Labari ne mai cike da...... *Tausayi* *Mugunta* *Zalinci* *Cin amana* *Yaudara

PAGE9

by @prettys01

      THE SLAVE 😭😭
💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠

E.P 9️⃣


______________Tafiya take yi amma ji take kaman a sama take, duk taku ɗaya idan ta ƙara sai ta ji gabanta na tsananta faɗi, addu'oi kawai take jerawa har ta ji sun hau kan step, ba ta ɗago ba amma ta najin tasirin idanuwa mutane akanta, haka dai ta ci gaba da dauriya har ta fara jiyo wani daddaɗan gamshin turare na kusanto ta.


__________Har ga Allah a yau wata Baiwa ta ɓa ta masa rai, daurawa kawai ke amma gab yake da ya miƙe ya fizgo ta, idanunsa ya lumshe ya mai jan dogon a jiyan zuciya a daidai nan Allah ya yi suka iso sannan ta zauna gefansa, take ya ji wani iri dan tinda yake bai taɓa zama kujera ɗaya da wata ƴa ba, in ba Mama da Sarauniya Zaituna ba, da kewa ya kuma yi yana ƙara haɗa fuskan.



_________Ta ji ta zauna amma ji take kamar tana ƙaya, gashi jin idanun mutane na yawo akanta, gashi ta ƙi ɗagowa da ko hangen fuskar ta za ayi a cikin gyalan net ɗin. A lokacin aka fara abin da ya kawo kowa gurin, na ɗi ne na sarauta, irin wanda ya ji ace mai na sarautar larabawa masu isa da dukiya.


__________Komai na al'ada haka aka yi, an gayyato sarakuna daban-daban domin haka ake yi, masarautar ɗaya ce ba bu ko wakilinta, wato masarautar Shuraib. Dokoki aka miƙa ma Unais akan ya karanta tare da yin rantsuwa akan zai yi adalci. Ta ƙasan ido ta kalla irin zaman da ya yi da kuma miƙewan da ya yi cikin izza - ƙasaida mai cike da mulki, tafiya ya fara yi har in da aka tana da domin yin rantsuwa agaban uban mutanen da ke zaune, yana tsaya a gun ya kalla mutanen dake kowa ya yi ƙasa da kai, murmushi ya saki sannan wani ya iso gaba ya fara raɗin sarautar, a daidai in da aka umarci ya yi rantsu da karanta paper hannunsa sai ya ce.

"Ba buƙatar faɗi, ni na san menene a ciki kuma zanyi yadda ya dace da jahata." Take sauran sakaran gurin suka buɗe bakuna dan jin sabon doka, dama su Sarauniya Zaituna da mutanen garin sun san za'a rina.

"Akwai mai ja da wannan umarnin?." Ya faɗa cikin mic ɗin gurin, in da sautin haka ya karaɗe gurin, ba ma wanda ya yi alaman tari sai wannan mutumin ya kuma ce wa.

"Shike nan, sai wannan shine tsarin....." Sai Unais ya yi saurin katse shi da ce wa.

"Komai zan sani daga baya, tsallake wannan faɗa jadawalin ƙarshe." ba musu ya kuma ce wa.

"Na ƙarshe shine, Sarauniya za ta iso gaban wannan wajen sannan ta yi jawabi akan Sarkinta, daga nan sai a tashi." juyawa ya yi ya kalla in da take zaune kamar gunki dan ko motsin kirki ba ta yi.



__________A al'dan ce Sarki ke isa gabanta sannan ya riƙo hannuta sai su tako har gun, a lokacin ne zai buɗe mata fuska domin kowa ya ganta sai ta yi jawabin waye sabon Sarki, da abubuwan da ta sani akansa. Murmushi wanda ya kanyi wiya ya yi sai ya nufeta, kowa dai kallonsa ya ce dan ansan dole Sarki Unais ya yi ba daidai ba. Ta jiyo sautin tafiyarsa har ya tsaya a gabanta, sai ya kalla Sarauniya Zaituna, dan marairaice fuska ta yi alam roƙo kar ya ƙwafasa, sai ya ɗaga mata kai sannan ya ɗan tsugunno sai tin Sopiyya ya fara raɗa mata wani magana wanda a take abu biyu suka dinga shiga kunnint, daɗin muryarsa mai taushi da natsuwa - da kalaman mara sa daɗi.

"Ban ta ɓa riƙe Baiwa ba dan haka bazan fara akan ki ba, Ina son karda ki motsa a gun nan ko da na miƙo miki hannu, ki ta girgiza kai kawai." Murmushi ta yi sannan ta sanya hannunta ta share hawayen idanta, miƙewan ya yi sannan ya miƙa mata fararen hannusa da yatsunsa farare ƙal masu baƙin ganshi a muhallin su, sai ya yi mugun kyau.


_________Hatta Mama sunyi mamakin ganin abin da Unais ya yi dan sun san halinsa, haka mutanen gari kowa ganin yake kaman almara domin sun raya idan ta miƙo mai hannu dole ta fuskanci hukunci bayan walima....... second ɗaya - biyu - uku - huɗu, har zai janye hannu da niyyan kowa ma ya musu bayanin Sarauniya na ba da haƙurin ba za ta iya tashi ba, kuma hakan zai yi ne don ƙar sauran ƴan masarautu suga gaba ɗaya ya bi tsarin doka ba. Take ya ji lallausar hannuta cikin nasa tana mai miƙewa tsaye a hankali......  


__________Dam, daram zuciyarsa ya buga da mugun karfi, haɗe fuska ya kuma yi sai kawai ya dake yana kallon yadda shigan ya mata mugun kyau, sai da ya gama hasasi irin muguntar da zai ma hannu tukun ya fara tafiya a hankali riƙe da hannunta, jama'a kowa yasha kallon soyayya ya ke hannun da yasha lalle mai kyau, sannan hannun mai matukar haske wanda sam ba kalan nasa ba ne.


_________Ta ɗau ma kanta wani alkawarin sai ta fara ƙasƙantar da jin kansa, ta miƙa hannu sannan ta ji ya ɗau lokacin kafin ya rike cikin mugunta, tafiya suke amma kaman ta fasa ihu saboda irin matsa mata hannu da ya yi, a daidai waje suka tsaya sannan ya cire hannunsa yana mai jin yau ba zai iya sa komai a baki da wannan hannun ba, sun ɗau lokacin a haka sai wannan mai jawabin ya ce.

"Sarki Unais saura ɗaga mayafi da jawabi." Haɗe rai ya yi sai ya kalla gefansa in take tsaye har lokacin kanta na ƙasa.

"Ke Baiwa cire gyalan da kan ki." ya ɗan mata raɗa, sai tai banza da shi, yasan ta ji, sai ya juya ya fuskance ta sannan ya sanya hannu biyu ya fara tattaro gyalen tin daga ƙafafunta................✍️
END.



   (HMMMMM *Baiwa* ki bi a hankali dai......)
[8/12, 08:39] ᑭᖇᗴTTY ՏK Novelist
 ✍️✍️✍️: ***
****
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A) 
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

*Pray for me, I'm sick, I need prayers.....😓*

> Ciwo ba mutuwa ba amma ba daɗi gaskiya, Allah ya sa kaffara ne, ya yaye mana🙏.