Labari ne mai cike da...... *Tausayi* *Mugunta* *Zalinci* *Cin amana* *Yaudara
PAGE4
by @prettys01
THE SLAVE 😭😭
💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠
E.P4️⃣
******YANKIN SHURAIB*********
______________ Masarauta gaba ɗaya ta rikice ta hautsine sakamakon Gimbiya Sopiyya ƴa ɗaya tilo gun Sarki, hankalin Sarki Ranan a matuƙar tashe ya ke, haka kowa na yankin, zuwa yammaci wasu suka kawo ma Sarki da mummunan labari, dan yatura a shiga dajuka dan dubata.
"Mai martaba kaga rigar gimbiya da muka tsinto, yajiƙe da jiki bushashshe, da alaman wani babban dabba ne ya mata mugun illa."
"Innalillahi wa'innan ilimi raji'un, ku tashi ku tafi." faɗin na hannun daman Sarki kenan, dan Sarki ba zai iya magana ba sai faman hawaye yake ta yi.
________Rigarta ce kwance akan carpet ɗin, ya yayyage sosai ga jini jikinsa sosai, shi yake ta kallo kaman ya haɗiye rigar.
"Me yasa Sopiyya ta fita zuwa daji ita kadai? shike nan sun halakamin ƴata tilo ya kenan." take ya hau tari, da sauri aka bashi ruwa ya amsa ya sha ya sai ya kwanta, dan zazzaɓi mai zafi ya kama shi.
_____________ Wasa-wasa yanzu har anyi sati ɗaya da faruwan haka, har jimaminta ya fara raguwa acikin zuciyar wasu, amma a zuciyoyin masoyan sa, banda banda Sarki Arma, Dan Sopiyya yarinya ce mai mutunci sosai da shiga rai, yana son ta fiye da misali dan ita kaɗai ce Allah ya bashi a gudan jinin sa.
____________Daure kisha magani kinji." Ummi ta faɗa tana ɗago Bintu daga kwanciyar da take, duk ta sauya har rama ta yi duk saboda ɓatar Sopiyya, da gyar ta sha sannan ta kwata tana tina abin da yafaru da har suka rabu da Bintu.
Flash back
_________Tin safiyar ranan suna tare, ko ina Sopiyya ta sanya ƙafa sai Bintu ta sanya, misalin 6:30pm na rana suka dawo gidan su Bintu, suna shiga suka zazzauan sai Sopiyya ta ce
"Bintu kinga na manta da kayan da zansa nai barci, dan sai gobe zan koma fada."
"Dan yau ana rafi, bara na ɗauko miki."
"Tom kisa fadawa su raka ki saboda hanya babu wani kyau ga yamma na yi."
"To ranki shidaɗe." dariya Sopiyya ta yi tana mai ɗan kwanciya akan wata tsohuwar kujeran da ke parlourn su.
________Bayan ta je ta ɗauko ta dawo, shine aka nema Sopiyya aka rasa, duk da an bar guards huɗu a bakin ƙofar gidan na su, da yake tasan halin Sopiyya akwai son yawo babu masu tsaro dan haka aka fara menanta, abu kaman wasa babu ita babu dalilinta sai gashi an kawo kayanta duk sun ɓaci da jiki kuma ya yayyanke.....
Continues.
__________Hawaye ne masu zafi suka kuma saukowa tasanya hannu ta share, a daidai lokacin yayanta ya dawo daga Yankin Sayyid, ganinta cikin wani hali yasa ya isa kusa da ita da sauri ya ce.
"Bintu lafiya? ko ba ki da lafiya ne?." Ya faɗa cikin damuwa sosai, sai ga mahaifiyar su ta fito daga ɗan kitchen ɗin su.
"Muhajid sai yau.?"
"Barka Mama, fatan kuna lafiya?."
"Lafiya lau, wannan karan ka daɗe, sati ɗaya baka gida, sannan ba ka ji mugun labarin da ya sa nemu ba, kuma shi yasa ƙanwarka wannan halin." ta ƙarasa maganar tana zama, shi kuwa duk yanayi sa ya sauya dan jin abin da ta faɗa.
"Subuhanallah. Me ke faruwa?."
"Hmmmm tin a ranar da ka tafi, abun ya faru, wato Gimbiya Sopiyya ce ta ɓace sannan bayan kwana biyu aka tabbatar da namun daji sun cinye ta." Zumbur ya miƙa da maɗaukakin mamaki yana maimaita abin da ta faɗa. Labarin komai ta bashi har da. "Kasan ina aiki a gida Sarki to ranan bana gida, kuma haka Abu Muhajid sai 10pm yake dawowa, abu dai sam babu daɗi.......... Lafiya." ta faɗa ganin Muhajid na riƙe kai dan wani jiri da yake ji, take kuma ya faɗi luuuuuuuuu ya suma.
END.
(Wai nikam duk ƙaunar ce ta kawo haka........✍️)