Labari ne mai cike da...... *Tausayi* *Mugunta* *Zalinci* *Cin amana* *Yaudara

PAGE10

by @prettys01

E.P🔟.


> “Ke Baiwa, cire gyalan da kan ki.” ya ɗan mata raɗa, sai tai banza da shi, yasan ta ji, sai ya juya ya fuskance ta sannan ya sanya hannu biyu, ya fara tattaro gyalen tin daga ƙafafunta.........✍️

*Continuation*

___________Ji yake ya yi mugun ƙasƙanta, tattarowa yake cike da baƙin ciki sannan bala'i na cinsa, ba komai yasa ya daurewa ba sai dan ganin yadda mutane ke nuna farin cikinsu a fili, a dai-dai kafaɗarta ya tsaya sai kuma ya yaye gaba ɗaya.


____________Take fuskar ta bayyana mai sheƙi da annuri, a karo na farko suka kalla juna, kallo na daƙiƙu, take flawers masu ƙamshi suka fara zuɓo musu, a karo na farko ya ga halittar da ta fishi ne sa ba kusa, murmushi ta sakar mai sannan ta kalla tari al'ummar dake kallonta, taku biyu ta ƙara ta tsaya a gaban mic sannan ta buɗe baki dan kwararo magana, da sauri ya matsa kusa da ita sannan ya yi magana yadda ita kaɗai za ta ji.

"Karki furta komai." kulle idanunsa ya yi saboda yadda ƙamshin turaren ta daya cika mai hanci, Idan bango ya motsa to ta motsa.


________Muryarta mai daɗi da zaƙi gamida sanyi mai haɗe da natsuwa ne ya fara amsakuwwa a cikin mic ɗin.

"Alhamdulillah, ina matuƙar godiya ga Allah da ya nuna min wannan ranan, sannan wannan lokaci ya zama abu mai daraja a guna, domin a yau na mallaki muradin rai na wato......." sai ta tsaya dan ta manta sunan sa, satan kallonsa ta yi taga fuskarnan babu annuri, sai kuma ta da sa da ce wa "Wato mijina kuma Sarkin a yanzu, ina mai alfahari da hakan domin Sarki na mutum ne mai sanin ya kamata, ina godiya ga dukkan wa'in da suka halicci wannan wajen dan ta ya mu murna, Allah ya mai da kowa gida lafiya." Take gurin ya hautsine da surutu, wasu na hamdala wasu kuma ƴan masarautar na faɗin 'hmmmm da alama wannan baƙuwa ce.'


"Mama a gaskiya, yarinyar nan akwai iya fidda lafazi cikin hikima, kalla yadda Sarakai ke jinjina da kalmomin ta." Sarauniya Zaituna ta faɗa tana ƙare ma Sopiyya kallo.

"Hmmmm ai yanzu aka fara."

"Amma a haka dole ta fuskanci hukunci abin da ta min."

"Ki dinga tinani mana, ki kalla ɗan kin, ko ba'a faɗa ba, taf yake dan haka dole daga yau ta fara amsa huƙubar Unais." Murmushi suka yi sannan suka mai da hankali ga kan step in da Sopiyya ta fuskanci Unais.


_________karo na biyu suka kuma kallon juna, kowa yana saƙa abu a ransa. 'Zan yi maganin wannan Izzan naka, sannan na yi ma kaina alƙawari dole na sai ta maka tinani, yadda kake da izza - ƙasaita haka na ke da shi, kuma jini na ne.' ta raya tana mai sakar mai murmushi. Shi kuwa 'A karo na farko na aikata abin da ban taɓa ba, saboda ke *Baiwa* dole na hukunta ki akan abubuwa da kika min a yau, na lura ba kisan waye Unais ba.' sai ya kalla mai jawabin dan jin abin da yake faɗi.

"Sarki Unais za ka iya mai da ta domin an kammala."  bai kalleta ba ya mai da mayafin yadda yake sannan ya miƙa mata hannu, ba musu ta riƙe sannan suka taka har in da mazaunin su yake, zama suka yi yana mai ce mata.

"*Baiwa* , wai ni na riƙe wannan hannayen na ƙi hmmmm, ki gode ma Allah domin ke ce mace ta farko da hakan ta kasance, zan iya ce wa kina na da sa'a ko rashin sa."

"Hmmmm Sarki U...Unais koh!?." Girgiza kai ya yi yana mai da idanunsa ga ƴam matan da ke rawan Larabawa dan shaƙatawa akan wani babban stage.



________An jima an shagali daga bisani aka tashi, wa'inda suka kawo Sarauniya Sopiyya sune suka mai da ita wani ɗaki mai shegen kyau. Shuru ta yi bayan an batta ita kaɗai, babu abin da ke mata yawo illa abu biyu da yake cikin ranta, na farko tana son ta kwada shin za ta iya sauya tsarin mulkin zalunci da ake yi, sannan ta gyara alaƙar da ke tsanin jahohi biyu, Masarautar Qumaiz da Shuraib.

"Ta ya ya?." ta tambaya kanta sai kuma ta ce. "Ta yadda ya dace, a na yawan faɗa min ina da basira da wayau to da wannan damar zan yi amfani gurin mallakan kowa a cikin masarautar nan." Sai ta saki wani shu'umin murmushi. 


________Tinda aka watse ya koma wani ƙataccan muhallin wanda nan ne nasa, shuru ya yi yana mai kallon p.o.p dake sama wanda ya sha kwalli na alfarma, tinanin irin yadda a yau ajinsa ya zube yake, ya na tunanin akan irin horon da zai mata, sannan ya ji Mahaifiyarsa ta ce 'Ɗa na Sopiyya *Baiwar* ka ce, duk abin da ya da ce shi za ka yi, kardai ka manta kai Sarki ne a yanzu, komai idan za ka yi kayi shi cikin hikima da dubara.' - A lokacin ɗaga kai kawai ya yi, amma a yanzu sai ya yi murmushi nan mai tsada, knocking ya ji an yi, amma sai da ya ɗau fasali ya ce.

"Waye?." 

"Sarki Allah ya ja kwana, Uwar mai muƙami ce ke neman ka." ya ji murya wata Baiwa daga waje, yasan Mahaifiyarsa ce ɗan haka ya ce.

"Ok."

"Zan isar da saƙo cikin gaggawa Sarkina - shugaba mai daraja." Bayan ta tabbatar ta bar wajen ya miƙe sannan ya mai da babban rigarsa, ta ku ya fara cike Izzan nan dai, yana fita ƙofar parlour fadawa suka zube dan kwasar gaisuwa, sannan masu taka mai baya suka bisa..........✍️
END.


[8/13, 11:39] ᑭᖇᗴTTY ՏK Novelist ✍️✍️✍️: ***
****
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A) 
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.


        THE SLAVE
By

Sakeenat Abdullahi.
   _______________ Pretty Sk ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


 Labari ne mai cike da......
*Tausayi* 
*Mugunta*
*Zalinci*
*Cin amana*.
*Yaudara* da kuma......
* SOYAYYA 💘*
   
    ______ Labari ne na wasu ƙabilan Larabawa a zamin da. Ƙagaggen labari ne, ban yin dan cin zarafin kowa ba, idan kunga ya yi kama da rayuwarku, to ki yi haƙuri, sharrin alƙalamine.



Page1️⃣1️⃣.


_____________Cikin wannan tafiyar na sa mai cike da izza ya isa ɓangaren Uwar mai muƙami, yana shiga bayi suka hau durƙuwa da mai kirari, Uwar mai muƙami da take zaune ta musu alama da duk su fita, take duk suka fice, zama ya yi sai ya kalleta dan jin kiran na menene, a kwai lokuta da yawa da baya yawan magana sai dai ya yi alama ta yadda saƙo zai isa ga mai kallonsa, a yanzu ma ɗaga manyan idanunsa ya yi, sai ta saki murmushi sannan ta ce.

"Sarki. a yau dai burin ɗana ya cika, na zama Sarki mai muƙami akan karaga.” sai ya sakar mata murmushi mai sanyi sannan ta ci gaba da ce wa " Al'ada a wannan lokacin a ke kai Amarya ɓangaren Sarki, sai dai ba zai yiwu a kaita kana ciki ba, zuwa yanzu na tabbatar har an kaita.” take fuskansa ya haɗe sannan ya yi magana cikin haɗe giran sama da ƙasa.

“Wace ce yarinyar!? sannan waye ubata?.” shuru Uwar mai muƙami ta yi sai kuma can ta ce.

“*Baiwa* ce, Baiwa kamar sauran Bayi, ba wani ne ubanta ba illa Bawa, dan haka karka mata kallon komai sai Baiwa." Jinjina kai kawai ya yi sannan ya miƙa dan barin ɗakin, da ido ta bisa har ya kai ƙofar fita sannan ya ta ji ya ce.

“Mu kwana lafiya.” bai jira ta ce komai ba ya ida fita, sannan masu taka mai suka bi bayan sa. 


__________Yana isa babban ɓangaren sa suka tsaya shi kuma ya shiga, parlour babu kowa sai faman ƙamshi na alfarma ya ke, a kallo ɗaya ya fahimci ɗakin da aka kaita, dan ƙofofi na bedrooms masu shegen ƙyau ne a jere, zama ya yi kawai a kan sofa dan bai ma san ta ina zai fara hukunta ta ba. Miƙa wa ya yi sannan ya shiga in da aka kaita, hannu ya sa ya tura ƙafan sannan ya shiga, a tsakiyar wannan round bed ɗin take, wanda ya ci uban ado sannan an zagayeta da flawers, ɗaga fararen idanunsa ya yi ya kalla shigan dake jikinta. Sanye ta ke cikin wanin kayan sarauta harda alkebba na larabawa, sannan an kuma yafa mata abu mai daraja na Sarakai, bai ga fuskar ta ba amma a shigarta yasan ta yi ƙyau.


____________Zama ya yi daga gefan gadon sannan ya buɗe baki kaman wanda aka ma dole ya ce

“Ke, cire wannan mayafin.” shuru ba ta motsa ba, sannan ya kuma maimaita wa, still ko motsi ba ta yi ba, har zai kuma wani maganar sai ya ji saukan muryar ta mai sanyin daɗi.

“Sunana Sopiyya ba Ke ba.” ta faɗa da iya muryan da zai ji. A gajiye yake amma dole zai aje a gefe sannan ya hukunta ta. Hannu ya sa ya yaye gaba ɗaya mayafin sannan ya ce.

“Da ko wani suna na gadama da shi zan kira ki, sannan ke Baiwa ce ba Mata ba, a idon duniya kike amsa wannan suna amma a guna sam baida wani tasiri.” ya kai maganar yana mai zuba mata ido duk da tana kallon ƙasa ne, a hankali ta ɗago da fuskar ta, ta sanya a cikin nasa, take ya kauda kai dan wannan masifar ƙyau na ta ji yake kaman na tsari.

“Ango so ake ya fara umartar matarsa da su gaida Ubangiji, na ji ni Baiwa ce amma ka sani kowa ma Baiwa Allah.........” bai jira ta ƙara sa ba ya toshe mata baki da hannunta sannan ya ce.

“Sauka a Parlour za ki dinga kwana, sannan zuwa gobe zan fara baki horo na musamman domin kin aikata min abubuwa a yau ɗin nan.” daga haka ya ja hannunta zuwa parlour.

“A nan za ki kwana.” sai ya koma room ɗin sannan ya koma ciki ya kulle, tsayawa ta yi a in da ya barta har na zafa minti uku sai kuma ta yi ƙwafa sannan ta nufi bedroom ɗaya daga cikin, bedroom wanda ya kasance komai na Unais ya na ciki, baya yadda kowa ya shiga ciki, domin abubuwan da ciki ya ƙunsa, ko mai gyara za ta shiga sai an haɗata da fadawa, ya na ji da wannan ɗauki fiye da misali dan kusan rayuwarsa ce a ciki, komai da ya shafi abin da yake so yan ci.


________Tana shiga ta ja wani dogon nunfashi domin ƙamshin da ke tashi a cikin ɗakin, kallon cike take yi cike da ƙaruwar ɗakin domin ya burger geta. Wani katifa ce mai hawa uku a tsakiyan ɗakin, in da aka kewayeshi da abubuwan kwalliya, sannan ga net mai ƙwalliya, gefe guda takaddune kaman tashin hankali, hatta kan mirrow papers ne, ba wani tinani ta haye kan katimar mai matuƙar taushi, dan har wani lotsawa take, murmushi ta sakar ma kanta sannan ta miƙe, ina da take zatan toilet ne ta shiga, nan ya haɗu, a gurguje ta watsa ruwa sannan ta fito ɗaure da towel, dama babban rigar ta ishe ta, kwanciya ta yi da bismillahil sannan ta karanto addu'oi barci, tana ƙara jan duvet, ji take kaman ta dauwama a cikin ɗakin sannan akan wannan katifar tsabar laushinsa........✍️
END. 

> Sopiyya in banda ja wakai masifaaa, na lura yarinyar nan ba ta da tsoro 🙄 hmmmmm mu dai je zuwa followers.