HAMAL Chapter 3
HAMAL
Arewabook@ayshadansabo
©️ Ayshat Dansabo lemu
Chapter 3
Hamal wacce take kwance cikin lallausar bargonta ta gyara kwanciya tare da damƙe wayar a kunninta tana ƙara takure jikinta guri guda,sabida zazzaɓin dake ratsa jikinta wanda ya zame mata ƙa'ida tayi shi matuƙar ruwan sama ya taba jikinta ko yaya ne.Wannan halittarta ce tun tana ƙarama,tayi shuru tana sauraren Engr.Attaheer dake faɗin,"Pretty kin gane mai maganar?" Bai jira amsarta ba ya ɗaura da faɗin,"Wanda ya baku lift ɗazu ne,hope kina cikin ƙoshin lafiya ya gajiyan kuka?" Ya ƙare kalamansa yana sauraren jin amsar da Hamal ɗin za ta bada.A ɓangaren Hamal tsuke baki tayi tamkar yana kallonta,domin lokuta da dama magana wuya yake mata balle a yanxu da take jin zazzaɓi a jikinta.Murya can ƙasa ta furta,"Lafiya lau,na gode." Ba don kunnin A.R ya kasance mai matuƙar ƙarfin ji ba daba lallai yaji me HAMAL ɗin ta faɗi ba.Gyara kwanciyarsa yayi yana faɗin,"Pretty are you okay kuwa? Naji muryarki na nuna alamun kina cikin damuwa." Cike da ƙarfin hali Hamal ta furta,"Zazzaɓi ne ya rufeni,so ina buƙatar in huta good night "Daga haka ta kashe wayar ba tare da ta jira jin ta bakin Engr. A.R ɗin ba domin sam ita bata mayi tsammanin samun kira daga garesa ba,da bata yi ƙarfin halin ɗaga wayar bama tun farko.Ahankali ta saki ƙaramin tsaki tare da aje wayar,tana sake ƙudundunewa a cikin bargo.Kuma bata ɗauki dogon lokaci ba bacci yayi gaba da ita,yayin da
a ɓangaren Engr. A.R Attaheer kuwa jin ta kashe wayar ya sanya shi saurin kallon screen ɗin wayarsa yana mamakin hali irin na Hamal.Me hakan ke nufi,bata da muradin saurararsa kome? Sake dialling lambarta yayi yaji is swich off,sai ya lumshe idanuwansa yana mai jin haushin hakan har cikin ransa.Faɗi yake a cikin zuciyarsa anya kuwa zuciyarsa ba tana son ɗakko mishi abinda bazai iya jurewa bane? Sam baya ɗaukar wulaƙanci bare raini,hakan yasa yake mamakin wai yau shine mace za ta kashema waya karo na farko a cikin rayuwarsa.Sake juyawa yayi daga hagu zuwa dama yana ƙudurcema ransa cewa bazai sake kiranta ba,da haka bacci ɓarawo ya sacesa cike da mafarkai masu daɗi na pretty ɗinsa kamar yadda ya laƙaba mata sunan.
**********
Washegary da ƙyar Hamal ta iya tashi ta gabatar da sallar asuba,bayan ta idar ne ta zauna tana karatun Qur'ani kamar yadda yake ƙa'ida a cikin rayuwarta duk idan ta idar da azkar sai tayi tilawar Qur'ani mai girma.A gogon ɗakin ta ɗaga kai ta kalla bayan gama tilawar nata,ƙarfe 7am dot ta gani hakan yasa ta miƙewa ta nufi toilet.Wanka tayo ta fito ɗaure da towel,cikin sauri-sauri ta fara shirinta kasancewar lacture ɗin 8:30am garesu yau ɗin.Shiri tayi cikin shigar riga da skat wanda yayi asalin amsarta,Hamal na cikin sahun kyawawan matan da Allah ya yiwa baiwar kyau da dirin jiki tamkar ita tayi kanta,fara ce sai dai ba irin fau ɗinnan ba.Tana da manyan dara-daran idanu masu matuƙar ɗaukar hankalin mai kallonta,dogon hanci gareta wanda ya dace da kyawun face ɗinta.Idanuwanta masu ɗauke da lashes baƙaƙe siɗik,sai ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da pink lips wanda ke matuƙar birge mutane.Tana da tsayi matsakaici sai dai bata ƙiba,amma jikinta a murje yake cike da tsoka ta ko'ina domin babu rama a tare da ita ko ƙanƙani.Tana da cikar ƙirji na dukiyar fulani waɗanda suke a tsaye cur,ga kuma hips ɗinta wanda duk yadda ta juya jiki ko mace ƴar Uwarta saita sake kallonta bare kuma namiji.Hijab ɗinta ta ɗakko wanda ya dace da shigar da tayi ta sanya,fuskarta sam babu kwalliya inka ɗauke ƴar powder data murza sai white lip glows data saka kaɗan amma tayi kyau kamar ka saceta ka gudu.Jakarta ta ɗauka bayan ta jefa wayarta samfurin Samsung a ciki,kai tsaye falo ta fito ta tadda babu kowa hakan ya nuna mata cewa duk sauran ƴan Uwanta sun wuce nasu skull ɗin kenan.Meemah itace babbarsu a mata,daga ita sai Hamal sai Muhibba da kuma Auta Nadeeyah.Muhibbah tana FCE ne tana karantar Hausa Islamic,yayin da Meemah take congo tana karantar law kuma shekararta ta ƙarshe take,sai auta Nadeeya ƴar shekaru 15 tana SS2 a Demostration.Yayansu wanda shi ne babba kaf a gidan kuma Namiji tilo wato Yaya Kamal,shi yana ƙasar Italy bai daɗe da tafiya ba kasancewarsa mai yawan tafiye-tafiye sabida shi ke kula da wasu harkokin business ɗin Abbansu.Hamal ita kaɗai ce tayi dace ta samu samaru,inda take karantar Chemistry tana level 2 ita ke bima Meemah a shekaru.Kai tsaye falon Abbansu ta nufa domin jiya tayi bacci da wuri bata san ma ko ƙarfe nawa ya shigo gidan ba,tura ƙofar ɗakin tayi ahankali tana addu'ar cewa Allah yasa Mami bata ciki.Sai dai kuma tana sanya kanta a cikin falon ta hangota hakimce akan kujera,ta ƙarisa ciki tana mai gaida Mami ta hanyar faɗin,"Mami ina kwana."Saida Mamin ta zabga mata harara sannan ta amsa da,"Lafiya,aina ɗauka yau baki da skull ɗin ne da kika bari ƴan Uwanki suka rigaki barin gidan."Ita dai Hamal bata ce uffanba banda tashi da tayi ta nufi bedroom ɗin Abban nasu yayin da Hajiya Bilki ta bita da harara tana mai ƙara jin tsanar Yarinyar tare da shan alwashin sai taga bayan Hamal ɗin.Bakin Hamal ɗauke da sallama ta shiga cikin ɗakin,Abban nasu na zaune a gefen katafaren bed ɗinsa yana danna laptop da alamun wani aikin yake ƙarisawa.Ya ɗaga fuskarsa ɗauke da murmushi ya dubi Hamal yana amsa sallamar da tayi tare da buɗe mata hannuwansa alamun ta taho garesa,a nutse ta ƙarisa garesa ya rungumeta yana faɗin,"Hamal kin tashi lafiya,jiya nayi shigowar dare duk kunyi bacci."Hamal ta ƙara lafewa a jikin Abban nasu tana mai jin matuƙar ƙaunarsa na bin jininta.Shi kaɗai ne ke bata kulawa baya ƙaunar yaga damuwarta ko ƙanƙani yanzu sai ya rasa natsuwarsa,yana matuƙar tausayin maraicinta na rashin Uwa kuma shi kanshi ba a son ransa take zaune a gurin Maminsu ba sabida ya daɗe da fahimtar cewa ƙuntata mata kawai ake a cikin gidan,sai dai shi baya son raba kan Yaransa ne ya fiso su tashi a inuwa ɗaya,amma ba don hakan ba da tuni ya daɗe da rabata da gidansa ya kaita gurin mahaifiyarsa inda yake da tabbacin cewa da tana hannunta ne ba za ta taɓa jin maraicin rashin Uwa ba.Shafa bayanta yayi ahankali bayan ya ɗago fuskarta time ɗin da take faɗin,"Abba ka dawo lafiya?"Ya amsa da cewa,"Lafiya lau daughter na sameku lafiya?" Hamal ta amsa da faɗin,"Lafiya lau Abba."Cikin jin daɗi Abbah yake faɗin,"To madallah Hamal,hope dai baki da wani matsala ko damuwa ko?" Ya jefa mata tambayar yana mai ƙurawa fuskarta ido domin karantar yanayinta.Ahankali ta amsa da faɗin,"Babu Abbah,sai dai ina so ka amince min na koma hostel da zama,domin hakan zai fi mini sauƙi akan jeka ka dawo ɗinnan Abbah."Takai ƙarshen kalamanta muryarta na rawa.Abban wanda har yanzu yake kallon ɗiyar tasa,take fuskarsa ta sauya damuwa ƙarara ya haska a saman fuskarsa.Cikin sanyaya muryarsa yake faɗin,"Sabida meyasa kika buƙaci hakan Hamal,alhali kinsan cewa batun yau kike magiya akan hakan amma ban amince ba,sanin kanki ne bana buƙatar ƴata taje tana zaman hostel,ki faɗa mini miye matsalar ba driver ke kaiki ya dawo dake ba kamar yadda na tsara komi,ko kuwa an canza tsarin ne?"Tuni Hamal har ta fara zubda hawayen da take ta maƙewa don kar Abban ya shiga damuwa,cikin rawar muryar da take ƙoƙarin saitashi take faɗin,"Abbah tun bayan tafiyarka Mami ta sauya komi,bata bari a kaini idan kuma har an kaini to ba za a je ɗaukata ba,lokuta da dama nasha rasa lactures duk a dalilin ina makara sai dai ta bani kudi tace inje in tari motar haya na shiga,don Allah Abbah ka amince mini idan Ya Kamal ya dawo a maidani hostel zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankalin da zanyi karatuna cikin natsuwa."Takai ƙarshen maganar tana zubda hawayen tausayin kanta.Abban wanda ransa yayi dubu ya ɓaci ya dubi Hamal yana faɗin,"Ita Bilkin ne ta tsara hakan,to wallahi bazan lamunta ba,taya nida gidana ban isa in tsara yadda za a yi ba sai an sauya tsarina don anga cewa ni ɗin ba mazauni bane?" Ya miƙe a fusace zai fita ya sami Mamin,Hamal tayi saurin riƙo hannunsa tana faɗin,"Abbah ka rifamin asiri don Allah karka ce komi Abbah,Abbah kayi haƙuri ka cika mini burina in koma Hostel hakan kaɗai shine mafita,wallahi nayi maka alƙawarin cewa zan tsare kaina ba za ka taɓa jin wani abin ɓatanci ya faru dani ba."Ta ƙare kalamanta cikin sanyin muryarta mai cike da rauni da damuwa.Ahankali Abban ya dawo ya zauna jikinsa yayi sanyi matuƙa,domin yana matuƙar jin Hamal a cikin ransa,shi kanshi ya amince cewa matsananciyar soyayyar Mahaifiyarta ce ya koma kanta bayan ya rasata a lokacin da yake tsananin ƙaunar ya rayu da ita.Idanunsa ya kaɗa yayi jazur kullum ya tuna da Halimatu sai yaji mutuwarta ya dawo masa sabo,haƙiƙa yayi rashin mace ta gari abin alfaharinsa.Ƙara janyo Hamal ɗin yayi zuwa jikinsa yana share hawayen fuskarta,ahankali yake furta,"Kiyi haƙuri Hamal ki ƙara juriya akan wanda na sanki dashi,ki cigaba da haƙuri da halin Maminku,kinfi kowa sanin nima haƙuri nake da halinta duk da cewa ni ɗin na kasance tsayayye amma hakan baisa Bilki tayi hankali ba,maganar komawarki hostel nayi miki alƙawari idan Kamal ya dawo zanbar komi a hannunsa sabida jibi zan juya ƙasar Canada ki ƙara haƙuri kinji Hamal."Da sauri tasa hannu ta share hawayenta,fuskarta da murmushi take kallon Abban nata tana faɗin,"Na gode Abbah da ka fahimceni,zan cigaba da haƙuri kamar ko yaushe Abbah."Cikin jin matuƙar jin tausayinta Abbah yasa hannu ya buɗe bedside drawer ɗinsa ya irgo kuɗi 10k ya miƙa mata yana faɗin,"Amshi wannan ki riƙe ko kina da buƙatar siyan wani abu." Ya sake irgo 20k ya sake bata yana faɗin,"Waɗannan ki aje sabida hidimar skull na siyan su handout zuwa yin assignment da sauran buƙatu,Allah yayi miki albarka Hamal ya kareki daga sharrin magauta,ki cigaba da tsare kanki duk da nasan cewa ke ɗin mai natsuwa ce,ki ƙara akan wanda aka sanki dashi ki dage kiba marar ɗa kunya kinji ko?" Hamal ta amsa da faɗin,"To Abbah na gode Allah ya ƙara buɗi."Sosai Abbahn yake jin daɗin yadda Hamal ke da hankali da nutsuwa matuƙa,domin duk tafi sauran Yaransa nutsuwa da tarbiya.Ita kaɗai ce yake ma kyauta tayi godia tare da yi masa addu'a,sai kuma Nadeeya da itama take kwaikwayon halin Hamal ɗin.Driver ɗinsa ya sanya yakai masa Hamal ɗin skull,kuma koda suka isa sai daya kaita har kusa da department ɗinsu ya ajeta sannan ya juyo.........✍🏻