazzafan fada ba.

..wuce ayaanah tay da sauri tahaura sama ta wuce dakin ta zauna akan gado tanata kuka.

acikin ruwan sanyi ibaad ya fahimtar da maheer cewa is best sudinga sassauta ma sultanah hukunci,ayi masifar dai amma banda duka, sabida karda next time wani abu yafaru da ita kanta agidan tafara boye musu asalin gaskiyar halin da take ciki.

maheer baiy gardama ba kuwa ya fahimcesa daga nan kowa yaje room dinsa domin shiryawa...

daga dakin su sultanan kuwa ayaanahce tashigo da sanyin jiki ta tsaya agefenta da niyyar bata hakuri, sede tun bata bude baki ba sultanan ta riko hannunta tana kuka suka hade ido cikin magiya tace ayaana dan Allah kiyi hakuri kiyafe min kinji? i dint knw what came over me. kiyi hakuri bada son raina nay shiru jiya ba, what happen was wrong, nd i wll neva do this to u again..dan Allah ki yafe min karkiji haushina kinji?

tausayi yasa ayaanah tafara zubda hawaye ahnkli tace "aibabu komi ni banyi fushi ba, daganan sai sultanan take gaya mata irin tashin hanklin data shiga jiya, da tsoro, da guilt daya hanata zuwa cikin dakin jiya tamata bayani, sabida gani tay kamr bata kyauta mata ba. ayaanah taji tausayin sultana bana kadan ba, tagane cewa tana da zuciya me kyau. bayan sun fahimci juna... sultana only confuses her more akan yadda dacan take kallon maheer a matsayin me saukin kai da sanyin hali a idanunta

tace ma ayaanah ai duk da murdadden halin yaa ibaad gara mata shi,baya daukar hukunci da zuciya da zafi sai yay bincike, amma ya maheer he will alwys act rarshly before even thinking abt the consequences..

...duk hakan da sultana take fada mata sai ya bala'in rage mata wnn shauqin da duk wani karfin amincewa da ta dauke maheer mai saukin hali acikin idonunta dashi...

after a while bayan sun gama surutunsu suka shiga wanka sultana ta fito tafara shirin schl sai ta bawa ayaana wasu sabin kaya ta karba ta saka ajikinta nan da nan wani sabon fahimtar juna yafara fara shiga tsakaninsu.

ata bangaren ammi babba kuwa dakyar ta bar kan sallahya taje tay wanka, badama taji dan motsi ko kara sai tajuyo da sauri ta kalle wayatta, tana tsaka da saka dankunne agaban madubi taji karar bude kofa ahankli.

maheer ne ya shigo all dressed up in pure black zagner suite da yay masa matukar kyau sede fuskansa ba sake ba, ya rusuna cikin ladabi yace ina kwana mummy...tana kan kallonsa tace lafya kalau ya naga har ka shirya da wuri haka?saddiqa ce fa zata muku breakfast yau.. dan wallah bana jin dadi jiya ai kuna sane babanku ya dauki budurwarsa suka bar kasar nan amma cikinku aka rasa wanda zai iya gayamin hakana na lalata kudina da lokaci na shirya masa abinci abanza..

da karamin rashin tsoro a idanunsa yace" munyi waya dashi jiyan sauri yakey lkcin shiyasa bai gaya miki ba, kuma daya kirani da daddare ai yace ya tura miki text messg ko baki gani ba?

..."da mugun mamaki ta juyo tana kallonsa tace "ohhh hmm, dama yana da lkcin kiranka jiyan amma ni shine text din kawai zai iya turamin? cikin karkada kai tace hmmm lallai ina ganin walakanci agidan nan, gashiku sam bakujin tausayi na upon duk wahalar danakey dan na nuna muku cewa zaman lafya nakeso agidan nan amma dolene dai sai an tunxira ni...

cikin katseta da wani salon manyance ahnkli yace but mummy you have to be careful akan wasu abubuwan da kikey agidan nan, which i think sune suke sakawa baba yake miki wasu abubuwan.... wani uban harara ta banka masa tunma be gama rufe bakinsa da tsawa tace kuttuman uba?maheer mani kake gaya wa haka?ta nunasa da yatsa" kai karka kara gaya min maganan banza anan..uban menake muku a gidan? kaidai fito fili kawai kace wata mace ta shanye ubanka baya ganina da daraja a idonunsa yanzu...

sounding sooo stiff nd arqumentative yace"...or, maybe he need alittle quite somehwer else, kece kullum fada tsakaninki da shi akan ammin ibaad, kuma haryau bai kare ba, mummu ke kadai kin tsani duk wani baqo yazo gidan nan, kin tsani ibaad, kin tsani yarinyar da aka kawo which u knw ba dawwama agidan nan zatay ba..shin baki tunanin duk sune suke gajiyar da baba yake miki haka?

hannu ta daga azafafe zata wanka masa mari ya rike hannuntan yana kallonta da calmness a idonsa ahnkli kamar wanda baison wani yajisu yace "mummy calm down" har cikin ranta taji tsoron cold voice din dayay maganan dashi ..manyan idanunsa ya dasa anata snn yace"nafasan cewa kin karbe kudi me yawa awajen ibaad, nd i knw how much u took frm him duk dan sabida yarinyar nan..and before u even started shouting at me kisani bani kadai nasan hakan ba, sultana ma tasani, dan itace tafara gayamin kafin nima na binciko

...even if ibaad does not plan to expose u, kinsani idan baba yazo yaji maganan bazaiji dadi ba musmn idan yazo yasan cewa yarkice ma tamiki satar nama ba yarinya ba...

wani irin kwace hannunta tay anashi da karfin hatsala tace da Allah sakeni karya kakeyi, i cought her red handed...cikim katseta yace "yes".. but sultana has already confessed har agaban ibaad cewa itace ta dauki miki namanki ta bata.. mummy, pls stop what eva ure doing dan Allah... ki rabu da yarinyar nan .bcos if u cant muma bazamu iya yin shiru akanki batare da mun gaya ma baba wasu abubuwan dakikeyi agidan nan da bayanan ba.

uve alwys said that bana kaunarki...well let me tell u, ranar da kika bar gidan nan da mukazo shiryawa zamuje schl da ibaad i came to dis room nd i picked ur phone up, na bude na naga text messgs da kukay ta exchanging da kawarki akan maganin dakikazo har schll kikamin karya akai wai na ciwo ne, mummy inda ace bana kaunarki wallah da sai na gaya ma baba kuma na nunasa abunda kiketa shirya akan rayuwarsa...but for god sake mummy pls dan Allah kibar aikata wann abubuwan.

u know i wll alwys know the truth..i am curently the best law student..but i cant save you if u cant save urself mummy dan Allah kibari wann batun sihiri sihirin let peace reing in this house for once..

wani irin cak tay da fuskar ta tana kallonsa a kangare ahnkli numfashinta yadinga fita sai tarasa borin kunya zata masa ko borin hauka..cikin jin tsoro da shan mamkn yanayinsa saitay maza taya juuya masa

baya cikin hatsala da fushi ta fashe masa da wani irin kukan makirci tafara wasu irin irin magangnu out of self pity tana cewa ai sharin shaidan ne kuma ai tunxirata ubansa yayi

obseving inta yay sosai snn yay murmushi me sanyi kmr bashi ba, jawota yay ta zauna akan gadon shima zama yayi kusa da ita yadan rungumeta yana rarrashinta daga ganin ta kasan ta mugun girgiza da kalaman nasa, sai kuka take tanata maganganu cikin borin kunya sai yay amfani da wann damar yayi silencing dinta gabaki daya akan haukar borin datakeyi a gidan nasu gabaki daya, he showed her yana tare da ita sosai kuma yana sonta amma bata wannann hanyar data dauko na cutar da mahaifinsa da yan uwansa ba.

bata da choice haka tay mazamaza ta zubar da makaman yaqinta a idanun maheer bawai dan ta saduda ba sai lura data cewa yasan abubuwa dayawa akanta ynxu wanda zasu iya kashe mata aurenta na har abada gashi mijinta yace inta sake furta zata tsine masa toh abakin aurenta, bata taba jin nadaman barin maheer ya karanta law ba sau yau, dan tsabar bincike iya kwakkafinsa da wayonsa yay yawa kuma tasan zafin ransa sarai dolene sai tabi shi a hankli...

bayan sun kammala maganan duk sai ta fasa zaman dakin ta fito kitchen ta fara shirya musu abincin karyawa da already batay niyyar yinsa ba.

sultana tagama shirin scholl kenan wayarta ya fara kara tana ganin ibaad ne da sauri ta dauka a ladabce tay sallama, yana amsawa yace tacewa ayanah tazo ynxun ta sameshi a dakinsa. tana sauke wayar a kunnenta tace ma ayaanah yaa ibaad yana nemanki a daknsa, itama bata wani jira ba ta cuccusa dogon sumanta acikin dankwalinta snn ta fito kai tsaye ta wuce dakin nasa..

kwankwasa kofar takey tun tanayi ahankli har tafarayi da karfi yana gama waya da mum dinsa ya miƙe yaje ya bude mata kofa batare da ya kalleta ba ya dawo wajen zamansa ya zauna yanakan karasa saka takalminsa, satan kallonsa ta dingayi harta karaso ta gabansa ta dan rusuna ganin ya kara mata haske yay kyau suman kansa yay baki ya wanku haryana sheki musmn daya saka wata well ironed dark blue long sleeve shirt da beige trousers wani dan uban qamshin xerjof naxos na tashi ajikinsa kamr ka lashe shi..

ayaana tay kasa da kai cikin ladabi muryanta na fita ahankli tace "ina kwana? tun be amsa ba idonta ya ciko da wani irin ruwa muryanta na rawa rawa tace"sultana ne tace min kana kira na.. kallonta ya karayi shima ahankli snn yace toh saiki bari na amsa gaisuwar kafin ki cigaba da fadin abunda bantabayeki ba, dan shiru tay,

harya gama saka takalmin da wani irin tausayi a cikin kwayar idonsa ya kalle sunkuyayn kan nata ahnkli yace "ya jikinki? wani irin sanyin muryansa ne taji ya rtsata sosai adan sakalce tace masa "da sauki" yace "toh yay. kai tsaye ya mike tsaye ya jawo wani madaidacin akwati acikin set in nasa ya aje agabanta, snn ya kalleta yace "zaki iya tuna duk abunda nace miki jiya? kanta na kallon kasa tace ehh,kace kar nasake daukar abun da banawa ba.. hawaye suka kara ciko idonta har suna neman zubowa,..atake ya haɗe rai yace" shikuma kukan dakike min ynxu na miye ne? ke na taba dukanki ne ko nataba cinyeki? da sauri ta girgiza kanta yace "idan har naga hawayenki daya akasa zakiga abunda zan miki'..

sauri tay ta tsare wanda ya fara zubowar da hannunta

yana daga zaune yace "i dint call u here to scold you, zan jadadda miki, kisani duk sanda kika taba abunda banaki ba shine zaki jawo makanki cin mutunci da zagi ako ina ba lallai sai gidan nan ba. dan haka ki kama kanki banason fitina, ko shishhigi,, bana son yawan surutu, ko son karban aro, babu ruwanki da abunda bana ki ba kinaji na ko?.

duk wani abunda kikeso a duniyan nan kizo ki gayamin, inbe fi karfina ba zan siya maki, idan bana nan kuma ki koyi hakuri inna dawo kizo ki gayamin ko karfe nawa ne bazai gagareni ba..kinga baki da lafyar jiki, duk wnn son kukan dakikeyn kisan yadda zakiy dashi ya dena zuwa inba so kike kema ayi janaizar ki da wuri kmr na yar uwarki ba, duk wnn shirmen ma yakamata kina yawan kiyayewa sabida mahaifiyarki tanaso taga rayuwarki yayi kyau, inkika zauna cikin ciwo kinga wata rana sanadiyarki zatazo tana kuka ko kinasone tay kukan rasaki kema???

hawaye masu zafi suka kara cikowa cikin idon kanta akasa ta girgiza mai kai da sauri da kuma muryan kukan tace "a'a banaso. amma...amma yaushe ummanan zatazo?kai tsaye yace" nima bansani ba. "see,. just forget abt her. inbaki nitsu kindena yawan mana koke koken banza ba bazata taba zuwa ba! da yaranta ayanayinta sosai ta share hawayenta da sanyin jiki tace mashi toh ai zan dena kukan

..baice komi ba ya kalle akwatin snn ya kalleta suna hade ido yace "kayanki ne aciki. karki manta idan kinason wani abu come to me first. tace mishi toh..sai ta danyi shiru bayan ta gama goge fuskarta ta kallesa tace nagode..baice komi ya dau wallet dinsa ya ciro kudi five hundred naira sabbi ya bata guda goma aciki yace ki aje acikin kayanki, shima naki ne.

hajiya zata dawo nan da kwana uku zamu wuce can gidanmu inda zaki zauna tare da ammi kafin musan me zaay anan gaba dan haka ki zama cikin shirin tafiya. tashi muje kije ki gwada kayan..snn ki tabbata kin mayar ma sultana nata dakike sawa. cikin ladabi tare da girmawa takara ce mishi toh..nagode" tana mikewa yasa hannu yadauki akwatin dakansa suka fita tana binsa abaya har ya kai matashi har kofar dakin sultanan snn ya kyaleta awajen ya juyo abunsa.

kallon inda yabi ta dingayi tanajin matsayinsa da kimarsa na dada yawa aranta bata daga ido akansa ba kuwa har saida taga ya bace a sashn gabki daya..

kwankwasa kofar tay sau daya sultana ta fito jin yadda qamshin turaransa ya kama wajen tafara waige waige

kusan atare suka shigo da akwatin ciki tana tambayar ayana a ina kika samu wnn qamshin turaren ayaanah tace banawa bane nashi ne shine ya kawomin akwatin nan yace wai kayana ne aciki

baki bude sultana tace kina nufin yaa ibaad ne ya rakoki? wow...i am sure he bot this for u. .toh mu bude mana mugani.

daura akwatin sukay akan gadon, sultana ta koya mata yadda ake budewa suka fara ciro kayan daya bayan daya

hadaddun Plain black abaya

da coloured A-line gowns da wata Front-open abaya da Kaftan with matching hijab, Two-piece prayer dress, su Inner Wears ne dasu Cotton underscarf da sleping dress guda biyu, Soft cotton veil da camisoles, Comfortable cotton underwear, leggings, da Hijabs, designer Jersey hijabs, Chiffon hijabs Instant pull-on hijabs da takalma in Black flats, Modest sandal ,Sneakr, da Simple dress shoes sai Gentle body cream, Lip balm, da Mild deodorant harda dan safe sunscreen inta mekyau kusan komin ta in 2-3 pairs bai cika mata ba dan yasan dolene inta koma gabansu amminshi zasu saya mata kaya sosai

Ita dacan abun bai wani darata ba saida taga sultana tanata mata murna tana gwadawa ajikinta kafin nan taji abun ya mugun burgeta itama, sultann ne ta nuna mata inda ake bude trolleyn din da inda ake rufewa snn ta nuna mata zipper inda zata adana kudinta kafin suka aje akayan agefe da zimman in ta dawo daga school zasu zo suyita gwadawa tare.

baifi minti goma da shiganta dakin ba aka kirasu breafst Duk da maheer yana sauri bai zauna yaci ba amma bai saka ammi babba tay wani wautar yin masifa ko wani bori agidan ba. infact tunda ta fito she was just cool with everyone batace ma ayaanah komi ba tunda ta amsa gaisuwarta.

bayan sun gama breakfast ayaanah ta koma daki tare da mai aikinsu siddika, ibaad ne yau ya ya aje sultana a schll ya wuce lectures dinsa.

tunda sukabar gidan ammi babba takasa samun nitsuwa sabida gabaki daya bhvious da maganganun da maheer yaa mata dazu ya kulle mata kai kuma ya bala'in girgiza ta babu abunda yafi damunta ma kamar sanin sirrinta na maganin asirin nan dayayi.

cikin rasa gane abunda ke mata dadi ta kira hajiy ramatu wacce a bugu na farkota dauka suna gaisawa da uban zumudi a voice na hjyn tace "kin kira mijin naki kuwa, kawata wai ya kuka krene da batun kudin?

cikin rage murya kasa kasa kamr na wacce ba lafya ammi babba tace hmm ramatu kibar wannan maganan wallh ina cikin matsala na shiga uku na.

da mamaki hajy ramatu tace meye ne, meyafaru? mijinkin yaje ya aure fatima acan ko?

cikin jan arniyar tsaki da hatsala ammi babba tace ke da Allah ni ba wann bane damuwata,..ramatu maganan maheer nake miki gabaki daya ban gane ma behvrs dinsa ba

...dacan na dauka raini ne amma yanxu gaskiya yafara bani tsoro..

cikin sauke ajiyan zuciya tace toh meyafaru da maheer din,..

babu wani bata lokci ammi babba tahau gaya mata duk yadda sukayi da shi da safen nan bata rage mata komi ba,

face saida take memetawan ne ma taji tsoro ya kara rufeta akansa sosai idanunta ya ciko da ruwan hawaye sosai....

cikin kyabe baki da karfi hajia ramatu tace tab di jamm lallai kina cikin matsala raihanatu amma nide wallah bani wani tsamanin cewa field inshi na law ne yake neman canza masa hali, mutane nawa ne suka karanta criminal law lafyarsu lau??? kuma kikace wai ya bincike wayarki tass tass yaga sirrinkanmu snn kuma ya mayar dashi ya aje miki a inda kika bari kamar be taba ba?

ammi babba tace kwarai kuwa..yadda nabar dakin haka nazo na sameshi wallah komin kwakkwafinki bazakice mutum ya taba wayar bama.

hjy ramatu tace tabbbb amma are u sure yaronkin nan bai fama da wani BIPOLAR disoder or some BORDELINE PERSONALATY TRAITS? dan haka kawai bazai sauya daga calm normal guy ya dawo miki kamar some cold dangerous control freak arana guda ba..yanzu kuma shikenan zaki zauna masa kina kuka dan yasan sirrikanka sai abunda yaga dama kenan yay da rayuwarki ko?

fashewa da kuka ammi babba tay tace wallah bansan ya zanyi ba ramatu..kuma wallah wallah babansa yaji daya daga cikin maganganun nan sakeni kawai zaiyi..fisabillahh ramatu shakaranjiya fa na dawo sai

ace kuma har ya sakeni a satin nan ai shikenan kuma kafin na sake dawowa gidansa kuma inaji hala har sai anyi tashin qiyama..dama yajima yana simi simi da maganan cewa ni nay musu asiri na hanashi auren fatima wallah inhar wnn maganann ta fito masa afili babu jira waje road zaiyi dani ni wallah bansan ya zanyi insa maheer yay shiru da zancen nan ba.

hajiya ta rafka salati tace "kai kai abu baiyi dadi ba, amma kema raihanatu wallah kinyi sakaci ai ba a barin hirar sirri irin haka awaya...koda shike abunda ya faru ya riga ya faru. yanxu de shawara daya zan baki kibisa ahankli kawai karki sake kiy wani abu agidan har saimun samu wata mafita

tana share hawayenta tace shikenan babu damuwa ramatu sai anjima kawai zan kiraki inna dawo daga asibiti dan kaina namun ciwo sosai. daga haka nan sukayi sallama ta mike ta shiga bayi ta wanke fuskarta ta shirya tsaf tasamu mai aikinsu saddika a daki suna zaune tare da ayaanah

ko kallon inda ayaana take batay ta lissafa mata abunda zata dafa musu da rana snn tafita driver yakaita asibiti ana dubata akaga jininta ne ya haura sama sosai 190, atake aka kwantar da ita for a while ana monitoring insa, da kyar kafin na yazo ya dawo 142/80 still Doctor bai qamsu ba haka ya zaunar da ita ya dan babbata wasu shawarwari snn ta dawo gida ko abincin kirki bataci ba ta kulle kanta a dakinta ta kwanta cikin tunani..

after some hours Maheer ne ya fara kammala lectures dinsa dake ibaad yana da club activities ba yanzu zai dawo ba shi ya biya ya dauko sultana a school yabi ya siya mata su ice cream da abubuwan dadi ya lallabata suka shirya tun ahanya kafin suka iso guda duk sauran kayan cime cime yace takai ma ayanaah..

Da murnan ta ta dawo gidan tasamu ayaana na zaune suka cigaba daga inda suka tsaya kominsu atare sukeyi sallah, arranging boxes, yau wuni sukayi suna gwada sabbin kayan ayanan ajikinsu har yamma yay lesson teacher sultana yazo

ayana tana gefe tana jinsu yana koya mata maths wanda duk iri dayane da wanda addanta inayah take koya mata lokacin suna anguwar tudu..

Bayan kwana biyu haka rayuwar gidan ya sauya gabaki daya, cikin kwanakin baifi sau biyu bappa zaidu ya kira ta ba shima sama sama suke magana daga sun gaisa ya tambayeta kotaga text dinshi da tace ehh sai shikenan basuyi wani dogon magana ba, tun yaran suna jiran suga wani emotional outbust ko zage zage daga bakin ammi babba har suka gaji suka saki jikinsu sabida tsabar yawan shiru da kin shiga ahrkan yaran da takeyi agidan sosai amintaka yazo yafara shiga tsakanin ayana da sultana kullum suna tare da juna, duk tabata labarin sauran mutanen famlynsu duk tagaya musu sunayensu da matsayinsu musmm ma kulthum data kasance kan su daya kuma suna shiri sosai

iyaka sultana taje school, ko islamiya ko lesson taje ta dawo su cigaba da hira. in just 2 days ta nuna ma ayanaah yadda ake abubuwa dayawa game da yin dressing wanda dacan bata sansu ba. ibaad hardly have time for himself, ga kiran prof tunda yasan ta dawo gari yake yawan kiransa office dinsa, wata rana sai da dare ma suke ganinsa ko da safe inya fito wajen karyawa shikansa mamakin shirun ammi babba yakey aransa, maheer kuwa ko kadan bai nuna musu alaman komi ayananinsa ba, infact normal yake magana da mamansan kamr ba shine ya gama tsorata ta agidan ba.

ranar alhamis kowa cikinsu yayi tsammanin cewa yaune su bappa zaidu zasu dawo nija amma hardare yay ba'a gansu ba,.

washe gari safiyar juma'a ma shiru ko maheer daya nemesu a waya bai samesu ba. gashi already can family house sun fara shirin zuwan hajiya mairo da ake tsammanin ganinta gobe asabar gashi babu alamn dawowarsa su bappa zaidu da su ammi karama kusan kowa dai da abun aransa dai aka yi shiru aka kyale uncle moh da matarsa anty safeerah suna managing wasu abubuwa acan gidan.

unxpectdely wajajen 10.am sharp jirginsu ya sauke su a aminu kano intl aiport, dan tun arnd 3am na dare suka taso

kowa ya gaji dan haka tun a aiport din sauran team duk akayi sallama kowa yakama gabansa dan already ammi karama ta bada hutun kusan 2weeks ga kowa dan bakaramin wahalar aiki suka sha awajen confence din nan ba.

it was a new project dan dolensu suka zage suka bada gudumawa sosai wanda ya mugun jawo suka samu wasu manyan key international visibilty nd connections a harkan philantropy nd humanatarins aids.

wanda zuwan bappa zaidu bakaramin taimaka musu yayi ba, cos he is the only true blood of the al-mansurs kowa yasan waye dan uwansa prof zayyanu, twins ne so suna kama sosai. ansan kuma iri power da suke dashi dan haka haba haba aka dingay dasu suna samun abubuwa da signings cikin manyan kungiyoyi a cikin sauki.

kasncewr sa tareda fatima ya samar masa sauki duk dama basa samun lokcin yin hira da junansu sosai amma at some point ire iren little candle light dinner da get together da akey yawanyi awajen ya samar masu nitsuwa da karin shakuwa da juna..

gashi da uban kishi dan yanayin yadda yake marking territoryn sa aknta duk inda take idonsa na wajen yasa maza da yawa suka dauka already ita matar aurece dan haka a mutunce akayi komi aka gama musmn ma da kowa yake ganin dacewarsun a fili.

suna sallamar kowa Driversa na office ya kira ya kawo masa babban mota shida kansa ya tukasu su biyu suna hirarsu me sanyi har ya kawota gida,

basu shiga ciki ba ya tsaya daga gate, sun jima suna magana akan yadda goben zai kasance,duk ta matsu sosai tashiga gidan dan ta tabbatar da cewa side din da hajya mairon zata sauka gobe is ready komi an kammala shi da kuma tsara iren iren abincin da zasuyi na tarbata goben inta iso.

kowa yasan ba ita daya take tahowa ba dolene zata jajibo wokers dinta musmn wanda take rike dasu basuda iyaye ta dawo dasu kanon tare da ita, all arngemnt regarding hakan bappa zaidu yace sunyishi da uncle moh dan akwai dan karamin workers lodge mai one room da ktchen da toilet guda hudu face me i face you da suka siya, wanda wokers din hajy wanda ahannunta suke zaman basu da kowa zasu na zama aciki.

babu yadda batay ya kyaleta ta tafi ba yace sam bai gaji da ganin ta ba, aikin gidan ma yace anfasa saidai akira indoor services suzo suy dan ita ma ta huta, tun tana ki harta amince masa ya kira akan za'a turo mata guda uku daga wani kamfani da zasuy share share da aikin kara shirya musu sauran abubuwan da ba'ayi ba.

harsaida suka gama setling komi kafin suka rabu cikin kewa, ya dawo gidan sa ana daf 11.30am bakaramin mamamkin ganinsa gatsau ammi babba tay ba saidai tsoron kar asirinta ya tono yasa ta kasa masa masifa ta masa tarban mutunci

su biyunsu ne a gidan tama tare dashi, duk dama kafin lkacin zuwa sallahn jumaa yayi gabaki daya saida yasaka tabi hatsala sabida ta lura da yadda hanklinsa gabaki daya yake kan wayarsa, yana kuwa aje wayar ya shiga wanka tay maza tadau wayar taga ashe ma exchanging tex messge yake da fatima, saida tabi kai kaff tana karantawa duk dama maganansun is respecful nd harmless, soyayya ce amma baiyi tsauri ko sun nuna zaqewarsu akan kalamai ba amma iya i miss you i miss u too data gani aciki bakaramin cakkinta yay a kirjinta ba.

kafin ma ya fito daga wankan tafaraji kishi na neman ya hallakata aje masa wayarsa tay akan text din dan yasan tagani ta wuce room dinta tasha kuka wani bin har cewa take dacan ma kyalesa kawai tay ya auro fatiman da hala bazataji irin zafin da yanxu takeji aranta ba

but she deeply know dat inhar fatima ta shigo gidan nan toh wallah nata ya kare kenan, in ancire maganan nitsuwa da iya abinci, bazata taɓa manta irin zamn fatima da baban ibaad ba yadda gabaki daya tabi ta mallakeshi baya ji baya gani sai ita..

gani take kamar fatima tana da wani special magnet na dadi ajikinta dan inda ace mahaifin ibaad yana da lafya sosai da hala ta haifa masa yara sunfi biyar..

koda can da basu hada miji ba balain kishnta takeji bare yanxu azo ace ta shigo cikin gidanta bayan tasan mijinta cikakken namiji ne gani take daga zarar ya samu fatima akan gadonsa bazata kara yin armashi da mutunci a idonsa ba, dan dakyar ma take iyayi dashi ynxu, bappa zaidu yana balain son mace dadi me aji akan gadonsa, yana son qamshi da gyaran jiki.. karshe ma tana haifar sultana cire mahaifarta tay gabaki daya tamasa karyan cewa tsagewa yay dan kawai sudena haihuwa sabida gani take bazata iya jurar yawan daukar bukatunsa anan gaba ba...

koda yazo yaga ta karance masa text insa dariya kawai yay, kuma yasha kwalliyrsa cikin bugaggiyar shadda milk colour me sheqi yana baza qamshi kamr ango yaje har dakinta ya mata sallama yace mata zaiwuce masallacin jumaa sai ya dawo.

tsabar kishi dakyar ta iya amsashi yana ficewa kuwa ta zube akasa ta rushe da wani irin kuka taredajin rudani me yawa na mamayeta...

ita kanta baata tashi sanin cewa tana mutuwar son mijinta har saitaga yana kula fatima sosai kuma yana yawan daukar wanka kamar sabon ango ita kuma yana basar da ita..

dake ranar jumaa ne koda yaran suka dawo sa wuri babu wanda ya gane mood dinta, ga sultana sai zumudi take na cewa wai anbasu midterm yau da dare kawai zatabi ayaanah

sukoma family house dan itama tay musu kwana biyu da hajy mairo acan..

babu yadda ammi babba bataso ta hanata ba amma taki sam, bappa zaidu na dawowa da yamma kuwa sukaje masa oyoyo he was happy dayagansu lafya kuma fes fess da sabon kaya ajikin su musmm ma ayaana, anan sultana ta gaya masa itama tana so tabi ayaanah family house shi kuma bai hanata ba yace mata in su maheer suka dawo yau da dare sai su tafi.

da murna taja ayaana sukaje dakin suka tattara kayansu duka kowa ta saka a trolley dinta suna jiran dare yay, haka kawai ayaana takejin dadi sanin cewa zata koma wajen ammi karama snn she wll have the chance to be with hajy mairo once again ko dan tanajin labarin mamanta taawure, duk murnn da sultana takey a fili sai baikai wanda ita takeji a zucyarta ba.

bangaren su ammi karama kuwa bata jima da warware gajiya ba wokers din da bappa zaidu suka iso, haka ta tsaya akansu aka kara tande sashen hajy mairo aka kara gyara koina yay kamar dakin amarya falonta da koina har bayan gida da su labule sun kama qamshin turaren wuta sosai har wajen gidan koina

saida aka gyarashi tsaf tsaf.

untilll evetything is set

kafin ta sallamesu tadora abincin rana kafin driver ya dauko safiya da kulthum a school suka dawo kowa yana murnan ganinta, as usual awajenta kulthum din take cin abincin rana kowani rana sabida antt safeera tana aiki kuma tana kan makaranta dake auren tay da wuri bata gama karatunta ba sai yanxu

bawani jituwa safiya take da kulthum ba sabida safiyar akwai ta fi'iili da raini, inba ibaad ba bata jin tsoron kowa

suna kammala cin abinci kowa yaje yay wanka a sashensu

at arond 5pm na yamma

anty safeerah ta dawo cikin lexu jeep inta looking clasy as usual tasaka wani pink atampa, wucewa sashenta tay bayan ta kimtsa snn tazo sashen ammi karama suka tattauna akan abincin da zasuyi na tarban bakin gobe,..

anty safeeera tasha mamaki da ammi karama taki ta dauki ayyukan da yawa, infact sai ta kyalesu da main couses din sabida tasan kansu a hade yake da ammi babba kuma dukansu suna jin balain kishi aransu cewa hjy mairo tafi fifita agidan sama dasu. saidai ita anty safeerah kullum a neutral take tunda tasan ammi ba a sa'arta bane, beside ita ex wife na eldest son na gidan ne so akwai wnn girman da take bata shiyasa ko kadan bata nuna nata kishin a fili.

haka suka gama tattaunawa ammi tace zatay chops da drinks su suji da main abincin kawai magana ya kare anan.

daga can gidan kuwa already zumudi yasa sultana ta kira kulthum awaya tace mata zata zo tay kwana biyu da ita da sabowr kawarta ayaana, kulthum duk tafi kaquwa tanaso taga waye ne ayaanah da sultana seem so excited abt dan tasan muddin jinin su ya hadu da sultana to itama jinunsu zai hadu.

ana idar da sallahn magrib sukayi wanka suka saka kayansu masu kyau ayaanah taki sam ta biyewa sultana tay kwalliya sabida tasan tareda da ibaad sazu tafi, ana idar da isha kuwa maheeer yace mata su fito su tafi.. hakanan yaja hannun ayaanah yakaita wajen ammi babba sukayi sallama duk dama ciki ciki ta amsa bai damesa ba tanaji tana gani duk suka watse agidan suka barta ita daya gashi bappa zaidu yafita shima da yamman bata san ina yaje ba....

duk dama tay dakon ganin wann ranan da ayaana zata bar mata gidanta amma kuma da aka watsen aka barta ita daya sai taji gidan gabaki daya bai mata dadin zama aciki ba.

cikin rasa na yi ta koma room dinta tana nazarin yadda zatay ta shawo kan bappa zaidu adaren yau dinnan koda zata samu wani nitsuwa tareda shi, tuna yaushe ma rabonsu da yin wani abu tsakaninsu na ma'aurata yasa ta mike sharply ta bude wani drwer ta dan debo kayan matan ta taje kitchen ta harhda na hadawa da madara ta dawo dakin ta shanye tass snn taje ta shirya ruwan wanka me dumi ta dau lokaci abayin sosai wajen tattale jikinta tay fess ta dawo room ta shafe koina ajikinta da turaruka masu kamshi da mayukan masu taushi snn tasa nitynta yar sharara me kyau, kafin ta gama duk shirinta har karfe goma saura yayi, kashe wutar dakinta tay ta fito kai tsaye tawuce room dinsa ta samu har yanxu bai dawo ba, dalewa tay gadonsa ta kwanta a dan rigingine kafin nan ta kashe main wutar dakin ta bar iyaka dim light na blue lamp tadan jingina da pillow tana latsawa wayarta kai zaka dauka duka mind inta na kan wayanne amma inaaa tunani kawai take kanyi na me zatay takure masa tunani yau agado nan dan koda wasa bataso gobe suje family house ya daga ido ya kalle fatima ita kuma ya shareta

...#SURAYYAHMS

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025