Labari ne mai cike da...... *Tausayi* *Mugunta* *Zalinci* *Cin amana* *Yaudara

PAGE 3

by @prettys01

    THE SLAVE 😭😭
💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠


E.P3️⃣

 🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹🔹
      Masarautar Shuraib😊
 
"Kana hauka ne ko me? idan na kuma jin wannan maganar daga bakin ka, hmmm" Abu Mujahid ya fita fuuuu bayan ya yi ƙwafa, ɗansa da ke zaune wanda suke matuƙar kama da shi, wato yayan Bintu, tsaki ya ja yana tina abin da yafaɗa ma Babansa.

"Baba inason ka nema min auran Gimbiya Sopiyya, nasan Sarki ya maka farin sani.........."

"Shuru, Allah ya tsari Gimbiya da auren ka." shine fa ya haushi da faɗa dan yasan halin ɗansa na son abin duniya.

********** ********* ********** ********

"Biyu, ina son wata rana na yi rayuwa cikin ƙasƙanci tamkar baiwa naji yadda ake ji. "

"Ayya Gimbiya, ke da kuke kwana a ko ina ma, ai ba wani sauyi da rayuwar sarauta saboda mulkin mahaifinki muna jin daɗinsa saɓanin masarautar Qumaiz."

"Haka ne, ina son zuwa na ga yadda babban burnin Qumaiz yake, an ce sunfi mu yawa da wadata albarkatun ƙasa amma na banza tinda ƴan garin nashan wahala."

"Eh Gimbiya, amma kibar sha'awan ganinta, duk wanda ya shiga balle ɗan yankin nan ai kisan hulaƙan ci suke ma mutum,"

"A hakan ina so naje naga yadda take"

"Kinsan yayana Mujahid ai?."

"Eh"

"To shi duk ƙarshen sati sai yaje Qumauiz ba tare da sanin Sarkin can ba." Gimbiya da ke kan gadon ta na alfarma ta kalla ƙawarta cikin mamaki.

"Taya yake shiga? wayyo ba yajin tsoron, mai ma yake zuwa yi ? "

"Sayar da abubuwa yake yi acan dan sunfi tsaɗa a ce wan sa, yankin Sayid take shiga daga can su yi Qumaiz."

"Gaskiya ya na ganganci kuwa." Daga haka suka bar  hiran suka kama wata.

💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠
    Masarautar Qumaiz😔

Dukkan mutanan gari sunyi jugum jugum a babban haraban gidan sarki, suna fatan kar sarki ya mutu dan yafi akan magajin shi. 

"Yaku mutanan Masarautan Qumaiz, A yanzu sarki Abbas Ali Qumaiz ya mu......." bai ƙarasa ba mutane suka hau ihu da kuka, gurin ya hautsine sosai. A haka masaurata ta zauna har na 10 babu wani sauyi ba. Mutuwan ya ta ɓa Yarima duk da fatan shi kenan yayi-yayi yahau mulki, ga iyayansa sunata ƙara kwaɗai ta mai.

********** ************** **********

"Yarima nan da kwana goma masu zuwa shine  naɗin sarauta kuma a ranar muke son aura maka ɗaya daga cikin wa innan yaran su uku." Sarauniya ta faɗa tana nuna mai wasu kyawawan bayi 3, dake tsugunne suna kallon ƙasa cikin ladabi. cikin muryanshi na natsuwa da ƙasaita ya ce.

"Koma wace ce ta muku ni banda matsala da hakan amma ta zama mau matukar ladabi." yana kaiwa nan ya fice a fusace. kallon juna suka yi Sarauniya da Mama.

"Kuje mun sallame ku." cikin gaggawa suka fita suna fatan  kar da a zaɓa ɗayan su dan duk wanda ta yi gangancin aura Yarima Unais ta shiga uku, dan shi mutum ne da babu wanda yataɓa ganin dariyarsa ga mugunta cike da ciki, sam basa fatan auren sa duk da gidan sarauta ne.

"Mama kingan su nan, Aimana ce doguwan, yarinya ce mai wayo sosai. sai farar ciki Azrah yarinya ce ita mai son duniya amma akwai ta fa tsoro sai ƙaraman zahra ita kuwa baruwanta duk yadda mukai da ita za ta yi dan sam bata da musu gana gaba da ita, ga ƙananun shekaru."

" Basu yi ba. so nake a samu mai dukka wa'inna abubuwan." ta miƙe daniyyan fita sai aka shigo da sauri sauri dan haka ta tsaya, baiwa Rashida ce ta shigo jikinta na rawa.

"Kuga farce ni, na zo na faɗa muku cewan yanzu nan naga wata yarinya a cikin buɗa" faɗin Rashida babban ta hannun daman Sarauniya,

"Kisa a kawo ta nan" daga haka ta koma da sauri, 

"Buɗa kar dai ace ƴar jahar Shuraib ce ruwa ya biyo da ita nan?."

"Dako ta ga uƙuba irin namu ko in ce mata barmu." Shugowa mutane uku ya sa suka kalla su, maza biyu ne suka aje wanda suka dauko akan babban carpet ɗin parlourn wanda yasha ado sosai cikin tempol take amma hannunta ya leƙo ta waje.

"Zaku iya tafiya." suka juya bayan sun kwashi gaisuwa, akwai mata masu tsaresu a gurin su 8, maza kuma na ta wajene.

"Ku buɗe muga wacece." take suka hau buɗewa, maca ce ta bayyana a ciki, wace gashin kanta ya rufe mata fuska.

" Ranki shidaɗe a sume take. " 

"Kira magajiya (mai maganin gidan sarautan)." cikin 5mnt sai ga Rashida da Magajiya.

"Ranaku shi daɗe, naji jira kuma na amsa cikin gaggawa, umarnin ki kawai nake jira." Magajiya ta faɗa tana tsugunne sai Sarauniya ta ce.

"Rashida." ba buƙatar dogon bayani Rashida ta na Mahaiya bayani take hau dubarun su na masu bada magani, cikin ƙanƙanin lokaci wacce ke kwance ta hau tari sai ta arka tare da aman ruwa sosai.

"Ruwa ne ya ratsa ta amma ba wata matsala tinda na mata ɗurin guwan dauri." sallamar ta Gimbiya ta yi sai ya wuce ta yi musu kirari, dukkan su idanu ya koma kan wacce ke kwance, kallonta suke yi adaidai nan ta fara tattare gashinta tana ta rasu gu ɗaya take tsaftacaccen kyahunta ya bayya, Idanuwa ta zuba musu yadda taga suma suna kallonta sai ta yi tai gyaran murya dan ya toshe, ta fara magana cikin yaransu na larabawa

 "Ina wuninku, a tsora ce nake ku kaini gurin mahaifina kunji." ta ƙarasa tana hawaye gashi dama idanuwan sunyi jaa sosai.

" Yi shuru ƴar nan daga ina kike? waya kawoki yankin nan ta cikin ruwan buɗa ?."

"Nii ƴar Yankin Sayid ce, bansan yadda aka yi nazo nan ba na daisan an aikeni zuwa kasuwa shike nan bansan me ya faru dani ba." tasan alaƙan dake tsakanin jayoyin biyu dan haka ta yi ƙarya da faɗin haka.

"Kin dai san nan inane ko, dan naga kinga tabbarin mu a kowani bango a ɗakin nan." Mama ta faɗa hannunta yana bin bangon, dan nuna mata tambarin su. ta gani dan tana buɗe idanuwanta ta yi arba dasu.

"Yanxu kisa aranki kin zama baiwa hajar nan, dan duk wanda ya shigo baya fita. kinci sa'a ke ba 'yar Masarautar Shuraib ba ce. da ba za ki kwana da raiba."

"Haka ne Mama, kinci darajan ke ƴar Sayid ce, munada alaƙa mai kyau dasu." take ta kalla Rashida.

"Kuje da ita ku bata abinci, ku sauya mata tufafi amma bana bayi ba karta fita, a yanzuanxu ma kurufe mata fuskanta......... "

"Skan me? ba yadda ba, ni zan koma in da na fito, bazan zauna anan ba........" tsawa Rashida ta daka mata.

"Hauka ki ke za ki dinga magana da ƙarfi agaban Sarauniya." 

"Batta Rashida so take na za a daureta."

"Nifa ko kwana ba zan yi a masarautan nan ba, a maidani tawa ko a barni na tafi akan me " ta kuma magana cikin tsiwa da faɗa, duk da jikinta sam babu kwari.

"Kalla kwayan idanuwa na kifaɗim ce wa ba za ki bi umarni na ba."

 Mama kallonsu take haka Rashida wanda duk jikinta ya mutu ganin yarinyar nan ba ta ji ba ta gani, za ta fuskanci mutuwar ƙasƙanci in dai har ta kalla cikin idanuwan Sarauniya. taku ta fara yi a hankali har ta kai dab da Sarauniya, take tamiƙe suka fuskanta juna kuma gab da gab.

"Bazan bi umarninki ba, a maidani in da aka ganni zan san hanyar koma wa gida." ta faɗa tana zazzare wa innan manya idanuwan na ta.
 

___________ Idanuwan Sarauniya duk sun kaɗa sunyi jaa, daga hannu tai ta tsinka ma yarinyar mari.

"Kaita ɗakin Uƙuba." abin da ta faɗa kenan tana zama a in da ta tashi.

Kiran Maza Rashida ta yi suka rufe fuskanta akai gaba da ita, sai faman birgima take, da fizfizgewa.


"Mama kinga wata ƴar iskan yarinya kuwa? ta ja ma kanta, wallahi mutuwar wulaƙancin zan sa a mata.." ta faɗa tana rintse ina duwa, dan yarinyar akwai ƙarfin hali.

"Na ga abin da baki gani ba Zaituna."

"Mama menene?." ta faɗa tanaɗan huci.

"Akan yarinyar nan mana, sak irin wacce nake so Yarima ya aura kenan......."

"Dakata Mama, wai wannan yarinyar! ina......... ai yanzu dana tashi daganan sai aike zuwa Yankin Sayid dan kwasomin danginta, dukka zan kashe."

"Hmmmm Zaituna basai kinyi komai ba, ai ta shigo kenan, faɗa min me kike so amata?."ta faɗa da dukkan gaskiyar ta, (ko ni Pretty sk Ina mamakin yadda ta ke da ƙarfin halin nan, dan ta tsufa sosai, aƙalla za ta hau 57, uhmmm Allah ya kaura.)

"Karta kuma furta ko da kalma ɗaya ce, tinda ni ta ɗaga ma murya."

" Karki damu, kinsan waye Unais, ya kamata ki yadda ya aureta dan duk wacce Yarima ya aura sai tafi kowa ƙasƙanta hatta bayi sun fita daraja, kuma a sannu  hala kata kina kallo."

"Uƙuba mai armashi kenan." tana murmushi ta miƙe sannan ta fara taku mai ɗauke da ƙasaita ta kuma ce wa.

"Allah sarki, Unais shine zai hukunta min ke cikin sauƙi."
END

(Kuna tinanin abin da nake tinanin kuwa ..............................✍️✍️)